Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 9

Sponsored Links

Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

009
___________________
_Emirate_
Yau fa fada An tashi da baƙar labarin rashin Lafiyar mai martaba ,saidai a kwantar saidai a tayar ,an kwana dashi lafiya an tashi ba baki ,ba shiri Mai babbar ɗaki ta bada umurnin saita tafiya zuwa Cairo don binciken lafiyar mijinta don ga dukkan Alamu ya shiga _*Coma* and if care is not taking will definitely loose the king….what is the way out?_

A lokacin da ake kuciniyar fitar da sarki ƙasan kuma a lokacin duk wasu king makers suka kutso ɗakin da me martaba ke kwance rai ga hannun Allah ,don a cewarsu ciwonsa ta iya yiwuwa sharrin magautane…..But it will shock you ,all this drama Yarima baya gida baisan ana yi ba ,ya shiga cikin gari ran gadi…..wani wainar ake toyawa ?
Gadai Waziri,Fagaci,Ciroma da sauran manyan fada kewaye da gadon sarki a daidai Lokacin da Babban Malamin fada ke durƙushe a gaban Sarkin yaja carbi mai dubu da Alluna cike da ƙasa ,sai dukan ƙasa yake yana shafewa yana sake zanawa duk don gano me ke faruwa da Sarkin a wannan safiyar?

Mai babbar ɗaki da Autar sarki a furgice suma suka shigo ɗakin suka yi carko carko a tsaye .

An kwashe sa’oi biyu cikin wannan halin gidan yayi tsit bakajin ko tarin bil’adam

Babu zato sukaji Malamin fada ya doki ƙasa cikin tashin hankali ,wani zufa nan take ya shiga karyo masa kamar an watsa masa ruwan famfo.

Cak ya kakkaɓe rigarsa yana haɗa kayan wuridinsa cikin jakar fatansa ,zuruuuu kowa ya bisa da ido ,haka ya taƙarƙara ya mike yana dogara sandarsa yaje gaban kan sarki ya tsaya kana a sanyaye cikin mutuwar jiki yace “Sauya sabon Sarki shine samun lafiyar mai martaba !!!!”

Dararass gaban kowa na ɗakin ya fadi ,saboda indai malamin fada ya fadi magana to yanki takene haka zai faru ,kenan Lafiyar sarki ne zataci gadon mulkinsa

Kowa yayi jungum jungum cikin tunani ,kafin su ankara har malamin fada yakai bakin ƙofa zai fice daga ɗakin ,taran gabansa auta tayi cikin kuka ta kange bakin ƙofa

“Ya malamin fada to mu ya makoman abban mu? Yanzu zamu wuce dashi Cairo ganin likita”

“Cutar mai martaba ba na asibiti bane ba,idan har kuka bar dashi dakin nan tamkar kun fita da gawarsa ne,Kuma fitintinu su zasu biyo bayan hakan”

Ƙara auta ta saki gamida rugawa da gudu gadon da babanta ke kwance tayi ta daura kanta a ƙirjinsa ta kece da kuka .

Mai babban ɗaki kam ƙeƙam tayi cikin wani irin jarumta ,fuskarta nuetral ba yabo ba fallasa.

A dake ta kalli malamin fada sannan ta magantu “Sai a shirya gagarumin bikin naɗa yarona yarima sarkin faƙat!”

Ɗagowa yayi ya mata wani irin kallo mai kama da tausayawa ko tsorataswa .
“Bamu da damar ɗaura wani mahaluki akan kujerar mulki har sai masu tsaron kujerar sun bada umurnin wanda zai hau ,don haka ba naɗin sabon Sarki sai nan da sati guda …..daganan ne yarima zai tabbata magajin kujeran nan ko akasin hakan….”

Yana gama magana ya fice daga ɗakin yana dogara sandarsa dakyar ƙafafuwansa ba takalmi

****
Wani irin gudu motocin Yarima suke shararawa akan kwaltan garin duk inda talakawa suka hango layin motocinsa sauka da ababen hawansu suke ɗingurgum akan kwaltan har sai ya wuce.

Baba kadarko ,dattijo ne dan shekara 58 ya hudo ta ƙararramar hanya yina gungura tsohuwar kekensa da ya ɗebo kara daga Gona ,cikin gaggawa yake tafiya sakamakon yarinyarsa Ummulsulaim ta dawo daga makarantar kwana tun safe ba abinci a gidan ,shine ya fita yayo masu karare a samu ko taliya ƴar muji ne a ɗan silala mata.

Yina dab da karya kwana shiga layin gidansa da ake hange tun daga farkon layi ginin jar yanɓu an ma ƙofar Gidan labulen tsumma,ko arzikin kofa basu da shi.

sukuma daidai motocin su yarima suka keto fiyauuun fiyauuuun a tsiyace ,Raɓewa ya yi ta gefen hanya zai cusa kekensa a hankali .
Saidai Wani ƙara ne ya ziyarci kunnensa na bazata, yaji kuuuuuuu ! wanda ya sashi firgita ya ɗago a tsorace.

Kafin kace meye wannan motocin Yarima sunyi dafifi a kan baba ɗan tsoho ,firgita kam iya firgita yayi ,amma haka ya aro mazantaka ya saka a ransa .

“Bayin Allah lafiya?”

Basu tamkasa ba suka fara kiciniyar ɗaukar kekensa su saka a Boot ɗin motarsu .

Baba sa azama ya damƙi hannun Yakubu

“Ɗan nan tsahirta…karka karya mun wuyan keke ,meye hadinka da keke na?”

Banza yayi da shi sai ma yana ƙoƙarin fincikarsa haɗe da keken ,don haka baba yayi tagal tagal zai kifa ,wannan abu ba ƙaramar ƙona ransa yayi ba ,don haka cikin zafin nama yabi bayansa daidai zai saka keken a mota ya daddage ya tsinke guard ɗin yariman da mari .

Ji kake faffassss!

Kafin ya sauke hannu a kuncin Yakubu yaji wani lallausan hannu ya kece fuskarsa da mari Wanda yasa baba sakin fitsari a wanda ,idanuwarsa ɗif suka daina gani na wucin gadi ,kafin yana farfadowa yaga anyi gefen hanya dashi an yasar ,sannan kuma an dauke kekensa an cusa a mota.

Ɗaga ido yayi yana kallon mutanen da suke ƙoƙarin yi masa fin ƙarfi haka ,yana kuma son ganin wanda ya shafe fuskarsa da mari.
Bakowa bane face Yarima

“Allah ya ɗaiɗaita aniyarku ,yanda kuka tozarta Ni fanni ya tozarta kuruciyarki ,da duk abunda kuke takama dashi”

Cakkkk yarima yaja ya tsaya yana kallonsa
Tsirrr cikin bana ya tsirga ya mike da sauri ya taka zuwa hanyar ƙofar gidansa

“ku dakatar dashi ” he ordered

Bai wahalar da Shari’a ba yaja ya tsaya

“WAYE YA BAKA IZININ RAYUWA A MASARAUTA TA?”

Kallon mamaki Baba ya bishi dashi ,kawai sai ya sunkuyar dakai yana kallon kasa yana mamakin wannan Al’amari ,an wani banƙareshi kamar yayi sata.

“Ina takardan ka na shedan zama ɗan garin nan” waro ido yayi
“Topah ,jidali sabo!

Bai tamkasa ba ya yi masa shiru

Tsawa ya daka masa
“Kai talaka! Ka bani amsa ”
Girgiza masa kai yayi ma’ana baida shi .

“Kuma baka da takardan shedan zama ɗan garin nan har kake da gut ɗin zagina? Har kake da encin noma a ƙasa ta! Wannan kana zagin masarautana ne ”

“Ni ban taba noma a gonar kowa ba sai gonar da na gada iyaye da kakanni

Subhanahi yarima ya hassala iya hassala Don haka ya daka masa wani mugun tsawa

“Rufe mun baki ina magana kana magana…..Yaƙubbb” ya ƙwalla ma yaronsa kira da yafi ji dashi a kaf cikin yaranshi

“Ɗauko mun littafin ɗaukan rai!”

Da gudu yaƙub ya nufa wajen mota sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da wani rafkeken littafi Kamar album an saka farin ƙyalle a tsakiya .

Yana zuwa gaban yarima ya wangale masa tsakiyar littafin ,bindiga ce kwance akan farin ƙyallen cike taf da bullet .

Sa hannu yayi ya ɗauketa ya gyara mata zama tayi ɗan ƙara alamar alburushi ya shiga cikin mazauninsa kana ya saita goshin baba kadarko.

Ummusulaim da mamanta suna daga cikin gida suke juyo Hayaniya sama sama daga waje wannan yasa ummuh leƙowa , subhanahi wa zata gani ? Babanta ne an rirrikeshi an saitashi da bindiga za’a kashe banza .

Wani irin ƙara ta saki mai tada tsikar jiki ta fyalla da gudu ta rumfashe uban tana kururuwa.

Baba hansai da gudu ta nufi gaban yarima ta tumu akan ƙafafunsa tana majinjinu tana gyara leɓen zani ,tana roƙonsa yayi masu rai kar ya kashe mata miji shikenan gatansu

Yanda baba ke tima take burgima a kasa yasa ya sauke bindigar ƙasa yana kafe ummuh da ta sha gaban babanta ta masa rumfa tana faman tutturo ƙirji kenan harbin ya sameta kar ya sami abbanta.

Murmushin ƙeta yarima ya saki ,gamida taune leɓe.

“Na yafe ma mijinki” wani ihun murna baba hansai ta saki

“Ehoo mun gode Yarima mun gode….”

“…Amma har zuwa lokacin da zai mallaki takardar shedar zama ɗan garin nan ,zata kasance Tawa…” ya Kare magana yana nuna Ummulsulaim dake jikin babanta

Wani ƙara maman ta saki “Innalillahi ka taimake Ni kar ka rabani da ƴata ita kenan mana wallahi ƴar makaranta ce yau ɗin nan ta dawo….” bai saurare su ba ya juya zuwa motarsa aikuwa guards dinsa hudu sukayi ƙawanya suka cicciɓeta wannan ya rike hannu wannan ya rike kafa ,tana zille zille iyayenta na binsu da gudu ummusulaim tana kurma ihun kiran iyayenta tana ɗaga masu hannu amma haka suka je motan da yarima yake ciki suka bude ɗayan side ɗin suka wullata ciki…..

Ƙura ta tashi da karfi cikin minti kadan duk motocin suka watse aka bar su baba a yashe suna kurma ihu.

***
Ihu Ummulsulaim ta cigaba da kurmawa shikam gogan ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karanta jarida tamkar ba kuka take ba waƙa take masa.

Zuwa wannan lokacin ba abunda ya ƙosa illah ya isa gida yayi wanka ya miƙe a ruwan cikinta ,don kallon farko ya hararo baiwan niima a ƙwarmin idonta .

“Ina fasa budurcin da kike taƙama dashi kuka ya ƙare ,as you know now you’re belongs to me,ko ki lallaɓani ko in maki shigar fata fata ,in maki cin wulakanci….

Ɗif Sulaimiy ta ɗauke wuta ko tari ta kasayi ,ta fara tunanin yankata yake nufi zaiyi ya cinyeta ɗanye ko ƙaƙa?

 

Oum Aphnan
09065990265

Wannan shine zai kasance page na kusa da ƙarshe na pages ɗin kyauta ,daga page 10 na kyauta ya kare
Ki hanzarta biyan kudinki don ayi tafiyar dake ,BAD BOYS Ba Littafin Yara bane muje zuwa💃

Wacce ta shirya biya
Regular 500#
VIP 1000#
Special 2000#

Katin MTN ko ta nan bank din
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb bank
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

Leave a Reply

Back to top button