Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 11

Sponsored Links

 

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 11*

 

 

 

“Kaya baki budaɗɗe tasa kafin tasa nikab bayan ta shafa farin hoda a fuskarta bakin abu ta goga a bakinta kafin tasa ja a hokorinta nanfa ta fito kamar aljana, murmushi tayi kafin ta ɗau makullin mota ta fita, me gadi ya buɗe mata kofa fita tafi daga gidan bata tsaya ko ina ba sai kofan gidan speaker, wato me bawa shugaban kasa shawara, daga nesa ta ajiye motan kafin ta fara tafiya ba takalmi, kasancewar dare ne sosai hakan yasa bata wani ji tsoro ba, wurin me gadi ta nufa ba tsoro atare da ita, yana ganinta yace “waye?”

ɗaga nikab ɗin tayi tana mishi dariya, baya yayi ya faɗi kasa atake ya suma bayan ya saki fitsari a wando, dariya tayi ta shiga cikin gidan akwai masu tsaro hakan yasa tabi ta baya baya cikin sanɗa ta shige har cikin falo, kallon yadda aka zuba kayan ado na gwala-gwalai tayi, hawaye taji ya cika mata ido gasu acan suna cikin wahala da tashin hankali suna rasa abinci da wurin kwana me kyau, shiga ciki ta fara, wata yarinya ta gani budurwa tana mika alama ƴarshi ce ta farka cikin bacci, zaro ido tayi ganin mutum a falonsu buɗe baki tayi zatayi ihu Amrish ta ɗaga nikab ɗin tayi mata dariya, faɗuwa tayi ƙasa bata kara numfashi ba dan ta matukar tsorata taga aljana.

 

ɗakin dake abuɗe ta shiga drower ta fara buɗewa tana kwashe duk wani sarka da ɗan kunne na gold ga kuma kuɗaɗe dayawa, zubawa tayi acikin rigan ta fita ba tareda kowa ya ganta ba.

 

Tsallake me gadi tayi wanda yake a sume har yanzu, a mota ta zuba kayan kafin taja motan tabar wurin, wani gida ta kuma zuwa alama gidan wani me mukami ne, gold ta kwashe sannan ta ɗaga katifan dake kan gadon taga wasu kuɗaɗe kwance, fara kwashewa tayi tana zubawa a aljihun riganta wanda yake da faɗi, bata bar komai ba saida ta kwashe kafin ta fita, cikin sa’a ta samu ta shiga mota, zubawa tayi ba ɓata lokaci tabar wurin da mugun gudu ta koma gidanta, da kanta ta buɗe makeken get ɗin tashiga da motan, kwashe kayan tayi ta shiga ciki, a wani ɗaki wanda ta tara kuɗi da gold ta zuba, murmushi tayi kafin ta rufe kofan da makulli ta fita.

 

 

*Asuba*

 

Tana idar da salla ta koma gidan marayu dan bataso asan bata kwana acan ba, gani tayi sunyi nisa a ginin tayi murmushi tana jin daɗi a ranta.

 

unty Sadiya data tambayeta ina take? tace tana bacci a karkashin bishiya.

 

Faruk ne ya kirata ta ɗaga sukayi hira ta nuna mishi ba komai, tana kashewa taga kira yana shigowa ɗayan wayan nata sunan Umar ta gani yana yawo, ranta idan yayi dubu ya ɓaci “mayaudari mugu”

ta faɗa kafin ta ɗaga wayan cikin yanga suka gaisa, yace “Umar ne”

 

“na gane ka”

 

hira sukayi sosai, saida ya kashe wayan taji kaman ta shakeshi ya mutu, amma ba komai zatayi maganinshi.

 

ɓangaren Faruk da kanshi ya bawa Umar wayan yace su gaisa kuma ya jata da hura so yake ya haɗasu gaba ɗaya, amma bai gaya musu komai ba surprise yayi musu su duka harda Amrish da Ameera, bai sanar musu shi ɗin twins bane, yanaso sai ranan daya shirya saiya je shida Umar suga juna daga nan sai afara maganan aure.

 

 

soyayya ke karfi ya shiga zuciyan Faruk yana son Amrish sosai kullum yana hanyan zuwa gidan marayu, Amrish tana sakar mishi fuska amma bata sakin jiki dashi dan tasan halinshi, ya fara yimata maganan aure ba abinda ta tuna sai teema wacce tace “yace zai aureni daga baya yace iyayenshi ba zasu bari ya auri marainiya mara galihu kamar ni ba”

 

share hawaye tayi tana kallon gefe, baice komai ba sai kallonta da yayi jikinshi yayi sanyi, may be ta tuno da wani abin ne wanda ya shafi rayuwarta saide yayi alkawari ba zai barta tayi kuka ba, idan ya aureta zai zama gatanta.

 

ba karamin gini aka yiwa gidan ba, Amrish tayi shiri cikin kaya masu tsada tafito a matsayin Ameera ta bada manyan kuɗaɗe tace a siyo gadaje a sawa kowa a ɗakinsu, ai kuwa a ranan aka siyo sai shigowa akayi dashi aka sawa kowa gado a ɗaki, murna harda tsalle sukeyi, ta cikin glass take kuka sosai, kayan abinci harda masu girki na musamman tasa aka kawo, sannan ta canja shugawabanni tasa marayu domin sune zasufi kowa fahimtan halinda suke ciki.

 

kowani maraya saida aka bashi kuɗi da kwalayen biskit da drinks, murna sukayi sosai, tana ganin yadda suke ta tsalle, kuka ta fashe dashi kafin ta fita daga gidan ta faɗa mota, haɗa kanta tayi da sitiyari tana raira kuka babu me lallashinta taso ace ta hanyan halal ta samu kuɗin, amma koba komai zasuyi farin ciki, tana kuka tabar wurin gidanta taje ta ajiye motan.

 

news ta kunna taga yadda labarin satan da akayi yake yawo tako ina, shiru tayi ta zubawa Tv Ido, Faruk ɗin dai shi aka sake nunawa yace yana nan yana kan bincike da hannunshi zai danƙa musu wannan me babban laifin, mutum ɗaya ne itace take kisa kuma itace take sata, saide wannan ta kware wurin sata domin bata barin alama ko ɗaya.

 

Nuna me gadi akayi time ɗin da Faruk yake mishi interview yana rarraba ido yace “aljana ce ba mutum ba”

murmushi Faruk yayi yace “ba aljana bace nayiwa mutane alkawari da yaddan Allah sai mun gano wannan me laifin”

 

saida aka ɗauke su kafin tasa waya ta latsa numbernshi, bugu ɗaya ya ɗaga “Amrish ɗita”

 

amsawa tayi da muryanta me sanyi, yace “ya kike?”

 

“Bana lafiya”

da sauri yace “meya faru?”

 

murmushi tayi tace “ina sata”

 

“Kinada tsokana wallahi”

hira suka fara saida zai kashe tace “da gaske fa ni ɗin babban ɓarauniya ce”

 

“na yadda amma ɓarauniyar zuciyata”

dariya tayi kafin ya kashe wayan, dafe kanshi yayi yana kallon kujeran dake gabanshi, hannu yasa ya zubar da kayan dake kai cikin fusata ya dunƙule hannu ya bugi jikin bango saida yaji zafi, runtse ido yayi “na daɗe ina gano mai laifi meyasa wannan na kasa ganewa? meyasa na kasa gano wacce take wannan ɓarnan, ba karamin ɓarna ba manya manyan laifuka take aikatawa”

 

buga kanshi yayi da jikin bangon tunani kaman zai fasa mishi ƙwaƙwalwa yace “kodai namiji ne?”

 

“ohhh no Faruk macece take wannan aikin”

ji yayi kamar kanshi zai rabe biyu, ya kasa tunanin abu me kyau, wannan wace irin shaiɗaniya ce? duk ranan daya kamata sai ya kasheta da hannunshi.

 

“no Faruk kodai idan ka kamashi ba? macece ko namiji?”

zama yayi ya kwantar da kanshi akan desk na cikin Office ɗin, turo kofa tayi a hankali tana yauki da yanga ta shigo, ganin ya kwantar da kai tace “sir kana bukatan wani abu ne?”

 

ranshi kamar wuta ya ɗago a hargitse idanunshi sunyi jawur yace “get out”

langwaɓe kai tayi tace “sir naga kana cikin damuwa ne”

 

hannu ya ɗaga mata kaman zai mareta yace “i said get out!!!”

 

sumsum ta juya tabar office ɗin bayanta ya kalla wanda ta zuba uban attached har ɗuwawu, wani irin tsaki yaja kafin ya koma ya zauna, wayake kisan? macece ko namiji?

wannan tunanin yana neman tarwatsa mishi kwakwalwa.

 

fita yayi yabar barack motanshi ya shiga da kanshi yake driving, saida yazo kofan hospital na Umar yayi parking ya fito, kai tsaye ya wuce office nashi, knocking yayi ba’a amsa ba, da karfi ya fara turawa ganin a kulle yaciro waya ya kirashi bugu ɗaya ya ɗaga murya ƙasa-ƙasa yace “ya?”

 

“ina kofan office naka buɗemin”

yana faɗan haka ya katse, baifi minti biyu ba wata yarinya budurwa tazo ta buɗe, gaisheshi tayi yaki amsawa kallo ɗaya kawai yayi mata ya ɗauke kai, shiga ciki yayi time ɗin Umar yana kwance akan sofa yana latsa waya, kallon jikinshi Faruk yayi yace “amma kaji kunya wallahi”

 

“kunyan me?”

 

“a office ma ba zaka daina iskanci ba? wallahi Umar bakada kirki ashe shine abinda kakeyi anan, to idan Ammi ce tazo ya zakayi? bama Ammi ba baka tsoron Allah ne?”

 

“ina tsoron Allah mana kuma ma Ammi ba zata zo ba ka daina min mugun baki, meya kawo ka?”

 

tsaki yaja dan yaji haushi ba kaɗan ba “ubanka ne ya kawoni”

taɓe baki Umar yayi baice komai ba yaci gaba da latsa wayanshi, tashi Faruk yayi rai a ɓace yabar Office ɗin, jin yadda ya turo kofan da karfi yace “idan ka ɓalle kofan saika biya”

 

 

motanshi ya shiga rai a ɓace ya koma gida, Elham ya gani a palour tana kallo, murmushi yayi mata da sauri tace “ya umar”

hannu ya ɗaga mata tazo ta faɗa jikinshi, yace “ba Umar bane Faruk ne”

 

da sauri tace “a,a nasan ya umar ne wasa kake min”

 

hannu yasa a kanshi ya baza gashin duka kafin yace “kalleni da kyau”

 

Kallon gashin kanshi tayi shi Umar yana aski rabi da rabi saɓanin Faruk da kanshi yake cike da gashi, a hankali tace “yah Faruk”

murmushi yayi “ina Ammi?”

 

“Ammi tana bacci”

sakinta yayi yace “okay je kiciga da kallonki”

komawa tayi ta zauna tana kallon yadda ya canja.

 

ɗakinshi ya shiga ya cire kayan jikinshi ya rage dagashi sai boxer toilet ya shiga ya kunna shower a kanshi, ruwa yana jika jikinshi ya lumshe ido yana tunanin abinda yake faruwa, ga sata ga kisa ya kasa gane komai, zama yayi a kasan shower ruwan yana ratsa jikinshi saida yaji ranshi yayi sanyi kafin yayi alwala ya cire boxer ya ɗau towel ya ɗaura a waist nashi ya fito, zama yayi a gaban mirror yana gyara gashin kanshi, turo kofan Umar yayi yana waya, kallonshi yayi ta cikin madubi sannan yaci gaba da abinda yakeyi, saida ya gama wayan yace “ba magana ne?”

 

Yana magana yana cire riga, murmushi yayi ganin Faruk ɗin ya murtuƙe fuska, shiga toilet yayi shima yayi wanka yayi alwala ya fito, salla yayi time ɗin Faruk ya idar da nashi sallan.

 

Zama yayi a akan gado bayan ya rage hasken ɗakin ya ɗauko laptop zai fara aiki, yana kallon Umar ya kwanta kan sallaya yana bacci, tsaki yaja a ranshi ba dole yayi bacci ba ya gama turmushe ƴar mutane a office.

 

Saida ya gana aikinshi ya ɗau blanket yaje ya rufashi dashi, rage ac yayi kafin ya kunna dim light ya haye gadon shima ya fara bacci.

 

 

 

*washe gari*

 

Basuyi magana ba har kowa ya shirya ya tafi wajen aikinshi Ammi tana kallonsu batayi magana ba, tasan faɗa sukayi bata nemi sanin meya haɗasu ba, zasu shirya sun saba hakan kuma tasan duk yadda akayi laifin Umar ne.

 

 

gidan marayu sun samu cigaba sosai domin ko wasu masu gatan ba zasu samu irin gatan da suke ciki ba a yanzu, Amrish tana gida yau ta ɗaura zani a kirji Unty sadiya tanayi mata tsifa, tulin gashin dake kanta tunda safe suke aikin kwancewa amma har yanzu basuyi koda rabi ba.

 

unty sadiya tace “gaskiya gashinki yayi yawa Amrish”

dariya tayi tace “kai untu sadiya gashi yana yawa ne?”

 

“gashi naki yayi”

dariya kawai tayi har ta gama mata ta fara yimata kitso kanana masu kyau, fatan kanta fari sol kaman jikinta, saida aka gama tayi wanka tayi alwala tazo tasa dogon riga tayi salla, addu’a tayi tareda rokan Allah ya yafe mata.

 

kiran wayan Faruk ne ya shigo ƴar karamar wayarta, a hankali ta ɗaga tace “Hello”

 

amsawa yayi sukayi hira saida zata kashe yace “am kinsan me?”

 

“A,a saika faɗa”

 

“inason yau mu haɗu a wani waje Please zanzo na ɗauke ki”

 

murmushi tayi tace “ba komai”

 

ya sanar mata time ɗin da zaizo, ta amince, tana ajiye wayan tayi wani shu’umin murmushi, Umar Faruk karshenka yazo yau, dama nasan wannan ranan zatazo dolene akwai ranan da zaka nemeni da iskanci kamar yadda ka nemi Teema, abinda baka sani ba shine ni Amrish na shirya duk abinda zanyi maka.

 

tashi tayi taje karkashin bishiya ta zauna tana kallon yadda kowa yake walwala a cikin gidan, murmushi tayi ko yau ta mutu ba zata mutu da bakin cikin komai ba saina wannan Faruk ɗin, share hawayen da suka gangaro mata a ido tayi a ranta tace “nasan yau shine ranata na karshe a duniya domin Faruk shima ba zai barni ba, kuma shi yana da bindiga ko yayi nasara a kaina ko nayi nasara akanshi”

 

Tashi tayi taje ta ɗau takadda tayi rubutu me tsayi tasa cikin kayan unty Sadiya a kasa, saida ta share hawaye kafin ta shirya ta zauna, a cikinta ta cusa wukan ta ɓoye.

 

da mamakinta taga Umar yana kirata ta ɗayan layin, ɗagawa tayi yace “Malama  Ameera yau inaso mu haɗu dake kaman karfe 4 na yamma”

murmushi tayi tace “okay ba komai aina zamu haɗu?”

 

“ki faɗi inda kike zanzo da kaina”

 

ran Amrish ne yayi sanyi nan take ta sanar mishi inda zasu haɗu tace ya sameta a gidansu, gidanta data siya ta bashi house number, yayi godiya ya katse kiran.

 

 

Bin wayan tayi da kallo a ranta tace “so yake ya nunamin me kama dani” wani murmushin shu’umanci tayi kafin ta gyara wuƙan dake gefenta cikinta, ta ɗago waya ta kira wani number, plan ta haɗa wanda zaiyi mata dai-dai.

 

saida ta idar da sallan la’asar ta kuma canja kaya, wani material wanda baki wanda har ya fara komawa fari tasa, yaji jiki sosai ta ɗaura ɗankwalin ta ɗau farin hijabinta wanda ya dishe sosai tasa, takalmin roba ta zura a kafarta taje wurin Unty sadiya tace “zata fita siyan gyaɗa”

 

ta amsa da “kada ki jima ki dawo yanzu”

 

“tom unty”

 

zama tayi a bakin kofa tana jiran kiran wayarshi, Ameera ya fara kira yace gasu nan tahota ta amsa da to, kafin ya kira Amrish yace “gashi nan a kofa”

ta kuma amsawa da “to”.

 

fita tayi daga gidan ta ganshi yana murmushi, shiga motan tayi ya kunna yana kallonta, yace “surprise zanyi miki”

 

itama tace “nima zanyi maka surprise”

 

daɗi yaji har cikin ranshi, yana sonta sosai ji yake kamar ya maidata cikin jikinshi ya huta, tafiya suke babu me magana, har suka isa gidan Ameera, buɗe mata kofa yayi ta fito, murmushi tayi mishi ganin shima yana yimata, bakin kofa sukaje me gadi yana ganinta ya buɗe musu kofa yace “sannu da dawowa Hajiya”

 

kallonshi tayi taga bai girgiza ba da jin maganan, shima ya kalleta yaga bata damu ba, ganin zai ganeta tace “kamar yaya kuma Hajiya?”

hannunta kawai ya riko suka shiga ciki, har ciki inda Ameera tace su jirata acan sukaje babban falo ne na kasa ta cikin gidan, zama sukayi akan kujera yana gefenta ta kalleshi tana rarraba ido yasan tana tsoro ne yace “kada ki damu ba abinda zai faru”

girgiza kai tayi tana kallon falon kamar wata baƙuwa.

 

waya ya ciro daga aljihunshi yayi dialing numbern Ameera, kira uku ba’a ɗaga ba, kallonshi Amrish tayi tace “bata ɗaga ba ko?”

 

jijjiga kai yayi, wani murmushin rainin hankali tayi kafin tace “ta yaya zata ɗaga bayan tana zaune a gabanka?”

 

kallonta yayi ya zaci wasan data saba yimishi ne, ya cigaba da kira, a hankali tasa hannu cikin riganta ta ciro waya kiran Iphone 14 ta cire a silent, saiga wayan yana ringing, da mamaki ya kalleta tayi murmushi tana kallon cikin idonshi, kara kira yayi ta nuna mishi, nan yaga numbernshi yana shigowa, ɗayan layin wanda yayi saving da Amrish ya fara kira yaga shima ya shigo wayanta ta nuna mishi da murmushi akan fuskarta.

 

tashi yayi yace “aina kika samu wayanta?”

 

“ba wayanta ba wayata dai mr Umar Faruk”

 

kallonta yayi yace “ina Ameera?”

 

“gani nan koba Ameera wacce kuka haɗu a wurin shan coffee ba? to ai nice kuma nice Amrish”

 

girgiza kai yayi yace “ban yadda ba”

 

Da hannu ta nuna mishi inda ya tashi tace “calm down koma ka zauna ba sai ka ɗaga hankalinka ba zan nuna maka nice Ameera Ibrahim dikko”

 

shiga cikin ɗakin tayi yana daga tsaye yana kallonta cikin mamaki, ya kasa koda ɗaga hannu tsaban shocking, bata jima ba ta fito cikin wani dressing na riga da wando baƙi da takalmi me tsini tasa glass tana taunan cingum, har gabanshi ta karaso ta zaunar dashi kan kujeran kafin ta zauna a hannun kujeran tana kallonshi tace “sannu da zuwa malam Faruk, nice Ameera kuma nice Amrish, marainiya ce ni wacce ta taso a gidan marayu babu gata babu abinci me kyau kuma babu sutura balle wurin kwana”

 

“haka muke rayuwa bamu damu da kuɗi ko wani abin duniya ba burinmu kawai mu samu abinda zamuci, kwatsam sai ku masu kuɗi kuka shigo rayuwarmu kuka nuna mana cewar kuɗi akwai daraja harma yafi ran ɗan Adam, abun bai tsaya nan ba har saida kuka fara amfani damu kuna lalata da mu, daga baya kuma sai kuce iyayenku basu yadda ku auri marayu marasa galihu ba”

 

tashi tayi ta ɗau dogon rigan data cire tasa akan riga da wandon nan ta fito a Amrish, tace “shin ka tuna da abinda kayi ko saina tuna maka?”

 

baiyi magana ba ya mugun kiɗima bai taɓa tunanin haka zai faru ba, zuciyarshi ta karye, dariya tayi tace “Mr Umar ko ince Mr Faruk ka tuna da yarinyar daka lalatawa rayuwa har ta kashe kanta ta hanyan rataya?”

 

ganin yayi shiru ta fashe da kuka, da ihu cikin zafin rai tace “Teema!!!! Teema ƙawata ce tare muka tashi a gidan marayu kazo ka yaudareta kayi amfani da maraicinta ka cuceta sannan ka jefata cikin halaka har saida ta rataye kanta a jikin fanka, idan ina kallonka fuskar teema kaɗai nake gani, kana tunanin zan aureka ne?

ko kuma ina sonka?

kaima nasan ba sona kake ba so kake ka lalata ni ka biya bukatanka dani sannan ka kyaleni kamar yadda ka yiwa Teema”

 

“ka zama busy wurin neman wacce take kisa ko? to ai nice nake kisan, kuma na faɗa maka da bakina amma ka maida abin wasa”

 

“a gaban idona masu kuɗi sukazo sukayi amfani da yara ƙanana suna ihu suna kiran sunana ina jinsu amma ban iya nayi komai ba, munje asibiti a dubasu akace saimun bada kanmu, zainab itace ta sadaukar da rayuwarta ta bada kanta kafin akayi musu aiki, abin bakin ciki shine yaran sun mutu mutum ɗaya ne ya tsira”

 

“zainab ta kashe kanta, bamu gama kukan mutuwan zainab ba kaci amanan Teema itama ta kashe kanta ta barmu….”

kuka me tsuma zuciya ta fashe dashi ta cire rigan dake saman ta kifa kanta a kasa tana kuka kaman tayi hauka.

 

ɗago kai tayi tana kallonshi da idanunta wanda sukayi jawur suna hawaye tace “shugaban gidan itace da kanta take kawalcin ƴammata hadda yara kanana, na kashe ta da hannuna kuma na kashe abokan tafiyanta”

 

tashi tayi taje wani ɗaki ta ciro wani katon akwati wanda take janshi da kyar, gabanshi tazo ta buɗe da makulli ta nuna mishi wasu gwala-gwalai da kuɗi da zinari tace “wannan duniyan mutanene, duk wani wanda yakeda karfi baya taimako saida nabi gidanshi na kwashe dukiya, sannan na gyara gidan marayu nasawa kowa gado da kuma katifa me kyau”

 

“nasan na aikata laifi amma zuciyata ba zata barni ba”

 

rufe kayan tayi ta maida ɗakin kafin ta dawo tace “kaima kanada kaso a cikin lalacewan da mukeyi, marayu ba sune suka roki Allah ya ɗaura musu maraici ba, Allah ne ya ɗaura musu”.

 

 

a hankali ya fara sulalewa daga kan kujeran ya sauka kasa, akan kafafuwanshi ya zauna ya ɗago hannayenshi biyu ya haɗa wuri ɗaya muryanshi har yana rawa dan kuka yace “ki min duk hukuncin da kikaga ya dace dani ni Umar nasan ban aikata daidai ba”

 

yana magana yana kuka dan yasan Umar ne ya aikata haka dolene ya karɓi hukunci akan abinda twins nashi ya aikata.

 

share hawaye tayi kafin ta matso kusa dashi tace “ka yadda cewa ka aikata laifi?”

jijjiga kai yayi yace “na amince”

 

“me teema tayi maka kayi mata wannan hukuncin?”

 

a hankali yace “batamin komai ba son zuciya ne irin nawa ni Umar Faruk”

wuka ta ciro daga aljihun rigan ta kuma matsowa dab dashi ta ɗago kanshi da hannunta tana kallon cikin idonshi da idanunta wanda suka rikiɗe suka zama jajur, runtse ido yayi ganin ta fito da wuƙa.

 

 

 

*Anan na kawo karshen free pages sai mun haɗu a paid group, Idan kinason cigaba ki biya ₦400 ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta wannan numbern 08144818849 masu vtu zaku iya kai tsaye ta numbern dana ajiye, dan Allah idan kinsan baki shirya ba kada kimin magana ki bari saikin shirya*

Leave a Reply

Back to top button