Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 18

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 18*

 

 

 

“Washe gari da Ammi da Elham da Faruk sun shirya breakfast me rai da lafiya suka shiga mota zasuje prison domin kaiwa Umar, a hanyarsu na tafiya Ammi tayi waya da governor tayi mishi bayanin duk abinda ya faru, yace ba komai zaiyi magana a bincika idan babu laifin Faruk zai fito a cikin satin nan, tayi godiya ta katse wayan, juyawa tayi tana kallon Faruk wanda yake tuki hankalinshi baya kanshi, kiran sunanshi tayi kusan sau uku sannan ya juyo a ɗan firgice yace “na’am Ammi”

 

“tunanin me kake haka inata magana hankalinka baya nan?”

 

shiru yayi baiyi mata magana ba yaci gaba da driving, bayan sun isa Elham ta rike flask na abincin suka shiga ciki dubasu akayi me kyau, akaga ba komai a jikinsu sannan suka wuce ciki, kiran Umar akayi wanda take zaune yayi tagumi a cikin cell yana tunanin munafurci irin na mata, ganinsu Ammi yaje ya rungume ta sannan ya rungumi Elham yazo wurin Faruk ya rungumeshi yaji daɗi da familynshi suka haɗu wuri ɗaya babu wanda ya kara missing.

 

samun waje sukayi suka zauna, abincin Ammi ta fara bashi a baki yanaci yana murmushi dan girkin yayi daɗi, Faruk yana zaune yana aikin kallon gefe, so yake ya hango ta ko da ta window ne ta leko, tunawa yayi babuma window a wurin, Umar ne ya lura dashi gyaran murya yayi da sauri ya juyo yana kallonshi, dabarcewa yayi kaman ba abinda yake nema.

 

Ammi ta kallesu batayi magana ba taci gaba da bawa Umar abinci har ya koshi, akace time ɗinsu ya kare, kamar tasan yanason ganinta ya hangota tana gaba hannu ɗaure da ankwa ƴan sanda mata suna biye da ita, Umar ya tashi aka maida mishi ankwa a hannu, su unty sadiya ne suka kawo mata abinci shiyasa aka fito da ita, jikinta duk yayi tabon cizon sauro, wurin yayi jajur fuskarta ya kumbura ba ɗankwali akanta sai gashinta daya zubo har gadon bayanta, leɓenta na kasa yana cikin bakinta tana aikin tsotsa saboda sauro ya cijeta a wurin ya ɗan tashi yayi mutane.

 

bata ankara ba taji ya bugeta da gefen kafaɗarshi saida ta faɗi kasa tayi ƴar siririyar karan azaba, gashin kanta suka zubo suka rufe mata fuska, ɗago kai tayi hannunta me ankwa yana kasa tana kallonshi, murmushi tayi mishi tana jin raɗaɗin zafi, taka hannunta yayi da kafarshi, kara ta kuma saki tana yarfa hannu, mikewa faruk yayi zaije ya ɗagata Ammi ta rike hannunshi tana girgiza mishi kai.

 

matan da suke kula da itane suka ɗagata, cikin azaba da ɗingisa kafa ta fara takawa suna bin bayanta, sai kiciniyar maida gashinta baya takeyi dan ya rufe mata fuska, da kyar ta maida kaɗan taci gaba da tafiya, dab wurinsu ta tsaya bata kalli kowa ba tace “ina kwana Ammi?”

 

Ammi ko kallonta batayi ba ta ɗauke kai kaman bata taɓa ganinta ba, murmushi tayi ta wuce, wajensu unty sadiya aka kaita sun kawo mata abinci unty sadiya tana ganinta ta fara kuka, ɗauke kai Amrish tayi ta karɓi abincin ta fara ci kamar ta shekara bataci komai ba, hannu baka hannu kwarya, saida ta gama ci ta ɗau goran ruwan tasha sannan tace “na gode”

hannu ta mikawa matar aka ɗaura mata ankwa sannan suka koma, a time ɗin su faruk sun fito zasu tafi, bata bari sunyi ido huɗu ba, ta raɓa ta gefenshi ta wuce, tsayawa yayi yana kallonta idonshi yana cika da hawaye Ammi ta riko hannunshi ta janyeshi suka tafi.

 

Elham ta zubawa Amrish ido saida suka shiga mota tace “Ammi ashe a fili tafi kyau kin ganta kamar balarabiya”

 

Shiru Ammi tayi ita da kanta take driving dan ta lura faruk baya cikin hayyacinshi.

 

hannunshi ya ɗaura a gefen motan yana tuna abinda ya faru, ba abinda yake ɗaga mishi hankali kamar yadda yaga fuskanta ya kumbura, ga cizon sauro ga kuma abinda Umar yake mata, lumshe ido yayi yanajin kanshi yana sarawa, me zaiyi ya fitar da Amrish cikin wannan halin? yasan Umar zai fita tunda yanada Ammi kuma yana dashi, to itafa? batada kowa ba uwa ba uba, waɗannan matan da suka kawo mata abinci batama sansu ba a gidan marayu suka haɗu.

 

“ka daina ɓata lokaci kana tunanin wannan yarinyar wacce batada tausayi batada imani, kayi tunani akan ɗan uwanka, Faruk ban taɓa sanin kai soko bane sai yau, yarinyar data jefa rayuwar ɗan uwanka a wannan halin kake tausayawa? yarinyar data saceka ta rabaka da ƴan uwanka kake tausayi? ashe Umar ya fika wayo ba kamar yadda nayi zato ba?”

 

“Kiyi hakuri Ammi, Amrish ba kamar yadda kika ɗauka take ba, wallahi rayuwar yarinyar abin….”

ɗaga mishi hannu tayi “kada ka kara ambatar sunan wannan yarinyar a gabana idan ba haka ba saide kaje ka nemi wata uwar”

 

baisan abin har yayi zafi haka ba, gum yayi da bakinshi yana tunanin abinyi a cikin zuciyarshi, gidanta wanda yake ɗauke da dukiyan data sato yasa a bashi tsaro na musamman cikin sirri, yanaso ya cika mata burinta koda an yanke mata hukuncin kisa yanaso taji labari me daɗi.

 

 

Ɓangaren Amrish, ta gaida Ammi ne saboda tana mutunta matan, duk wanda ya taɓa taimako a gidan marayu tana bashi girma fiye da zato, har yau ganin darajan Ammi take dan ta ciyar da marayu, ba wai ta gaisheta dan ita maman faruk bane, kuma ko yanzu ta haɗu da ita zata kuma gaisheta saide karta amsa.

 

haka suke rayuwa cikin cell har sukayi sati ɗaya, Umar anyi magana kuma an duba baida laifi, gobe da safe zasu sakeshi, Amrish kuma an shigar da maganan kotu alkali ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, tunda faruk yaji wannan labarin ya gagara zama, bazai taɓa yadda a yiwa Amrish wannan hukuncin akan gaskiyan ta ba, waɗannan mutanen sun cancanci kisa.

 

Ammi cikin murna ta shigo ɗakin tace “faruk gobe zasu saki ɗan uwanka”

babu annuri akan fuskanshi ko kaɗan hasalima ya kwanta a gefen gado yana kuka kamar ranshi zai fita, jikinta a sanyaye ta karasa wurinshi ta ɗago kanshi, cikin sanyin murya da lallashi tace “meyasa kake kuka?”

 

“Ammi bazan iya faɗa miki ba saboda kince kada na ambaci sunanta a wurinki”

 

“kayi magana faruk meyasa kake kuka? baka murnan sakin Umar da zasuyi ne?”

 

 

“ina murna amma ita Amrish wa zai saketa? ya zatayi da rayuwarta? itaɗin marainiya ce batada kowa, batada me tsaya mata akan gaskiya take babu me fahimtan hakan sai wanda ya zauna da ita”

 

shiru Ammi tayi “bamu da hanyan taimaka mata koda tana da gaskiya, ba karamin laifi ta aikata ba, idan munsa baki laifin yakan iya juyawa ya hau kanmu, Gara muyi shiru mubar abinda zasuyi”

 

share hawaye yayi wanda rabonta da ganinshi yaka kuka tun rasuwan mahaifinshi, cikin lallashi tace “je kayi wanka kazo kaji”

tashi yayi ya shiga toilet bai wani yi wankan kirki ba ya fito yasa riga jallabiya yazo gaban Ammi ya zauna, pillow ta bashi tace ya kwanta, kwanciya yayi taga idonshi ya ɗan kumbura alaman jiya bai samu yayi bacci ba, hannu tasa a kanshi tana shafawa tace “zamuyi kokari muga abinda Allah zaiyi karka damu kaji?”

giɗa kai yayi da haka har yayi bacci zuciyarshi a cakushe.

 

 

 

 

_Hauwa shu’aibu jiddah✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button