Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 2

Sponsored Links

 

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 2*

 

 

 

~Safiyar ranan an wayi gari da labarin mutuwan wannan babban ɗan kasuwan wato Alhaji Hamza Dila, gidan jaridu, gidajen Tv, social media ko wani lungu da sako na cikin garin Abuja wannan labarin kawai akeyi, wannan mutuwan bana Allah da Annabi bane kasheshi akayi akasa gawan a cikin buhu saida ya fara wari kafin mutane suka fahimci akwai gawa a wajen hakan yasa a kira sojoji da police domin gudanar da bincike, wurin cike yake taf da mutane da kuma jami’an tsaro har zuwa yanzu babu wanda ya taɓa gawan.

 

 

tambayoyi akeyi a gidan tv na cewar me ake jira ba’a taɓa wannan gawa ba har yanzu? gashi kuma ƴan sanda ne a wurin shin suna tsoron taɓa gawan ne ko kuma akwai abinda suke jira? har yanzu dai babu wanda yayi magana suna dai wurin suna cigaba da tsaro, wani babban soja ne ya fito daga mota nan take ƴan jarida sukayi caa akanshi suna mishi tambayoyi “yallaɓai shin me zakace game da mutuwan Alhaji Hamza? kuna zargin wani ne da aikata wannan kisan?”

 

Amsawa yayi “a halin yanzu babu wanda muke zargi har sai an gudanar da bincike”

 

“to yallaɓai shin kai ake jira ne yasa basu taɓa gawa ba har izuwa yanzu?”

girgiza kai yayi “a,a baki ake jira ba, muna jiran wannan kwararren me binciken kuma wanda bashida tsoro, zai iya fadan wanda yayi kisan kai tsaye ba tareda yaji shakkan kowa ba”

 

“Yallaɓai wanene wannan?”

 

cikin girmamawa yace “CAPTAIN FARUK AHMAD DIKKO wanda akafi sani da captain F.A”

hannu ya ɗaga yace “gashi ma ya karaso”

juyawa sukayi da gudu suka nufi wurin motar daya tsaya, a bayanshi sojoji ne masu yawa motar tashi baki ne kirin ga kuma glass ɗin tinted ne, saida yayi kusan 5mins yana cikin mota kafin yayi knocking da gudu wani soja ya buɗe yazo gefenshi cikin girmamawa ya buɗe mishi marfin motan tareda kamewa waje daya alaman respect, kafarshi wanda yake sanye da takalmin irin na soja ya sanya izuwa waje, a hankali ya fito daga motan fuskanshi sanye da bakin glass, jikinshi da kayan uniform na manyan sojoji, saida ya juyo na hango shi, saura kaɗan biron da nake muku rubutu dashi ya faɗi da naga fuskan wannan sojan, kyakkyawa ajin fari, namiji me kwarjini da haiba, har wani yellow yellow ya zama tsabar farantaka da hasken fata tareda glowing da murjewa, sajen fuskarshi yafi komai ɗaukan hankali tareda dogon hancinshi wanda yake da tsini ga kuma karamin bakinshi wanda yake red ne, gashin kanshi me yawa ne domin a gyare yake ba kaɗan ba, fuskar nan a murtuƙe babu alaman dariya ko kaɗan, kana ganinshi sai gabanka ya faɗi tsabar kwarjini, ƴan jarida ma saida sukayi baya, cire glass ɗin fuskanshi yayi yasa a gaban riganshi kafin ya fara takawa sauran suna binshi a baya, hanya aka fara bashi cikin dandazon mutanen da suka taru a wurin, ƴan jarida suka fara aika mishi tambayoyi bai amsa ko ɗaya ba, hasalima ko kallonsu baiyi ba, saida yazo dab inda gawan yake kafin ya jiyo wani a cikinsu yace “yallaɓai kai kurma ne?”

 

tsayawa yayi cak, ba tareda ya juyo ba yace “A,ah”

shine kawai abinda ya faɗa kafin ya karasa inda gawan yake, sawa yayi a kwance ta hanyan nuna musu da hannu, facemask yasa tareda handglove kafin ya karasa yana duddubawa, biro ya ciro yayi rubutu, ya kai 30mins yana dubawa kafin ya kalli mutanen wurin cikin muryanshi ke zaƙi da daɗin sauraro yace “anyi mishi alluran poison saida gaɓoɓinshi suka mutu kafin aka kasheshi, wanda yayi kisan doctor ne ayi bincike da wani doctor suke gaba?”

 

yana faɗan haka ya juya, suna mishi tambayoyi bai ko kara kallonsu ba ya shiga mota, nan driver ɗin shi yaja suka bar wajen.

 

dafe kai yayi a cikin mota yana tunanin me zaisa mutum yayi kisa kuma ya zauna lafiya ba tare da ya damu ba?

wannan abin yana bashi mamaki yasha samun case kala kala akan kisa kullum abin ci gaba yake hasalima karuwa abin yake, lamarin kasan ya lalace, tissue ya ciro ya goge hannunshi kafin ya jefar zuwa waje, goran ruwa ya ɗauka ya buɗe kafin ya ɗaura a bakinshi ya fara sha, saida yayi rabi kafin ya sauke, wayarshi dake gefe ta fara ruri ya ɗaga ganin sunan Ammi da yake yawo a gaban screen ɗin, a hankali yace “Ammi? good evening”

 

amsawa tayi kafin tace “ina kake?”

cikin shagwaɓa yace “ina hanyan gida”

“okay Ina ganinka ai news wai har ja gama binciken ka tafi?”

 

“yeah Ammi kinsan banson tsayawa a wurin tausayi mutumin yake bani banson ganin gawa sosai”

 

“okay saika dawo”

kashe wayan tayi, ya kallo driver yace “hanyan gidan Ammi ba barack ba”

“okay sir”

shine abinda driver ya amsa, tafiya sukayi me nisa kafin suka isa unguwan da yake shiru ne sosai ga kuma manyan gidaje, a bakin wani maƙeƙen get wanda aka yishi kamar da glass sukayi horn, getman nasu ma soja ne shine ya buɗe suka cusa hancin motar zuwa cikin gidan, babban gida me ɗauke da manyan fulawoyi duk cikin gidan tyles ne, ga ɗakin me gadi a gefe ɗakin me gadi ma kaɗai abin kallo ne, buɗe mishi mota akayi nan ya fita ya fara takunshi me kasaita, tun daga kofa ya cire rigan sama wanda yakeji ya takura mishi, shiga babban palour na kasa yayi bakinshi da sallama ya faɗa kan wani sofa me laushi da tsantsi, yabi ɗakin da kallo, komai a kimtse ga wani kamshi dake tashi, komai na cikin palour blue ne sky, wato ruwa sararin samaniya, agogon hannunshi ya cire tareda biron dake aljihun wandonshi ya zubasu akan centre table ɗin dake gabanshi, kanshi ya jingina da jikin hannun sofan ya ɗaga yana kallon sama, faɗawa yayi duniyar tunani a hankali saida yayi nisa yaji an tafa hannu da karfi a gefenshi, firgigit yayi yana salati, dariya ya kwashe dashi harda rike ciki ganin yadda ya tsorata, abin mamaki wani matashi ne mai kama da Faruk babu abinda ya rabasu kamar an tsaga kara.

 

yatsine fuska yayi cikin shagwaɓa yace “dan Allah me haka? kullum saika tsorata ni?”

 

zama yayi a gefenshi yana rike kunne yace “am sorry dude, ka fiye tsoro gaka kamar jarumi amma sai tsoro”

haɗa fuska yayi yace “na kaika tsoro? kaida baka iya kwana kai ɗaya? zanga yadda zakayi ai idan nayi aure”

 

“ai koda aure kayi saina bika ɗakinka mun kwana tare”

mari Faruk ya kai mishi a baya, da sauri yasa pillow ya tare “to to zaku fara ko?”

cewar wata mata kyakkyawa wacce take saukowa daga stair, a hankali take taka matattakalar jikinta sanye da tsadadden leshi ruwan kasa yasha adon duwatsu sai sheƙi yake, farace sol da gashi sosai wanda tayi kitso ta watsa shi a bayanta, saida ta karaso cikin shawaɓa yace “Ammi kinga shine ya fara tsokana ta”

 

shiru Faruk yayi ganin yadda yayi mishi sharri a take, murmushi kawai yayi Ammi ta zauna a tsakaninsu tace “nasanka Umar kaine ka fara tsokana, Faruk baya tsokana kaine dai karami kuma kaine fitinanne”

 

Faruk ne ya kwantar da kanshi a cinyar Ammi a hankali yace “Ammi ta shaideni sosai, koda banyi magana ba tana gane abinda ya faru”

 

kallon Umar tayi ganin yadda yasa sarka a wuya wani siriri fari ga kuma wani aski da yayiwa gashin kanshi ya tarasu waje ɗaya, lumshe ido tayi tace “cire sarkan nan”

turo baki yayi yana cirewa yace “Ammi sarkan gayu ne fa, ya zaki rabani dashi?”

 

“to ko zaka hana ne?”

mika mata yayi yana cigaba da turo baki, cikin faɗa tace “Umar ka nutsu kana ganin ɗayanka baya irin abinda kake yi, meyasa kai ba zakayi koyi dashi ba? rana ɗaya na haifeku lokaci ɗaya, kamanninku ɗaya komanku ɗaya amma halinku ya bambanta”

 

tashi Umar yayi a wajen ya haura sama, wandon jikinshi har yana sauka gashi a yage wai a hakan wanka ne, tsaki taja ta ajiye sarkan a gefe, lumshe ido Faruk yayi yana jinsu baice komai ba, shafa kanshi tayi “ka rinƙa sa twin brother ɗinka a addu’a Allah ya shirya mana shi”

 

baice komai ba yayi kaman yana bacci,

wata yarinya ce da bazata wuce 15years ba ta shigo da gudu tana kiran Ammi, dariya Ammi tayi tace “Elham ɗina ta dawo”

rungume ta tayi ta zauna gefenta, tace “ya school ɗin?”

 

“lafiya kalau Ammi”

kallon Faruk tayi “good evening ya Faruk”

bai buɗe ido ba kuma bai amsa ba, taɓe baki tayi dama tasan halinshi ba lalle ya amsa ba, a hankali ta mike itama tana kama dasu Faruk da alama kanwarsu ce, ɗakinta ta nufa domin cire uniform, saida ta cire tasa riga da skirt na kanti kafin ta fito tana sa hula akanta, ji tayi an rungumeta ta baya, murmushi tayi “Yah Umar?”

 

“Kin dawo?”

“eh na dawo”

sakinta yayi ya riko hannunta suka karasa wurinsu Ammi, abinci Ammi ta matso musu dashi, nan suka zuba a plate ɗaya suka fara ci, Ammi ta zuba musu ido tana kallonsu, Umar ɗiba yake yana bawa Elham a baki, tana ansa cikin shaƙuwa suna hira abinsu, kallon Faruk wanda yake kwance tayi, shikam bai fiye sabo da mutane ba, haka yake idan kaga ya saki fuska ko baki yana hira to shida twins ɗinshi ne wato Umar.

 

 

 

 

*Littafin Hamshakiya na kuɗi ne akan naira 400 ki biyani hakkina kafin ki karanta 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo evidence of payment ta nan 08144818849 masu kati kuma zaku iya turo mtn ta numbern dana ajiye*

Leave a Reply

Back to top button