Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 6

Sponsored Links

 

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 6*

 

 

 

“Bayan yaran sunci sun koshi sunyi bacci Amrish ta kallo Zainab tace “mun gode”

ɗauke kai kawai zainab tayi tana jin kunyan ace ga abinda takeyi tana samun kuɗi, yauma da safe shugaba ta kirata ta haɗata da wani babban me kuɗi shine ya bata dubu ɗari biyar hakan yasa tayi musu siyayyan kayan abinci masu yawa ta kawo musu ɓangarensu, hannu tasa a cikin jakan dake gefenta ta ciro wasu kuɗaɗe masu yawa ta mikawa Anty sadiya, kallonta tayi cikin waro ido tace “zainab wannan kuɗin daga ina? ba dai sata kika fara ba”

 

murmushin takaici tayi wanda yafi kuka ciwo tace “ba sata nayi ba anty sadiya bani akayi”

 

“waya baki wannan uban kuɗin”

 

“wani me kuɗi ne yayi amfani dani ta bayana shine ya danƙa min wannan kuɗin” tayi magana tana share hawaye, salati suka fara atare hadda tafi anty sadiya tace “Zainab? zainab baki da hankali ne? aina ya ganki?”

 

kuka ta fashe dashi sosai tace “shugaba ce ta haɗani dashi, anty sadiya ji nake kamar na kashe kaina”

 

Amrish batayi magana ba sai kallon zainab take jin abin takeyi kaman almara, me kuɗi? ta baya? kenan ɗan luwaɗi ne? Ko matsafi?”

ganin zainab ta haɗa kai da gwiwa tana kuka sosai, Amrish ya matso, batayi magana ba kawai ta janyota jikinta tana bubbuga bayanta, anty sadiya ma kuka ta fara tana kallonsu, kwashe kuɗin tayi tace su biyota, bayan gidan ta kaisu kafin ta tona rami ta zuba kuɗaɗen a ciki, kallonta tayi “zainab saide mu mutu bamuci komai akan mu bari kici gaba da wannan halin, daga yau ba zaki kara fita ba saida izinina”

riko hannunta tayi suka koma ɗakin tare da Amrish wanda abin ya mugun bata tsoro bayan sun koma tayi ta mata nasiha har tayi shiru, ranan basuyi bacci ba nasiha kawai suka kwana tana yiwa zainab, ya shiga jikinta sosai hakan yasa ta tuba ta ayyana a ranta zata ci gaba da zama kaman da.

 

Da safe suna zaune bayan sun gama breakfast Amrish ce ta ɗauko qur’ani ta baiwa Zainab itama ta ɗau nata ta fara koya mata karatu, cikin ikon Allah ta harshenta ba nauyi ta fara ɗauka, Amrish taji ta rinƙa murna tana koya mata karatu, itama zainab data karanta Kur’ani sai taji nutsuwa ya sauko mata, taji daɗi ta ayyana a ranta kullum sai tayi karatun saboda ta samu sauƙi a zuciyarta.

 

da yamma sunyi wanka suna karatun dare aka aika musu akwai taro yanzu duk su taru, ɗaki-ɗaki aka shiga aka sanar musu, nan mata da ƴammata da zawarawa duk na cikin gidan marayun suka fara fitowa suna taruwa a babban filin cikin gidan,  Amrish da zainab hannunsu rike dana juna suka halarci taron suma, zama sukayi akan tampol da aka shimfiɗa, shugaba da sauran manya masu muƙami a gidan sune suka fara jawabi.

 

“Kowacce da take cikin gidannan tasan mune muka riketa tun tana yarinya, saboda haka abinda mukace kuyi shi zakuyi, mun kiraku ne muyi muku gargaɗi domin wasu basajin magana, bamu isa mu sasu suyi ba, kuma bamu isa mu hanasu ba, saboda haka daga yau idan shugaba ta kiraki ta faɗa miki magana ba musu zaki amince kunji?”

 

Amsawa sukayi da “to”

sallamansu akayi jikin Amrish ya mutu dan tasan da ita suke wannan maganan, hannunta zainab ta riko tace “kada ki damu nasan dake suke maganan amma hakan ba zai sanyaya miki jiki ba, kada kiji tsoronsu nikam shugaba ta gama dani, banida sauran amfani a rayuwa keda baki shiga wannan halin ba kiyi kokari ki kama mutuncin kanki, kada kiji tsoronsu idan sunyi niyan saki a wani halin kinji?”

 

gida kai tayi tace “na gode zainab zanyi aiki da shawaranki insha Allah”

tafiya sukayi zuciyan Amrish cike da tausayi.

 

 

“Yayi shiri tsab cikin kakin sojoji yasa bindiga a aljihun wandon, ba karamin kyau dressing ɗin yake mishi ba, yana kara fito mishi da asalin kyau da kwarjininshi, fuska ba fara’a ya fara tafiya, a hakan ba karamin kyau fuskarshi tayi ba, a gefen Ammi ya zauna yana gaisheta, amsawa tayi tareda cewa “Babana yau aikin safe ne?”

giɗa kai yayi “Ammi akwai wani case ne da aka danƙa a hannuna, an kashe mutumin a cikin gidanshi, a bincikenta na gano dasa hannun ɗanshi babba a mutuwan saide naga shine yake kula da komai na gidan, gashi mahaifiyarsu tafi sonshi yana kula da kannenshi wallahi na kasa faɗa musu gaskiyan lamarin”

 

shiru Ammi tayi tana kallonshi, hakika yana da tausayi kuma ya kware a wurin aikinshi dalilin da yasa suke bashi girma kenan, case na mutuwa indai ya gagari sauran a hannunshi suke mikawa daga nan kuma saiya gano komai.

 

“ka sanar musu ba’a ɓoye laifin kisa, kada ka manta kayi ta rantsuwa lokacin da zaka shiga aiki cewar ba zaka ɓoye komai ba, saboda haka duk abinda ka gani ka faɗa kawai”

 

“Toh Ammi na zanyi kokarin hakan”

 

Umar ne ya sauko shima cikin shirin likita, kayan ya mishi kyau ba kaɗan ba, riga da wando kanana ne a jikinshi blue saiya ɗaura rigan likitoci wanda yake daidai gwiwa fari da abin sawa na wuya irin na gwaji ɗin nan, murmushi yake domin shi a koda yaushe fuskarshi tana ɗauke da murmushi, zama yayi a gefen Ammi yace “good morning”

amsawa tayi da “ka tashi lafiya?”

 

“Lafiya kalau”

kallon Faruk yayi wanda yake kallon yadda kanshi yake bai taje ba, Signal yayi mishi “Ya? ka tashi lafiya?”

 

“Lafiya kalau”

cewar Faruk, mikewa yayi ya ɗau mataki yazo ta saman kan Umar ɗin, fara taje mishi kanshi yayi, Ammi tana kallonsu cikin zuciyarta tana yimusu Addu’a, saida ya gama yace “let’s go”

 

tashi Umar yayi ya kalli madubi sai yaga kanshi yayi kyau kamar na Faruk ɗin, jerawa sukayi bayan sun yiwa Ammi peck a kumatu, shiga motar Faruk sukayi su duka, kallonshi yayi “kai ba zaka tafi a motanka bane?”

cewar Faruk.

 

“A,a a taka zamu tafi”

baiyi magana ba kawai ya kunna motan, buɗe musu get akayi suka fara tafiya, saida suka hau hanya Umar yace “kai ba zakayi aure bane wai?”

 

juyowa yayi ya harareshi yace “kai ubanme ya hanaka?”

 

“ubanka ne”

shiru kawai yayi suka ci gaba da tafiya.

 

“zanso mu auri ƴan biyu masu kama ɗaya kaman yadda muke muma”

 

“nima hakan shine a raina ƴan biyu masu kama ɗaya nakeso mu aura”

 

hira sukaci gaba dayi saida sukaje bakin hospital ya kalli Faruk yace “ka shiga mana kanina”

harara ya ɓalla mishi “waye kanin naka?”

 

“kai mana”

 

“niba kaninka bane rana ɗaya aka haifemu lokaci ɗaya”

 

“to amma ai na rigaka fitowa, so koda auren zamuyi nine zan aure babban na bar maka karamar”

 

goran dake gefe ya ɗauka zai kwaɗa mishi da gudu ya bar jikin motan yana dariya, shiga cikin hospital yayi, shikuma Faruk ya juya ya fara driving,   Yana son ɗan uwanshi sosai, zai iya yin komai a kanshi, baya son ganin Umar a cikin wani hali, ko tagumi yaga yayi shima sai yaji har cikin ranshi, ubangiji ya kare mishi ɗan uwanshi duk inda ya shiga”

 

Barack yaje ya shiga ya fara bincike akan gawan da aka kawo bada jimawa ba, saide wannan karon binciken yaso ya bashi wahala, makashin yanada wayo sosai, rubuce rubuce yayi sannan ya mikawa babbansu, bayan yaje Office nashi, cikin mamaki yace “Faruk ka tabbata wannan kisan kai ne ba kashe kai ba?”

 

Jijjiga kai yayi cikin kamewa irin na sojoji da bawa babba girma yace “Yes sir bugeshi akayi da babban mota”

 

“Okay faruk jeka zan kara kiranka a kowani lokaci”

saida ya sara mishi kafin ya juya ya fita, abokan aikinshi suna cikin filin Barack ɗin daga masu shan taba sai masu shan giya, gefe guda kuma wasu suna zaune da ƴammata, sam wannan rayuwan bai dameshi ba, shi abinda yake gabanshi shi yakeyi wato aikinshi, hakan yasa oganshi yake bashi girmamawa, dama daga ogan saishi a wurin aikin.

 

zama yayi a gefe ya kira wani soja yace a ɗauko mishi Laptop nashi, ɗauka mishi akayi nan ya kunna yana dube dube kaman yadda ya saba, goran ruwa da champagne aka kawo mishi me sanyin gaske da glass cup a gefe, ɗauka yayi ya tsiyaya a Cup ɗin a yana ya fara sipping yana cigaba da Aikinshi, wani abokin aikinshi ne yazo wurinshi ya zauna a gefe, kallonshi yayi yace “Khalil? ya kake?”

 

“Ina lafiya faruk”

 

“Kwana biyu ina ka shiga?”

 

“Wallahi Madam ne ba lafiya muna asibiti da ita”

 

“Okay Allah ya bata lafiya”

 

“Ameen”.

 

 

 

Umar yana shiga ya wuce Office ɗin Kamal, budewa yayi yace “kai kamal ina wancan file ɗin na jiya?”

dafe kirji kamal yayi kafin yace “gaskiya ka tsoratani Umar babu ko sallama?”

 

dariya yayi sosai hadda rike ciki ganin yadda kamal ɗin ya zaro ido time ɗin daya shigo, turo kofan yayi yashigo yana cigaba da dariya, zama yayi akan kujera yace “ka fiye tsoro kaman mace.”

 

“To ai kai ka tsorata ni”

wani file ya ɗauko ya mika mishi, tashi yayi ya fita da file ɗin, Office nashi wanda aka ƙawata da kayan ado ya shiga ya zauna akan kujara me juyi da mutum, wayanshi ya ɗaga ya kira Teema, kira biyu ta ɗaga yace tazo hospital ta sameshi yayi kewanta, da fari bataso zuwa ba saida ya rinƙa yimata shagwaɓa kaman zaiyi kuka kafin tace tom zata zo, ajiye wayan yayi yaci gaba da jera files yana sawa cikin drower, saida ya gama yaje yabi room room yana duba marasa lafiya, masu allura yana musu masu ɗaura drip Yana ɗaura musu, saida yaga babu wani aiki ya koma Office yana jiran zuwan Fatima.

 

Ba jimawa ta shigo Office ɗin fuskanta ɗauke da murmushi dama gata innocent, Shima murmushi ya mata ganin yadda tayi dressing cikin riga da skirt na atamfa da hijabi fari guntu, hannu ya ɗaga mata ta karaso ta zauna a cinyarshi, ɗago fuskarta yayi yana kallonta yace “nayi kewanki”

murmushi tayi kanta kasa tace “nima haka”

kallonta yayi yau yanayinta ya sauya sosai, da mamaki yace “meya faru? na ganki shiru”

 

ido ta zuba mishi yayinda idanunta suke cika da ruwa, a hankali tace “ina sonka umar, ina sonka sosai”

 

shiru kawai yayi yana kallonta, saida ta rungumeshi yace “nima ina sonki teema na”

 

“Kace kanaso ka aureni inaso ka aureni da gaske”

ɗagowa tayi tana kallon cikin idonshi tace “inaso ka yiwa mahaifiyarka magana akan aurenmu”

 

gabanshi ne ya faɗi ganin da gaske take maganan har cikin ranta, kallonshi tayi sosai tace “kwarai da gaske nake, nima inason barin gidan marayu amma sanadiyyan aure ba wani abin daban ba, inason nima na rike koda yaro ɗaya ne maraya, zakayi mata magana?”

 

shiru yayi yana kallonta, hannu tasa ta shafa sajenshi tace “Umar fa zaka aureni?”

sauketa yayi daga jikinshi yace “teema yau kaina yana ciwo kaɗan ki bari sai zuwa next time muyi magana”

 

“Ko dai ba zaka iya auren marainiya bane? wacce bata da uwa, batada uba, batama san inda aka tsinto ba, gashi kuma ta bawa wani kanka a waje, amma ai ba wani daban na bawa ba kaine na bawa kaina, daga kai ban kuma yin zina ba, kaine ka fara koyamin, kai kace zaka aureni idan na amince da kai, nikuma zafin maraici da yunwa yasa na amince da kai…”

 

hannu ya ɗaga mata, “teema banson wannan maganan kije zamuyi magana idan nayi sauki”

 

mikewa tayi tana murmushi wanda yafi kuka ciwo tace “to ba komai zanje duk lokacin daka shirya sai kayimin magana”

fita tayi daga Office ɗin tana ji kaman zata faɗi kasa saboda jiri.

 

mai adaidaita sahu ta tara shiga tayi bayan ta faɗa mishi inda zai kaita, yana ajiyeta ta biyashi kuɗinshi ta shiga cikin gidan marayun, bata tsaya ko ina ba sai ɗakin su Amrish, time ɗin Amrish tana zaune da wata yarinya ƴar karama sabuwar zuwa wacce aka tsintsa a cikin kwata tana kuka, farcenta wanda yayi tsayi sosai take yanke mata, tsayawa teema tayi a bakin kofa tana kallon yadda Amrish take kula da yaran, itakam ta ɓata lokaci kullum tana tare da Umar bata kula da yaran gidan saide taje tana ɗaukan nauyinshi, da gudu ta karasa ciki bayan ta fashe da kuka ta rungume Amrish tana cigaba da wani irin kuka me tsuma zuciyan me sauraro.

 

Amrish ajiye abin gyaran farcen tayi tana jin Teema tana kuka sosai, hannu tasa a bayanta tace “lafiya Fatima meya faru?”

 

Kallon yaran ɗakin tayi tace “kuje waje”

fita sukayi, tace “meya faru?”

 

cikin kuka tace “ashe gaskiya kike gayamin Amrish? nasan cewar na aikata kuskure, gashi naga alaman ba aurena zaiyi ba”

 

shiru kawai Amrish tayi, saida ta karashi kukanta tace “nima na tuba yanzu zan fara zama a gida ina kula da sauran kannena marayu”

 

murmushi tayi mata “ba komai Teema kiyita addu’a kawai kinji?”

 

“Tom zanyi”

tashi tayi taje ɗakinsu, kwanciya tayi akan katifa tana tunanin ranan da Umar ya fara lalata mata rayuwa, a ranan take kasuwa ne siyan kayan maganin ciwon ciki, a hanya ya tsayar da ita yace zai rage mata hanya, bataso shiga ba saida yayita rokanta, bayan ta shiga ya rinƙa janta da hira da barkwanci, itama dama tanafa son hira, haka dai har ya bata karamar waya bayan ta fita ya bata kuɗaɗe masu yawa, kin amsa tayi saida yayi da gaske, bai nuna mata halinshi ba saida suka faɗa soyayya me zurfi, yace zai aureta hakan yasa ta saki jiki dashi, ashe baida niyya kawai lalata ta yake son yi, share hawaye tayi tace “ba komai duniya ne”.

 

Amrish taji zafin abinda aka yiwa Teema shiru kawai tayi batayi magana ba, tasan dama babu ɗan masu kuɗi da zaizo nan gidan ya samu budurwa yace zai aura saide suzo dan su lalata su, gashi yanzu ya ɓatawa teema rayuwa yaki aurenta.

 

cigaba tayi da kula da yaran ba tareda tace komai ba, wanka take musu zainab tazo wajenta dama daga kasuwa take, hannunta ta riko suka shiga ciki tace “Amrish bayana ya fara fitar da tsutsa gashi bana iya rike kashi”

 

zaro ido Amrish tayi tana kallon zainab sai yanzu ta lura da kawar tata ta rame sosai, jikinta ne ya fara rawa ganin zainab ɗin tana kuka, cikin rawan jiki tace “zainab dan Allah kada kice haka, ki kara dubawa dai da kyau”

 

“wallahi tallahi Amrish bana iya rike kashi gashi ina fitar da tsutsa kuma ina wari idan na zauna a gefen mutane”

zama Amrish tayi akan kafanta itama ta fashe da kuka tace “meyake faruwa? ya Allah meyasa kake jarabtanmu da irin wannan jarabawan?”

 

zainab ta jingina kanta da bango itama ta fara kuka sosai, tashi tayi da gudu taje banɗaki tacewa Amrish ta biyota da buta, gaban Amrish ne ya kara faɗuwa ta tabbatar da zancen yanzu.

 

Wani irin gudawa ta fara tana jin cikinta yana murɗawa, saida ta kai mata buta kafin taje ta kira Unty sadiya.

 

Unty sadiya tana zuwa tayi mata bayanin abinda ya faru, itama dafe kirji tayi, a lokacin Zainab ta fito, hannunta akan cikinta, riketa sukayi suka kaita ɗaki, zama sukayi a gefenta bayan ta kwanta duk sukayi tagumi, hannun Amrish ta riko tace “ki daina yawan tunani kada ya kawo miki hawan jini kinji?”

 

gida kai tayi idanunta cike da hawaye, Unty sadiya ɗauke kai tayi tana sharan kwalla a ɓoye, ruwan zafi Amrish ta kawo mata ta karba tasha, sannan ta koma ta kwanta, shiru sukayi, kara tashi tayi time ɗin har ta fara kashi a kwance ta shiga toilet babu ko takalmi, hannu Amrish tasa a baki tana wani irin kuka me tsuma zuciya, Unty sadiya ce ta daure ta ɗibi ruwa ta kai mata.

 

saida ta gama ta rikota ta kawota ɗaki, kwanciya tayi har ta zabge, ashe tayi kusan sati tana jin alaman tafiyan wani abu a cikinta abinka da yaranta bata tuno hakan ba, domin dukkansu da Amrish ɗin ba zasu wuce 18 ba, zazzaɓi ne ya rufe ta ga gudawa yaki tsayawa, haka suka kwana ranan idonsu biyu.

 

da safe abin yayi tsanani, anti sadiya da kanta taje ta tono kuɗaɗen da suka birne ta dawo tace su kaita hospital, Teema ta shigo ta gaishesu taga halinda ake ciki tare da ita suka tafi zuwa asibiti, su suka rike zainab wacce ta fita daga hayyacinta, pampas suka samata kafin take gudawan aciki.

 

babban asibitin sukaje, bayan sun jira layi akazo kanta akayi mata gwaje-gwaje likita yace idan basu ajiye miliyan ɗaya ba bama zai fara taɓata ba, domin alluran tsaida gudawan ma kaɗai dubu ɗari shida ne, gashi kuɗin da yake hannunsu dubu ɗari biyar ne.

 

Amrish ce ta durkusa ta rike kafafunshi tace “dan girman Allah ka dubata nayi maka alkawarin zuwa nan da yamma zan kawo maka miliyan ɗaya kota halin kaka”

 

Janye kafarshi yayi yace “idan ba kuɗin cash ba zaiyi komai ba”

teema tana rike da zainab wacce take ta nishi idonta yana rufewa.

 

Unty sadiya ma tana rokanshi ya taimaka harda mika mishi kuɗin ya ɗiba ya watsa musu zuwa yanzu ya fara fusata, yace “idan ba zasu bayar ba su fita subar mishi asibiti”

 

girgiza kai Amrish tayi kaman sabuwar kamu a hauka tace “a,a ba zamu fita ba kayi hakuri zanje na nemo kuɗin”

gefe suka kwantar da ita inda babu hayaniyan mutane, Teema tace “aina zaki samu kuɗi Amrish?”

 

“Zanje na nemo koma a ina ne”

 

“Bari ina zuwa zan gwada tambaya”

wayanta ta ciro tana kiran numbern Umar, kusan sau uku kafin ya ɗaga cikin zafi yace “mene?”

a hankali tace “ina neman miliyan ɗaya ne idan zan samu”

 

“Ke bafa ki isa kiyi blackmail ɗina ba, kinaji ko? kinje kin gama yawon karuwancinki zakizo kice na aureki kinyi hauka ne? to bari kiji Ni bazan iya auren marainiya mara galihu irinki ba”

 

kashe wayan tayi tanajin zafi a ranta, Amrish tana iya jiyo duk abinda yake faɗa ta cikin wayan, bata tsaya tayi mata bayani bama ta mike tana sharan kwalla, itama teema hawaye ta share tana rike hannun zainab wacce take ta aikin miko hannu da alama akwai abinda takeso.

 

Amrish take kira da sauri Amrish ta durkusa, ganin tana magana ta matso da kunnenta domin taji me take faɗa.

 

“Kada ki lalata rayuwarki domin ceton nawa rayuwan kinga hakanne ya faru dani domin na ceto rayuwar su Na’eem na jefa nawa a haɗari, to haka zamuci gaba da rayuwa muna ceton juna muna mutuwa? Ki bari kawai idan na mutu lokacina ne yayi, kuyimin addu’a ku rokamin Allah ya yafemin”

 

Da kyar take maganan, hannunta Amrish ta riko tace “kimin kwatancen gidan mutumin da kike zuwa zanje na sanar mishi halinda ake ciki”

 

cikin fitar da magana da kyar tace “sunada yawa kuma gidajensu akwai tsaro sosai domin ba kananan masu kuɗi bane, shugaba tasansu duka, amma zan miki kwatancen gidan ɗaya idan kinje ya hana ko ya nemeki kimin alƙawarin ba zaki yadda dashi ba”

 

Cikin kuka tace “na miki alkawari”

 

“Yana g.r.a shine a ginin farko zakiga babban gidane da security’s kice alhaji ne yace kizo daga gidan marayu kike zasu barki ki shiga, amma ki karamin alkawari ba zaki jefa kanki cikin halaka ba? domin kece kike kula da yaran gidannan idan bakya nan komai zai daɗa lalacewa ne”

 

“nayi miki alkawari”

ta faɗa da sauri kafin ta mike ta kalli Unty sadiya tace “na tafi”

teema tace “ki kula da kanki”.

 

 

 

 

*Littafin Hamshaƙiya na kuɗi ne akan ₦400 ki biyani hakkina kiyi karatu cikin salama 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta wannan layin 08144818849, saiki turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

Leave a Reply

Back to top button