Hamshakiya 7
*
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 7*
*Littafin Hamshaƙiya na kuɗi ne ki biyani hakkina ki karanta cikin salama, ₦400 ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan numbern 08144818849 masu vtu kuma kuyi, turo katin shaidan biyanki ta nan 08144818849, dan Allah kada kimin magana idan baki shirya ba, banda doguwar gaisuwa kawai kice inason littafin kaza domin messages sunyi yawa*
“Fita tayi daga asibitin tana kuka sosai, gudu ta fara har ta isa bakin titi ta tari adaidaita sahu ta shiga, sanar mishi inda zai kaita tayi, sunyi tafiya me nisa kafin suka isa g.r.a. a bakin titi ya ajiyeta ta sauka ta biyashi kuÉ—inshi, saida ya saita kanta ta share hawayenta ta goge zufan da tayi kafin ta karasa inda Zainab tayi mata kwatance, a hankali taje wajen security’s na wurin ta gaishesu, suka amsa tace “daga gidan marayu nake Alhaji ne yace inzo”
basu yadda ba saida suka kirashi a waya sukace watace daga gidan marayu, yace ya sunanta, suka tambayeta tace “sunana zainab”
jin haka yace abari ta shigo, buÉ—e mata kofa akayi ta shiga, babban gidane wanda aka Æ™awata da kaya kaman gidan gwal ne, bayan ta shiga wani yayi mata iso har zuwa katafaren falon Alhaji, yana zaune akan kujera yana jiran shigowanta dagashi sai wani wando karami, ganin ta shigo kuma ba zainab bane yace “lafiya?”
gabanshi taje ta faÉ—i tana kuka tace “Alhaji zainab batada lafiya tana asibiti ance ana neman miliyan É—aya kafin a fara aiki dan Allah ka taimaka mana ka biya kuÉ—in aikinnan”
Kallonta yayi yana lashe baki yace “ai dole na taimaka mata, wannan kyakkyawar tana rokana abu kuma naki amincewa? dolene na yadda da bulatanki yarinya”
hannu yasa ya É—auko wani takaddan cheque yayi sign, yace “gashi miliyan biyu ne idan kin bawa likita zaiyi aikin nan take harma ya baku sauran canjin”
murmushi tayi tana share hawayen ta mike taje zata karÉ“a domin miÆ™a mata yake, É—aukewa yayi da sauri ta kalleshi da manyan idanunta, murmushi yayi yace “ai bazan baki haka kawai ba Æ´ammata”
cikin sauri tace “meyasa?”
dariya yayi “yaro yaro ne, zan baki naga kin damu da kawarki, kizo kawai muyi sau É—aya saiki karÉ“i takadda kiyi gaba”
kallon agogon É—akin tayi karfe 12 narana yayi, cikin kuka tace “Alhaji ka taimaka dan Allah idan naje anyi aikin ta samu sauki zanzo da kaina”
wani irin dariya ya kwashe dashi wanda yasa ta tsorata yace “ba zanyi miki dole na amma kinsan ai kawarki tana bakin mutuwa ko? to saiki zaÉ“i ko rayuwar kawarki ko mutuncinki”
Jikinta ne ya fara É“ari a hankali ta fara tuna maganan da Zainab tayi mata, kasa ta faÉ—i ta kamo kafanshi tana kuka tana rokonshi ya taimaka mata, yaki yadda saide idan ta bada kanta, tashi tayi ganin tana É“ata lokaci ta fita, har taje bakin kofa ta juyo taga ya ciro kuÉ—aÉ—e bunch bunch, yana kaÉ—awa yana kallonta, hawaye ya kuma wanke mata fuska a hankali tasa takalminta tana tunanin kamar taje ta amince da zancenshi, saida taje bakin get kafin ta kuma dawowa, kallonta yayi yana dariya yace “kin canja shawara ne Æ´ammata?”
kanta kasa tace “ban canja shawara ba zobena na manta”
durkusawa tayi ta É—auko wani zobenta wanda ya faÉ—i lokacin da take rokonshi sannan ta juya tace “kaji tsoron Allah zaka mutu”
fita tayi daga gidan, ta fara bi layi layi tana shiga gidan mutane tana roko daga meyi mata maganan banza sai mata masu kuÉ—i suke mata tayin lesbian, kin yadda tayi haka ta juya ta koma gidan marayu Office na shugaba taje ta sanar mata abinda yake faruwa buÉ—an bakinta tace “ai ita zainab batada wayo, da tara kuÉ—in tayi ta É“oye lokacin da sukeyin abin ai”
cikin kuka Amrish tace “ki taimaka mana yanzu ki musu magana su bada kuÉ—i ayi mata aiki”
“to ai zasu yadda amma sai idan zaki yadda dasu idan kin amince saina kira Alhaji boti”
tashi tayi ta fita daga gidan ma gaba É—aya ba tareda ta amsa mata ba, asibiti ta koma, wurin data barsu taje, mutane ta gani sun taru akansu, gabanta ne ya faÉ—i da gudu taje wurin tana kiran zainab, Unty sadiya ta rungumeta tana kuka tace “zainab ta mutu”
sai wari wurin yake domin tayi gudawa sosai, fitar da ita sukayi daga asibitin, mutane suka bisu Amrish ko hawaye bai É—iga mata ba, tana kallon fuskan zainab har suka isa gidan marayun, shigar da ita akayi mutane suka taru aka fara jana’iza saida aka gama akayi mata salla, kaita makwanci akayi teema har kanta yana ciwo tsaban kuka.
Amrish batayi kuka ba tana bin masu kukan da ido har aka fita da gawan zainab, addu’a kawai tayi, daga nan mutane suka watse, gidan marayun ya zama shiru mutane kowa jikinshi a mace, su Unty sadiya ma suna daga gefe suna aikin kuka, Najma tana kwance tana tsala ihu unty Sadiya ta zuba mata ido tana tunanin makoman rayuwarta idan ta girma, Amrish ce ta mike ta É—au yarinyar tana girgiza ta, saida tayi shiru ta goyata, jijjiga ta tayi har saida tayi bacci kafin ta kwantar da ita tana kallon mamanta tana kuka sosai.
Teema ɗakinsu ta koma ta kwanta tana tunanin abinda Umar ya faɗa mata a waya, kasa bacci tayi a ranan, Kawayenta suna bata hakuri har tayi kaman tana bacci kafin suka barta, da safe taje har hospital aka hanata shiga yace idan tazo kada su barta ta shiga, kiran wayarshi tayi bai ɗaga ba kusan misscalls goma bai ɗaga ba, juyawa tayi ta koma ta kwanta a ɗaki, kuka takeyi bata bari suji sautinta dan bataso a bata hakuri, sai can tsakiyar dare ta tashi bayan kowa yayi bacci tasan Amrish ma tayi bacci yanzu, a hankali ta fara takawa har ta isa ɗakinsu Amrish a kasan Pillow ta ajiye mata hoton Umar wanda ya naɗe hannu a kirji yana murmushi, fita tayi daga ɗakin ta koma ɗakinta, mayafi ta ɗauka ta ɗaura saman fanka, kafin ta ɗau wani kujera ta hau, sa wuyanta tayi acikin mayafin ta buge kujeran, shure-shure ta fara tana da hannu a wuya tana hawaye, da haka har ranta ya fita ta sanƙare a jikin fankan.
Amrish tana bacci tayi wani irin mummunan mafarki a firgice ta farka tana addu’a, fita tayi daga É—akin taje wurin randa tasha ruwa, dafe kanta tayi tana cigaba da yin addu’a a ranta, duba yaran tayi taga kowa yana bacci, Najma da mamanta suna suna bacci, hamdala tayi kafin ta koma ta kwanta, saide wannan time É—in saida ta tofawa wurin kwanciyarta addu’a.
data rufe ido zainab kawai take gani, kasa bacci tayi sai juye-juye take akan tabarman, ganin haka ta mike ta kuma fita tayi alwala, komawa É—aki tayi ta shimfiÉ—a sallaya ta tada salla, nafila tayi ta É—aga hannu sama tana rokan uabngijin sammai da kassai, haka kawai taji gabanta yana faÉ—uwa Alkur’ani ta É—auko ta fara karantawa cikin ikon Allah taji ranta yana sanyi, a hankali bacci ya fara É—aukanta, ajiye Kur’ani tayi ta kwanta taci gaba da baccinta, Unty sadiya tana kallonta domin Najma ta tashi tana bata nono, hawaye ta share na tausayin duk wata mace da take gidannan kai bama matan ba har mazan Æ´an luwaÉ—i basu barsu ba.
*Washe gari*
sun tashi da asuba kamar yadda suka saba kowa yayi alwala yayi salla, ƴan ɗakinsu Teema suka fito da gudu suna ihu ganin yadda take lilo a sama harshenta ya fito waje idonta ya juya alaman ta jima da mutuwa, mutanen gidanne suka taru a ɗakin ciki harda Amrish da Unty sadiya ganin yadda ta bushe jikinta ya sanƙare Amrish tayi wani ihu taje da gudu tana rike kafan Teema kan kace me shuwagabannin gidan sun taru a wurin, mutane sun matsa musu sukayi dube-dube sun tabbatar da cewa itace ta kashe kanta, Amrish tana gefe tana kuka ba ita kaɗai ba harda Unty sadiya tana kuka tana tasbihi tareda ambaton sunan Allah.
Shugaba ce ta kallesu tace “ba kuka zaku tsaya kuna yiwa mutane ba addu’a zakuyi mata” wani irin kallo Amrish tayi mata wanda yasa ta tsorata da sauri ta É—auke kai, idanun Amrish har yanzu a kanta ga hawaye ga idanun yayi jawur sai kallonta take zuciyarta tana tafasa, É—aukan Teema akayi aka fara shirye-shiryen yimata wanka, saida aka gama akayi mata salla, kawota akayi akace kowa yazo yayi mata addu’a Amrish tana zaune a gefe bata mike ba, shugaba takalleta tace “kema kizo kiyi mata addu’a”
wani kallon data kuma aika mata saida taji hanjin cikinta ya murÉ—a, kawar da kai tayi, Amrish ta mike ta shige É—aki bata tsaya ganin lokacin da za’a fita da gawan ba, suna kuka kawayenta da Æ´an É—akinsu da sauran mutanen gidan, haka aka fita da ita.
Amrish kuka ta fashe dashi ta É—aga Pillow zata rufe fuskanta taga hoto, É—agawa tayi tana dubawa, ganin rubutu tayi a jikin hoton, a hankali ta share hawayen idonta ta fara karantawa.
“Amrish kada ki É“ata rayuwarki kamar yadda nida zainab muka É“ata, wannan shine ya É“atamin rayuwa, ina cikin rayuwa tare daku a gidan marayu yazo yace zai aureni daga nan ya fara É“atamin rayuwa gashi yace iyayenshi ba zasu barshi ya auri marainiya mara galihu kamar ni ba, hakan yasa zan kashe kaina, Amrish kuyimin addu’a”
runtse ido tayi tana jin kaman ta tsala ihu, cikin kakkausan murya tace “fansan ranki yana hannuna Fatima, ke ba marainiya bace mara galihu tunda kina dani, laifin da kika aikata shine na kisan kai, be kamata kiyi haka ba, Allah bai yadda ba, ya hanamu aikata wannan laifin, amma bazan bari ranki ya tafi a banza ba”
Kallon hoton tayi sosai a take ta shaidashi, a cikin jakanta tasa hoton.
Bata gayawa kowa ba harda Unty sadiya batasan komai akan hakan ba.
Bayan kwana uku, a ranan akayi sadakan ukun teema, addu’a sukayi mata sosai kafin sukayi masa suka raba, Amrish tana zaune a bakin baranda tayi shiru tana kallon gefe hankalinta baya jikinta sosai duk ta mayar kan tunani, a haka har dare yayi saida ta kimtsa yaran kafin itama ta kwanta tayi kaman tana bacci, saida taji gidan yayi shiru kowa yayi bacci kafin ta mike a hankali ta fara tafiya, saida ta fita ta rufe É—akin, bata tsaya ko ina ba sai wani É—aki dake gefe, wasu bakaken kaya riga da wando ta É—aga tana kallo, hawayene suka fara wanke mata fuska a hankali tasa hannu a bayanta ta janye zip É—in bayan riganta, sauke rigan tayi kasa idanunta suna cigaba da fitar da hawaye, ya rage daga ita sai wani wando guntu wanda ya wuce pant da kaÉ—an, da kuma bra, rigan wanda yake kaman leda tasa kafin ta É—ago wandon shima tasa, wani hula wanda yake rufe fuska tasashi ya rufe mata kai kuma ya zame mata kamar facemask, bakin glass tasa a idonta kafin taÉ—au wani takalmi sahu ciki tasa a kafarta, har yanzu bata daina kuka ba, wuÆ™a tasa a gefen wandon sannan ta fita daga É—akin cikin sanÉ—a, ganin me gadi yayi bacci ta tsallaka ta katanga ta fita daga gidan, tafiya ta fara cikin duhun dare tana sharan hawayen bakin ciki ba abinda take tunawa kaman su na’eem da Ahmad ga kuma zainab wacce ta mutu tsutsa yana fita daga jikinta, ga teema itama ta mutu mutuwan wahala, mutuwan da ko a kotu sai wanda yayi kisa ake yanke mishi wannan hukuncin.
hakika ba zata bar duk wani me kuÉ—i yayi rayuwa cikin jin daÉ—i ba, saita rama duk abinda akayi musu, zuciyarta tafarfasa take yi kamar ta zuba wuta, da kafa har ta isa g.r.a a bakin titi ta hango gidanshi domin akwai hasken solar, ganin akwai security ta tsaya gefe tana tunanin abinyi, murmushi tayi bayan ta gano abinyi, a gefe ta tsaya ta É—au dutse ta harba a gefe, jin karan yasa suka taru su duka sukabi inda su jiyo sautin.
da gudu taje ta shige gidan ba tareda kowa ya ganta ba, kai tsaye ta wuce har cikin É—akin da aka kaita ranan, bata ganshi a falo ba, ta kalli wani É—aki wanda takeda tabbacin shine bedroom ba tsoro zuciyanta ya bushe ta fara tafiya har ta isa cikin É—akin, tura kofan tayi da kafarta nan take ya buÉ—u, shiga tayi ta hangoshi yana bacci harda minshari, wani kuka taji yazo mata a ranta tace “yana nan yana bacci cikin Ac baima tunanin ya lalata rayuwar yarinya, baya ma tunanin zata iya mutuwa a kowani lokaci?”
Æ™arasawa tayi ciki bayan ta rufe kofan, jin karan rufe kofa ya tashi yana tambaya “waye? waye?”
murmushi tayi wanda ya fito tareda hawaye tace “nice”
“Ke waye?”
“Ni mutuwanka”
a firgice ya mika hannu kan gadon zai É—auko waya tayi wani irin tsalle ta wurga mishi wukan dake waist nata saida wuÆ™an ya tsaga mishi hannu, zaro ido yayi ganin tazo wurin ta É—ago wukan ba É“ata lokaci ta daÉ“a mishi a ciki, baki ya buÉ—e yana zare ido ganin yadda jini yake malala daga jikinshi, jikinshi ne yafara rawa yanaso yayi magana amma ya kasa, cire hulan tayi nan take fuskanta ya bayyana tana murmushi tana hawaye, hannu ya É—aga cikin ciwo yace “ke…ke..ke”
matsowa tayi dab dashi tace “eh nice, wacce tazo neman taimako a wurinka za’a yiwa kawarta aiki wacce kayi lalata da ita har bayanta ya fara fitar da tsutsa sannan ka hana kuÉ—in aikin kace sai munyi zina zaka bani”
baki ya buɗe da sauri ta ɗau Pillow ta danna a kanshi yana ɗaga kafa yana shure-shure har saida taga ya daina motsi kafin ta sauko daga gadon ta ɗau wukan ta goge jinin a jikinshi kafin ta maida a ƙugunta ta juya ta buɗe drower ta ciro wasu kuɗaɗe masu yawan gaske kafin tasa a cikin aljihun dake gaban rigan ta fita daga ɗakin.
Kamar yadda ta fito haka tayi dabara ta fita daga gidan, bata tsaya ko ina ba sai gidan shugaba wanda yake manne da gidan marayun, sallama tayiwa me gadi wanda yake aikin bacci, murmushi tayi ganin yana bacci ta tsallakashi ta shiga ciki, dama tasan gidan domin ana aikansu wani lokacin.
kai tsaye ɗakinta ta shige, bedroom taje saide ta ganta kwance da ƴarta a gefe, ta rasa ta yadda zatayi, cikin dabara taɗau wani kwalba dake gefe ta buga da kasa kafin ta ɓuya a jikin bangon dake manne da ɗakin, a firgice ta farka daga bacci tana murza ido, jin kara yasa ta tashi tana dubawa, ganin babu komai a ɗakin ta fara fitowa waje, Amrish tana daga gefe ta rike wuƙa tana kallon kasa, ganin ta tako kafarta zuwa waje ta janyota, baki ta buɗe zatayi ihu da karfi ta danne bakinta ta tura kofan a hankali, janyeta ta fara bayan ta daɓa mata wuƙa a gadon bayan.
kwantar da ita tayi a kasa sannan ta cire hulan dake kanta, cikin zaro ido tace “Amrish?”
murmushi me haÉ—e da kuka Amrish tayi kafin ta zauna a gefenta tana wasa da wukan hannunta tace “shugaba ko kuma ince Halima, kece babba a gidan marayu kece kika kula da rayuwarmu tun muna yara, baki bamu tarbiyya me kyau ba a matsayin ki na uwa, abin be tsaya anan ba kina kawalcin Æ´ammata, kina haÉ—a maza Æ´an luwaÉ—i da yara Æ™anana, hatta mata baki barsu ba, sannan bakya sauke hakkin da Allah ya É—aura miki na bamu abinci kamar yadda mutane suke aika miki, yunwa yasa sauranmu suka fara bin maza, wasu hakan yasa sukesa ran masu kuÉ—innan zasu auresu, abin mamaki da sun gama dasu saisu kyalesu, hakan ya faru da teema har ta kashe kanta dan bakin ciki, sannan su na’eem sun mutu domin fyaÉ—en da wannan mutanen sukayi musu, kina ganin Allah zai barki kici gaba da abinda kikeyi?”
ganin tana miko hannu tana cewa “ruwa zansha ruwa”
ta kuma É—aukan wukan ta daÉ“a mata a ciki, tana kuma tana kallon fuskan shugaba, cikin muryan kuka tace “bada sona na kasheki ba, haka zan biku da É—aÉ—É—aya har saikun bar duniya”
cire wukan tayi sannan ta kara daÉ“a mata tana cigaba da kuka sosai tace “Zainab ta mutu kinada hanyan taimaka mata kika ki”
kara daɓa mata wukan tayi saida taga ta daina motsi kafin tana kuka ta goge jinin a jikinta ta mike tabar gidan, gidan marayu ta shiga kafin taje ɗakin ta sauya kaya ta ɓoye wuka sannan ta fito ta koma ɗakinsu, hamdala tayi ganin duk suna bacci, kwanciya tayi a kan tabarma ta fara kuka sosai tana toshe baki.
*Washe gari*
Labarin mutuwan Alhaji Hamza da Hajiya Halima shugaban gidan marayu shine labarin da yake yawo acikin garin Abuja, a binciken da akayi an gano a wuri É—aya aka É—aba musu wukan, alama wanda yayi kisan mutum É—aya ne.
case ɗin mutuwan da bincike an damƙa a hannun kwararre kuma jajirtacce wato Captain Faruk, da kanshi yaje gidan Alhaji hamza yayi bincike anan ya gano wanda yayi kisan mutum ɗaya ne dana hajiya Halima.
Ƴan jarida sun taru a kofan gidan Hajiya Halima suna jiran fitowan faruk, cikin sa’a ya fito da sojoji masu gadinshi a bayanshi, tambayoyi suka fara aika mishi, bai amsa ba saide kawai yace “wanda yayi kisan ba namiji bane macece”
abin ya bawa kowa mamaki ta yaya mace zatayi wannan mummunan kisan?
Amsan daya basu shine “nima ban sani ba amma ina kan bincike idan bincike ya kammala zai mika a hannun general”
tafiya yayi daga wurin aka buÉ—e mishi kofan mota nan ya shiga suka bar wurin, Æ´an jarida saida sukaga ya tafi kafin suka watse.
_Hauwa shu’aibu jiddah 08144818849_