Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 23

Sponsored Links

023
____________________
Yareema
Motar Yareema ita kaɗai tal ,take sharara gudu a biya kwaltar cikin garin ,ba motocin masu bashi tsaro yau fitan daga shi sai Amintaccen yaronsa Jabeer ,shine ma yake tuƙasa a motar shi yana ta baya ,idanuwarsa kar akan kwalta baya ko ƙiftawa,Kai daga ganinsa kasan yana cikin damuwa amma yanayin fuskarsa da fushin sa da baƙin halinsa na dindindin yasa mutane basu gano tashin hankalin da ya ke ciki ba.
***
“Waziri,wannan fa ba abu bane da zamuyi shiru mu ƙyale ya cigaba da faruwa ba,Yaron nan Yareema kowa tsoronsa ma yakeji ,kenan mu bazamu tsawata ba ,har sai ya zama yayi riƙan da ya ƙwace a ikon mu…?…bazai yiwu ba!”

Waziri kallon Galadima yayi da yafi kowa fusata a cikin taron manyan fadan,wanda suka taru a gidan wazirin a safen nan don tattauna matsalar Yareema da yake neman Gallazar kowa a gari.

“Galadima! Na fada maka Yareema fa baifi ƙarfin mu ba ,kawai muna bi ne a hankali ,saboda en gaza gani…kuma ma ai bamu isa muja da ikon Allah ba,in Allah yasa Yareema zai sarki babu ja…in Kuma baida rabon sarauta ,tijaransa da Izzarsa bai isa ya bashi ba”

Ciroma da sauri ya amshe maganar da cewa “Muma ai ba ja da ikon Allahn muke ba ,amma gasky ɗaya ce daga ƙinta kuma sai ɓata …..kowa yasan Yaron nan Yareema Asalinsa fa soja ne,kenan mulkinsa zai zama mai zafi,kowa yasan mulkin soja akwai tsanani talakawa nashan wuya….Shi yasa Ni ɗabiunsa basa bani mamaki ,yana da gautsi sam ! Baya mulki irin mulkin sarautan babanshi….In fa yana ran gadi ,da bindiga yake yawo!!! Waziri wlh! Idan Yaron nan ya zama sarki ba mutane ba mu kanmu kashinmu ya bushe…”

Galadima katse Ciroma yayi da cewa “Don Allah mu tsagaita maganar nan,ynz dai ina mafita? Kunsan cewa dai sauratar nan gadonshi akeyi tun iyaye da kakanni bawai zaɓe akeyi ba ,don haka Yareema shine kaɗai ya cancanci hawa gadon mulkin nan ,to mu tayaya zamu tunkuɗe faruwar hakan?…”

A fisace Fagaci ya katse shi “Ban yarda da maganarka ba Galadima ,mu ne masu naɗa sarki ,mu muke da damar ɗaura sarki ,in muka soke mu din nan ta soku…don haka Yareema bazai zama sarki ba da wannan ɗabi’un nashi gwara ma ku sauya tunani”

Ciroma ɗaga ma Fagaci hannu yayi “Yi hakuri Fagaci nasan kana da zafi,Amma ga mafita”

Kowa gyara zama yayi yana kallon Ciroma

“Tunda dai mu ba ƙwace masa sarautarsa muke son muyi ta ƙarfi ba…ina ga me zai hana mu haɗa kan mutane suje su sameshi su tattauna a masa nasiha ya daina abunda yakeyi ba”

“Ehen kaji batu mai kyau,naji dadi da kuka gane ba abu mai sauki bane mu tunɓuke Yareema a kujeran ubansa ba……to tunda Ciroma ka kawo wannan shawara mai haske ina ganin abunda za ayi mu tsaida ranar da zaka shugabanci mutane kamar bakwai ,aje wajen Yareeman ayi masa magana gemu da gemu” cewar waziri

Yaƙe Ciroma ya soma yi “Wannan abu yayi kyau sosai wlh….saidai wani hanzari ba gudu ba ,kasan dai Ni matafiyi ne ,zai iya yuwuwa ranar da za’a yi meeting din bana nan,kawai dai waziri kaine shugaba inaga kawai ka jagoranci zaman dole ya saurareka”

“Haba meye haka ? Aini ba tsaranshi bane ,saidai tsohon sarki da yana da lafiya tabbas shine zan sama kai tsaye amma yanzu da tsufana sai aga naje Ina ma Yaron nan magana haba ai baiyi ba…duk gakunan,Fagaci,Ciroma ,Turaki ga galadima ,a cikinku za’a fidda wanda zai jagoranci zaman dole!….” tsuru tsuru sukayi da ido kowa yaƙi magana. Wannan yasa waziri harzuka

“Shiknn a matsayina na waziri na zartar Galadima yaje ya magana da Yareema ,tunda dai shine mai ilimin fada kuma akwai baki,tunda ai ɗan jarida ne ,nasan muna da kyakyawar wakili….”

“Yawwa haka ne kuwa mai girma waziri” duk sauran suka amsa

Girgiza kai Galadima ya shigayi ,yana karkaɗa ƙafa daga kan kujeran da yake yana faman hura hanci har saida yaji sun natsa da Hayaniya sannan yayi gyaran murya

“Hmm kazaɓo wanda zai iya cin zarafin Yareema kuwa….amma kasan sai Ni Galadima ina da mugun fushi ai ko?ta yaya zakace inje in samu yaran nan da bashi da kunya bayan kasan ina da fushi…?So kake Yaron nan ya fada mun magana in Yi fushi in kakkarya shi? Wallahi in yanemi mun rashin kunya ɓaɓɓalashi zanyi ,sai na kashe shi a ƙarshe ace Galadima ya kashe magajin masarautarku…” kallon juna sukeyi suna caɓe baki irin tabi ta farkon kunni ta fita a ta hagu

“Waye yariman ? Yariman banza da wofi… Ni ba sai in kashe banza ba..”

“Kai don Allah ka dame mu da barazana ,Dukkan mu tsoro ke ɗawainiya damu,kowa sai….sai…sai….” kasa ƙarasa maganarsa yayi saboda hango motar yarima da yayi ta shigo harabar gidan wazirin

Yanda bakinsa ya kama rawa yasa kowa waigawa yana kallon ƙofa….Tsit sukayi tamkar ruwa ya cinyesu ,Turaki kam hannu yasa ya kanƙame kujeran da yake kai ,sai maimaita duk addu’ar da yazo bakinsa yake yi a zuciya ,wani irin gumi yake tsatsofa masa….tsoronsa ɗaya kar yarima yaji maganarsa sanda yake masifa n Nan

Jabeer yana faka motar ya fita da gudu yaje ya buɗe Boot ya kinkimo dankareriyar kujeran royal Amma mara nauyi an masa adon gwal. Ya taho gaban tsofaffin ,ba tare da yayi masu magana ba ,ya kafe kujeran a gabansu
Sannan ya sake runtumawa da gudu ya bude gidan baya,cikin tafiyar ƙasaita ya shiga takowa inda suke yana tafe alkyabbarsa na sharar ƙasa.

Da wani irin Almighty murya ya ke masu magana a daidai sanda yake tunkaro inda suke zaune.

“Duk na fahimci dalilin taruwarku a nan wajen….Sbd Ni ne …Ni…Ni sarkin ku” ya kare magana yana zama a kan kujeran gabansu jirim kamar namijin zaki.

Yanda ya zauna jirim da ƙarfin Allah saida kaf gabansu ya fadi ras!

 

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button