Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 12

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 12*

 

 

 

“Matsowa tayi dab dashi tace “Umar Faruk bada sona nake aikata kisa ba, ku mutane kuke kuka sani aikata hakan”

wuyanshi ta matso da wuƙan zata yankashi ta runtse ido hannunta ya fara ɓari, ajiye wuƙan tayi a gefe ta fara kuka me cin rai, ba zata iya kasheshi ba haka kawai taji a jikinta batason ta kasheshi.

 

kallonta yayi “ni mai laifi ne ki hukuntani Amrish”

 

juya mishi baya tayi tana cigaba da kuka kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, saida tayi me isanta kafin ta mike taje tazo da wani igiya dogo fari, ɗaureshi tayi da igiyan ta fita ta barshi a wurin, wayoyinshi ta ɗauka ta kashe tasa a jakanta, fita tayi daga gidan gaba ɗaya ta sanarwa masu aiki a kai mishi abinci idan lokacin cin abinci yayi, sun amsa mata da to.

 

gidan marayu taje bata yiwa kowa magana ba ta faɗa kan gado taci gaba da kuka me tsuma zuciya, saida tayi me isanta kafin ta mike taje ta wanke fuska ta dawo ta zauna.

 

a haka ta kwana ranan da dare ta sawa ranta dole sai tayi mishi hukunci, washe gari dataje gidan batayi mishi magana ba tana kallonshi ya harɗe hannu da kafa yana kallonta, ɗauke kai tayi zuciyan Faruk kaman wuta baison aci amanarshi gashi Amrish taci, tun da fari da bata nuna mishi tana sonshi ba tunda tasan fansa takeso ta ɗauka akanshi yana sonta saide yanzu ji yake bama ya sonta ta rusa mishi plan nashi, a cewarshi itaɗin ƴan biyune sai ya aureta Umar kuma ya auri Ameera ashe abin ba haka yake ba, ɓangare guda kuma yana jin zafin abinda akayi musu a rayuwarsu meyasa Umar zai zama sanadiyyan mutuwan ɗan adam?.

 

saida zata fita tace “kana bukatan wani abu ne?”

 

baiyi magana ba itama bata kuma magana ba ta fita, saida ta fita tace anjima su watsa mishi ruwan sanyi, sun yadda sun amsa da to, ai kuwa haka akayi suka ɗibo ruwa daga frij suka watsa mishi, sanyi ya fara ji amma haka ya daure, zai karɓi duk wani hukunci daga gare ta, baison abinda zai taɓa mishi Umar, ya gommaci shuɗin ya karɓi hukuncin.

 

 

*Ammi*

 

Hankalinta a tashe yake domin kwana biyu kenan babu Faruk babu labarinshi, Umar ne yake kwantar mata da hankali duk da shima ba kwanciyar hankalin ya samu ba, waya yake kira yana tambaya ko an sameshi? amsan duk iri ɗaya ne shine basu ganshi ba har yanzu, ba karamin tashin hankali yake ciki ba saide ganin condition na Ammi ya sashi danne nashi damuwan ya maida hankali a kanta, riketa yayi ya kaita ɗakinta alluran bacci yayi mata dan tunda abin ya faru har yau batayi bacci ba, zama yayi a gefenta yana shafa kanta har tayi bacci, kanshi ya ɗaura a hankali hawaye suka fara wanke mishi fuska, cikin muryan kuka yace “twins bro ɗina bai taɓa barina na kwana biyu ba ko aiki zaije sai mun rinƙa yin video call wannan karon ya tafi ya barni am so lonely”

 

kuka yake sosai gani yake kaman ya rabu da ɗan uwanshi kenan har ƙarshen rayuwa, a hankali ya tashi ya fita daga ɗakin sauka kasa yayi yaga Elham tayi tagumi tana kallon kasa alama itama tana cikin damuwa, a hankali ya karasa wurinta yace “jeki samu Ammi kuyi bacci kafin ku tashi zanje na nemoshi kinji?”

 

giɗa kai tayi kafin ta mike ta haura sama zuwa ɗakin Ammi, kwanciya tayi a gefenta tana kallon fuskanta, hannu tasa a bayanta ta rungumeta kafin ta fara bacci.

 

 

Zama Umar yayi akan sofa ya rasa ta ina zai fara nemanshi, tagumi yayi yana tuno lokacin yaranta Faruk baison ko ɓuyane yayi ya barshi sai kaga ya fara kuka, gashi yau Faruk ɗin da kanshi ya tafi ya barshi baisan wani hali yake ciki ba, yaso da shine ya ɓata ba Faruk ba, tunawa yayi da lokacin yarantansu.

 

 

*Asalinsu*

 

Mutanen Adamawa ne domin mahaifinsu wato Alhaji Ahmad Dikko haifaffen garin ola ne, asalin bafulani ne gaba da baya, acan garin ya haɗu da mahaifiyarsu Salamatu wacce ake kira da Salma, acan sukayi aure Abba yana kasuwanci tun kafin su haɗu da ita yana zuwa har Abuja yana saida motoci da kuma mashin da sauran kayan karafuna, shekara biyu da aure basu samu rabo ba, ganin kasuwanci yana cigaba da tafiya mishi ya tattara ta suka koma Abuja da zama, anan ya kafa kasuwanci sosai ya zama babban ɗan kasuwa, sai kusan shekara huɗu da aurensu kafin Ammi ta samu ciki inda ta haifo ƴan biyu wato Umar da Faruk Umar yaci sunan mahaifin Abbanshi shikuma Faruk yaci sunan mahaifin Ammi, yara suna samun kulawa sosai sun tashi cikin shaƙuwa da Abbansu, sunyi karatu me kyau kuma Abba ya zaɓa musu aikin da zasuyi tun suna yara Faruk ya zaɓi soja Umar ya zaɓi doctor, ya tsaya sosai akan karatunsu har Allah ya dafa musu suka girma suka zama abinda sukeson zama, yayi farin ciki da hakan saide Allah ya karɓi rayuwanshi lokacin da Ammi take da cikin Elham, sunyi kuka sunyi bakin cikin rabuwansu dashi, bayan mutuwanshi suka kara haɗa kawunansu har Allah ya sauki Ammi lafiya ta samu baby girl, aka sa mata sunan mahaifiyar Abba wato A’isha suna kiranta Elham.

 

A yanzu Faruk da Umar sunada 30years Elham kuma tana da 13years.

 

 

 

share hawaye yayi tunawa da mutuwan Abbansu baison Faruk yatafi ya barshi kamar yadda Abba ya tafi, tashi yayi ya fita, zama yayi a mota yana tunanin inda zai fara zuwa, horn yayi aka buɗe mishi get ya fita, tafiya ya fara akan titi duk wani gida da yasan Faruk suna alaqa dashi saida yaje amma baiga ko alamanshi ba, a cikin motan ya zauna yana kuka, waya ya ɗaga ya kara dialing number yaji a kashe, yasar da wayan yayi yana sa hannu akai tareda murzawa da karfi yace “ina kake dude?”

 

a cikin mota take tafiya tana kallon hanya hankalinta akan titi, ganin mutum ya tsaya a titi ya tarewa mutane hanya tayi mishi alama daya matsa, horn tayi da karfi alaman ya matsa ta wuce dan tana sauri.

 

Umar baya hayyacinshi sai kuka yake kamar karamin yaro, a fusace ta buɗe motan ta fito wurinshi ta nufa tayi knocking a jikin glass nashi, ɗago kai yayi yana kallon hannunta wanda take buga jikin glass ɗin dashi.

 

Baison a gane yana kuka hakan yasa ya ciro facemask yasa kafin ya sauke glass ɗin yana kallonta, cikin faɗa tace “haba bawan Allah anayi maka horn ka kyale mutane munada uzuri a gabanmu dan Allah ka bamu hanya”

 

baiyi magana ba dan idan ya buɗe baki zai iya gaya mata maganan da har ta mutu ba zata manta ba, ɗaga glass nashi kawai yayi yaja motan yabar wurin,  hannunta ta yarfa dan ya haɗa da hannunta ya rufe, cikin masifa tace “mugu kawai”

komawa cikin motanta tayi taja yabar wurin.

 

yana tafiya yana tunani wani irin stop yayi yana kallon baya, tunawa yayi da muryan daya ji yanzu, aina ya taɓa jin muryan? tunani ya fara da karfi yace “a wurin faruk yayi recording voice nata time da suke waya bayan sun gana yayi playing yana ji har yayi bacci”

 

da mugun gudu yayi reverse inda ya barta yaje may be tasan inda Faruk yake, fitowa yayi daga motan yana tambayan mutane ina motan daya tsaya yanzu yabi? kowa cewa yake motoci dayawa sunzo kuma sun wuce.

 

hannu yasa ya mari kanshi yanajin haushi, cikin jin haushin kanshi yace “Umar kai wawane”

marin kanshi ya rinkayi har saida fuskan ya canja kala ya koma ja sannan ya buɗe motan ya shiga.

 

nemanta ya fara a cikin gari ba zai manta fuskanta ba, ita kaɗai ce bai tambaya ina Faruk ba, bai sameta ba har dare yayi, juyawa yayi ya koma gida cikin mutuwan jiki.

 

 

yana komawa ya zauna akan sofa yayi tagumi Ammi ce ta sauko daga ɗaki taganshi a haka, bataji daɗi ba sam, a hankali ta karaso ta zauna a gefenshi, baima san tazo ba ya dulmiya cikin duniyan tunani, hannu tasa ta janyoshi jikinta, sai a lokacin yasan tazo, a hankali yasa bayan hannunshi ya share hawayen dake fuskanshi, kanshi ya ɗaura akan cinyan Ammi cikin muryan kuka yace “ban ganshi ba Ammi”

 

itama dauriya kawai take tace “sorry zai dawo ka kwantar da hankalinka kaji?”

 

hawaye yana cigaba da sauka yace “Ammi bansan wani hali yake ciki ba, bansan ina yake ba nasan baya cikin hali me kyau ina zan ganshi?”

 

jikinta yayi sanyi sosai tasan Faruk bai taɓa tafiya haka ba, ba tareda ya sanar musu ba, ɗago kai yayi yace “Ammi? kodai binciken da yakeyi na ɓarayi da masu kisa ne yasa suka ɗauke shi masu aikata laifin?”

 

shiru tayi tana nazarin maganan umar.

 

“kwarai Ammi kuma naji yana cewa macece take yin kisan to kodai tasa an kamashi dan ya daina binciken ne?”

 

“Kayi gaskiya Umar ya kamata mu fara bincike daga inda aka fara kisan”

 

da sauri yace “gidan marayu can ne aka fara kisan an kashe shugaban gidan”

 

Ammi tace “to amma kana tunanin idan munje gidan zamu samu wani Information? kodai muje barack mu duba files da yayi bincike muga wa ake zargi?”

 

“no Ammi bai gano me kisan ba muje gidan marayu first acan zamu fara bincike daga nan saimu shiga duk wani gida da mukaji anyi kisa a ciki”

 

“shawara me kyau”

sai yanzu taji hankalinta ya fara kwanaciya saide basuda tabbacin zasu samu inda yake, Umar ya koma ya kwanta yace “Ammi mu tashi da dare muyi addu’a Allah ya bayyana mana inda yake”

 

“insha Allahu inakan addu’a kuma addu’an uwa yana saurin karɓuwa a wurin ubangiji.

 

tana barin wurin ta nufi gidanta batako kalleshi ba dan izuwa yanzu ya galabaita, shiga ɗaki tayi da kaya da kuɗaɗen da tazo dashi, saida ta ajiye ta zauna a bakin gado tana tunanin ta ina zata fara shiga gidan gomnati tayi babban sata?

 

gidan marayu takeso ta kara ginawa me kyau me kyau wanda zasuji daɗi idan sun shiga ciki, tasan akwai marayu dayawa waɗanda suka fisu neman tallafi dolene kuma ta taimaka musu.

 

Fita tayi tana kallon Faruk wanda ya kwanta a kasa cikin sanyin tiles yana baccin wahala, ruwan kankara suke watsa mishi gashi sun kure Ac ga sanyin tiles, ɗauke kai tayi ganin yadda ya taƙure, waya ta kira tace “kada abashi abincin dare yau”

fita tayi daga gidan cikin sharan kayanta na marayu ta kama hanya, saida ta isa taje ɗakinsu ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta sato manyan kuɗaɗe, Najma wacce ta fara ganeta tana ɗago hannu daga kwance tana mata dariya, hannu tasa ta ɗagota tana mata wasa.

 

 

*08144818849*

Leave a Reply

Back to top button