Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 25

Sponsored Links

025
___________________
Dr Adnan Yana dawowa daga wajen aiki a gidan sayyida yayi branching bayan ya tsaya a Kasuwa yayi mata siyayya.

Knocking yayi a ƙofar main door ɗin ,ya tsaya yana waya da kyakyawar larabcin sa cikin nutsuwa.
A haka tazo ta buɗe masa ƙofa.
Bai sallama ba itama bata tankasa ba har ya shigo yana cigaba da wayarsa ga dukkan alamu yana magana ne da mutum ne mai muhimmanci a rayuwarsa.
Wayar na manne a kunnensa ya miƙa mata jakar hannunsa mai ɗauke da siyayyan da yayo mata .
Sarara tayi ,tai ma kayan lalataccen riƙo cikin mamaki take karanta sunan store din da akayi sayyayan ,babban store ne na gaske .,ɗan ɗage mata gira yayi yana mata nuni da hannu alamun ta buɗe.

Kayane abayoyi guda uku,ɗan kunne ɗan kukub a cikin box ɗinsa da zobe ,sai ɗaukan ido yake bai wuce yayi rating 1.2M ba Amma yana da ɗaukan hankali .sai takalmi ɗan Dubai mara nauyi guda ɗaya sai tarkacen kayan kwalliya da turaruka da mayukan wanke gashi,set ɗin gyaran ƙumba da sauran su.

Cikin rashin fahimta tace “Na meye wannan ? ” daidai sanda ya sauke wayar a kunne alamun ya gama wayar “Nakine na siyo maki ”

“Akan me? Harda ɗan kunne da zoben gold da wannan tulin kayan kamar mai shirin haɗa lefe?”

“😃Godiya ne bisa karamcin da kike nuna mun,duk da baki Sanni ba,ta iya yiwuwa Ni mugune amma kika rike Ni zuciya daya matsayina na makocin ki ,I’m really grateful ”

Rau rau idonta yayi da ƙwallan murna “Awwwn Nagode Nagode ,Allah ya biyaka da maɗaukakin Alkhairi yasa ka gama da tsofaffinka lafiya…Wai dama haka maƙota suke kyautata ma maƙotansu ? Kodai nice nayi sa’an nawa maƙocin…?”

“Bakiji hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ba akan muhimmancin maƙoci?…Indai har zan maki wannan to jin daɗi na ne,kisa ki gayu abunki kinji ”

Zaro ido tayi “Wow kana nufin wai in ringa gayu da gold ear ring a gida ba sai tani unguwa ba?”
“Eh mana! Meye amfanin kayan gayun da bazaa sakashi ba sai za’a fita”

Marairaice fuska tayi tana daɗa jujjuya kayan tana masa godiya ,cikin ƙwalla
***
Ƙarfe 6pm Na yamma Sayyida Salima ta zauna tasha wankanta ta wanke gashinta tas da mayukan wanke gashin da Dr ya siyo mata tayi amfani da hand dryer ta busar dashi ,ta gyara gashinta ta tsaga ta gaba ta kwantar da gashin tayi edging Mai kyau har wajen sajen ta ,kana ta zaɓo abaya mai ruwan jinin kare cikin kayan da Dr ya saya mata ,ta maƙale ɗan kunnenta da zoben gold ,ta gyare fuskarta da light make up ,powder da wet lips sai tozali da mascara.

Tsaywa tayi a gaban mirror tana kallon kanta tana feshe ilahirin jikinta da turare ,tana mamakin dama haka take da kyau? Dama matan nan da suke flexing a shafukan IG dasauransu ba abunda suka fita dashi sai wanka da iya saka sutura?

Tana tsaye tana admiring kanta bataji buɗe ƙofar Ya Sheikh ba saidai ganinsa tayi a ɗakin ya shigo cikin kumfar baki zai mata masifa ,ta ƙure can ciki tabar ƙofa a buɗe kalan tana can ɓarawo yazo ya cire masa TV ko AC

“Salima wani irin Issk… ” kasa ƙarasawa yayi ganin kyakyawar dirarriyar mace a gaban sa sai zuba ƙamshi take bakinta na sheƙin man leɓe.
A sanyaye kamar wanda aka zare ma ido yace “Kinyi kyau abinki cif cif” yana maganar yana cigaba da ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa

Murmushin jin daɗi tayi ,gamida masa fari da ido “Hm Nagode”

“Aina kika samo kyawawan kaya haka? Waya baki aro?”

“Aro kuma? Wallahi sabon Maƙofcin nan namu ne ya siya mun…ka gansu kyauta🤗”

Ranshi ne yaji haka kurum ya tsinke ,a hassale yake tambayar ta cikin tabbatarwa
“Maƙofcinmu…?” Jinjina masa kai tayi tana washe baki
“Maƙofcinmu dai?”
“Eh mana😠”
“Tohpah me yake so da ya baki sabon kayan nan,kamar ma ɗan kunne nake gani da zobe”
Faffaɗan Murmushi tayi har ana gani duk haƙoranta ,da sauri ta kai idonta kan yatsunta tana wasa da zobenta “Eh Zobe da ɗan kunnen Gwal ne ,wai na godiya ne da yanda muka karɓe shi da karramawa ,while bamu sanshi ba ,Ya Sheikh kaga muhimmancin girmama mutane ko? Ɗan adam daraja gareshi…”

“Yehhhn ….Yi mun shiru”! Ya kwatseta cikin tsawa
“Wai ke wani abu ne ne ne kike mun kwana biyun nan? Waye ya baki lasisin ringa kula wancan gardin? Sai wani kuyi ta magana ba tareda izini na ba …meye hakan kenan ,baki san darajan igiyoyin auren da suke wuyarki ba ko?”

“Haba ya Sheikh Ni fa ba yarinya bace ba ,ina da tunani kafin in Yi abu mutumin nan baida matsala….”

Cikin hargagi ya karɓe maganar “Amma kuma Ni mijinki ne ba ….eh Aljannarki na ƙarƙashin ƙafata,da kin matsa mun sai in take!!!”

“Ko Allahn da ya halicce ni ya halicceka da wuta da Aljannar yasan abunda nayi ba laifi bane ba ,Kai wai me yasa ka faye bauɗewa ne? Gaba-daya ka fiye musu ya Sheikh ”

“Saboda ban yabi kayan nan da mutumin nan ya baki bane kike cemun mai bauɗaɗɗen hali? Na tabbatar duk an ƙi siyansu ne yaje ya samo maki shi sharan kasuwa ke ga matar Sheikh baki gayu an kawo maki ki gayu…..kin saka jan kaya sai kace ƴar ƙungiyar asiri ,kin wani taje gashi duguja kamar dorinar ruwa”

“🤣🤣🤣” dariya ta fashe dashi har tana kwanciya a kasa

Sakin baki yayi yana kallonta ,yana tunanin ko Aljannun nata sun tashi ne

“Ya Sheikh 🤪🫵🏻Ya sheikh🤣🤣🫵🏻…” tana dariya tana kiran sunanshi tana nunasa da yatsa tsabagen dariyar ƙeta ta kasa maganar dake cikin ta .

Ɗaure fuska tayi yana hura hanci ,ransa in yayi dubu ya ɗugunzuma.

“Ya Sheikh yaushe ka fara kishina?…kishi fa kake yi da Adnan ya sheikh ”

Duburburcewa yayi yana nuna ƙirjinsa da yatsa

“Ni? Miqdad inyi kishi ,Allah ya tsare Ni ….,tafɗi😃😃🤣🤣🤣😂 kawai sai ya kama dariyar tusa haushi ,kana ya ɗaure yana nuna ta

“Salima gwara ki ƙara kallon kanki da kyau a madubi wallahi da Aljana kikayi kama”

“Saboda kyau ba,kasan ƙurewar kyau kai kama da ƴar Sarkin Aljanu…..wuwuuuu🐾👺 Ni Aljana ce wuwuwuwww zan haɗiye ka” tana magana tana tanƙwara yatsu tana zazzaro ido tana hura hanci kamar yanda ake firgita yara .

Matsawa ya somayi da baya da baya har ya jingina da jikin cupboard

Itakuma ta raɓeshi ta fice tana surutai cikin dakiya ba sauran Alamun wasa kuma “Hmmm wannan baƙar kishin da zargin na menene?”

Sakin baki da hanci yayi yana kallonta Saida ta wuce sanann ya soma ƙwankwasa kansa “Tabbas Salima ba lafiya”

Komawa kan gado yayi ya rafka tagumi ,cikin tunani gamida zullumi“Yaron nan fa ya ciko wuta,yana neman ya lalata mun mata ta ringa neman fin ƙarfina…anya bazanje har gida in sameshi ba kuwa?

Zumbur ya miƙe ya shuri takalmarsa ,ya fice daga gidan sai gidan Adnan…..tsabagen sauri bai tsaya knocking ta jikin gate ba sai kawai ya kama gajeran katangar gidan mai kama da na turawa da bai wuce tsayin yaro ɗan shekara goma ba,Haka ya kame masa katangar gida ya ɗirka cikin tsakar gidan.

Adnan Yana zaune daga varendar ɗin shi akan farar kujerar roba ,yana sababben aikinsa wato waya.
Kawai yaga magidanci ya kamo masa garu ya dirko masa katanga.

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button