Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 20

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 20*

 

 

 

“Umar zama yayi a gefen Ammi yana kallon fuskanta ji yayi hawaye sun cika mishi ido, hawayen tausayin mahaifiyarshi, yasan basuyi mata daidai ba, ɗago kanta yayi ya wanke inda yake zuban jinin, yasa mata farin bandage karami, kwanciya yayi a gefenta ya rungume hannunta wanda babu drip akai, kuka ya fashe dashi yana tuna abinda ya faru tsakaninshi da faruk yanzu, rabonsu da faɗa haka tun suna yara ƙanana sai gashi yau sunyi faɗa har suna neman illata juna, ba dan kowa sukayi haka ba sai dan wannan yarinyar Amrish, wani zuciya ne ya bashi shawara da sauri ya tashi ya fita daga ɗakin, motanshi ya shiga bai tsaya ko ina ba sai prison, kuɗi ya basu suka mishi iso har ɗakin da Amrish take, tana ganinshi haka ta mike tana cije baki dan bata jin daɗi, a hankali tace “meya sameka faruk?”

daɗi yaji data kirashi da sunan Faruk, murmushi yayi ya karaso wurinta ya ɗagata, zaunar da ita yayi me kyau shima ya zauna a gefenta, hannu yasa ya dafa kanta cikin siririyar murya tace “auchhhh”

“ciwo yake miki?”

da kyar ta giɗa kai tace “eh”

 

murmushi yayi kafin ya kamo kan a hankali da wani irin karfi ya buga kanta da jikin bango, wani razanannen ihu ta buɗe baki zatayi, hannu yasa ya toshe bakin ya kara buga kanta da bango, sai waro manyan idanunta take tana kwace kanta daga hannunshi, bai barta ba saida yaga ta kusan suma sannan ya saketa, faɗuwa tayi a wurin ta lumshe ido alaman ta suma, ruwa ya watsa mata, da kyar ta buɗe ido bata iya magana ta kalleshi.

 

cikin zafin rai yace “kamar yadda kika janyo Ammi taji ciwo kema kiji a jikinki, kuma ina miki warning ki fita harkan ƴan gidanmu, ki cire sunan faruk daga bakinki”

 

tashi yayi yana kallon matar dake gefe ta tsorata da abinda taga ya yiwa amrish, fita yayi daga ɗakin yabar prison ɗin, hanyan gida ya nufa, faruk dake kwance ya mike ya ɗau makullin mota tunawa da yadda ya barta ba lafiya a cikin cell ɗin.

 

fita yayi daga gidan bayan ya leka Ammi yaga tana bacci, peck yayi mata a goshi ya shafa kanta a hankali yace “sorry”

 

bai tsaya ko ina ba sai prison kuɗi ya basu suka amsa sannan sukayi mishi iso zuwa dakin da take, tana kwance ta rike kai bata iya ko ɗagawa ta kalli mutum, matan tana gefenta tayi tagumi babu abinyi, gashi tana ganin yarinya cikin ciwo.

 

da sauri ya karasa yana kiran sunanta cikin zafin rai da kunan zuciya matan tace “bakada imani yanzu kazo nan ka rinƙa buga kanta da bango shine har ka dawo zaka kuma yimata mughnta? yarinyar nan fa marainiya ce batada kowa sai Allah amma shine kake mata wannan muguntan?”

 

anan take ya gane Umar yazo nan, yasan koda yayi mata bayani ba zata fahimta ba, da sauri ya karasa ya ɗaga Amrish ya ɗaura kanta akan kafarshi, ganin yadda yake jini yake zuba ya yaga gefen riganshi ya ɗaura mata akai saida ya tattara gashin kanta ya maido gaba, ganin gashin yana takura mata yasa hannu ya gyara mata kwanciyar, kitsawa yayi gida biyu yayi kaman kitson fulanan daji, gyara mata kwanciyan ya kumayi bayan ya kitsa mata, kwantar da ita yayi a jikinshi bata iya magana sai hawayen azaba.

 

hannunta da taji ciwo ya rike yana gogewa da riganshi, saida ya gama ya ɗago ya kalli matan data zuba mishi ido tana ganin ikon Allah ko dai yanada taɓin hankali ne? yanzu yazo yayi abu kuma yazo yana dubata?

 

“bani ruwa”

ruwa ta miko mishi, saida ya duba yaga babu me kallonshi sannan ya ɓalli maganin ciwon kai dana bacci wanda ya ɓoye a cikin takalminshi ya bata, kin karɓa tayi sai lumshe ido take kamar zata mutu, bakinta ya buɗe ya zuba maganin ciki tana shirin tofarwa yasa ruwa a bakin, atake ta haɗiye, kwantar da ita yayi akan riganshi daya kwaɓe wanda ya yayyaga, hannu yasa a kanta yana shafawa a hankali yana so tayi bacci sannan  ya tafi, bacci ne ya fara ɗaukanta a hankali ya cire hannunshi daga kanta ya shafa fuskarta, saida tayi nisa cikin baccin sannan ya mike zai tafi, ji yayi ta riko hannunshi, dawowa yayi yana kallonta yaji tace “na gode”

janye hannunshi yayi ya fita daga wurin, tausayin Amrish yana nema yasa zuciyarshi tayi bindiga, cikin zafin rai ya isa gida da tunanin abinda zai yiwa umar dan ya rama mata, yana iya jiyo sautin kukan da takeyi a zuciyarta.

 

 

yana yin parking ya fito cikin zafin rai ya buɗe kofan falon, ganin ya zauna ya juya baya yaje bakin kofa ya ɗau sandan mopping me kauri yazo ta bayanshi, zai kwala mishi yaga abinda umar ɗin yakeyi, a hankali ya saki sandan ta bayanshi sannan ya koma baya, hotonsu su biyu yake kallo ta cikin waya yana sharan hawaye,sai shafa hoton yake yana jin zafin abinda ya faru tsakaninsu, barin wurin faruk yayi jikinshi a mace ya shiga ɗakin Ammi, time ɗin ta farka Elham tana bata abinci taki karɓa sai hawaye yake sauka kan kuncinta.

 

Murtuƙe fuska yayi sannan ya karaso ciki, karɓan spoon ɗin yayi ya ɗibo rice ya kai bakinta bayan ya zauna akan gadon yana fuskantar ta, ɗauke kai tayi tana cigaba da kuka yace “kici”

 

ba wasa a tare dashi ganin haka ta buɗe baki kaɗan yasa mata, taunawa ta fara kamar tana taunan maɗaci haka takejin abincin a cikin bakinta, saida ya bata kusan rabi sannan ta kalleshi tace “na koshi”

 

ajiye spoon ɗin yayi ya mike zai bar ɗakin tace “faruk?”

cak ya tsaya bai juyo ba, kallon bayanshi tayi “meya haɗaka faɗa da umar? ba dai akan Amrish bane ko?”

 

“a kanta ne kuma kija mishi kunne kada ya kara zuwa prison koda wasa idan ya kuma haka koni koshi”

ya faɗa sannan fita daga ɗakin ya rufe gam, har saida suka tsorata, Elham ta matso kusa da Ammi tace “i hate Amrish ammi I hate her”

 

janyota ammi tayi jikinta tace “muyi addu’a Allah ya sasanta tsakanin Umar da faruk”

 

ɗakinshi ya shiga ya faɗa kan gado ya janyo pillow ya rungume da karfi, runtse ido yayi yana tuno halinda ya sameta a cell, ɓangare ɗaya kuma yana tunanin halinda umar yake ciki.

 

Umar saida ya gama kuka ya kashe wayan ya tashi, ɗakin Abbansu ya shiga dama akwai kayanshi acan, hannunshi ya kalla wanda yake jini ya ɗau box ya fara wanke duk wani ciwon dake jikinshi, saida yayi dressing na ciwon sannan ya haɗiyi magani ya kwanta akan gadon dake cikin ɗakin, janyo pillow yayi ya rungume da karfi yana tuna abinda ya yiwa amrish a cell, baiyi mata daidai ba amma babu yadda ya iya hakan ne zaisa ta fita a harkansu Allah ya sani ya tsani yarinyar har cikin ranshi tunda ta zama sanadiyyar faɗanshi da twins brother ɗinshi.

 

 

 

 

_jiddah ce✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button