Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 20

Sponsored Links

020
____________________
Yanda taga yana yi ,ita kanta ta firgita,kamar wani Mai mood swing? Da sauri ta ɗaura towel dinta tayi falo da gudu.
Yana jin ta rufo ƙofar,ya bude ido gamida sakin ajiyar numfashi ya zauna ya rafka tagumi ,sam bayason tunano abunda suka faru ma,duk Izzah na nake goga jikina a jikin wannan ƙazamar? Ina izzar take ,I went badly on her meye hakan?

***
12.20pm
Ya shigo ɗakin riƙe da kaya a leda ,yana zuwa ya cilla mata
“Dress well Zaki tafi gida bayan an fito sallah”
Full of joy ta sauka ƙasa zatayi masa godiya ,karaf idanuwansa suka sauka a saƙon wushiryar nonuwanta ,Da sauri ya kautar da kai “Ya isa go and dress up jooorr”

***
Yareema tsawon ranar tun bayan tafiyar Sulaim yini yayi a kwance likitansa yazo ya duba shi ya tabbatar da malaria ne ,and ya sashi akan magunguna don haka ba sauran ciwo saidai zuciyarsa a tashe take idan ya zurfafa cikin tunanin nan da kwana biyar za ayi masa juyin mulki….

***
Cikin dare ya Sheikh haka nan ya tsinci kansa da kasa barci ,sai zirga zirga yake cikin tunani ,wani abu mai nauyi yaji yana taso mai daga ƙirji wanda baisan ko menene ba .
Karfe biyun dare ya ɓalle ƙofa ya fito harabar gidansa ko’ina yayi tsit sai hasken fitilu a unguwar kamar dumly ,tsayawa yayi daga compound ɗin sa yana hango compound din Adnan
“To Amma akan meye zai baiwa mata na kudi ,dole in ja masa burki kamun ya ɓuɗe mata ido da kuɗi ya zama Ina tufka yana warware wa ,a karshe fa nine zan sha wuya ….gwara In masa burki akan ya fita hanyar mata na period!” da sauri ya gangara zuwa wajen gate,har ya dafa ƙofa zai buɗe padlock din sai kuma ya dakata

“Amma ai kudin bata yayi tayi cefanen girki ,kuma duk munci munsha ,kar inje yana mun kallon kasashe wanda ban iya bada kudin cefane ba……. mtsewwww kai su ƙarata kaji,yayi ta bata mana,nidai nawa ba inci abu mai daɗi ba.Amma fa ko Salima taso yi mun tsaurin ido next step shine in zaneta musulunci ma ya bani dama…..

***
Washekari karfe 8am ya Sheikh ya gama shirin sa tsaf ya sha tea ɗinsa ,watery mara isasshen madara ,ya ɗauko hulansa a hannu yana ƙoƙarin murzawa a kai ya tafi aiki sai ga kiran hajiyarsa.

“Hajiya kira da sassafe? Ubangiji yasa ba wata hidimar bane ,don wallahi satin nan na kashe kudi fiye da abinda nayi budget ma satin

“Hello ….ummi sabahul khair”
_Ina kwana mama_

“Miqdad in ka natsa Inason ganin ka a gida”
Ta tabbata kudi zata amsa wayyo Allah na wai me yasa indai wajen tambayan kudine ,to Ni aka raina?
Da wannan janantawar zuci yace “Hajiya lafiya dai ko”
“In kazo zakaji!”

Ɗisss ta kashe wayarta

 

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS
Have a splendid morning 👍🏼

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button