Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 24

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah Shu’aibu_

 

 

*Chapter 24*

 

 

 

“Toilet ta shiga tayi wanka ta fito, ɗaure da towel a kirjinta ta zauna a bakin gadon tana kara kallon ɗakin, mayuka masu ƙamshin daɗi ta shafa sannan ta ciro wani riga yellow wanda yayi mata kyau, sawa tayi da wando pencil blue, bakaramin kyau tayi ba, hula shima blue tasa a kanta, kallon kanta tayi a jikin madubi tana dariya, a hankali kuma ta fara kuka, tunawa dasu unty sadiya da sauran ƴan gidan marayu.

 

tasan yanzu suna can suna alhinin mutuwanta, Allah sarki Najma ko ya take yanzu oho? faɗawa tayi kan gadon tana kallon saman ɗakin, tunanin rayuwarsu nada ta fara, sai kuma na yanzu da suke cikin daula domin gidan marayu ya zama kamar gidan masu kuɗi.

 

Tashi tayi daga kan gadon tace “ya zama dole na fara basaja dan gudun kada a kamani, buɗe drower tayi taga takaddu da sunan Ameera akai, murmushi tayi sannan ta kara barbaza takaddun nan ta hango wani reza wanda itace ta ajiye da kanta, ɗauka tayi ta mike daga wurin.

 

gaban madubi taje ta janyo stool ta zauna akai, rigan jikinta ta cire sannan ta matso da fuskarta dab madubin ta yadda zataga kanta da kyau, rezan ta ɗaga ta ɗaura a gefen hancinta, dannawa tayi sosai nan ya fara jini ta runtse ido tana jin yadda yake zafi yana fitar da jini, saida ta tsaga wurin da kyau sannan ta cire rezan, goge jinin tayi da tissue ta ɗau wani bakin abu a gefe ta shafa a wurin, nan take jinin ya tsaya gefen hancinta wani wuri kaɗan yayi baki kirin, da alama tabo takeso tayi a wurin.

 

ai kuwa ba karamin kyau yayi mata ba dan ya zama kaman tawadan Allah, kallon wurin tayi tana murmushi tace “wannan ba Amrish bace Ameera ce”

tashi tayi ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda zata fara daga gobe dan so take ta ɗibo su unty sadiya su dawo karkashinta da zama, zaifi mata kwanciyar hankali idan suna tare da ita, amma ba zatayi gaggawan ahak hakan ba, a hankali zatabi abun yanzu zata fara da gina school ne da sauran abinda tasa a ranta zatayi da makudan kuɗaɗen data sato daga.

 

Ɓangaren faruk ganin tana murmushi shima yaji daɗi a ranshi yana tuki yana tuno yadda take dariya time ɗin da taga gidan ya sauya, haka kawai yakejin yarinyar a ranshi, tausayi da soyayya sun ɗarsu mishi a zuciya kuma yayi alƙawarin zai sanya ta farin ciki har zuwa karshen rayuwarshi.

 

Bayan ya isa gida Ammi taga bai dawo da yarinyar ba, hamdala tayi a zuciyarta koba komai zasu dawo zama lafiya da ɗan uwanshi, zama yayi akan dining ya fara cin abinci, umar ma yaga duk abinda ya faru har lokacin da suka fita, murmushi yayi yazo shima ya zauna ya fara cin abincin.

 

basu yiwa juna magana ba har suka gama, Ammi da Elham sai kallonsu suke har kowa ya mike yaje ya shirya a tare suka yiwa Ammi peck sannan faruk ya fita, shima Umar ya fito ya shiga motanshi, kowa yayi tafiya daban-daban ba tareda sun haɗa koda hanya bane.

 

 

*Washe gari*

 

Amrish ta fito daga  toilet ɗaure da pink na towel a jikinta gashin kanta wanda yake lema-lema ta bazashi a bayanta, stool ta janyo ta zauna akai fuskanta yana facing madubi, drayer ta jona ta fara busar da tulin gashin dake kanta, mayuka masu tsada da kamshi ta shafa sannan ta buɗe drower na kayan kwalliya, zubawa kayan ido tayi rabonta da kwalliya har ta manta, hannu tasa ta ɗauki powder ta shafa a fuskanta, ba karamin kyau yayi mata ba ya kara fito da haskenta sai glowing take.

 

bayan ta gama shafawa ta ɗau mascara ta shafa a zara-zaran gashin idonta, nan ya kara tsayi sosai, bakin kwalli ta shafa a idonta, sannan ta ɗau lipstick red ta shafa a ƴar karamin bakinta, ayeshadow shima red ta shafa a saman idonta, gashinta tayi parking da jan ribbon sannan ta shafa gel ya kwantar da gashin dake gaban goshinta, kallon dara daran idanunta tayi ta cikin madubi sannan ta ciro wani abu irin wanda ake sawa a cikin ido na kwalliya, buɗe idonta tayi sosai tasa nan fa idanunta suka dawo blue daga brown.

 

tashi tayi ta shafa glowing powder wa duk jikinta sannan taje wajen wardrobe ta ciro riga red me yankakken hannu hannun dogone irin me style ɗin nan, wando pallazoo tasa wanda yake a buɗe kaman skirt black color, mayafi ɗan karami black ta ɗaura a saman ribbon ɗin sannan ta ɗaura belt na wandon.

 

Kallon kanta ta kumayi a madubi tana murmushi, takalmi red me tsinin gaske tasa a kafarta cover me ya rufe feet nata, turare ta fesawa jikinta sannan ta ɗau wani maƙeƙen glass baki cikinshi red tasa a saman gashinta, cingum na centre fresh ta wurga a bakinta sannan ta ɗau makullin mota tana kaɗawa a hannunta, waya kiran Iphone 14 tasa sim nata a ciki, jaka irin na ratayawa ta ɗauka a hannu ta fara taku kamar model ɗin data taso daga kasar london.

 

Already tasa an wanke mata mota kirar benz wanda yake ɗauke da glass tinted, motan duk jikinshi baki ne yana sheƙi kamar kwai.

 

cikin taku ta isa wurin motan ta ɗagawa wasu mutane biyu da suke tsaye majiya karfi da bakaken kaya alama excort nata ne, da ɗan gudu suka karaso da alaman girmamawa sukace “barka da fitowa hajiya”

 

wani irin murmushi wanda batasan ma ta iya ba tayi musu sannan ta sauke glass ɗin daga saman mayafin ta kawo idonta tace “ba hajiya ba HAMSHAƘIYA”

 

“barka da fitowa hamshaƙiya”

murmushi ta kumayi sannan tayi musu alama dasu buɗe mata marfin mota, buɗe mata sukayi ta zauna a gefe, already driver yana ciki ita kawai yake jira.

 

da sauri sukaje suka shiga mota suka su biyun bayan an fita da ita sukabi bayanta da motarsu.

 

kofan gidan marayu sukayi birki, mutane dayawa suna tsaye a kofar ciki harda ƴan jarida da masu gidan tv kowa yayi ready yana jiran isowanta, excort nata ne sukaje da sauri suka buɗe mata mota, kafarta ɗaya tasa a waje ganin takalminta ƴan jarida suka fara rige-rigen zuwa wurinta, bata fito ba ta tsaya gyara mayafin dake kanta, saida ta gyara ta saita glass ɗin a idonta tasa ɗayan ƙafan ta fito waje, dandazon jama’a ya cika kofan gidan ciki harda matan gidan su unty sadiya da najma wacce ta ɗan fara wayo, gefe guda kuma su Ahmad da sauran yaran data renesu sune suka ɗan girma, murmushi tayi bayan ta fito daga motan, ƴan jarida suka fara aika mata tambayoyi.

 

 

“Malama Ameera me zakice game da kama da kikayi da Amrish wacce ta kasance marainiya mara imani har hakan yasa take kashe manyan masu kuɗi tana sata a gidajensu”

 

ɗago kai tayi ta kalli matar data aika matan datayi mata tambayan tace “ba Ameera gatsau zaki kirani ba kice hamshaƙiya Ameera”

 

“malama hamshaƙiya Ameera me zakice game da hakan?”

 

“abinda zance shine Amrish bata kyauta ba, bai kamata tayi hakan ba bai kamata ta bisu tana kashesu ba komai laifin da suka aikata koda kuwa laifin na yin luwaɗi da yara ƙanana ne da kuma safaran ƴammata wanda suka fara tasowa da kananan yara na cikin gidan marayu ba, ya kamata ta bari gomnati ta ɗau mataki da kanta, domin inada tabbacin gomnati zasuyi musu horo me kyau, horo irin na wanda suke zaune a cikin ac suna shan kayan sanyi da kayan more rayuwa daga karshe za’a wankesu daga kotu ace sunada ciwon taɓin ƙwaƙwalwa”

 

da mamaki kowa yace “to kina nufin gomnati ba zata iya maganin waɗannan azzaluman ba?”

 

“babu abinda gomnati ba zata iya ba, amma abin tambaya anan shine su wayene gomnatin? masu kama wanda sukayi laifi su suke aikata laifi waye zai fara kamasu?

Amrish bata kyauta ba daga karshe ina yimata fatan Allah ya yafe mata yasa tayi mutuwan shahada”

 

“to malama Ameera shin kina ganin kama da kikayi da Amrish sosai ba zai iya kawo miki kalubale ba?”

 

“rayuwa dole saida kalubale idan baka fuskantar kalubale to kasa a ranka baka rayuwa, saboda kama da nayi da ita ba zai sa naji komai a raina ba, dama a duniya ai kowa yanada me kama dashi har mutane bakwai kema kanki me tambayan da zaki maida hankali akan rayuwarki da zaki samu me kama dake”

 

 

“to malama meya kawoki gidannan?”

 

“nazo ne na duba mutanen dake cikin gidan na basu tallafin kayan abinci da kuma kuɗi su fara sana’a hakan zai taimaka musu”

 

tana faɗan haka ta fara tafiya, bin bayanta suka fara har suna tureta, excort nata ne suka zo suna sa hannu kada kowa ya taɓa ta koda wasa.

 

da haka har ta samu ta shiga gidan bayan shugaba ta sanar kowa ya shiga idan ta shigo zasu rufe get, hakan kuwa akayi tana shiga da excort nata aka rufe get.

 

Unty sadiya ta hango tazo wurin da gudu zata rungumeta da sauri tayi baya tana kallonta, cikin nuna rashin saninta tace “miye haka malama?”

 

turus ta tsaya tana kallonta “Amrish?”

 

“malama bakiji hiran da nayi da ƴan jarida na ƴan sakonni bane zaki kirani da suna Amrish take ko wa? be careful kada ki.kara wannan gangancin”

 

 

 

 

_kuyi hakuri banajin daɗi shiyasa bana jin daɗi shiyasa ba zamuyi littafin da tsayi ba_

 

 

 

_Jiddah shu’aibu✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button