Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 22

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 22*

 

 

 

“Bini-bini yana juyawa ya kalleta sai sannu yake mata har suka hau titi, lumshe ido tayi kaman ta suma bai kula ba yaci gaba da driving, daidai checking point ya tsaya ya rufe fuskanta da wani kyalle dake gefe suka leka ganin shine suka sara mishi, jan motan yayi ya kama hanyan gida ganin tayi shiru bata numfashi yaji gabanshi ya faɗi a hankali yace “Amrish?”

 

bata motsa ba, bai tsaya da tuƙi ba saida ya isa gida, horn ya yiwa megadi da sauri ya leƙa ganin motan gidanne ya buɗe mishi, shiga ciki yayi bai tsaya wani gaya parking ba ya buɗe motan ya fito, gidan baya inda take kwance yaje ya ɗagata sama ya sata a kafaɗarshi sannan ya nufi hanyan cikin gida, idonta biyu amma gajiya da yunwa ba zai bari tayi magana ko kwakkwaran motsi ba.

 

Tura kofan falo yayi da kafarshi nan take ya buɗe, shiga ciki yayi da ita a kafaɗarshi yana so yaga ya kwantar da ita ya bata ruwa da abinci, Ammi da take zaune tana shan oats taga mutum ya shigo hannunshi rikeda yarinya kamar ba rai, da sauri ta mike tana kallonshi, ganin yana shirin shiga da ita ciki tace “wacece wannan?”

 

“Amrish ce”

ya faɗa yana shirin zuwa ɗakinshi, time  ɗin umar ya fito hannunshi rike da maganin Ammi ganin faruk da yarinya a bayanshi ya tsaya turus yana kallon ikon Allah, ya ɗaga kafa zai taka stair Ammi tace “idan ka haura da ita sama bazan yafe maka ba”

cak ya tsaya ya juyo yana kallon Ammi, ranshi a ɓace yaji zafin rashin tausayin data nunawa Amrish, a hankali ya sauke ƙafan ya juya ya kwantar da ita a kasa, da sauri yaje gaban frij ya ciro goran ruwa da fresh milk yazo, buɗewa yayi ya ɗago kanta sai lumshe ido take tana buɗewa, sa mata bakin goran yayi a bakinta, a hankali ta fara kurɓa saida ta shanye duka sannan ya ɗau fresh milk ɗin ya bata, sha tayi, ta koma kasa ta kwanta tana rike ciki, ta jima bataci abinci ba shiyasa datasha abu me sanyi ya fara murɗa mata ciki.

 

hannu yasa akan nata hannun dake kan cikinta cikin tausayi yace “meya faru kuma?”

 

“cikina”

 

ruɗewa yayi ya tashi da gudu ya haura sama, ɗakinshi yaje ya buɗe drower ya duba magani, ganin maganin ciwon ciki ya ɗauka ya fito, saida ya karo goran ruwa sannan ya ɗago kanta ya bata maganin, haɗiyewa tayi tana runtse ido.

 

a hankali ta fara lumshe ido daga kwance, kallon kafanta yayi yaga yana jini, da sauri ya ɗaga yaga kwalba ne ta taka, cire kwalban yayi saida tayi ƴar kara dan taji zafi sosai.

 

“Sannu”

ya faɗa mata, Ammi ta harɗe hannu a kirji tana kallon yadda ɗantan ya susuce akan soyayya, wannan saide soyayya ya wuce tausayi.

 

Bacci ta fara bayan ta naɗe hannunta ta taƙure wuri ɗaya, ido ya zuba mata yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali, umar da yaga haka ya ciro waya yace “ko ka fita da ita ko na sanarwa ƴan sanda tana nan gidan”

 

murmushi faruk yayi sannan yace “da gaske? to kirasu mana, idan sunzo nasan abinda zan faɗa kaima ba barinka zasuyi ba, idan ka manta ne bari na tuna maka kaima babban me laifi ne rufewa kawai mukayi kafi kowa sanin kaine ka yiwa Alhaji Idris illa kodai ka manta ne? ko taɓun hankalin naka har yanzu yana nan? ka manta time ɗin da kayiwa ƴarshi ɗaya tilo fyaɗe har ya kamu da ciwon zuciya da hawan jini har ya faɗi ya samu ciwon ɓarin jiki?

ka manta cewar da hannuna naje na yanka maka katin shaidan karamin hauka da haka aka kashe case ɗin? to kirasu ka tona nima nasan abinda zan faɗa saide a fita da masu laifi biyu a gidan nan”.

 

Ammi data waro ido tana kallon Faruk cikin kiɗima tace “faruk yau kaine kake yiwa umar gori akan abinda ya aikata a baya?”

 

murmushi faruk yayi, Ammi tace “to ka ɗauke yarinyar nan ka fita da ita banson ganinta koda na minti ɗaya ne tunda a kanta kuke neman ɓatawa da juna”

 

“Ammi saide mu fita tare da ita, dan umar babban me laifi ne, yana zuwa har gidan marayu ya ɗauki kawarta ya fita da ita, basa dawowa sai tsakiyan dare da haka har yarinyar ta lalace daga baya yace ba zai iya aurenta ba iyayenahi sun hanashi, wannan bakin cikin yasa ta rataye kanta ta mutu, akwai me laifin daya wuce umar ne?”

 

kallon umar yayi wanda ya dunƙule hannu yana huci, a fili yace “mazinaci me lalata yaran mutane”

cikin zafin nama ya sauko daga stair ya shaƙo faruk, nan suka fara kokawa suna kaiwa juna duka.

 

hannu Ammi ta ɗaura aka tana tsala ihu, ihunta ya tashi amrish daga baccin wahalan da take yi, a hankali ta fara buɗe ido, ganin suna dambe ta mike tana jan kafarta, da ɗan gudu taje tana janye ɗaya daga cikinsu wanda batasan ko waye bane.

 

saida tayi nasan janshi sannan ta kalli rigan jikinshi wannan ba faruk bane, da karfi umar ya jata ya haɗa kanta da bango ya zaro belt zai fara dukanta, faruk ganin haka ya ɗau sandan dake gefe wanda aka tanada domin kashe tsaka ko kenkyaso, akanshi ya kwala mishi nan take ya faɗi kasa bai kara motsi ba.

 

ihu Ammi tayi taje wurin da gudu tana cewa “ya kashe ɗan uwanshi ya kashe shi”

 

Amrish da take jin ciwo ta ko ina a jikinta taje wurin tana shirin ɗaga umar, da karfi Ammi ta tureta, saida ta faɗi gaban faruk tana cije leɓe, dan ba karamin azaba taji ba.

 

cikin kuka Ammi tace “tunda kika shigo rayuwarshi abubuwa marasa daɗi suketa faruwa, bakida albarka, ki rabu da ƴaƴana ki fitamin daga gida, duk ba kece sanadin hakan ba?”

 

hannunta faruk ya rike ya jata tana ɗingisa kafa tana cewa “kaje ka dubashi kar dai yaji ciwo kaje ka duba ɗan uwanka zan lallaɓa na koma gidan marayu ba matsala acan”

 

bai tsaya ba yaci gaba da jan hannunta, ɗakin baki ya zaunar da ita ya bata snacks yace “kici”

a hankali ta fara kuka tace “kaje ka duba ɗan uwanka kada wani abin ya sameshi ni nasan yadda zanyi da kaina, na saba da wahala ba wata damuwa idan ka barni na tafi, banso na shiga tsakaninka da familynka”

 

murtuƙe fuska yayi yace “kici”

karɓa tayi ta fara ci tana hawaye, ido ya zuba mata, tausayi take bashi, yasan batada kowa idan an barta ita kaɗai zata iya zama muguwa wacce batada imani, barin mutum shi kaɗai a halin damuwa yana iya sawa yayi tunanin da ba kyau, wani ma har ya fara shirin kashe kanshi.

 

hakan yasa yake kasancewa da ita a duk lokacin da take cikin damuwa, saida yaga taci sosai sannan yace “kwanta” tareda nuna mata inda zata kwanta, three seater ne me faɗi kaman gado, kwanciya tayi yace “ki huta sai ki shiga can kiyi wanka”

 

giɗa mishi kai tayi yace “kada kiyi kuskuren fita daga gidannan idan kikayi haka ranki zai ɓaci”

 

“tom”

 

fita yayi daga ɗakin ya dawo da kaya a hannunshi, mika mata yayi riganshi ne jallabiya wanda mata zasu iya sawa,  fita yayi daga ɗakin yace taje tayi wanka, tana cije baki ta mike taje toilet ɗin haɗa ruwan zafi sosai tayi sannan ta kwaɓe kayan ta shiga bathtub ta zauna a cikin ruwan, kwantar da kanta tayi ajikin bathtub ɗin hawaye yana gangara daga idonta yana sauka har cikin ruwan da take zaune a ciki, tunanin rayuwarta takeyi Allah ya yita da kyau sai bakin jini, gashi Ammi da umar sun tsaneta hakan yanaso ya haifar da rashin fahimta tsakanin faruk da umar.

 

saida tayi kuka me isanta ta rasa me lallashi sannan tayi wanka da sabulai masu kamshi, wanke gashin kanta tayi wanda ta kwance kitson da faruk ɗin yayi mata lokacin da taje cell, wankewa tayi me kyau da shampoo sannan ta fito daga cikin bathtub ɗin, ɗaura karamin towel tayi a kanta sannan ta ɗaura babba a kirji ta fito fuskarta fayau, ido huɗu sukayi ya kawo mata man shafawa ne dan yasan babu anan, da sauri ta durkusa kasa tana gyara ɗaurin towel ɗin daya kusan sauka, juya baya yayi yace “ga mai”

ajiyewa yayi bai kara juyowa ba ya fita daga ɗakin, saida taga ya fita sannan ta mike taje ta busar da kanta, man yana ƙamshin kwakwa ta ɗaga ta shafa, kallon jikinta tayi ta cikin mirror, duk yayi tabo da shatin cizon sauro ga kuma ciwukan da tayi taji, lumshe ido tayi sannan ta ɗau jallabiyan daya ajiye mata tasa, kallo tayi yayi mata yawa dan ya fita tsayi, hannun ma yayi mata yawa saida ta nannade sannan taga yayi mata daidai.

 

jin kanta tayi kamar har yanzu bai bushe da kyau ba, sakin gashin tayi a bayanta ya sauko har yana taɓo ɗuwawunta, kwanciya tayi akan sofan ta janyo bargo me laushi daya ajiye mata ta rufa jikinta dashi, lumshe ido tayi tanaso tayi bacci tunanin duniya ya hanata, abinda ya faru tsakanin umar da faruk shi yafi komai ɗaga mata hankali, gefe guda ga mahaifiyarsu tana ganin itace ta haɗasu faɗa, gaba ɗaya tana cikin damuwa ta rasa inda zatasa kanta.

 

ganin tunani ba zaiyi mata komai ba ta fara kuka tana rufe bakinta da blanket ɗin, ko wani irin rayuwa takeyi? Allah kaɗai yasan halinda zata tsinci kanta a gaba, meyasa iyayenta suka sallamata wa duniya? suna raye? ko sun mutu? Allah ne kaɗai ya sani, taso ace suna raye ta gansu tayi musu tambaya meyasa suka yar da ita, meyasa basu riketa komin wuya komin rintsi su zauna tare ba? Yau gashi sanadin maraici ta zama me kisa, ta zama ɓarauniya ta zama me aikata babban laifi a kasa, sanadin haka har an yanke mata hukuncin kisa, ba dan faruk ba da yanzu kanta baya tare da gangan jikinta, hukuncin rataya ba karamin hukunci bane.

 

 

 

 

_Jiddah Shu’aibu✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button