Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 11

Sponsored Links

011
___________________
Tunda Dr Adnan ya fita ,Sayyida ta kasa zaune ta kasa tsaye ,wani irin farinciki take ciki ,har hawayen daɗi saida tayi ,a daidai lokacin da mijinta ya bata 500# ta siya naman da zata ma surukuwarta abinci ,nadama ya shigeta na tunanin rashin aikin yi ,da tana da aiki da yanzu saidai ta cika ta siya desired quantity da takeso ,saidai kafin hawayenta su ɗiga na tsantsan damuwa sai Allah ya turo mata Adnan ya Bata dreamt money da zai isheta kaf siyayyarta that will impress her Mother inlaw, lallai bazata manta da Adnan ba , kirkinsa na musamman ne ,kwata kwata ba irinsu ɗaya da Ya Sheikh ba ,maƙoƙo.

Da wannan farincikin ta tafi kasuwa ta siyo cefanen en gayu….lol
Ta ɗebo kayanta a hannu ledoji bibbiyu ,ta miƙo titi biya_biya da hijabi ,kaf kudin sun ƙare don haka ba kuɗin ɗaukan taxi saidai ta dako sayyadodinta 🦶🏻

Tana cikin tafiya taji horn ɗin mota a bayanta “Ɓiiiiy,..Ɓiyyyyyy”

Waigawa tayi da sauri itadai a tunaninta ai bata hau kan hanya ba ,to meye na mata horn kamar wata mai laifi?

“Saleemart?”
Sanyayyen muryarsa ya daki ƙoƙon zuciyarta ,a ranta ta maimaita “Tabarakarrahman ! Tsarki ya tabbata ga Allah da ya iya saisaita murya mai daɗi a maƙoshin kyawawan maza ” kafesa da ido tayi ba tare da tayi magana ba,fuskarsa yayi mata kama da wanda ta sani amma a’ina shine bata sani ba.
Leƙo da kansa yayi daga cikin motar
“Saleemart Ina zaki haka ,ke kaɗai da ranar nan ina Ya Sheikh ɗin naki”

Tanajin haka tasan wanda ya santa ne don haka ta washe baki as usual ,faraa available

“Yana Wajen Da’awa”

Ɗaure fuska yayi kamar garwashin wuta
“Nace in bai iyawa ya barmu a filin nan yaja gefe…..(Sai kuma ya ɗaga murya cikin fushi)…Shine ya barki kike yawo a ƙafa? Kamar ma dai kallon rashin sani kike mun ko? Bakijin sunan Ambassador a bakin mijinki? I’m his close friend”

“Oh Ambassador😄Wallahi daga kasuwa nike fa ,kuma dai ai ba nisa ,shine nace bari in ɗan yi tracking zuwa gida ,kasan tafiya ma part of exercise ne”

Fitowa yayi daga motar a furgice kamar yaga abin tsoro “Sukuma kayan nan masu nauyi fa? Me yasa bazaki iya ordern ride ba ko kiyi hayan taxi…oya now”

Yanda ya haƙiƙice yana faɗa kamar tayi wani gagarumin laifi shi ne ya bata dariya ta kuwa fashe da Dariya

“Hehehe , Ambassador kenan , atleast kasan dai abokinka indai kudin da ya bani na samu ya isa cefane meye aibu dan na biyo hanya a ƙafa? Ni wacece da sai nayi ordern ride?😃😃 Kana da ban dariya wlh mtseww”

“Uhm kuma fa kina da gasky ga kaya sunyi tsada a kasuwa” Yayi magana kamar wawa saboda yayi daidai da tunaninta

“Ehen ashe ka gane,indai har kudin zai isa ayi siyayya ba sai ayi maleji ba,Ni kuma ina tako a ƙasa”

Haka ne now,shiga mota in kaiki gida it’s sunning”

“Karka damu ai na kusa gida ka barni in ƙarasa kawai”
Sa hannu yayi ya karɓe ledan hannunta
“Na tsani gardama karmu fara kinji?…ko Matana bazan barta tana wahala ba,to kema kamar Matana haka nike kallonki ” a tsorace ta ɗago tana kallonsa.
Sosa ƙeya yayi sai ya wayance da cewa “Tunda ke matar abokina ne ,Miqdad”
Rausayar da kai tayi ta ɗan saki Murmushi suka shiga motar ya soma driving a hankula kamar yana tuƙa ƙwai ,kar yayi giji_giji su gogi junansu su tittiske. Ya bata haƙuri kuwa ba adadi ,yaja tsaki uncountable duk don tayi tafiya a kafa da kayan nauyin nan.

Itadai Salima haka ta sunkuyar da kai ,amma dai tabbas kwana biyun nan zuciyarta yina mata rauni ,Sanda ta haɗu da Adnan ya gwada mata halin kirkinsa da ta alaƙantashi da mijinta sai tace Adnan na musamman ne ,dabam cikin Mazan duniya.
A yau kuma da Ambassador yake gwada mata yanda ake ririta mace sai tunanin ta ya daɗa hautsinewa ,anya ba nata mijin bane ya fita dabam cikin sahun Mazan duniya ba? Duk Mazan kirki garesu natane na dabam?

A haka ya sauke ta a gida yana mata barkwanci zan dawo cin abincin nan ,nasan yanda zaki rikita abokina a bed haka Zaki rikitashi a table da delicious girki ,so ayi sanwa dani fa ,I’m foodie kuma raina ya biya😉😋” ya kare magana yana kashe mata ido guda yana lashe lebe kamar tsohon maye ke ba sai an fada maki ba wannan yayi haddar sace zukatan matan mutane .

Girgiza kai tayi ta sunkuya ta ɗauki kayanta “InshaAllah zanyi da kai ….Ma’assalamah”

“Ke Ni ban wani jin larabci in dai muna tare ayi turancin ko Hausa kawai” yanda yayi magana yana tutturo baki shi ya bata dariya ta kuwa dara 😆😆

***
Ambassador yana dauke Salimart ya zarce Office ɗin ya Sheikh yana tsakiya da sorting sunayen en agaji da zasu tafi masallatan jumu’a .

“Aah abokina kaine har Office ? Lallai yau za ayi ruwa da ƙanƙara”

Ɗaure fuska yayi ya samu kujera suna kallon juna ya ɗan mika masa hannu sukayi musabiha

“To yane!? Na ganka kamar bakada walwala”

“Bros, yanzu ina hanya na haɗu da matarka ta fito daga kasuwa da kaya niƙi_niƙi a hannu”

“Oh Salima baiwar Allah😃 Eh wai za ayi ma surukuwa girkine ,wai bata cin kwanannen miya shine fa aka matsa mun saida na bada 500# a siya nama”

Ƙwaƙwalwarsa daɗa hautsinewa tayi don haka yace
“Hum dakata Ni wannan ba shi ya dameni ba….. Miqdad ta yaya zaka bar matarka tana zuwa kasuwa da ƙafa ehen meye haka wannan fa kamar mugunta ne”

Harɗe giran sama da ƙasa yayi “Malam,ji mana, yanda fa kake sakin baki kana jejjefe mun magana son ranka a sha’anin gidana yana bani mamaki. Ita tace maka ban bata kudin mota ba ehen?”

“Ai ba sai ya fada ba,ga dukkan alamu kudin ya yanke mata ne…..amma kaima zuwa yanzu yaci ka gane matarka nada kawaici ,shekara uku fa kuna tare ba kwana uku bane ba,watarana zata soma tara yara haka zasuyi ta wahala a ƙafa….? Alhaji ka siya mata mota mana full the tnk,ka Bata personal Atm card ,dik inda zata tayi siyayyarta enough bata tunanin yankewar kudi, shikenan fa ka sallameta”

“Hhhhh mtsew ,Bros kanayi Kamar bakasan mata ba,sufa matsalar su basu iya tayi bane ,da sunje kasuwa in an fada masu kudin kaya kawai sai su miƙa bazasu ɗan latsa ba ,nawa wannan kaza NE ,sai su miƙa kudi irin ga Hajiyar nan matan mai kudi ,takama!!! Humm kayi amfani da tunaninka🧏‍♂️”

“Anyways, kasan dai Saleemart tafi ƙarfin shiga local shaguna tana taya kayayyaki ,ya kamata ne tana shiga super market tana siyan kayayyaki original ba ana bata jabu ba in low price ”

“Taf a hakan ma ana cutanta ina ga ta shiga super market hmm”

Harzuka ambassador yayi ya soma jaraba
“Miqdad kaifa babban yarone ,karka shige leman Muslunci ka fake da haka kana cutar da matarka,kana da kudin nan you’re dealing with millions meye haka? Kana hawa manyan kaya ,jibi motarka latest amma kana gidadantar da matarka wannan zalunci ne…”

“Ahh ahh ahhh,kaga kaga dakata dakata…matarka ce? Nace saleema matarka ce? Infact kana ma da aure ne ? To wannan magana akeyi ta ma’aurata ka bari idan kayi auren mayi maganr 🧏‍♂️”

“Oh gori zakayi mun😳😞to shine your eyes in Nayi aure zakaga yanda ake ririta mace ahaaa ”

“Mens calm down nariga da na gama maganar yanzu ka bari sai kayi auren sai mu cigaba ,lokacin ne zaka gane yau da gobe yafi ƙarfin wasa kuma ciyarwa kullum zaka ciyar da mace is not easy”

“😏Nidai gama muje inja girki sbd nace mata ma ina dawowa ayi sanwa dani”

Rass! Gabansa ya faɗi ,shknn yau tiya ma ƙila zata dafa ga buhun shinkafar ɗazu da na shiga kicin na ɗan girgiza naji ya auka ,waima yaushe kwata kwata na siyo shinkafar nan 50k?

Alhaji ya naga kana ta zufa ,a kara AC ne? Me ya sauya kane ,kamar a furgice kake?”

“Oh No…No…No it’s okay

“Wai Matar mutum tana yawo kasuwa da ƙafa kai ma meyasa bazaka ringa zuwa Office a ƙafan ba….”

“Ahnnnn 🤦🏻‍♂️wayyo Allah zaka kashe Ni da baƙin nacin tsiya,inasha mun gama maganar nan kuma?”

 

Oum Aphnan✍🏽
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button