Hamshakiya 25
*🌸HAMSHAƘIYA*🌸
Na
_Jiddah Shu’aibu_
*Chapter 25*
“Sunana hamshaƙiya Ameera don’t ever call me Amrish, kinaji?”
giɗa kai tayi cikin tsoro dan wannan akwai masifa saɓanin Amrish da take da sanyi, da hannu ta yiwa excort alama daya mika mata kuɗin da suka zo dashi, miƙa mata yayi kuɗine me yawa a cikin jaka, buɗewa tayi fuska ba annuri tace “manya su koma gefe yara su koma gefe”
bin umarninta sukayi unty sadiya sai rarraba ido take tana kallon Ameera sai yanzu ta gano wannan akwai tabo a gefen hancinta ita kuma Amrish fuskarta ba tabo.
wasu kuɗade ta fara irgawa da taimakon shugaba tafara basu naira dubu ɗari ɗari, yara ƙanana kuma ta bawa shugaba kuɗin tace a nemo waɗanda suka iya koyar da sana’a a biyasu suzo su koyawa yaran, kallon Ahmad tayi wanda ya zuba mata ido yanason yimata magana amma yana tsoro, hannu ta ɗaga ta yaficoshi, matsowa yayi a tsorace dan yaga tsawan da tayiwa umman Najma shiyasa bai matso dab itaba ya tsaya a gefe, murmushi tayi ta ɗan durkuso tace “ya sunanka?”
“Ahmad” ya faɗa murya a rarrabe, murmushi ta kumayi sannan ta ciro kuɗaɗe masu yawa ta fara basu dubu dubu a hannunsu, godiya sukayi suna murna harda tsalle, murmushi kawai tayi aka kawo kwalin sweet da biskit ta rarraba musu tana ganin yadda suka rungume juna suna tsalle.
hawaye ya cika mata ido da sauri ta sauke glass ɗin ta rufe idonta, saida ta gama suka shiga office da shugaba duk inda zataje excort ɗin suna biye da ita, a kofan office suka tsaya sun hana kowa shiga ciki.
zama tayi a kujeran da shugaba ta nuna mata sannan ta cire glass na idonta cikin girmamawa tace “ina wuni?”
“Ameera kina lafiya?”
“lafiya kalau”
“dama wani alfarma nake nema a wurinki hajiya Halima”
“ina jinki Ameera wani alfarma ne haka?”
“inaso duk ranan jumma’a zan rinƙa kawo ziyara gidannan daga nan idan na saba dasu zaki bani wasu daga cikinsu su koma gidana karkashin kulawata”
“ba komai hakan ba zai zama matsala ba tunda an sanki a gari kowa ya shaida bakida wani mugun hali”
murmushin jin daɗi tayi sannan tace “na gode shugaba hajiya Halima”
tashi tayi ta fita daga office ɗin, tafiya ta fara aka buɗe mata kofa ta fita daga gidan.
a mota ta cire glass ɗin ta haɗa kanta da jikin kujeran mota ta fara raira kuka, duk lokacin data ziyarci gidan marayu sai tayi kuka kamar ranta zai fita, tayi missing nasu ba kaɗan ba, goslow yayi yawa a hanya shiyasa motan ya tsaya suna jira saura su wuce sannan suma su wuce, ɗagowa tayi tana zaro tussue zata share hawayen dake fuskanta.
hankalinta ne ya koma kan wani mota, wata yarinya ce budurwa zata kai shekara 17 tana zaune a motan tana kuka shi kuma mutumin dake gefe yanata shafa jikinta yana murmushi, sai bige hannunshi take yana juyo da ita, Amrish tana gani ya haɗa bakinshi dana yarinyar sai kiciniyar kwace kanta take da sauri ya ɗaga glass ɗin motar, gabanta ne ya faɗi me yake mata? mijinta ne? ganin motan ya wuce tayi sauri tacewa driver “bimin wancan motar”
babu ɓata lokaci ya fara bin bayan motan ba tareda yayi gudu ba dan kada su gane yana binsu, ba karamin tafiya sukayi ba sannan suka isa wani unguwa wanda babu mutane dayawa a cikinsa, ganin motan ta tsaya a kofar wani katafaren gida itama Amrish tace su tsaya daga gefe, tsayawa sukayi aka buɗewa meshi get suka shiga, megadi be rufe kofa da wuri ba Amrish tana iya hango yadda mutumin ya fito hannunshi rike dana yarinyar tana kuka har suka shige ciki.
fita tayi daga motan tasa glass nata da facemask sannan ta karasa wurin megadi wanda yake shirin rufe kofan tace “sannu Baba”
dakatawa yayi yac “yawwa ƴata”
kuɗi ta ciro daga aljihun wandonta ta mika mishi, karba yayi yace “nagode”
kallonshi tayi tace “ba haka kurun na baka ba inason sanin wani abu ne wanda na gani yanzu”
“to hajiya me kikeson ji?”
“wannan mutumin daya shiga ciki shin matarshi ce suke tare?”
“A,a ƴar kaninshi ne wanda ya daɗe da mutuwa kullum yana zuwa gidannan da ita kamar yarinyar bataso amma haka naga yana yimata kaman dolene ya shiga ciki da ita watarana ma anan suke kwana”
“kana ganin yau zasu kwana anan?”
“eh to banida tabbaci amma mafi yawan lokuta yana kwana da ita anan kinsan shi matafiyine yana zuwa kasashen waje to idan ya dawo shine yake zuwa da ita anan, ƴar kaninshi ce”
“nagide Baba”
juyawa tayi ranta yana tafasa, kirjinta kamar ya faso fili tsaban zafi da kuna, ƴar kaninshi? kenan ma marainiya ce yake zina da ita?”
shiga mota tayi suka tafi, dunƙule hannu ta rinkayi tanaji kaman ta koma ta kasheshi ko zataji sauki a ranta.
suna isa gida bata jira sun buɗe mata mota ba ta buɗe ta fita, cikin zafin rai take tafiya bata tsaya ko ina ba sai cikin ɗakin data ɓoye kayanta wanda ta jima batayi amfani dashi ba, a karkashin gado ta durkusa ta ciro, sannan ta zauna a gefe ta ajiye kayan a gabanta, hawaye ya fara wanke mata fuska a hankali tasa hannu ta ɗago kayan cikin muryan kuka tace “mutane kune kuke bada babban gudumawa wurin aikata abinda babu kyau a rayuwar mutum, ka duba ka gani wannan yarinyar marainiya ce kanin mahaifinta yake aikata abinda babu kyau da ita ta yaya zan iya kyale wannan mutumin yaci gaba da rayuwa?”
ajiye kayan tayi sannan ta kwantar da kanta akai, hawaye yana sauka daga idonta yana bin kayan, cire takalmin kafarta me tsini tayi sannan ta mike tabar ɗakin, ɗakinta ta faɗa tana cigaba da tunanin yadda zatayi da wannan mugun mutumin.
da zafin zuciya har takai dare tana zaune a wuri ɗaya kasancewar bata salla shiyasa ko mikewa batayi ba, sai tsakan dare ta kwaɓe kayan dake jikinta ta koma ɗakin data bar kayan can tasa a jikinta, wukanta wanda ta ɓoye shi ta ciro tasa a waist nata daga nan ta fita taje compound, mota ta shiga tana kallon agogo karfe 1 na dare kunna motan tayi bayan ta buɗe get da kanta, a hankali ta fita daga gidan, tuki take cikin nutsuwa tana sharan hawaye, babu kowa a hanya ita kaɗai take tafiya addu’a take Allah kada ya haɗata da ƴan patrol, tayi sa’a kuma bata haɗu da ƴan patrol ba har ta isa kofan gidan daga nesa ta ajiye motarta sannan ta fito da kafa ta fara takawa har ta isa kofan gidan.
Getman yana bacci ta tsallaka shi ta wuce, ta saman katanga ta haura domin akwai kofa tsakanin megadi da cikin gida, kai tsaye ta nufi inda taga kamar shine palour, buɗewa tayi ta shiga, ganin falon ya jika da kuɗi ta lumshe ido ta karasa bedroom, a rufe, mannuwa tayi da jikin bango sannan ta fara knocking, yana daga kwance yaji ana knocking cikin muryan bacci yace “waye?”
batayi magana ba sai kara knocking take, a hankali ya mike yazo ya buɗe kofan, tana daga tsaye a gabanshi tana mishi murmushi, kallonta yayi daga sama har kasa yace “wacece ke?”
“mutuwa”
amsan data bashi, dariya yayi kaɗan yace “a hakan?”
“kana mamaki ne?”
hannu yasa zai rufe kofan ta rike gam, kallonta ya kumayi yace “daga ina kike?”
“daga mutuwa”
kokarin rufe kofan ya fara da karfi ta tura ta shiga, yarinyar tana kwance a kan gado tana bacci a taƙure, kana ganinta kasan dolene yasa take zaune anan.
wuƙa ta ciro tana shafa jikin ta kalleshi tana murmushi tace “ka taɓa jin labarin Amrish serial killer?”
a halin yanzu ya fara tsorata baya yayi yana kallon yadda take shafa jikin wukan tana murmushi.
“Amrish ta mutu ke ɗin wacece”
“nice Amrish”
Yana ja da baya tana binshi har ya faɗa kan gado, binshi tayi ganin yana sa hannu a sama yanaso ya ciro ko bindiga ne oho, tasa hannu ta ɗau Pillow ta danna kanshi dashi, tureta ya fara ta ɗau wukan zata daɓa mishi ya bugeta da kafa, faɗuwa tayi kasa tana shirin tashi ya ɗau bindiga zai harbeta dashi, yarinyar dake kwance ta ɗau pillow ta bige hannunshi dashi, nan take bindigan ya faɗi, cikin zafin nama yaje zai shaƙeta da karfi Amrish ta shaƙe wuyanshi ta baya, tana ganin wuƙa tasa hannu ta ɗauka, toshe bakinshi Amrish tayi, ɗaga wuƙan yarinyar tayi ta caka mishi a ciki, cirewa tayi ta kara daɓa mishi, tana kuka ta rinƙa caccaka wukan a cikinshi Amrish tana rike dashi har ya mutu, kwantar dashi tayi a kasa ta rufeshi da blanket tana ganin yarinyar ta fara rawan ɗari alaman ta tsorata sosai.
hannunta Amrish ta riko suka fita daga ɗakin, a falo ta ajiyeta ta ɗau roban ruwa da towel ta goge jinin daya ɓata dakin ta ɗau wukan ta mutumin karkashin gado sannan ta fito ta riko hannunta suka fita daga gidan.
_jiddah shu’aibu✍🏻_