Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 21

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 21*

 

 

 

“Da haka kowa ya kwana a gidan zuciyanshi ba daɗi, washe gari ma babu wanda ya shiga harkan wani, Elham ta tafi school umar ya tafi hospital faruk kuma ya tafi barack ya rage Ammi ce kaɗai a gida, itama batajin daɗi ne da zata tafi wurin aiki, yanzu ciwon kan yayi sauki sai tsinkewan zuciya da take ciki, dan ranta ya tsinke ba kaɗan ba jiya.

 

 

Faruk yana zaune a office yana tunanin abinyi, so yake ya taimaki Amrish ko ta halin kaka, kiran wayan Ammi yayi ya tambaya ko tana lafiya?

amsawa tayi da “lafiya kalau”

 

daga nan ya kashe wayan ya zubawa waje ɗaya ido yana tunanin abinyi, turo kofan tayi ta shigo tana yanga sosai, yau kayan jikinta ya mugun ɗameta ganin kwana biyu yana sakar mata fuska batasan cewa bashi bane umar ne, tana shiga ta zauna akan kujera murya cike da yanga tace “sir yau babu welcome ne?”

wani irin kallo ya aika mata wanda yasa hanjin cikinta kaɗawa, a hankaki ta mike tace “meya faru sir?”

 

kallonta yayi yace “rufe kofar nan kizo”

rufe kofan tayi a tunaninta ya amince da itane, tana girgiza kirji da baya har ta rufe kofan ta juyo tazo gabanshi, kallonta yayi ya sakar mata murmushi yace “cire kayan jikinki”

 

ta fara tsorata saide ta daƙe ta fara cire kayan tana kallon cikin idonshi, saida ta rage daga ita sai pant da bra sannan tazo zata zauna a cinyarshi, hannu ya ɗaga mata “cire duka”

 

cirewa tayi cikin rashin jin kunya sannan tace “am full off”

murmushi yayi banda kyama ba abinda ta bashi, domin fatan tayi bleaching wani wuri fari wani waje baki, da hannu ya nuna mata kofa yace “fita”

 

da mamaki ta kalleshi zatayi magana yace “nace fita”

durkusawa tayi zata ɗauki kayanta ya taka hannunta da karfi taiy ihu yace “ki fita a haka”

durkusawa kasa tayi tana rokanshi “sir kayi hakuri ba zan kara shigowa office naka ba”

 

murmushi yayi yace “na hakura fita”

 

ganin ya mike yana zare belt na jikinshi gashi duk karfene a jikin belt ɗin tasan zai iya mata mugun duka, ta tashi jikinta yana ɓari tana harharɗe kafa tanasa hannu a kirji ta fara tafiya tana kuka, komawa yayi ya zauna yana kallonta har ta buɗe kofa, juyowa tayi tana kallonshi cikin kuka tace “sir dan Allah ka bani koda rigana ne”

ganin ya tashi a harzuke.

 

murɗa handle na kofan tayi sannan ta fita daga office ɗin, gudu ta fara tana neman wanda zai bata riga tasa, kallonta aka fara anan nunata a cikin barack ɗin, da kyar ta samu ta shige wani ɗaki wani ya miko mata riganshi ta amsa tasa.

 

ganin ta fita ya dau wani sanda dake gefe ya ɗaga kayanta dashi ya watsa mata a waje, komawa yayi ya zauna yana cigaba da tunanin hanyan taimakon Amrish, baison damuwa a cikin kwanakin nan, yana son kaɗaici yana son ya samu daman yin tunani, shiyasa ya koyawa wannan shegiyar hankali, dama barinta yake yanzu yasan ba zata kuma dawowa ba.

 

da wannan tunanin na taimakon Amrish ya bar barack ya koma gida, umar yana hospital bai dawo ba sai Ammi da Elham suke kallo a falo, zama yayi a gefensu yana sa hannu akan bowl ɗin da elham ta cika popcorn, Ammi murmushi tayi mishi shima ya maida mata, saida yaci kaɗan ya mike zai koma ɗaki yaji an fara sanar da hukuncin da zasu yiwa amrish gobe, tsayawa yayi yanaji suna cewa gobe za’a rataye wannan me laifin…”

 

canja tasha elham tayi dan ammi ta mata signal, da wani irin muryan da basu san yana dashi ba yace “waya kashe tv?”

 

jikin Elham Yana ɓari ta cillawa ammi remote tace “ammi ne”

barin wuri yayi ya haura sama, watsi ya fara yi da kayan ɗakin yana zaune ashe har sunsa ranan da zasuyi mata hukunci? ya zama dole yayi maganin abin cikin gaggawa.

 

Umar ma yana zaune akan kujeran office nashi me jujjuyawa yana kallon news inda aka nuno Amrish hannu ɗaure da ankwa gobe zasuyi mata hukunci, murmushi yayi domin idan ta mutu komai zai dawo daidai tsakaninshi da ɗan uwanshi faruk.

 

da wannan murnan ya koma gida, ganinsu Ammi a falo ya zauna yace “gobe zasuyi mata hukunci”

ammi jikinta a sanyaye dan ganin halin da faruk yake shiga idan akayi maganan hukuncin Amrish.

 

saukowa yayi jikinshi sanye da wandon soja da farin riga da alama sauri yake, cikin sakin murya umar yace “ammi ai dama me laifi dolene a hukunta shi, itama laifi ta aikata dolene a ratayeta, yarinya karama da kisan manyan mutane”

 

baiyi magana ba yana jinshi ya buɗe kofa zai fita yaji umar yace “babu me taimakonta kuma dan kowa yasan abinda ta aikata saide idan criminal ɗan uwanta ne zai taimaketa”

 

cakk ya tsaya yana jin abinda Umar ɗin yake faɗa, idanunshi sun sauya kala jijiyoyin kanshi sun miƙe a haka ya juyo yace “gara me taimakon criminal da me bin gidan marayu yana lalata da ƴammata wanda basuda iyaye”

 

buɗe kofan yayi yabar gidan ranshi a mugun ɓace, kan umar ne ya kusa yin bindiga jin abinda faruk ya faɗa, me yake nufi? kenan ya san da zaman soyayyansu da teema? tashi yayi yabar wurin yanaji ammi tana kiranshi bai juyo ba, saida ya shiga ɗaki ya rufe ya jingina da jikin kofan yana tuna maganan faruk, yaji zafin maganan har cikin ranshi.

 

runtse ido yayi yana tuno teema wacce ya samu labarin ta mutu a gidan marayun.

 

Ammi dake zaune akan kujera maganan yaso ya tarwatsa mata ƙwaƙwalwa, ne faruk yake nufi? wa yakebin gidan marayu yana lalata musu yara?.

 

tashi tayi taji kaman zata faɗi itafa gani take kaman ta kamu da hawan jini, wannan maganan ya kara mata ciwon kai akan wanda takeyi a cikin kwanakin nan.

 

 

 

*Washe gari*

 

Faruk bai kwana a gida ba yaune ranan da zasuje su yiwa Amrish hukunci, yasan hanyan da zasubi su kaita kotu acan ne za’a ratayeta, shiri yake shi ɗaya bai haɗa baki da kowa ba, kaman karfe sha biyu na rana, yaje cikin dajin ya tsaya akan bishiya yana jiran wucewansu kasancewar shi soja yasan irin motan da ake kai masu laifi kotu domin yanke hukunci, ya kai awa ɗaya akan bishiyan har ya fara gajiya sannan yaji karan zuwan mota.

 

saida ya bari suka iso sannan ya mannu sosai da jikin bishiyan ta yadda babu wanda zai ganshi koda sun ɗaga kai.

 

a daidai wurin suka taka kusosi motarsu ta tsaya cak, murmushi yayi ganin driver ya fito, dubawa sukayi sukaga akwai matsala, basu fito da Amrish ba tana daga ciki hannu ɗaure da ankwa gabanta sai faɗuwa yake.

 

A haka har karfe ɗaya da rabi yayi lokacin sallan azahar, ce musu tayi su barta tayi salla, suma ruwa suka fito dashi sukayi alwala, itama alwala tayi suka sata a tsakiya kafin suka tada salla.

 

Ready yayi saida sukayi sujadda sannan ya saki wani igiya ya faɗo kasa, hannu yasa cak ya ɗagata zaro ido tayi zatayi ihu ya toshe bakinta, saman bishiyan ya haura da ita har yanzu hannunshi a bakinta.

 

daga gefe can da nisa ya saita wani abu ya harba nakiya, mayafin jikinta ya cire ya wulla tareda abin, takalmin kafarta ma ya cire ya wurga, suna salla sukaji karan tashin bomb, da mugun gudu suka bar wurin, ganin bata wajen suka fara dubata cikin dajin, daga nesa suka hango takalminta da mayafinta, ɗaya daga cikin ƴan sandan tace ta mutu fa a cikin bomb ɗin.

 

ido suka zaro sannan suka haɗa baki sukace su ɓoye suce itace ta tashi bomb ɗin suma da kyar suka tsira.

 

kiran waya  sukayi bayan sun ɗauki hoton wurin sukace ai bomb ya tashi har wasu daga cikinsu sunji ciwo ita kuma mai laifin ta mutu”

 

da kansu suka jiwa kansu ciwo sannan suka cinnawa mota wuta suka bar wurin, murmushin nasara da jin daɗi faruk yayi, baisan time ɗin da yayi mata kiss a gefen kumatu ba, sai yanzu ta kalleshi tana daga sama tace “waye kai? umar ko faruk?”

 

bai bata amsa ba saida ya sauko da ita akan bishiyan, ya riko hannunta da gudu suka bar wurin, gudu me nisa sukayi a cikin dajin ganin basu iso ko ina ba ta durkusa kasa tace “na gaji inajij ishi”

 

ɗagata yayi ya fara gudu da ita a hannunshi, saida ya kara tafiya me nisa sannan ya iso motanshi, buɗewa yayi ya shigar da ita ciki shima ya shiga, goran ruwa ya buɗe ya kafa mata a baki, sha ta fara har tana lanƙwasa goran tsabar ishi, saida ta shanye ya sauke yace “are you okay?”

 

jijiga kai tayi idonta yana lumshewa, kwantar mata da kujeran baya yayi sannan yace ta kwanta, cikin gajiya da yunwa ta kwanta akan kujeran, jan motan yayi suka fara ratsa daji sai jijjiga takeyi jikinta har ya fara rawan ɗari.

 

 

 

 

_jiddah ce✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button