Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 4

Sponsored Links

 

🌸 *HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

Jiddah S Mapi

 

 

*Chapter 4*

 

 

 

~Da dare tana zaune a gefe tana kallon shige da ficen mutanen gidan, can ta hango wata budurwa anzo da babban mota an ɗauke ta, kin komawa ciki tayi domin tana so taga yaushe zata dawo, abin mamaki har kusan karfe goma bata shigo ba, sai kusan sha biyu kafin taga motan ya dawo yarinyar ta sauka, ganin ya juya ya tafi taje tana haska toci tace “daga ina Fatima?”

dabarcewa tayi “naje siyan abu ne wallahi ya kike?”

“siyan abu shine a wancan tsadadden motan?”

shiru Fatiman tayi domin bata fiye magana ba shiru-shiru da ita, haskata tayi taga hawaye take, riko hannunta tayi suka zauna daga gefe tace “ki gayamin gaskiya meke faruwa?”

kuka ta fara tace “ɗan masu kuɗi ne shine yake taimakamin ina samun abinda zanci mai kyau, wannan gidan baya cike da komai sai yunwa, bazan iya jura ba hakan yasa nake binshi yana amfani dani yana bani manyan kuɗaɗe”

 

shiru Amrish tayi kanta ya ɗaure Fatima ba zata wuce shekara 16 ba amma ta faɗa wannan halin?

tashi tayi ba tareda tace mata komai ba, saida tayi nisa tace “kiyi hakuri ki rungumi ƙaddara”

komawa ɗaki tayi, saida ta gyarawa yaran kwanciya kafin itama ta kwanta a gefe tana tunani, meyasa masu kuɗi basa taimako sai idan zasu samu biyan bukata?

tunawa da abinda aya faru dasu Na’eem shi yafi komai ɗaga mata hankali, itama zainab batayi bacci ba, idonta biyu har gari ya waye.

 

 

 

tun daga wannan ranan kullum sai sunzo sun kwashi yara maza a cikin gidan sun biya bukatansu, Amrish tana gani ba zata iya komai ba.

 

 

gashi kuma yara sai yawa suke karayi a gidan a kullum sai an kawo yara sun kai ishirin ko fiye da haka, cikin gidan kowa ta kanshi yake.

 

girki take domin yau yara zasuje school Hafiz ne yazo ta bayanta ya faɗa kanta yace “Unty ga can Feena a ɗaki tana ta kuka”

 

tashi tayi ta shiga ɗakin taje wurin feena, yarinya ce ƴar shekara goma tana zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka, da mamaki tace “Feena kukan me kike?”

share hawaye tayi tace “babu”

ta kalleta sosai akwai alaman tsoro a tare da ita, zama tayi tace “ki faɗamin gaskiya zan taimaka miki kinji feenah ta?”

 

“wallahi ba komai Unty Amrish kaina ke ciwo”

ɓallo paracetamol tayi ta bata, karɓa tayi ta haɗiye kafin tace ta kwanta, kwanciya yarinyar tayi har tayi bacci, zuwa tayi ta bawa kowa abinci ta shiryasu ta kaisu school, dawowa tayi taga Feena bata nan, bata damu ba dan dama ba wani zama suke waje ɗaya ba.

 

 

Bayan yara sun dawo daga school feenah ta dawo da hannunta a cikin hijabi idanunta a kumbure, kallonta Amrish tayi “daga ina?”

 

kuka ta fashe dashi kafin ta faɗa jikin Amrish “ke meya faru?” ta faɗa cikin tashin hankali.

 

Sakinta Feenah tayi kafin ta cire hijabin jikinta ta nuna mata hannunta da yake a yanke, wani irin ihu Amrish tayi ganin hannun feenah ɗaya babu, a tsorace tace “ina ɗayan hannunki?”

 

cikin kuka tace “sun yanke”

“su waye?”

a tsorace take mata tambaya, cikin kuka tace “ke ɗaya zan gayawa wannan maganan kimin alkawarin ba zaki gayawa kowa ba”

 

jijjiga kai tayi “nayi miki alkawi feenah”

 

“dama wasu mutane ne sukace zasu tafi saudiyya dani shine suka yankemin hannu ɗaya domin su rinƙa samun sadaka a wajen larabawa”

 

Zama Amrish tayi domin jiri takeji “shugaba taji?”

 

“itace ma ta kirasu dama sunyi mata magana tunda jimawa”

kanta ta rike jin yana sara mata, zainab dake tsaye a gefe tana jinsu itama ta jingina kanta da bango tana hawaye, wani irin masifa suke ciki?

 

Feenah tafiya tayi ta barta a wurin dan sunyi mata barazana ba kaɗan ba shiyasa take mugun tsoronsu.

 

 

 

“bincike yake sosai a cikin Laptop nashi, anyi kisa a kasar waje tsabar kwarewanshi a aiki aka turo mishi hoton gawan domin yayi bincike, yana kwance akan maƙeƙen bed nashi jikinshi sanye da wando gajere blue, sai vest fari, gefenshi juice ne a cikin glass cup yana sipping kaɗan kaɗan, hankalinshi gaba ɗaya akan Laptop so yake ya gano shaida guda ɗaya ya tura musu, sanyin Ac yan ratsa shi, Umar ne ya fito daga toilet waist nashi ɗaure da babban towel fari, kallon Faruk yayi ya wuce gaban babban mirror ya fara shafa oil, saida ya gama ya taje kanshi ya buɗe sif ya ciro kayan likitoci yasa, yayi kyau sosai kamanninsu ya kara fitowa, ko Ammi bata iya bambance su, saida ya gama kafin ya fesa turare ya ɗaura tsadadden agogo a hannunshi, faɗawa yayi kan Faruk “auuchh”

shine abinda ya faɗa domin har ya ɗanji ciwo, dariya kawai Umar yayi kafin yace “agogo sarkin aiki yau kuma me kake bincikawa?”

 

“dan Allah ka tashi kayi nauyi dayawa kuma aiki nake”

tashi yayi ya zauna yana kallonshi a hankali yace “gaskiya kana kokari a kasar nan, duk wani kisa kaine kake bincike akai kuma kana gano mai laifin, Allah yayi maka basira, da Abba yana raye nasan zaiyi alfahari da kai”

 

rufe Laptop ɗin yayi ya mike ya zauna, kallon Umar yayi cikin sanyin murya yace “kaima Abba zaiyi alfahari da kai saboda kana taimako kaima likita ne kana bawa mutane gudunmawa”

 

rungumeshi Umar yayi yace “na gode da yabona da kayi kayi hakuri da munanan halayena zan daina wata rana”

lumshe ido yayi yana jin soyayyan ɗan uwanshi a ranshi, yace “ba komai ka tafi aiki nima yanzu zan fita”

 

Sakinshi yayi kafin ya tashi yace “Bye”

fita yayi daga ɗakin, yaje ɗakin Ammi tana zaune Elham tana gefe tana kwance kitsonta, “Ammi na tafi hospital”

 

“tom saika dawo ka kula da kanka”

fita yayi yaje Parking space nan ya zaɓo wani galleliyar mota ya shiga ciki, waka ya kunna na english yana bin bakin wakan yana kaɗa kai alaman wakan yana mishi daɗi, bai tsaya ko ina ba sai kofan hospital, shiga yayi yana amsa gaisuwan mutanen wajen, Hassan and Hussaini hospital shine sunan asibitin, duba marasa lafiya yayi kafin ya shiga mota yabar hospital ɗin bai tsaya ko ina ba sai babban hotel, kofan hotel ɗin ma kaɗai abin kallo ne, Parking yayi ya fito yana takawa, bai tsaya ko ina ba sai cikin ɗaki yayi knocking wata kyakkyawan budurwa tazo ta buɗe, jikinta sanye da gajeren wando irin na mata, da rigan vest, farace sol sai murmushi take, janyota yayi jikinshi suka shiga ciki, rufe kofan yayi ya jata zuwa kan gadon wanda yake shimfiɗe da farin bedsheet, kissing ɗin ta ya fara yana cewa “i miss you my teema”

dariya tayi “jiya da muka rabu da kai shine har kayi missing nawa?”

 

lumshe ido yayi yana shafa kirjinta yace “nace miki kibar gidan marayun nan naku ki dawo wajena zan kama miki gida, banson shiga gidan marayun nan wallahi”

shafa kanshi tayi kafin tayi kissing nashi a goshi tace “kada ka damu watarana zan bari, ai kasan acan na tashi iyayena tun ina yarinya suka jefar dani, a gidan marayu na tashi hakan yasa bazan iya rabuwa da mutanen ciki lokaci ɗaya ba”

 

rigan jikinta ya cire a hankali ya kai bakinshi kan nipples nata ya fara sucking, hannunta ta cusa a gashin kanshi tana jin yadda yake yi da ita, hakika tana son Umar saide ba zata iya barin gidan marayu ba, acan ta girma, kashe wutan ɗakin yayi ya fara aikata masha’a da ita.

 

 

 

Faruk saida yayi wanka ya fito ya shirya cikin rigan soja da bakin wando, taje tulin gashin kanshi yayi kafin ya taje kwatancen sajen dake kewaye da fuskarshi, kallon eyelashes nashi yayi wanda yake a kwance sosai, turare ya fesa, yasa agogo kafin ya buɗe drower ya ciro bindiga piston yasa a aljihun wandonshi ya fito yana latsa wayarshi kiran Iphone 14, fuskar nan a murtuƙe ba fara’a sam, kwarjini da kyau ne kawai yake bayyana a tare dashi.

 

ga wani irin haske da murjewa da hutu wanda ya bayyana akan fatarshi, bai yiwa Ammi sallama ba ya shiga mota, driver yazo suka fita, hanyan barack suka nufa, ajiye wayan yayi ya ɗau jarida yana karantawa, ganin labarin an kama wanda yayi kisan Alhaji Hamza da taimakon Captain Faruk hakan yayi mishi daɗi, ajiyewa yayi ya ciro waya ya tura sako a watsapp, sunyi tafiya me nisa kafin suka iso barack, shiga sukayi ciki, bai tsaya ko ina ba sai office nashi, yana ɗagawa duk wanda ya gaisheshi hannu ba tareda ya amsa ba, bai daɗe da zama ba aka turo kofan, mary ce wata soja da take nanike mishi, jikinta sanye da wando wanda ya kamata sosai, sai rigan soja, tsayawa tayi ta zuba mishi ido kafin tace “sir kana bukatan shayi?” cikin muryan yanga tayi magana, bai ko ɗago ya kalleta ba yace “no get out”

fita tayi jiki a sanyaye, haka yake baya kula mata, aikinshi ne kawai a gabanshi.

 

Bayan ta fita yayi tsaki, ita batasan ma kyama take bashi ba, shifa baison harka ma da mata, bai fiye yadda dasu ba, cigaba yayi da aikinshi saida ya gama ya mike ya fita, bai tsaya ko ina ba sai wajen motarshi, driver ne yazo suka tafi.

 

 

 

*_Littafin Hamshakiya na kuɗi ne ki biyani hakkina kafin ki karanta akan ₦400 ne, 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo evidence of payment ta nan 08144818849, masu kati zaki turo mtn ta wannan numbern 08144818849*_

 

 

*Na sadaukar da wannan littafin wa ORPHANS AND NEEDIE CHARITY FOUNDATION wato gidauniyar taimakon marayu da mabuƙata, ga duk wanda yake da niyyan taimakon marayu ya tuntuɓi wannan number 09031299157, zata tura muku account number, Allah ya taimaki duk wanda ya taimaka Ameen*

Leave a Reply

Back to top button