Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 15

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 15*

 

 

 

“da kafa har ta isa bakin titi ta tari me taxi ta sanar mishi inda zai kaita, shiga tayi tana tsaki a ranta dan har yanzu tana jin zafi a jikinta, bayan sun iso ta biyashi kuɗinshi ta shiga ciki, ta gaji da zirga-zirga between gidanta da gidan marayu ya kamata tasan abinyi, tana wannan tunanin har sukaci karo da shugaba, kallonta tayi “Amrish daga ina da sassafe haka?”

kai kasa tace “wallahi shugaba naje neman kosai ne”

 

murmushi tayi tace “Amrish rigima dakin aika yara ai zasu siyo miki”

“ba zasu dawo da wuri ba siyasa naje da kaina”

 

“to hakan yanada kyau ya kamata ma a fara soya kosai da safe dan nasan mutane dayawa suna son kosai”

 

“eh wallahi shugaba ko Unty sadiya ma tanaso”

 

“to shikenan yau zan faɗawa masu girki su rinƙa sa kosai a ciki”

 

taji daɗi sosai matan tana son su, batasan itace take ɗaukan nauyin gidan ba amma ta saki jiki da ita harma tana cewa zatasa a fara yin abinda suke so na breakfast hakan ba karamin darajan matar bane ya karu a idonta.

 

Bayan ta shiga office ita kuma Amrish ta wuce cikin gidan, da kallon tuhuma Unty sadiya ta bita, cikin ranta tace “na shiga uku”

 

zama tayi a gefenta tama murmushi, murtuƙe fuska unty sadiya tayi tace “aina kika kwana?”

 

“gidan shugaba” ta tsinci kanta da faɗan haka, sai a lokacin ta saki fuska tace “meyasa baki sanar min ba?”

 

“wallahi na tafi ba shiri ne time data kirani ina can bakin pompo, kuma banyi tsammanin zan kwana ba dan aikine ya rikeni nida ƴarta mukayi ta gyaran naman da zasuyi miya dashi yau shiyasa na zauna acan”

 

“okay ai na zata wani wuri kika je har na kwana cikin fargaba”

 

“a,a babu inda naje”

tayi magana tana ɓoye jikinta ta yadda ba zataga shatin bulala ba, ɗaukan najma tayi wacce take mata dariya tace “kin sanni ne? kikemin dariya”

wasa ta fara yiwa yarinyar da haka har ta samu ta sulale daga wurin bataso unty sadiya taga shatin bulala a jikinta, ɗaki ta koma ta zauna tareda kwantar da najma a jikinta tana tuno abinda ya faru tsakaninta da umar ne ko faruk bata sani ba, abin ba daɗi dan da bai ɗaureta ba da yau yana kwance a kabari.

 

so take kota halin kaka ta gane wayene me laifi a cikinsu, ga kuma tunanin yadda zatayi da tulin kayan data ɗibo daga gidan gomnati, da manyan masu faɗa aji, so take ta cire ta siyar ta gina babban makarantan marayu amma ta rasa yadda zatayi ta fara.

 

tayi kwana biyu bata leka gidan can ba tana gidan marayu a zaune abinta da ƴan uwanta yau tasa a ranta zataje ta duba gidan, da yamma sosai ta sulale ta fita, taxi ta shiga har kofan gida ya kaita, saida ta biyashi ta shiga gidan.

 

 

a falo ta ganshi kwance sanye da boxer yana karanta jarida, kallo ɗaya tamishi sannan ta watsar tace “kasa riga”

yi yayi kamar bai jita ba itama bata kuma yin magana ba ta shiga ɗaki ta duba komai yana mazauninshi sannan ta fito taga yasa jallabiya maroon tace “zaka iya tafiya a duk lokacin daka so”

 

ya bari ta iso bakin kofa zata fita yace “bazan tafi ba sai kinyi hukuncin daya dace dani”

 

“ba zanyi hukunci ba saboda ba kaine me laifi ba, hukunci yana kan mai laifi ne”

 

“nine mai laifi kawarki teema nine na fara ɓata mata rayuwa, Umar nine doctor shikuma faruk shine soja ki daina wahal da kanki”

 

“ba wahal da kaina nake ba, abinda naga ya dace nakeyi, zaka iya tafiya a duk time ɗin da kaso”

fita tayi daga ɗakin ta wuce bayan gidan inda yake ɗauke da lambu kayan itatuwa dayawa, wani bowl ta ɗauka ta fara tsinkan inibi da saitun, ayaba da rabina shima ta tsinka ta cika bowl ɗin dashi take bakin swimming pool ta ɗibi ruwa ta wanke, komawa gefe tayi ta zauna kan grass carpet ta fara ɗauka tana ci, sunada zaƙi lumshe ido tayi, rayuwar duk ta fita a ranta dama burinta ta gyara gidan marayu ya shiga hannun mutane masu imani to Allah ya cika mata buri yanzu batada wani burin daya wuce ta gina school wanda zasuyi karatu kyauta ba tareda sun biya ba, daga nan saita miƙa kanta wa ƴan tsaro suyi mata duk hukuncin da sukaga zasu iya, domin itaɗin mai laifi ne, ba zatayi haka ba saita cika burinta ta miƙa kanta wa ƴan sanda.

 

hannu tasa ta share hawayen fuskanta sannan ta kalli gidan da take zaune a ciki, anan ya dace tayi nursery da primary idan yaso sai a nemi inda za’ayi secondary, sunan nursery zatasa Na’eem and Aliyu nursery school, yaran da manya suka yiwa fyaɗe ta hanyan luwaɗi har suka mutu, na primary kuma zatasa Manal and Feenah primary school, manal wacce akayi kawalcinta har tun tana yarinya akayi mata fyaɗe da feena wacce suka yankewa hannu suka tafi saudiyya da ita har yau babu ita babu labarinta , sai secondary kuma tasa zainab and teema secondary school, zainab wacce ta bada rayuwanta domin taimakon yara ƙanana, zatayi high institution shikuma zatasa Orphans university ma’ana jami’an marayu”

 

tana tunanin hawaye yana wanke mata fuska har yana jiƙa gaban riganta, kai ta ɗago ganin yana miƙa mata tissue, kallonshi tayi bata karɓi tissue ba taci gaba da kuka tana sharan hawaye, zama yayi a gefenta yasa hannu cikin bowl ɗin ya ɗau ayaba ya ɓare sannan ya kai bakinshi ya fara tauna hankali kwance yana kallonta tana sharan kwalla.

 

saida ya cinye kusan uku kafin ya ɗau inibi ya fara sha, saida yasha kusan rabin bowl ɗin ya ɗau zaitun yanaci yan lumshe ido, batayi mishi magana ba taci gaba da kukanta, bai bar komai a bowl ɗin ba ya cinye tass yana kallonta ya kara sa hannunshi a roban bowl ɗin ganin ba komai cikin mamaki ya ɗago kai yace “laa ya kare”

kallonshi tayi, yayi murmushi wanda ya kara fito da asalin kyaunshi na bafulani yace “kinga yadda na cinye wannan fruits ɗin ba tareda na sani ba kuma ban ƙoshi ba? to haka rayuwarki zata kare, bakisan me kikayi ba kina tunani kina kuka, abu ɗaya da zakiyi kiji daɗin rayuwa shine jajircewa da dauriya da kuma yadda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, saɓanin haka zaki kare rayuwarki ne cikin kunci akwana a tashi kizo kina tsanan kanki, tabbas mutane sun miki laifi to ai laifin da mutane suka miki shine rayuwa, idan kina zaune ba’a ɓata miki rai kuma ba’a yimiki laifi ta yaya zaki ɗau darasi a cikin rayuwa?

Amrish zama na kwana kaɗan da nayi dake na gano ke ɗin macece jaruma keba raguwa bace kinada zuciya kuna kina aiki da hankali, kamar yadda kikayi kika ɗibo wannan tulin dukiyan daga gidan manyan mutane haka zakiyi amfani dashi ko gina rayuwan mutanen da suke da bukata koda kin mutu babu wanda zai manta dake.

 

nasan akwai zafi maraici dan nima na tashi ba uba, to amma babu maraya sai rago, ki tashi ki daina kuka ki manta da baya ki fuskanci gaba, sawa a rai sai kin ɗau fansa ba shine ba, ni nan da kike gani na daɗe da sanin kece kike kisan barinki kawai nayi dan nasan kinada hujjan yin hakan.

 

na gano hakan ne ranan dana fara duba cctv footage a gidan Alhaji hamza naga duk yadda kukayi dashi kuma nasa a kunnena naji duk yadda kukayi, hatta lokacin da kikaje gidanshi na sani, na kyale abin ne saboda nasan kinada hujja kuma ya cancanci kisa, amma fa ɗaukan doka a hannu ba kyau, zoben hannunki na gani a gidan hajiya Halima ranan da aka kasheta, da kaina na ɗau zoben na kai kofan office nata a gidan marayu ina sa ido naga wanda zai ɗau zoben sai naga kinzo wucewa, a tsorace kika ɗaga zoben kika sa, tun daga lokacin na fara bibiyanki duk inda kikaje, akwai ranan da akayi sanyi sosai kika wurga dutse masu gadi suka bar mutum ɗaya nine naje wurin na nuna musu id card nawa na jasu da hira dan ina jira ki fito ki tafi ba tareda an kamaki ba, sai kuma naga kin fito kin gudu daga nan nayi musu sallama na tafi, bakisan wannan zancen ba amma ni nasan komai a kanki Amrish, abinda ya bani mamaki shine yadda ke ɗaya kika zama mutum biyu wato Ameera da Amrish”.

 

 

“da kanki kuma kika kara sanar min ke ɗin kina kisa kuma kina sata, a lokacin na yadda da magananki Amma na nuna miki kamar da wasa kike, kinsan dalilin da yasa nayi hakan?”

 

shiru tayi ta zuba mishi manyan idonta tana kallonshi cikin mamaki da tsoron abinda yake faɗa mata, murmushi yayi yace “saboda na wanke ɗan uwana a wurinki wato Umar”

 

nasan Umar yayi laifi hakan yasa na karɓi hukunci a kanshi, ina son Umar sosai banason abinda zai taɓashi domin shine babba akaina, a haka ya hakura ya barmin girman ya zama nine babba, ni nake amsa sunan babba akan Umar, dan Allah ki cire idonki akanshi kinji?”

 

ba zato ba tsammani yaji ta faɗa jikinshi ta fashe da kuka sosai tana ƙankameshi, zubawa bayanta idanu yayi yana jin sautin kukanta yana ratsa jikinshi, a hankali ya ɗago hannu yasa a bayanta yana ɗan taping, cinin muryan lallashi yace “is okay”

 

“dama kasan wannan labarin kayi shiru akai? meyasa baka mikani wurin ƴan sanda ba? meyasa ka rufamin asiri?”

 

“ki daina kuka nasan an zalunceku shiyasa na ɓoye komai daya shafi case ɗin, duk wani alama ko shaida na kawar dashi nasan idan an kamaki dole zaki ambaci suna yayana a cikin masu laifi”

 

sakinshi tayi tace “kenan kayi haka ne dan ka kare yayanka?”

 

“bakiyi laifi ba idan kince haka, amma ni nayi ne domin nasan bakuda laifi”

 

share hawaye tayi “ta yaya zan yadda da kai? ta yaya zan yadda cewar ba tuggu kake haɗamin ta yadda zaka mikani wa ƴan sanda kai tsaye ba tareda wani fargaba ba?”

 

“ta yadda kika yadda dani ta haka zaki yadda dani”

 

bata gane zancenshi ba, zuba mishi ido tayi tace “to meyasa ka yadda ka zauna dani?”

 

“na yadda ne saboda nasan kina cikin kaɗaici zama ke kaɗai zai iya sa miki wani tunani wanda bai dace ba, kizo ki aikata abinda zakizo kina dana sani”.

 

 

 

_hauwa shu’aibu jiddah 08144818849_

Leave a Reply

Back to top button