Hamshakiya 16
*🌸HAMSHAƘIYA*🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 16*
“Kenan ba dan Allah ka rufamin asiri ba? dan ka rufawa ɗan uwanka kayi?”
“wannan shine dalilin da yasa masu kuɗi basa birgeni kuna da son kanku dayawa, indai zaku taimaki kanku zaku iya yin komai, saɓanin haka kuma saide kowa ya cutu, na zaci kayi haka ne don ka taimaki rayuwar marayu amma dan ɗan uwanka kayi”
murmushi yayi sannan ya kara gyara zama yace “nima maraya ne, ban tashi da uba ba, mahaifiyata kawai take raye yanzu, kinga nima ai za’a sani sahun maraya, banyi haka dan na cece rayuwar Umar ba, nayi ne dan na cece rayuwar ku dana marayun gidan”
“ka tabbata?”
jijjiga mata kai yayi “kwarai na tabbata”
“ta wani hanya zaka iya taimaka min na gina school?”
“ta hanyan shawara”
murmushi tayi tasa bayan hannu ta share hawaye tace “Tom na gode”.
*Umar*
ba karamin bincike yake ba yake yiba akan case ɗin mutuwan su Alhaji Hamza, yau yini yayi a cikin office yana duba files bai fito ba saida ya samu wani alama da kuma shaida, ya sa a zuciyarshi cikin kwana biyu saiya samo twins brother ɗinshi wato Faruk.
da ƴar karamar takadda ya nufi gida, yana zuwa gida yaje ya ɗakinsu da Faruk ya fara bincike cikin ikon Allah ya samu takaddan da yake nema, dubawa yayi cikin ikon Allah sai ga wani shaida, buɗewa yayi yaga suna an rubuta da manyan harafi AMRISH da mamaki ya cire yana karantawa, zama yayi daɓas yana cigaba da karantawa.
a fili yace “Amrish?aina na taɓa jin sunan? miye alakanta da kisan?”
da takaddan a hannunshi ya fara tunani aina ya taɓa jin sunan Amrish?
da sauri yace “teema a wurin teema da faruk, to miye alaqarta da kisan da akeyi?”
tashi yayi ya fita parking space yaje ya shiga mota da mugun gudu ya bar gidan, hanyan gidan marayu ya nufa, saida ya iso bakin kofa ya samu me gadi suka gaisa, yace “Baba wacece Amrish anan gidan?”
“Amrish yarinyar kirki itace me kula da yaran gidan tana zuwa ɗaukansu daga school”
a tunanin Baba megadi yazo neman aurenta ne, zama Umar yayi a gefen baba yace “Baba zan iya ganinta yanzu?”
“A,a gaskiya ta fita ɗauko yara daga makaranta amma idan ka ɗan zauna zata dawo bada jimawa ba”
godiya yayi sannan ya koma cikin mota ya zauna yana zuba ido yana jiran ta inda zata fito.
kallon agogo yake lokaci yana ja kuma har yanzu bata dawo ba, har ya kunna motan zai tafi ya hango yara da uniform suna dawowa, tana bayansu jikinta sanye da hijabi dogo har kasa fari, tayi kyau cikin hijabin sai dariya take da alama yaran suna bata labari, kashe motan yayi ya zauna yana kallonta har ta iso bakin get, mikawa baba goro tayi sannan ta rike hannun biyu daga cikinsu suka shiga ciki, sauke ajiyan zuciya yayi “wannan ce Amrish? ba zata iya kisa ba”
ji yayi kamar ya kirata yaji daga bakinta wani ɓangaren yace “no ka bari ka kara bincike”
jan motar yayi yabar wurin zuciyarshi cike da tunani, bai tsaya ko ina ba sai gida, samun Ammi yayi tana kan kujeran falo tana bacci, bai tashe ta ba ya wuce ciki, barbaza kayan ɗakin yayi bai bar komai ba saida ya kara samun wani takadda wanda faruk ya ɓoye yana dubawa yaga list ɗin mutanen da aka kashe, daga kasa kuma yaga an rubuta Amrish da jan biro, zama yayi a bakin gadon yana yamutsa gashin kanshi, gaba ɗaya kanshi ya kulle, me hakan yake nufi? itace take kisan? to meyasa faruk bai sanar an kamata ba? ko yana jiran more evidence ne?ajiye takaddan yayi wani abu yana cewa ya kaiwa general, wani ɓangaren yana cewa ya kara faɗaɗa bincike.
kanshi ya kulle ya rasa abinyi ya rasa ta yadda zaiyi ya ɓullowa al’amarin, shifa burinshi kawai ya samu Bro ɗinshi ya dawo gida, waya ya ɗaga ya ɗau hoton takadda sannan ya mike ya fita daga gidan gaba ɗaya ya susuce.
Barack ya koma yaje office na faruk ya kara zurfafa bincike, ya duba duk wani takadda dake kan table ɗin, sunan Amrish yaga an kara rubutawa da jan biro, sannan akayi alaman cancel a jikin sunan, fita yayi ya shiga mota yana kallon takaddan, wayanshi ya ɗauka ya buɗe data rabonshi da hawa online tun Faruk yana gida, ganin sakonni suna shigowa ya ajiye wayan a gefe ya maida hankalinshi kan driving, saida suka gama shiga ya ɗaga wayan yana searching sunan general, da mamaki yaga faruk ya tura mishi sako, a daren ranan daya ɓata, da sauri ya shiga yana dubawa, tsayawa yayi da motan ya zubawa hoton daya tura mishi ido, yarinyar daya gani a gidan marayu itace a jikin hoton saide wannan a waye take gashi da gani ta jiƙa da kuɗi, dressing na jikinta riga da wando ne ya kamata sosai ga katon glass tasa a saman siririn mayafinta, scrolling yayi yaga wasu hotunan kuma, wannan itace ya gani ɗazu dan kayan jikin sun gaji babu alaman hutu a tare da ita, rubutun ya zubawa ido “wannan na farko itace Ameera ta biyu kuma Amrish, surprise zanyi maka dan inaso ka auri Ameera ni kuma zan auri Amrish”
“Ohhhhh itaɗin twins ne”
shiru yayi kana daga bisani yace “to amma ya meyasa ɗayan take gidan marayu? ya zama dole nayi magana da ita”
da sauri ya figi motan ya nufi gidan marayu, parking yayi yana shirin fitowa yaga ta fito tana juya baya, saida tazo bakin kofa ta cire dogon hijabin dake jikinta ya rage daga ita sai dogon riga baƙi tasa space a fuskanta tasa dogon takalmi ta kalli gefe wani mota ne danƙarere a pake, zuwa tayi ta shiga da kanta ta fara driving ta bar wurin.
kanshi ne yayi wani irin hayaki kamar zai fashi, a fili yace “double roll take takawa kenan? ita ɗin ba twins bace mutum ɗaya ce, itace take aikata duk wani kisa da satan da akeyi a garin nan, itace ta sace twins brother na”
baiyi yunkurin bin bayanta ba ya wuce gida kawai, a ranshi yana kitsa abinda zaiyi yarinyar nan saita gane shayi ruwa ne.
*Washe gari*
hoton Amrish ne ya fara yawo a social media wanda ta yishi a gidan marayu da kuma wanda tayi a jikin motarta tana shan champagne da cup da kwalban a hannunta, WANTED aka rubuta a jikin hoton, kasancewar bata social media bataga komai ba.
zaune take a gefen shi tana tsara mishi yadda ginin school ɗin zai kasance, idan ta ɓata sai ya gyarata, zama tayi me kyau tana nuna mishi katon zanen dake gabanta, lumsashun idanunshi ya zuba mata yana kallon yadda take motsa baki tana magana cikin nutsuwa da sanyin murya, hannunta kuma tana nuna mishi yadda tsarin zanen zai kasance, jin yayi shiru ta ɗago kai tana kallonshi ganin yana kallonta ta tafa hannu tace “ya dai mr faruk, kallon fa?”
“zanyi missing naki idan na tafi”
shiru tayi, yace “kina da zuciya me kyau, nasan iyayenki suna can suna nemanki idan kuma sun mutu Allah zai basu lada sanadiyyanki”
lumshe ido tayi “nima a ƴan kwanakin da nayi da kai na gane kai mutumin kirki ne, ka bani shawara nayi amfani dashi kuma naji daɗi, duk gold ɗin da zinare na kai bank, sannan na tara kuɗin na ajiye a account zanyi ginin makaranta da islamiya, dan Allah idan ka koma karka manta dani”
yau zai tafi shiyasa yake jinshi ba daɗi, baiso tafiya ya barta ba, haka kawai take bashi tausayi ta sadaukar da ranta akan yara marayu duk da itama tana bukatar taimako a matsayinta na marainiya, hakan yasa ya rufa mata asiri gefe guda kuma yana missing na Umar da amminshi da Elham, ba zai iya rayuwa babu su ba, gashi kuma yana ji kamar ba zai iya zama ba Amrish ba.
tashi yayi yace “bari naje na shirya” giɗa mishi kai kawai tayi, ya wuce yaje ciki yayi wanka ya shirya cikin kaya me kyau wanda tasa aka siyo mishi, tana zaune a wurin tayi tagumi.
lungu da sako ƴan sanda da sojoji neman Amrish suke, manya waɗanda aka yiwa sata a gida da matan wanda ta kashe duk sun taru sun samu general a gaggauta nemanta, gidan marayu an zagaye da masu tsaro ba shiga ba fita, duk wanda zai shiga sai an bincike shi sosai.
unty safiya ta gagara zama sai safa da marwa take, ganin hoton Amrish da suka nuna na cewar ita suke nema, Innalillahi wa inna ilaihiraji’un shine kalman da take ambata a cikin ranta, wannan wani irin tashin hankali ne? ta yaya zasuce Amrish ce tayi wannan ɓarnan? abin haushi har yanzu bataga Amrish ba, Najma tana kasa tana kuka ko kallonta batayi ba, tashin hankalin da take ciki kaɗai ya isheta.
Yayi shiri tsab yace “zan wuce gida da fatan kin yafewa ɗan uwana laifin daya aikata?”
Murmushi tayi “yaci albarkacin ka na yafe mishi”
“mu fara zuwa gidan marayu sannan na wuce inason yin magana da shugaban gidan”
gida kai tayi “ba komai ai sai muje”
tashi tayi ta rufe gidan sannan ta shiga mota ya kalleta “ke zaki jamu ai ko?”
“a,a gaskiya kayi nauyi saide kai ka jamu”
murmushi yayi ya fara driving suka bar gidan, kasancewar motansu tinted ne saide su hango na waje amma ba za’a iya ganin na ciki ba.
har suka isa gidan marayu tin daga bakin titi suka hango sojoji da polisawa sunyi arresting gidan kowa yayi ready da bindiga a hannu.
gaban Amrish ne ya faɗi manyan idanunta ta waro waje tana mishi kallo, kallo irin na tuhuma da tambaya, ɗaga kafaɗa yayi shima yana kallonta yace “bansan komai ba”
“dama kace muzo nan ne dan ka miƙani hannun ƴan sanda?”
“A,a wallahi ba haka bane ni bansan da zamansu bama”
hawayene ya cika mata ido “mutane baku da amana kuna son kanku dayawa kenan tuggu ka haɗamin Faruk?”
“ki yadda dani bansan komai ba”
“ta yaya zan yadda da kai?”
“ta haka”
yayi magana yana shirin tada motan su gudu, hannu tasa akan hannunshi tana kallonshi da Jajayen idanunta bata ce komai ba ta ɗaura dogayen yatsunta akan mabuɗin motan buɗewa tayi tana shirin fita ya riko hannunta “kada kiyi haka Amrish ki dawo”
“babu amfanin dawowata da haɗin bakinka akayi hakan”
fita tayi daga motan ta ɗaga hannunta sama alaman ta miƙa kanta, ƴan sanda da suke tsaye a wurin suka fara zuwa inda take, ganin ta miƙa kanta ba wani gardama suka sa mata ankwa.
ɗaya daga cikin matan Alhaji Hamza tazo gabanta ta rinka sauke mata mari a fuska, saida fuskan yayi jajur sannan ta fara tureta tana cewa “muguwa kina mace kike wannan muguntan kin kashe iyayen wasu dan bakisan amfanin iyaye ba, naki iyayen sun watsar dake a titi shiyasa kike jin haushin iyayen wasu dan suna kula da ƴaƴansu? dan baki taɓa haihuwa bane kuma ba zaki taɓa haihuwa ba da yaddan Allah”
Amrish kanta a kasa har mayafin kanta ya fita ya rage batada ɗan kwali, gashinta da yake cikin ribbon a atake ya bazo fuskarta.
jin kalaman da matan take yaɓa mata ta ɗago Jajayen idanunta tace “shi mijin naki daya haihu yasan zafin haihuwa ne? da ya sani da bai rinƙa luwaɗi da yaran mutane ba…”
ɗan sandan ne ya wanketa da mari saida ta faɗi kan gwiwanta, gashinta ya rufe mata fuska ta dukar da kai kasa bata kuma ɗagowa ba, caraf a kunnen Unty sadiya, dama sun firfito waje jin an kama amrish.
da gudu taje wurin ta ɗago fuskan Amrish ta wanketa da wasu zafafan maruka cikin kuka ta durkusa kasa tace “me kikayi Amrish? me kika yiwa rayuwarki? da kin hakura aje gaban Allah zaiyi mana sakayya meyasa zakiyi haka Amrish? meyasa?”
batayi magana ba kanta a kasa har yanzu sai zafafan hawaye da suke zubo mata, ɗan sandan yace “tashi munafuka mota zamu saki”
Faruk yana cikin mota yana ganin duk abinda yake faruwa, ganin suna dukanta ya buɗe motan ya fito zaiyi magana ya tsinkayo muryan Umar yana cewa “dakata Officer”
tsayawa tayi cak jin muryanshi dana tana dab da shiga motan ƴan sandan, ganin kayan dake jikinshi ta gane wannan ba faruk bane Umar ne, yana karasowa ya wanke fuskarta da maruka guda huɗu a jere, saida gefen bakinta ya fitar da jini, cikin zafin rai yace “kinyi tunanin asirinki ba zai tonu bane? kinyi kuskure da kika shiga gonata kin sace ɗan uwana kina tunanin zan kyaleki ne? no Ameera kike ko Amrish whatever, kafin nan da karfe shida na yamma inason ganin ɗan uwana a gida”
dariya tayi tana kallonshi, saida tayi me isanta suna kallonta tace “ɗan uwanka? sojan kake nufi? dan kai ba soja bane kafi kama da doctor, amma ba sai an kai karfe 6 ba yanzu zaka ganshi idan ka juya bayanka”.
juyawa yayi yana kallon bayanshi da mamaki ya hango Faruk tsaye yana kallon komai, wani irin gudu yayi yaje gaban Faruk ya rungumeshi yana tambayan “ba abinda ya sameka?”
shiru Faruk yayi bai bashi amsa ba hankalinshi yana kan Amrish ɗagowa yayi yana kallonshi ganin ita yake kallo yace “kai Faruk? nine fa Umar naka meyasa baka kallona?”
a hankali ya dawo da idonshi kan Umar ɗin yace “meyasa ka tona abinda na ɓoye da hannuna?”
Amrish ta kalli ɗan sandan da yake tsare da ita tace “ba ni kaɗai nakeyin aikin ba akwai me taimaka min”.
“wanene?”
da hannu ta nuna Umar wanda yake cikin kakin sojoji, tace “shine yake taimaka min, shine yake ɓoye duk wani laifin da nayi, ya gane nina kashe Alhaji Hamza amma bai faɗawa kowa ba saboda ina bashi kaso me tsoka a cikin kuɗin da nake samu, captain Faruk shi yake taimaka min”
kiran wayan general akayi dan babu wanda ya isa ya kamashi a wurin, genaral da kanshi yazo jin abinda ta faɗa ya kalli Umar wanda ya daskare a tsaye yana mamakin sharrin data kulla mishi yace “You Are under arrest”
da sauri Faruk ya mika hannunshi yace “nine faruk wannan Umar ne”
kallonshi genaral yayi sannan yayi dariya yace “Faruk shine soja kuma shine da uniform yanzu, bai daɗeda barin office ba sabida haka baka isa ka juyamin hankali ba”
ankwa akasa a hannun Umar Faruk yana bin bayansu yana cewa “nine faruk ku rabu da ɗan uwana”
a motan da kasa Amrish a ciki aka sashi nan suka kama hanyan cell, Amrish tana kallonshi tana murmushi.
_08144818849_