Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 3

Sponsored Links

🌸 *HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

Jiddah S Mapi

 

 

*Chapter 3*

 

 

 

~Amrish ta shiga damuwa akan wannan maganan kullum tunani take tana kuka sa ido akan shige da ficen yaran, bata bari su raÉ“i kowa sai ita bata barinsu su zauna su kaÉ—ai koda yaushe tana tare dasu, yau ba school tasa kowa a gaba tana yimusu lesson, suna fahimta sosai da sosai, sai dariya suke burinta tasa yaran cikin farin ciki kada suyi kewan iyayensu, a gefen É—akinsu suke zaune anan take musu lesson É—in domin ita Allah ya bata ilimi bata samu me tsaya mata tayi karatu bane, aikawa akayi a kirata, a hankali ta mike jikinta a mace tacewa yaran bari taje ta dawo, tana zuwa office taga manyan mutane ciki harda shugaba wacce ta zuba mata ido tana kallonta, Æ™arasawa tayi ta zauna a gefe ta gaishesu, Amsawa sukayi É—ayan yace “ke É—ago kai ki kalleni”

a hankali ta É—ago ta kalleshi idanunshi jajaye gashi baÆ™i dashi, yayi dariyan mugunta yace “kece kika hana a É—auki yara?”

cikin storo da rawan jiki tace “eh”

daka mata tsawa yayi “zaki buÉ—e baki kimin magana ne ko saina saÉ“a miki mara mutunci kawai”

 

Da karfi tace “eh nice”

 

“kenan wuyanki ya isa yanka, tunda kika tashi a cikin gidannan kece kike É—aukan É—awainiyan kanki?”

girgiza kai tayi cikin tsoro, yace jeki kawomin maza guda biyu yanzu zan nuna miki na fiki taurin kai, gabanta yana faÉ—uwa tace “kayi hakuri bazan iya É—aukosu na kawosu da hannuna ba, idan nayi haka bazan taÉ“a yafewa kaina ba”

 

kallon juna sukayi su duka uku da suke zaune a wajen, shugaba ta kaÉ—a kai alaman dama ai na gaya muku tana da taurin kai, murmushi yayi irin na mugaye kafin yace “to ki zaÉ“i É—aya, ko ki kawo guda uku ko kuma mu muje mu É—ibo guda goma”

a tsorace tace “zan kawo su”

jikinta yana rawa ta mike, tana jinsu suna cewa “marasa galihu kun samu ma zamu taimaka muku shine zakice bakwaso mu muke ciyar daku mu muke baku sutura kuma ku watsa mana kasa a ido”

 

fita tayi daga office É—in har wani jiri yana shirin É—ibanta, kanta taji yayi nauyi ta rasa ta ina zata fara, gaba É—aya jikinta ya mata nauyi, hawaye ma nema tayi ta rasa, a hankali take takawa har ta isa inda take musu lesson, Na’eem ne ya kalleta yace “Unty Amrish kin tafi kin barmu baki dawo da wuri ba”

 

Wasu zafafan hawayene suka cika mata idanu, ji tayi kanta yana cigaba da sarawa, a hankali tasa hannu ta share hawayen dake shirin sauka daga idanunta, zama tayi a gefe ta rasa ta inda zata fara, Ahmad ya matso ya rungumeta yace “Unty meya sameki?”

fashewa tayi da kuka me tsuma zuciya, tare sukazo su duka suna share mata hawayen

“ki daina kuka Unty bamaso kina kuka”

 

share hawaye tayi tace “kun san me?”

girgiza kai sukayi, cikin kunan rai tace “kuyi rige rigen zuwa office na shugaba duk mutane uku da suka riga shiga sune first, wanda basu shiga ba kuma saisu dawo zan kara yi musu wani kunji?”

 

Da ihu sukace “yes zamuyi”

kallonsu tayi tace “Aisha banda mata maza kawai”

matan suka koma gefe, mazan kuma suka jeru su goma sukayi haÉ—a kafa waje É—aya nan ta fara kirga musu 1.2.3 cikin kuka sosai tace “go”

da gudu suka bar wajen suna rige-rigen shiga office É—in, kifa kanta tayi a kasa ta fara wani irin kuka me tsuma zuciya, da ihu Ahmad yace “wayyo unty bamu ci ba”

hankali a tashe ta É—ago tace “wa suka shiga?”

 

“su na’eem ne dasu Aliyu”

wani irin bugawa taji kirjinta yana yi, Innalillahi wa inna ilaihiraji’un shikenan Na’eem ya faÉ—a hannunsu gashi babu inda zata kai kara a karÉ“a mata”

 

kallon yaran tayi tace “ku shiga É—aki lokacin break ne”

shiga sukayi ita kuma taje bakin Office É—in ta tsaya jikinta yana É“ari, shugaba ta fito ta tafi ta barsu da yaran a ciki,

jim kaÉ—an ta jiyo ihun na’eem yana kiran sunanta, hannu ta dunkule tana kuka sosai, kusan 30mins kafin taji yaran sunyi shiru, su kuma mutanen suka fito suna murmushi, kallonta sukayi su duka suka ciro kuÉ—aÉ—e masu yawa “gashi ki kaisu hospital a dubasu”

bata karɓi kuɗin ba sai zubewa tayi akan gwiwanta tana cigaba da kuka, watsa mata sukayi kafin suka juya suka tafi.

 

tashi tayi ta shiga É—akin jikinta a mugun sanyaye, da kyar take iya É—aga kafarta, kwance ta gansu basa ko motsi ga jini daya É“ata wajen sosai, Æ™arasawa tayi da gudu ta rungumesu tana kuka, babu wanda yake motsi a cikinsu, cikin tashin hankali ta fita da gudu ta kira su zainab dasu umman manal, suna tambaya meya faru hanyan Office kawai take nuna musu, da gudu suka shiga ganin yara kwance a cikin jini suka fara tambaya meya faru? bata iya tace komai ba dan tana gudun abinda zaije ya dawo, É—agasu sukayi aka kira me adaidaita sahu suka sa yaran a ciki, a tare da ita dasu zainab É—in suka kaisu asibiti mafi sauki wato general, suna zuwa doctor sukace ba zasu karÉ“esu ba saida police, zubewa kasa Amrish tayi ta rike Æ™afan likitan tace “dan Allah ka taimaka ba dan halinmu ba ka dubasu”

ciro kuÉ—in data kwaso daga kasa wanda suka watsa mata tayi ta mika mishi “gashi dan Allah shine iya kuÉ—in dake hannunmu ka taimaka mana mu marayu ne”

 

karÉ“an kuÉ—in yayi ya irga kafin yace “gaskiya wannan kuÉ—in ba zaiyi komai ba hajiya ku fitamin da wannan yaran anan, kuna ina har kuka bari akayi musu wannan lahanin? yanzu ko kashi bazasu iya rikewa ba”

watsa mata kuÉ—in yayi tana zaune daram a kasa ta gagara tashi, gaba É—aya ta kasa motsi, zainab da Umman manal ba abinda suke yi sai kuka, Amrish ta mike batayi magana ba ta É—au Na’eem zainab ta É—au Aliyu sai Umman manal ta É—auki Hafiz, fita sukayi dasu daga asibitin suka kuma kama napep suka shiga, asibiti me É—an sauki sukace ya kaisu, ya kaisu kofan wani hospital me kyau, fita sukayi suka biyashi kuÉ—i yace kuÉ—in yayi kaÉ—an, saida Amrish ta kara mishi kafin ya karÉ“a suka shiga ciki.

 

kati suka yanka na ganin likita, saida suka É—an jima kafin akace mutum É—aya ta shiga, Amrish ce ta shiga domin ganin likita, tana zama yace “meya samu yaran?”

 

Tace “yawo sukaje shine aka dawo mana dasu haka, ka taimaka ka duba mana su dan Allah kada su mutu”

murmushi yayi yana daga zaune akan kujeranshi me jujjuyawa yace “calm down zan dubasu zasu samu lafiya amma ni kuma me zaki bani?”

da mamaki ta kalleshi cikin rashin gane me yake nufi tace “ga kuÉ—in da yake hannuna kayi hakuri dashi”

 

dariya yayi ya mike ya matso kusa da ita yana shirin taÉ“a ta ta buge hannunshi tace “me kake nufi?”

 

“Ohhh Baby girl haka kawai zan taimaka miki ba tareda nima kin taimaka min ba? sau É—aya kawai zamuyi saina dubasu idan kuma baki amince ba saiku barmin hospital”

a firgice ta É—ago dara daran idanunta wanda suka sauya kala daga fari tass izuwa jawur ta kalleshi, durkusawa tayi kasa ta haÉ—a hannayenta biyu tace “dan Allah dan Annabi ka taimaka mana”

komawa yayi ya zauna “idan kin shirya sai kizo”

 

turo kofan akayi da karfi, ganin zainab ce ta mike da gudu taje ta rungumeta tana kuka tace “zainab ki tayani rokonshi”

janyeta zainab tayi daga jikinta tace “kije waje Amrish”

cikin kuka tace “me zakiyi?”

 

“kije waje kawai nace”

a hankali ta juya ta fita zuwa waje, zainab hijabin jikinta ta cire sannan ta fara cire riganta, matsowa tayi kusa dashi, saida ta kwaÉ“e ta zama ba komai ta kwanta a kasa tana kuka tace “kazo kayi amma kasa a dubasu first”

cikin jin daÉ—i ya kira waya yace a dubasu, matsowa yayi kusa da ita ya fara taÉ“a ta, wasu irin zafafan hawaye ne suke bin gefen fuskarta tana jin yadda yake taÉ“a jikinta, kashe wutan office É—in yayi daga nan ya fara shiga jikinta, wani irin azaban zafi takeji saide batace komai ba, saida ya shiga jikinta ya rinÆ™a yin yadda yaso da ita, ya kai 20mins yana abu É—aya kafin ya mike yace “good girl you’re so sweet”

lumshe idanu tayi tanajin raÉ—aÉ—i haka har ta maida kayan jikinta, a hankali ta tashi ta fita daga office É—in.

 

an bawa su Na’eem gado su Amrish ne a kansu bata wani kula da zainab ba hankalinta akan su Na’eem É—in, Umman manal tana gefe tana bawa Aliyu ruwa, saide yaki karba sai shure-shure kawai yake, ganin ya sanÆ™are yana kiran Unty Amrish tayi ihu ta kira Amrish da gudu tazo tana kiran sunanshi “Aliyu?”

hannunta ya riko yana É“arin jiki har ranshi ya fita, time É—in zainab ta turo kofa ta shigo da kyar take takawa tana cije baki, jin suna kuka likita ya duba yace “ya mutu”

 

Kuka sukayi, Na’eem ma bai jima ba ya rasu, mutum É—aya ne ya rage shine Hafiz Shima rai a hannun Allah, a hospital É—in akaje wajen binne gawa aka binne su, Hafiz kuma suna bashi allurai har yayi bacci.

 

suna zaune su duka sunyi shiru babu me magana cikinsu, Amrish ce ta lura da yanayin Zainab tace “kina lafiya kuwa? me kika gaya mishi har ya yadda ya duba yaran?”

 

kallon Amrish tayi idanunta pal hawaye cikin muryan kuka tace “amfani yayi dani”

 

“what!!!?”

suka faÉ—a a tare, cikin kuka tace “kwarai nayi haka ne domin na taimaki rayuwan su Na’eem gashi kuma sun mutu”

kwantar da kanta tayi a jikin Amrish tana kuka me tsuma zuciya, da karfi Amrish tace “meyasa kika yadda dashi? nice ya kamata nayi wannan sadaukarwar ba ke ba zainab meyasa?”

 

umman manal ba abinda take iya faÉ—a sai kuka, haka har aka sallami Hafiz ba laifi jikin yayi sauki, su sukayi jinyan zainab har ta warke suka koma gida.

 

Amrish tana jin tambayoyin da yaran suke aika mata ta kasa amsa koda É—aya ne, suna tambaya ina Na’eem da Aliyu tace “sun koma gidansu na asali”

basu fahimta ba sukace “muma yaushe zamu koma?”

cikin hawaye tace “sai ranan da Allah ya kiraku”

 

daɗi sukaje dan ance zasu koma asalin gidansu, raɓewa tayi a gefe tana kuka harda toshe bakinta dan bataso kowa yasan tana kuka.

 

 

 

_*littafina na kuɗi ne ki biya kafin ki karanta ₦400 ne kacal 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo evidence of payment ta nan 08144818849, masu kati kuma zaku iya turo mtn ta numbern dana ajiye*_

 

*Na sadaukar da wannan littafin wa gidauniyar ORPHANS AND NEEDIES CARE FOUNDATION, wato kungiyan marayu da mabuƙata, ga duk wanda yake da niyyan taimakawa sai yayi magana wa wannan number 09031299157, mu taimakawa marayu Allah zai bamu lada, idan anyi magana zata baku account number Allah ya sakawa masu taimako Ameen*

Leave a Reply

Back to top button