Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 42

Sponsored Links

042
*Bonus*
___________________
“Kinga mun yarima? This morning?”

“Nima shi nake nema ,mama hankali na a tashe yake ,I even needed to have some words with him ,yeah I Doubted if sarautar gidan nan har yanzu ta gado ne ,bai zama contesting akeyi ba a watsa tsaba mai rabo ka tsinta…”

“Auta baki da fatar alkahiri a rayuwar ɗan uwanki ne? To ko ma menene da ke da sauran masu tunani irin naki su jira ,suna kallo yarona zai gaji karagar ubansa ,Abbad zai zama sarki na 4 da yardar Allah”
Kafin Auta ta kawo nata objections ɗin ta wuce ta fuuu.

Zafi zafi taje ta ɗauko car key dinta Bata jira Driver ba ko guards ta shiga motar ta mata wani mugun key ta figeta da gudu tun daga parking lot ta nufi hanyar gate ,da sauri masu gadin ƙofa suke tale gates har guda duka ukun ,haka ta fice daga gidan a hargitse.
Ita kanta bazata taɓa iya tuna yaushe ne rabon da ta tuƙa mota da kanta ba ,zata iya cewa tun kafin sarki ya zama sarki. Tun sarki na yarima kafin babansa ya mutu ya gaji mulki.
***

“Sarki yana da ɗa a wani waje,kuma Matsawar yana raye yiwuwar zaman ka sarki rabi da rabi ne ,ma’ana kowa yana jan ƙarfin ikon gadon sarautar………! ”
Kalmar da kakan jabir ya soma gaya ma Yarima knn a sanda suke shiga daga cikin kogon.

Itama kuma mai babbar ɗaki kalmar da bokanya ta soma gaya mata kenan a daidai sanda take rusune a gabanta cikin tashin hankali.

“Kana nufin akwai wanda zai iya zama sarki ba Ni ba?”

“Ko yayi nasara ko kayi nasara ,amma kayi ƙoƙarin ganin bayan sa kafin ya shigo fadar nan ,saboda taurarinsa suna da haske …yana zafin halshe fiye da kai,yana makirci kamar mace ,da kayi sakaci ya shigo fadar zai tarwatsa maka gida kuma dole yayi sarauta.”

“How and why?,Mai Baki ya fi mai aiki? Munafuki yafi mai sarauta…ban taɓa ganin yanda banbaɗanci yafi zaurance ba”

“Yana da ɓoyayyen Sihiri a tare dashi ….a taƙaice an tsumashi ,a shirye yake”

A hankali yarima ya maimaita “He’s battled ready,waye shi?”

“Kaje ka cigaba da roƙon mutanen ka gafara…Zaku haɗu ƙarƙashin inuwar wata budurwa,Allah yaba mai rabo Sa’a ,kar kayi sakaci da Addu’a yarima! Ina maka fatar Nasara.” yasa hannu yana shafa masa kai yana masa en Addu’oi.

***
Ambassador ne gurfane a gaban mamanshi ,baƙa baƙa ƙirin da ita , mummunan gaske ,kana ganinta kaga shu’uma ,duk da yaronta yayi kudi baisa ta sauya ba tana nan a wahalenta.

Miƙa hannu tayi gefen ta ,ta kamo wani ƙwarya shaƙe da wani abu kamar jini ta miƙa ma Ambassador .
Jikinsa na rawa yasa hannu ya amsa

“Yarooo!”

A hargitse ya ɗago yina kallonta
“Shanye”

Watsa idonsa yayi cikin tashin hankali cikin ƙwaryar jinin Hannunsa.

“Ina bazan iya ba mama”
Tsawa ta daka masa wanda yasa tantabarun gidan yin kuka suka firfito daga kejinansu ,wanda suke tsube a ƙasa suna tsintar dawa suka tashi firrrr saboda firgita.

“Shanye nace! Ni zan ringa magana kanayi? Ni zan baka umurni kana mun jayayya? To waye silar dukiyar da kake taƙama dashi? NINE! waye silar zamanka Ambassador? NINE! Yau ne ranar cikar girmanka,yau zan bayyanar da ɓoyayyen takobin da na daɗe ina wasashi…yau zan gabatar ma maƙiyyiyata Lauje mai dafi da zai Zaro en hanjinta waje ,zaki fito gidan sarautar nan Ummi ,yau zaki bar gidan da na baki aro kikaci zamaninki a cikinsa Ni kuma ina raɓe cikin wahala Ni da ɗa na,Yanzu lokaci na ne zaki bar mun gidana da uban ɗa na mai martaba! Yarona zai zama sarki zai wulakanta mun ku…”

“Yaroooo” ta sake kiran sunan Ambassador cikin Hayaniya da fitina irin na gawurtattun matsafa

“Kaje ka kashe mun,yaron nata da take taƙama dashi,ka ƙwato mun kujeran babanka….yau lokacin girban haƙurinka ne,yau wanda suke maka gorin shege zasu san yarona ba shege bane da ubansa! Uban kuma maɗaukaki da yafi ubansu….taka a hankali ɗan sarki jikan sarki ,sarki da kansa nan da sa’oi arba’in da Takwas ….ka tafi ina nan ina kallon duk abinda ke faruwa a cikin ƙwaryar tsafi na,Gabanin nan shanye mun wannan tsimin jiƙon tas! Don anan nasarar ka take”

Ɗaure fuska yayi Nan da nan ya rikiɗe ya zama wani kalar mutum mai suffar mugaye ,cikin ɓacin rai na tuno wulakancin da yasha a rayuwa ya kafa kanshi a kan ƙwaryan jinin ya ƙyanƙyame

“Hiihahahahahaahhaa” ta barke da wata mahaukaciyar dariya ,wanda yasa gurin ya fara girgiza kamar jirgin sama ne yazo giftawa.

“Oya Oya jeka fuskanci maƙiyinka..jeka ƙwato mana mulkin da ya guje mana tsawon shekaru ,saboda makircin waccan bakar dagar(Mai babban ɗaki, mahaifiyar Yarima Abbad)” a zabure ya miƙe yana gyara kwalar riga .

“Yes yarona” taje da sauri ta ɗauki kaskon wutar dake ta ɓulɓulo da hayaƙi ta na kewayeshi tana turare masa jiki da hayaƙin.

 

 

_A yawan lokaci muna tare da mugayen mutane bamu sani ba,kai dai ka kasance da Addu’ar safiya da maraici ka fice gida da Addu’a sai Allah ya kareka daga sharrin mutum ko Iska,wannan shine abokin Ya Sheikh wanda yake barinshi a gidansa a koda yaushe ,shine wanda yake son Sayyada a birne a ƙasar zuciyarsa,shine wanda ya bayyana mata yana sonsa ta tozarta shi,a karshe ma ta gunmaci zaman gidan ya Sheikh da ta kula shi….ƙaraƙaƙa kaka_

 

Oum Aphnan
#Bad boys
09065990265
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button