Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 13

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 13*

 

 

 

“Ɗaukanta tayi suka fita ta goyata tana bin cikin gidan da kallo, yanzu pompo ne ba bohold ba ruwa ya wadaci kowa murmushi takeyi ita kaɗai domin taji daɗi sosai data kawo sauyi a gidan.

 

har dare yayi tayi bacci a gidan da safe ya shirya zata fita taji zancen za’ayi ɓaki fasa fita tayi domin tanaso taga suwaye ne bakin, sai kusan karfe 2 na rana Ammi da Umar suka karaso kofan gidan marayu, kayan abinci masu yawa suka zuba a bayan mota dan basason nuna bincike sukazo, shiga da kayan abincin me gadi ya fara, Amrish tana daga zaune akan kujera tana leƙe so take taga su waye zasu shigo, ganin kayan abinci taji ranta yayi sanyi koba komai an fara kula da gidan marayun.

 

saida ya gama shigo da tulin kayan ya jibge a kofan office na babban mace wace aka ɗaura a matsayin shugaba na yanzu, Ammi ce ta fara shigowa tasha leshi baki da da mayafi fari sai farin glass data sa a idonta sai murmushi take hakorin makkan dake bakinta yana sheƙi ido huɗu sukayi da Amrish murmushi tayi mata kafin ta ɗaga mata hannu alama tazo ta amshi jarkan man dake hannunta tayi mata iso zuwa office na shugaba, tashi tayi itama fuskarta da murmushi taje ta ɗan duƙa kafin tace “ina wuni?”

 

“Lafiya kalau”

karɓan jarkan tayi ta shiga cikin office bakinta ɗauke da sallama, matar da take matsayin shugaba yanzu itace Hajiya zainab uwar marayu, tayi karatu sosai ta fannin addini tasan haram ta san halal kuma bata take sani, gaisheta Amrish tayi cikin girmamawa ta amsa tana tambayan waya aiko jarkan mai? sallaman Ammi ne ya hanata bada amsa Ammi tana murmushi ta zauna tace “barka da warhaka”

Amrish ta juya zata fita Ammi tace “na gode ƴata”

wani irin daɗi taji har cikin ranta dan bata taɓa jin wannan kalman a bakin mutum ba, saide taji ana faɗawa wasu amma ba ita ba, juyowa tayi ta kalli Ammi idonta cike da hawaye kafin tayi murmushi ta fita daga office ɗin, fara shigar da kayan abincin sukayi itada megadi, taje ajiye buhun gishiri a gefen shugaba taji muryanshi yana cewa “Ammi ai na tsaya amsa call ne shiyasa ban shigo ba”

 

gabanta ne ya faɗi jin muryan Faruk, a hankali ta durkusa kasa ta ɓoye fuskanta ta bayan shugaba, gabanta ne ya kuma faɗuwa jin Ammi tace “ba komai ai Umar”

 

“Innalillahi wa inna ilaihiraji’un yaushe ya fito daga gidan dana ɓoyeshi? na shiga uku na lalace shikenan sun kawo karata gidan nan”

 

kin ɗago kai tayi sai ɓoye fuska take ta bayan kujera, a hankali ta leƙa tana kallonshi ta ɓulin kujeran, baya tayi ta haɗa kanta da bango tanajin bugun zuciyanta yana karuwa, tabbas Faruk ne, kenan ya gudu?.

 

Shugaba ta lura da ita tace “ya dai? ba lafiya ne?”

shiru tayi batace komai ba, hijabin ta janyo har idonta ta rufe fuskanta kafin ta mike cikin rawan jiki da ɓoye fuska ta fita daga offic ɗin, binta Ammi tayi da ido tana murmushi tace “kunya takeji ko mai?”

 

Dariya kawai shugaba tayi tace “wannan yarinyar haka take halin yara gareta kinsan itace take kula dasu”

 

murmushi ammi tayi tace “tanada kirki sosai”

Amrish bayan ta fita ta manne da jikin bango tana haƙi, zaro ido tayi tana jin yadda kirjinta yake dukan uku-uku, dafe kirji tayi tana lumshe ido Allah yasa bai ganeta ba, ya zama dole ta ruga da gudu tabar gidannan har sai sun tafi, wani ɓangaren na zuciyarta yace ta kira getman na gidan can ta tambaye shi ya akayi har ya bari Faruk ya gudu?

 

waya ta ciro daga bakin skirt nata kira tayi ya ɗaga cikin tsoro tace “ina wanda na baku ajiya?”

“Hajiya yana nan a inda yake”

 

“kaje ka duba ya gudu”

da gudu ya shiga ɗakin yaga Faruk kwance yana rawan sanyi, da mamakinta taji yace “gashi nan hajiya yana nan”

 

“samin wayan naji numfashin shi”

kai wayan yayi zuwa bakin faruk jin sautin numfashin shi taji gabanta ya kuma faɗuwa, kashe wayan tayi tace “to waye wannan?”

 

taji kuma Amminshi tace Umar wancan ma Umar faruk ne meke faruwa?”

 

Jingina tayi da jikin bangon office ɗin tana son jiyo abinda suke tattaunawa, bata jiyo komai gashi kuma bakinsu yana motsi, lumshe ido tayi ta zauna a gefe tana jiran fitowansu, sun jima suna magana da shugaba sannan suka fito yana rike da hannun Amminshi, kallonsu tayi har suka shiga mota, ba ɓata lokaci ta tari taxi tace yabi mata bayan motansu zata biyashi ko nawa yake so, shiga tayi suka fara bin bayansu ba tareda sun sani ba, ganin kofan gidan da suka tsaya aka buɗe musu ta gane wannan shine gidansu.

 

ta bari sun shiga sannan ta fito ta biya me taxi kuɗi me yawa, me gadi ta samu tace “sannu baba”

 

“yawwa”

 

“dan Allah tambaya nakeson yi baba”

 

“Ina jinki ƴata”

 

“shin wannan da suka shiga gida yanzu suna cikin wani damuwa ne? naga sun kusa bugeni amma hankalinsu baya kansu”

 

kallonta yayi sannan fuskarshi ya zama alaman tausayi yace “Allah sarki ɗayanshi ne ya ɓata ba’a ganshi ba har yau, kiyi hakuri suna cikin wani hali ne shiyasa”

 

“Allah sarki baba to wanne ne ya ɓata a cikinsu naji ta kirashi da Umar?”

 

“eh to abinda ban sani ba shine ko Umar ɗinne ya ɓata ko faruk ne Allahu a’alamu domin ko ita uwar tasu bata ganesu sai tayi da gaske”

 

“tom baba na gode”

 

 

kuɗi ta ciro ta bashi tace ya siyi goro, yana godiya ya amsa tace amma shi wannan ɗin wani aiki yakeyi?”

 

“eh to shi umar shine doctor shikuma Faruk shine Soja”

 

godiya tayi tabar wurin, zuciyarta a cakushe yake ta rasa meke faruwa to wanene a wurinta? umar ko faruk?”

 

Ɓangaren Umar ya kalli Ammi yace “Ammi kada mu nunawa mutane Faruk ne ya ɓata ace nine na bata wato Faruk, daga gobe zan fara sa kayan soja inje har wurin aikinshi da haka zamu gudanar da bincike wanda suka saceshi idan sunji cewar Umar suka sace zasu sakeshi su fara neman faruk”

 

kallonshi Ammi tayi “baka ganin wannan risk ne? kada ka faɗa hannunsu kaima basu saki faruk ba su kama ka?”

 

“no zanyi taka tsan tsan ai sakinshi mukeso suyi ko?”

 

giɗa kai tayi yace “daga gobe zan fara fita a matsayin faruk” waya ya ɗaga ya kira numbern Kamal yace “duk wanda yazo nemana kace an kwana biyu ba’a ganni ba wannan ya zama sirri tsakanina da kai”

 

“haba Umar sirrinka ai sirrina ne”

 

“na gode kamal”

kashe wayan yayi da niyyan gobe zai fara fita a matsayin faruk, dafa Ammi yayi wacce ta lula cikin tunani kwana uku har ta rame, yaƙe kawai takeyi zuciyarta ba daɗi.

 

Amrish a firgice ta shiga taxi ya kaita gidanta tana shiga babu ko sallama ta faɗa ɗakin da yake, ganinshi a kwance yasa taji ranta yayi sanyi ta zata wasa da hankali yake mata irin wanda tayi mishi.

 

ido ya zuba mata ta ɗagoshi ta jingina kanshi da jikin bango kallon cikin idonshi tayi tace “kaine Umar ko kaine Faruk?”

 

“nine umar kuma nine faruk”

 

wani irin mari ta ɗaukeshi dashi saida gefen bakinshi ya fashe cikin masifa da zafin rai tace “kaine umar ko kaine faruk?”

 

“kece Amrish ko kece Ameera?”

 

wani marin ta kuma ɗaukeshi dashi tace “duka biyu nice, nice Amrish kuma nice Ameera”

 

“to nima duka biyu nine, nine umar kuma nine faruk”

 

ranta ne yayi wani mugun ɓaci ta nunashi da yatsa tace “idan baka faɗamin gaskiya ba saina kashe wancan”

 

murmushi yayi wanda bata taɓa ganin yayi irinshi ba sannan ya ɗago kai ya kalleta kallo irin na gargaɗi yace “babba kuskuren da zakiyi a rayuwa shine taɓamin ɗan uwa, duk abinda zakiyi kiyi akaina idan kika taɓamin ɗan uwa zaki gwammace ba’a kawoki duniya ba, bama zama marainiya ba haifanki kaɗai sai kinyi dana sanin yinshi da akayi”

 

cikin zafin rai tayi ball da cup ɗin dake gefenshi saida cup ɗin ya tarwatse ta ɗau glass ɗaya daga cikin wanda ya fashe ta yanka gefen kafarshi, ko gezau baiyi ba sai cije leɓe da yayi.

 

matsowa tayi kusa dashi tace “idan kanaso ya tsira saika faɗamin kai waye ne? umar ne ko faruk?”

 

“nine umar”

 

tashi tayi zata tafi yace “kuma nine faruk”

tsayawa tayi cak tanaji kaman ta daɓa mishi wuƙa ya mutu kawai ta huta, a zafafe ta fita daga ɗakin, murmushin gefen baki yayi cikin ranshi yace “zaki tafka babban kuskure”.

 

 

 

_hauwa shu’aibu jiddah 08144818849_

Leave a Reply

Back to top button