Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 23

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah Shu’aibu_

 

 

*Chapter 23*

 

 

 

“Tana kuka har jikinta yana ɓari sannan ta ɗan dakata jin numfashinta yana shirin ɗaukewa, iyayenta ta ɗaurawa duk wani laifi data aikata, tasan da tana hannunsu ba zatayi hakan ba, abu ɗaya take tunawa tayi farin ciki shine yadda ta gyara gidan marayun ta basu ingantaccen rayuwa, runtse ido tayi tana tuno unty sadiya wacce ta zame mata kamar sun fito ciki ɗaya wani lokacin ganin uwa take mata, ta tuna lokacin da take prison ta rinka kuka idan ta haɗa ido da ita.

 

da haka har bacci ya ɗauketa baccin da babu daɗi sam saima ciwon jiki da ta rinƙa ji a duk juyin da tayi.

 

 

Faruk yana fita yaje ya ɗaga umar ya kaishi ɗakinshi kwantar dashi yayi akan bed sannan ya ɗibo ruwa ya bawa Ammi yace “ki watsa mishi zai farfaɗo”

ganin ya juya zai fita Ammi tace “kana nufin tafiya zakayi ka barshi a cikin wannan halin? macece zata shiga tsakaninka da ɗan uwanka wanda kafi sonshi fiye da kowa a duniya? ka bani kunya ban taɓa zaton zakayi haka ba, hasalima umar nake yiwa ganin mara hankali ashe ga babban mara hankali nan tsaye a gabana, to idan dai har nice na haifeka kazo da kanka ka kula da ɗan uwanka, kuma kafin zuwa safiya inason ganin wannan yarinyar ta fita daga gidannan”

 

“zata fita amma tare zamu fita, bazan bari ta kara shiga kuncin rayuwa ba”

yayi magana yana zuwa inda umar yake, ruwa ya shafa mishi a fuska a hankali ya motsa ido alaman zai farka, da sauri ya matsa a wurin ya tsaya a jikin bango yana kallonshi, buɗe ido yayi ganin Ammi tsaye a wurin ya mika mata hannu, ɗagashi tayi ta jinginashi da jikin gadon.

 

kanshi yana sarawa dan yaji ciwo sosai, “sannu”

ta faɗa tana mika mishi cup na ruwa, a hankali ya ɗago kai ya kalli faruk dake tsaye a gefe, baiyi magana ba ya karɓi cup na ruwan yasha tareda mika mata, karɓa tayi ta ajiye a gefe, tana kallonshi tace “akwai abinda kake so?”

 

 

da hannu ya nuna mata drower “akwai magunguna acan ki miko min”

 

buɗe drower tayi ta ɗauko magunguna sannan tazo ta ajiye a gabanshi, saida ya duba sannan ya ɓare biyu ya shanye, maidawa tayi, faruk ya buɗe kofan ya fita, bin bayanshi tayi da kallo, shi kuma Umar ko kallonshi baiyi ba.

 

Ammi ta zauna tayi tagumi tana kallon umar hannu yasa ya cire tagumin da tayi yana girgiza mata kai alaman ta daina, hawaye suka cika mata ido tace “ta yaya zan daina umar? kaida ɗan uwanka kun zama abokan gaba a lokaci ɗaya, meyasa ba zakaci girma ka daina kulashi ba? idan kuka cigaba da haka zan iya rasa rayuwata”

 

hannu yasa ya rufe bakinta cikin sanyin murya yace “ki daina faɗan haka, hakan ba zata sake faruwa ba”

 

“kayimin alkawari?”

giɗa kai kawai yayi.

 

murmushi tayi ta riko hannunshi tana murzawa, lumshe ido kawai yakeyi yana jin son Amminshi har cikin ranshi,baison abinda zai taɓa ta, faɗanshi da faruk yasan yana taɓa mata zuciya amma duk shida Faruk ɗin babu me iya control ɗin fushin shi.

 

Faruk yana fita ya ɗaura kanshi a jikin kofan yana jin zafi a ranshi, baison yana faɗa da ɗan uwanshi gashi kuma baya iya control na kanshi, dolene ya ɗauke Amrish a gidannan idan yaso sai ya rinƙa zuwa yana dubata, dama tanada gida wanda Allah yasa ta gina da kanta acan zai kaita ya rinƙa kula da ita, yana tausayin maraya ba zai iya ganinta a wannan halin ya kyaleta ba.

 

 

*Washe gari*

 

Bayan ya idar da sallan asuba yayi addu’a ya mike yaje ɗakin da take, knocking yayi itama tana kan sallaya tana lazimi, abin duniya ya taru ya mata yawa, shigowa yayi ya zauna a bakin gado yana kallonta, a hankali ta ɗago tana lumshe ido tace “ina kwana”

 

“lafiya kalau ya jiki?”

 

ɓaki ta ɗan turo batace komai ba, tashi tayi ta cire hijabin jikinta, kallon yadda kayan ya mata yawa yayi, kayan ya matukar karɓeta ya mata kyau, murmushi yayi yace “ki shirya zan kaiki gidanki”

 

bata juyo ba ta nufi inda man shafawa yake ta shafa sannan ta dawo tasa hijabin akan jallabiyan dake jikinta tace “na shirya”

dama kanshi a kasa yana kallon darduman dake shimfiɗe akasa, ɗago kai yayi ya kalleta, tashi yayi yace “muje”

 

yana gaba tana biye dashi har suka sauka kasa, Ammi tana shiryawa elham abincin break nata ta gansu sun sauko, ɗauke kai tayi Amrish tayi murmushi taje gabanta ta durkusa tace “ina kwana Ammi?”

 

bata juyo ba balle ta amsa, tashi tayi tace “na tafi”

 

Elham da ta ke gefe ta kalleta ta taɓe baki, ƙarasawa wurin Elham ɗin tayi ta lakaci kumatunta tace “elham kin tashi lafiya?”

ɗauke kai elham tayi, a hankali ta mike tace “na tafi”

 

yana bakin kofa yana kallonta har ta gama tazo, tsayawa tayi ya nuna mata hannu “muje ko?”

fita sukayi a tare har wurin compound, motarshi ya buɗe mata ta shiga ta zauna, shima shiga yayi yana kallon yanayin fuskarta bata cikin yanayi me daɗi.

 

buɗe mishi get akayi yaja motan suka fita, yana driving yana kallonta tana ɓoye fuska tana kuka bataso ya gane.

 

hannunshi ya ɗaura akan nata ya rike, cikin sanyin murya da lallashi yace “Amrish dana sani bata kuka akan abu ɗan ƙalilan, zama kaɗan da nayi da ita na gano batada saurin giveup, to wannan Amrish ɗin kuma naga tanada son kuka da raunin zuciya, ke marainiya ce kuma an zalunceku ɗaukan fansa yana da daɗi koba komai zakiji sauki a ranki, to amma yawan kuka yana raunata zuciya ya zamana bakya iya taɓuka komai a rayuwarki”

 

shiru tayi tana jinshi, juyowa yayi kaɗan yana kallonta sannan yace “zan baki wani shawara wanda idan kinyi aiki dashi zakiji daɗi, ki canja suna daga Amrish ki koma Ameera duk rintsi duk wuya kada ki yadda ace ke Amrish ce, kisa duniya su yadda cewar Amrish ta mutu wannan Ameera ce, idan bakiyi haka ba mutane zasu sa miki ido a kara kamaki kiyi rayuwa a gidan yari”

 

“ta yaya kake ganin zan iya yin hakan? kasan Amrish bata iya fita da kayan banza wanda suke kama mata jiki, saɓanin Ameera wacce take fita da kaya masu kama jiki da fitar da sura, da kyar nake iya tafiya idan nayi dressing na Ameera, kana ganin zan iya cigaba da rayuwa a haka? ya zanyi da ƴan uwana na gidan marayu?”

 

“hakan da zakiyi shine zai baki daman taimakon ƴan uwanki marayu, amma idan kika nuna ke Amrish ce aka kamaki kika koma gidan yari ta yaya zaki taimaka musu?”

 

shiru tayi tana nazarin magananshi, sai daga bisani tace “na gode faruk zan gwada hakan, Allah ya baka ladan taimakon marayu da kayi na gode”

 

“Ki daina godiya yiwa kaine nima nasan zafin zaman kaɗaici amma kiyi kokari ki koya sannan ki zauna kiyi nazari sosai insha Allahu komai zai zo da sauki”

 

yana bata shawara har suka isa gidan data ajiyeshi a wancan karon, me gadi saida ya duba yaga itace sannan yace “hajiya yaushe a gari?”

 

“jiya ne Baba”

“sannu da zuwa hajiya ai nace kin ɓata ɓata shi kuma wannan bawan Allah kullum sai yazo ya duba gidan, shine ma yake biyanmu kuɗin aiki”

 

yayi magana yana nuna faruk, murmushi tayi ta kalleshi tace “na gode”

 

shiga da motan yayi ciki, budewa tayi ta fito, shima ya fito ya tsaya a jikin motan tareda harɗe hannu a kirji ya zuba mata ido, yana kallon yadda take bin gidan da kallo, komai ya tsaru tsab harma yafi na da, kamar ba gidan ba, dama yanada kyau amma yanzu yafi kyau an canja fenti harma an kara ɗakuna, kasa ta durkusa zata gode mishi da sauri ya shiga mota yace “banson godiya”

 

karamar wayanta ya bata yace “gashi idan akwai damuwa ki kirani ki sanar dani malama Ameera”

 

karɓan wayan tayi tace “nagode”

 

da hannu yayi mata alama da tashiga ciki, a hankali ta fara takawa tana kara kallon gidan, kaman aljannan duniya komai tsab tsab.

 

Ashe a waje bataga komai ba saima data shiga ciki, taga falon ya canja furnitures kamar da ruwan zinare akayi, hawaye masu ɗumi suka fara bin kuncinta, bedroom ɗin da take ajiye kayanta ta shiga, taga shima an gyara, daga sama taga an rubuta Welcome back Ameera.

 

share hawayen tayi taga wasu balam balam jajaye masu adon heart a jikin bango anyi ado da kaya masu sheƙi kan gadon anyi ado da jajayen flowers an rubuta welcome back Ameera, faɗawa tayi kan gadon ta fara kuka, rungume pillow tayi tana kuka sosai.

 

ɗagowa tayi ta kalli wardrobe taje ta buɗe, sabbin kayane irin wanda take sawa taje coffee shop, abayas da wanduna budaɗɗu da kuma top da kayan ƴan gayu.

 

gefe guda glass ne manya manya kala daban daban, ga takalma dogaye da flat, fa kuma kan dressing mirror an cika da turaruka masu kamshi.

 

a hankali tace “na gode faruk”

 

 

 

_Jiddah shu’aibu✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button