Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 10

Sponsored Links

 

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 10*

 

 

 

“Kanshi kasa yana duba kafarshi har saman takalmin ya huje ba karamin taku ta yiwa kafarshi ba, É—agowa yayi ya ganta yaga bata nan ta tafi, coffee da baisha ba kenan ya mike ya fita daga wajen yana É—ingisa kafa yana cije leÉ“e, kallonshi tayi ta cikin bakin glass É—in tited dake jikin motan, zata iya hangoshi ta ciki shikuma ba zai ganta ba, daÉ—i takeji domin yadda taga yana cije baki alaman yaji zafi sosai, murmushi tayi a ranta tace “saina rama duk abinda ka yiwa Teema”

jan motan tayi tabar wurin, gidanta taje ta kwaÉ“e kayan ta É—au takaddun gidan ta ajiye a wuri keÉ“antacce ta É“oye, canja kaya tayi izuwa wanda yaji jiki ta fita da hijabi fari a jikinta, taxi ta tara ta hau, a kofan gidan marayu ta sauka, shiga ciki tayi ta samu Unty sadiya tana yiwa yara wanka, karÉ“a tayi ta fara yimusu tanaji Unty sadiya tana tambaya ina kikaje haka kika jima? yi tayi kamar bataji ba taci gaba da yi musu wanka, Najma ta É—auko tayi mata wanka me kyau kafin ta juya ta koma É—aki, zama tayi a bakin katifa ta fara shafawa yaran mai, saida ga gama tasa musu kaya tace suje suyi karatun kur’ani, tare suka fita sukaje suka fara karatu.

 

kallon unty sadiya tayi tace “naje kasuwa ne kuma ban samu abinda ya kaini ba”

“to ki daina jimawa idan kin fita kinji?”

 

jijjiga kai tayi tana kallon wani koÉ—aÉ—É—en riga da Unty sadiya take sawa Najma, yarinya karama babu surutan kirki, É—auke kai tayi kafin ta mike ta fita daga É—akin taje banÉ—aki, waya ta ciro ta danna call, cikin kasa da murya tace “gobe da safe zaku fara aiki”

amsawa akayi da “tom hajiya”

murya Æ™asa tace “hamshaÆ™iya ba Hajiya ba”

 

murmushi tayi jin ance hamshaÆ™iya, fita tayi daga toilet É—in ta fara tafiya tana kallon cikin gidan, É—akinsu teema taje taga kawayen teema a zaune sunyi tagumi, wacce sukafi shaÆ™uwa da teema itace Abida, zama tayi a gefen Abida tace “ku daina tagumi idan kun zauna insha Allah muma mun kusa zama mutane, zamuyi rayuwa kamar yadda kowacce mace take rayuwa”

 

“har yaushe? har zuwa yaushe Amrish? masu kuÉ—i saide suzo su kwashemu su biya buÆ™atarsu damu, kowa bayason aurenmu saboda bamuda gata, bamuda masu kula damu, ya zamuyi da rayuwarmu?”

 

shiru tayi bata kuma cewa komai ba, batason ganin Æ´an uwanta a wannan halin, a hankali ta mike ta fita, waje kofa taje domin dolene ta kashe wancan É—ayan likitan wanda shine ya fara jefa zainab a wannan halakan, abin mamaki ta ganshi yau ya fito daga mota yana kallon kofan gidan, É—auke kai tayi shina yana ganinta ya haÉ—a fuska yana kallon gefe, wucewa tayi ta samu taxi ta shiga, asibiti taje akayi mata kwatancen gidanshi, batayi kuskuren cire facemask ba, saida ta samu information akanshi kafin ta juya ta koma gida.

 

ajiyan zuciya ta sauke ganin baya wurin, ta shiga ciki ta zauna tana jiran dare yayi, abinda zai hanata kisan yau saide ikon Allah.

 

aikinta ta gama da yamma sosai ta shirya yara ta gama komai itama tayi wanka ta zauna ta kara musu karatu.

 

*Tsakiyan dare*

 

Tafiya take cikin shirin data saba yi, fuskanta rufe da bakin kyalle jikinta sanye da kaya irin na maza, gidan da akayi mata kwatance ta tsaya duba ko ina tayi taga ba wasu masu tsaro sai me gadi, shima ya fara gyangyaÉ—i, cikin sanÉ—a ta shige ciki, kai tsaye inda tasan shine bedroom ta wuce, yana bacci matarshi tana gefenshi, kallon matar tayi taji ta bata tausayi akwai zafi rayuwa ba miji amma ya ta iya? mijinta ne ya janyo hakan, cikin sanÉ—a ta karasa cikin É—akin, pillow ta É—aga a hankali ta É—aura akan fuskarshi, hannu ya É—aga zai bigeta tasa wuÆ™a ta yanka hannun, zaiyi ihu ta danna kanshi da pillow nan suka fara kokawa yana son kwatan kanshi tana dannewa da pillow, ganin ya suma ya daina numfashi ta É—ago wuÆ™an ta daÉ“a mishi a ciki, bata cire Pillow a kanshi ba ta kuma É—aba mishi a ciki, a hankali ta kai bakinta kunnenshi tace “bada sona na kashe ka ba, kune kuka jefani a wannan halin”

 

cire wukan tayi ta É—aga pillow ta tafi dashi, dan tasan idan anzo bincike zasu auna pillow kuma zasuga shatin hannunta, barin gidan tayi, ta koma gidan É—ayan mutumin shima a daren ta kasheshi, bata dawo gidan ba saida ta kashe mutane shida kafin ta kama hanyan gidan a galabaice tana tafiya tana layi dan jini yana shirin hawa kanta, tafiya take kamar zata faÉ—i, da kyar ta isa gidan marayun hannunta rike da babban jaka wanda yake cike da manyan kuÉ—aÉ—e taje É—akin ta É“oye kafin ta cire kayan tanajin kanta yana nauyi, da kyar ta koma É—akinsu ta faÉ—i kasa.

 

ZazzaÉ“i ne ya rufe ta kanta ya fara sara mata, bargo ta janyo ta lulluÉ“a tana É“arin jiki har hakoranta suna haÉ—uwa, cikin nishi tace “Unty sadiya ruwa”

 

tana kwance a gefe taji muryan Amrish tana kiran a bata ruwa, da sauri ta tashi ta É—ibo ruwan tazo wurinta, É—agota tayi taga sai É“arin jiki take, “zazzaÉ“i ne? sannu”

 

Girgiza kai tayi, ruwan ta bata ta É—auko paracetamol ta bata hadiyewa tayi kafin ta koma tana bacci, har yanzu jikinta bai daina rawa ba, ga wani zafi da jikin yayi, ruwa Unty sadiya ta É—ibo tazo da tsumma ta fara goge jikin a hankali ya fara yin sanyi, rufata tayi da bargon Najma tana cewa “sannu” har bacci ya É—auketa.

 

komawa tayi ta sauke najma akan katifan tazo ta tashi Amrish tace ta koma katifan kasa akwai sanyi, ba musu ta mike ta faÉ—a kan katifan taci gaba da bacci.

 

 

*Washe gari*

 

Ta makara tashin sallan asuba domin zazzaÉ“in daya dameta jiya da dare, kafin ta tashi anzo gidan an fara rushewa, ba’a taÉ“a part nasu ba, saida aka gama kafin ta tashi tayi alwala tayi salla, fita sukayi su duka suka tsaya a waje wasu daga cikinsu har sun fara kuka sun zata koransu za’ayi daga gidan tunda shugaba ta mutu, Amrish tana kallonsu batayi magana ba, hatta Unty sadiya ta tsorata saide kawai batayi magana bane dan batason hankalin su Amrish ya tashi.

 

Saida aka gama rushewa a ranan aka fara gini, anan ne hankalinsu ya kwanta, gini me kyau upstair zasuyi a wurin.

 

a bakin masu gini taji suna cewa an fara gudanar da bincike akan kisan da akayi jiya da dare kuma komai yana hannun captain Faruk, cikin ranta tace “wannan gayen shine captain Faruk ko?”

 

wurin Abida taje tace “miye sunan saurayin Teema me rasuwa?”

 

“sunanshi Umar”

 

godiya tayi kafin ta koma ta zauna a karkashin bishiya “UMAR FARUK?”

sunanshi Umar kuma sunanshi Faruk, Umar Faruk kenan, mutumin daya lalata rayuwar yarinya har ta kashe kanta shine zaiyi bincike akan mutuwan wasu? baima dace da aikin soja ba yafi dacewa da zaman hotel.

 

tunanin ta yadda zata É“ullo mishi tayi, ta zurfafa cikin tunani kafin ta tashi tana kallon masu ginin wani daga cikinsu yace “ke bamu ruwa”

kallonshi tayi yadda yayi maganan da gadara zakace shi ya haifeta, ganin ta zuba mishi ido yace “ba zaki kawo bane? ina duk wahalan da akeyi saboda ku ne, ko mune zamu zauna a gidan idan an gyara?”

 

cikin tsawa yake maganan bata mishi magana ba taje ta É—ibo ruwan ta kawo mishi, karÉ“a yayi yana cigaba da surutu “ana shan wahala akanku baku gani, ire-iren yaran da suka taso a irin wannan gidan su suke girma su zama karuwai wasu kuma su zama mashaya wasu su fara kawalci duk ba abinda basayi, gashi basa ganin darajan mutum, iyayensu su haifesu shegu su yar dasu a titi a É—aukesu a taimaki rayuwarsu suzo suna watsawa mutane kasa a ido”

 

barin wurin tayi bata taÉ“a jin tsanan iyayenta ba kamar yau, wata kila itama shegiya aka haifeta, haÉ—a kai tayi da gwiwa ta fara raira kuka, saida idonta da fuskarta sukayi jajur kafin ta mike zata tafi wurinsu unty Sadiya taji yace “zo kije ki siyomin gyaÉ—a”

karÉ“an kuÉ—in tayi ta fita zuwa waje, har yanzu idonta jawur tana cigaba da share hawaye, a hankali ya zuba mata ido jikinshi yayi sanyi ganin tana kuka, ganin babu me gyaÉ—a anan kusa ta fara tafiya zataje gaba ta duba, da mota ya fara binta har ya iso inda take, tsayawa yayi bayan ya mata sallama, a hankali ta juyo ta amsa, cigaba tayi da tafiya yace “idan ba damuwa ki shigo na kaiki inda zakije”

kin shiga tayi tace “ba komai zan iso yanzu nan ne ba nisa”

 

Murmushi yayi “ko baki yadda dani bane madam?”

 

a ranta tace “wa zai yadda da mugu azzalumi irinka?”

a fili kuma tace “a,a kawai de zan isone ba damuwa”

 

“dan Allah ki shigo ba abinda zai faru dake”

a hankali ta tsaya tana kallonshi buÉ—e mata marfin yayi ta shiga ta zauna tana wasa da yatsun hannunta kanta kasa, murmushi yayi yace “sunana faruk”

 

a ranta tace “na sani ba sai ka faÉ—a ba”

a fili tace “ayya”

 

“ke kuma ya sunanki?”

 

“Amrish”

 

“wow suna me daÉ—i, anan gidan kika taso?”

 

giÉ—a kai tayi kafin a hankali tace “a nan gidan na taso tun ina yarinya inada kawaye inada Æ´an uwa wanda bazanso wani abu ya samesu ba, idan ma abin ya samesu zan rama musu kota wani hali”

 

murmushi yayi “ashe madam É—in tana da surutu, nima ina yawan ziyartan gidan amma yawanci da dare nake zuwa gaskiya”

 

wani irin kallo ta aika mishi “kenan da dare yake zuwa shi yake zuwa sauke Fatima?”

 

“me zakije siya?”

 

“gyaÉ—a”

tsayawa yayi ya fita gyaÉ—a dayawa ya siyo ya ajiye mata a gefe kafin ya juya da motan suka kama hanyan gidan, juyawa yayi ya kalleta tana kallon gefe, murmushi ya kumayi haka kawai yana jin nutsuwa yana sauko mishi daya zauna da ita, yau ya yini hankali tashe akan case na mutuwa wanda yayi yawa a cikin kwanakinnan, ya rasa yadda zaiyi gashi sai kashe mutane ake babu shaida babu hanyan gano makashin, kallonshi tayi “kai soja ne?”

 

“Eh ni soja ne me binciken gawa”

murmushi tayi tace “me binciken gawa kuma? kenan kana iya gano wanda yayi kisan”

 

“eh ina iya ganowa koda a ido ne”

 

dariya tayi sosai harda É—an tafa hannu kafin ta juyo tana kallon cikin idonshi tace “kalli idona to mutum nawa na taÉ“a kashewa”

 

Kallon dara daran idanunta yayi wanda suke É—auke da dogayen eyelashes yace “mutum shida kika kashe jiya”

 

gabanta ne ya faÉ—i da kyar ta daÆ™e tace “wow ka gano kaman ka sani ciki harda kai, ko kuma kai sai wani lokacin zan kashe ka”

 

dariya ya kwashe dashi kafin yace “kinada barkwanci, yau na wuni cikin É“acin rai haÉ—uwata dake yasa nayi dariya kuma naji farin ciki a raina”

 

“Meya saka É“acin rai?”

 

“case ne yamin yawa gashi babu wani abinda za’ace an gano me kisan, gaba É—aya kaina ya kulle”

 

“Allah ya bayyana me kisan”

 

cikin dariya yace “gashi Allah ya bayyana wata kyakkyawar mace a gefena”

 

dariya tayi tace “kaima kyakkyawa ne”

 

“Ban kaiki kyau ba”

 

“harma ka fini”

 

daga nan basu kara magana ba har suka isa kofan gidan, bayan ya tsaya ya ciro kuÉ—i ya mika mata, ido ta zubawa kuÉ—in “da wannan ya cuci Fatima nima haka yakeso ya cuceni”

 

Kallon tayi tace “a,a na gode”

 

shima kallonta yayi yace “ki siyawa yara sweet dan naga kinason raba musu”

 

“Kenan idonshi a kanmu? duk wani motsin gidan yana kallo?”

 

murmushi kawai tayi tace “saide n karÉ“i rabi”

karÉ“a tayi ta cire rabi ta ajiye rabi a gefenshi, yace “ke Æ´an biyu ne?”

 

“A,a niba Æ´an biyu bane ni Æ´ar É—aya ce” tayi magana tana kokarin buÉ—e marfin motan, ganin bata iya ba yayi murmushi ya matso dab da ita ya buÉ—e, zubawa bayanshi ido tayi ji take kamar ta ciro wuka ta caka mishi ko zuciyarta zata daina zafi, É—agowa yayi yace “ga yadda zaki buÉ—e”

jijjiga kai tayi “na gode”

da gayya tayi hakan ta nuna mishi batama iya buÉ—e mota ba.

 

tasan tambayan da yake mata kanshi ne ya juyu dan yaga me kama da ita a coffee shop, lekowa yayi bayan ta fita yace ta bashi phone numbern ta.

 

wata karamar nokia ta ciro ta mika mishi karÉ“a yayi ya É—au numbern yasa mata nashi tareda yin saving da Faruk, mika mata ledan gyaÉ—an yayi cikin sanyin muryanta tace “na gode”

 

Yan kallonta har ta shiga ciki, tana basu gyaÉ—an ta juya zata tafi yace “baga irinta ba, basu da tarbiyya ko kaÉ—an, suna da rainin hankali, kalli yadda taje ta daÉ—e a wurin aika may be ma tana tare da saurayi ne”

 

a hankali tace “kayi hakuri”

juyawa tayi tabar wurin, batayi mishi magana ba so yake ya maidata yarinya, bai sani ba lokacin datake karÉ“an kuÉ—in gyaÉ—an taga hannunshi da ink na biro kuma taga takadda a gefen aljihun shi wanda ta zubawa ido taga rubutu da tambarin Æ´an sanda a jiki, atake ta gane wannan jami’in sirri ne, turoshi akayi domin yayi bincike a cikin gidan.

 

tasan yanzu har gidan marayu bazasu bari ba dan gudanar da bincike shiyasa take binshi yadda yaso.

 

tana shiga toilet ta faÉ—a tana kuka sosai, bataso zama kusa da saurayin Teema ba balle su canja number, kuka tayi sosai har taji kanta yana ciwo kafin ta wanke fuska ta fito daga toilet É—in, alwala tayi taje É—aki ta fara salla, bayan ta idar tayi addu’a ta kwanta akan sallayan.

 

 

Faruk yana murmushi har ya isa gida yau yaji daÉ—i da ya aro jarumta ya yiwa innocent Amrish magana, da alama batasan da zaman me kama da ita ba, zaiyi surprising nata watarana ya nuna mata me kama da ita, cikin farin ciki ya isa gida, yana shiga yaje falo da gudu ganin Umar ya fito da brush a baki yaje da gudu ya rungumeshi ya fara juyi dashi, waro ido Umar yayi yana kallon bayanshi, saida ya gama juyi yana murna ya sakeshi, yaje wurin Ammi ya rungumeta ya É—agata sama, da sauri ta fara marin hannunshi tace “saukeni karka yaddani”

saida ya juya da ita kafin ya ajiyeta yana dariya yayi mata kiss a goshi kafin ya rungumeta.

 

har yanzu da brush a bakin Umar sai binshi yake da kallo, yau ya fita rai a É“ace ko fara’a baya yi yanzu kuma ya dawo yana tsalle yana murna? meya faru?”

 

Ammi daÉ—i taji ganin Faruk yana murna haka, cikin jin daÉ—in tace “meya faru babana?”

 

kanshi kasa yace “Ammi nayi budurwa”

 

waro ido Umar yayi yana cigaba da goge hakoranshi, É—auke kai tayi domin ya bata kunya tace “wace yarinya ce me sa’a haka?”

 

“sunanta Amrish”

 

“nice name aina take? Æ´ar gidan waye?”

 

wayarshi ce tayi kara ya ciro daga aljihu yana dubawa, ganin kirane daga wurin aiki ya É—aga ana nemansu da gaggawa, sallama yayi musu yana cewa “idan na dawo zan faÉ—a miki”

fita yayi da É—an gudu ya koma cikin mota driver yaja suka tafi.

 

zama Ammi tayi akan sofa tana jin dadi, yau taga murna da farin ciki a tareda É—anta, saida Umar ya wanke bakinshi ya dawo yace “Ammi Faruk yayi hauka ko? akan soyayya yake wannnan tsallen?”

 

dariya tayi tace “kasan wanda baya soyayya idan ya faÉ—a ciki yafi kowa haukacewa”

 

“Tabbas na gani akan Faruk koma wacece wannan yarinyar tanada babban kyauta daga wajena domin tasamin É—an uwa cikin farin cikin dana jima ban ganshi a ciki ba”

 

a mota ya kira numbern ta, cikin sa’a ta É—aga da muryanta me sanyi ta gaisheshi, amsawa yayi yana lumshe ido, shiru sukayi su duka biyu, É“angarenta har wani hucin zafin zuciya takeyi, kenan yana kiranta dan ya samu ya fara soyayya da ita har ya fara lalata da ita ko?

 

a hankali ya fara bata labari sai eh da a,a take faÉ—i idan abin dariya tayi dariya da haka har sukayi sallama.

 

 

*Da yammaci*

 

Yaje shagon coffee yana kallon inda ya saba ganinta, ai kuwa sai gata nan zaune tasa dogon riga baby pink da headband shima baby pink, tasa glass ma baby pink, sai murmushi take tana chatting da babban wayan dake hannunta.

 

Sakin murmushi yayi a hankali ya fara takunshi cikin izza da nutsuwa ga kuma kwarjini yana isowa yayi mata tafi, É—ago kai tayi tana taunar cingum ta kalleshi sau É—aya ta watsar, janyo kujera yayi ya zauna yana fuskantar ta, yace “ko zan iya yin magana dake?”

 

a tsiyace tace “ina jinka”

 

“ya sunanki?”

 

kallonshi tayi saida ta taÉ“e baki tace “sunana Ameera Ibrahim dikko”

 

“wow malama Ameera kina kama da wata kawata”

 

“Oh really?”

ta faÉ—a tana ajiye wayan, murmushi yayi wanda ya kara mishi kyau yace “yeah da fari na zata ku É—in twins ne saida na tambayeta tace ita kaÉ—aice ba twins ba”

 

“nima ni kaÉ—aice a wurin mahaifina har ya koma ga Allah bai kuma haihuwa ba, mahaifiyata ta mutu lokacin da take haifa na”

 

“Allah sarki Allah yaji kansu da rahama”

 

“Ameen”

 

“zan iya samun numbern ki?”

 

murmushi tayi nan ya kara ganin tsananin kamansu da Amrish, wayan mika mishi ya karɓa yana kallon hotonta na gaban wayan, ɗaukan numbern yayi yasa mata nashi yayi saving da Umar.

 

mika mata yayi yace “sunana Umar”

 

murmushi tayi ta kalli numbern daya sa mata tace “nice name”

 

“Thanks”

 

tashi tayi tace “ni zan wuce”

 

“Tom malama Ameera sai munyi waya”

 

tafiya tayi tabar wurin, motanta ta shiga ta jingina kanta jikin kujeran kirjinta taji kamar zai faso ya fito waje, zafi takeji kaman tasa hannu aka tayi ihu, acan yace sunanshi Faruk anan kuma yace sunanshi Umar da haka yake amfani da suna yana lalata Æ´ammata, bugun kirjinta tayi “dolene na gama da wannan dolene na kasheka Captain Umar Faruk”

 

 

jan motan tayi da mugun gudu ta fita daga wajen gidanta taje ta zauna a kan sofa tayi crossing leg tana shan wani tsadadden drinks saida ta shanye kwalba É—aya kafin ta ajiye tana kallon Tv, news take kalla taga ance ana neman wannan Serial killer wacce take kashe masu kuÉ—i da masu muÆ™ami, mikewa tayi tana zagaye babban falon tana cigaba da kallon Tv, hannunta ta goya ta baya tana cijan leÉ“e tana kallon yadda suke nuna Faruk yana bayanin yadda me kisan takeyi da dabara, da yatsa ta nunashi, “saura kai kaima bazan barka ba”

 

bata koma can gidan ba dan tasan yau ana gyara babu me kula da ko tana nan ko bata nan, kallon katafaren gidan tayi a hankali taje É—aki tasa kayan shan iska, kofan baya tabi nan ta haÉ—u da wani wuri na shan iska babba, gefe guda lambu ne me É—auke da kayan itatuwa ga kuma swimming pool dake gefe, zama tayi a bakin ruwan tana plan na abinda zatayi Anjima.

 

a fili tayi dariya hadda tafi tace “zaku gane kuranku”

 

 

 

 

*Ki biya ki karanta cikin salama ₦400 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849 masu vtu kuma kuyi, ki turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

Leave a Reply

Back to top button