Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 2

Sponsored Links

It’s Oum Aphnan
Karku jirga ,sharen fagen labarin ne dai.
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

002
___________________
Motocine Manya manya baƙaƙe wulun wulun suke giggiftawa da gudu akan kwaltar ,kowanne maƙale da plate number ɗinsa an rubuta Prince 1…Yarima 2…Yarima 3 haka har Yarima 5 ,Iyakan Rubutun da akayi a jikin plate maimakon plate number din kenan ,sai wani tanfatsetsen Farin Mota ƙirar Land Cruiser a tsakiyarsu shikam baida plate number a ta gaba Sai aka kafe ƙatoton Kan Zaki 🦁 Wanda aka Sassaƙashi (Molding) da Zallan Zinare.
Wannan Kambinsa ne dake faɗar ma duk wanda ya gansa Gaba,Basai an faɗa maka wanene ke tafe da tawagarsa ba daka hango walƙiyar kan zakin dake wulwulawa asamar farin motarsa kasan YARIMA ABBAD ne.

Sharara gudu suke tamkar basu shigo titin unguwa da zai sadaka da tangamemen Masarautar ba,wannan yasa duk wani mahalukin dake son tsira da mutuncinsa yake kaucewa .

Haka suka dangana har tsakiyar Fadan Bayin ƙofa na tale gets suna zubewa a wajen har suka shige tsakiyar rungujejen fadar maɗaukaki ,mai ƙunshe da tarin bayi maza da mata cikin uniform iri ɗaya ,Daf da ƙofar ɗakin Mai babbar ɗaki motarsa ta tsaya a yayinda sauran motocin bodyguards ɗinsa suka kwalmaɗa zuwa parking lot.

ATHEELAH budurwar Yarima Abbad ko ince matarsa da ake dab da aure ,fitowar ta kenan cikin kwalliya da fararen sutura na Alfarma ,gefenta surukuwarta ne ,wato mahaifiyar Yarima zata rakata gaban farar motarta da tazo a ciki ,tana ganin motocin yariman sun shigo ,shaukin ta ya karu fara’arta ya kasa ɓuya ta fara washe haƙura kamar wacce akayiwa bushara da Aljannah ,taja ta toge a gefen mamansa tana jiran fitowar Prince daga mota.

Motarshi na tsayawa ,drivernsa da ya kasance Amintaccensa ,ya fito da gudu ya ɗauko jan carpet ya malala tun daga farkon ƙofar motar har gaban ƙofar ɗakin mamansa

Sarkin busa kuwa tuni ya fara busa mabushinsa ,don Ankarar da duk wani mai lunfashi dawowar yarima. Tuni kowa ya soma kamewa a inda yake gwuiwoyinsa a ƙasa ,wannan Dokan yarima ne ko kana kan toilet ne yazo waje dole ka sunkuya ka dinga masa kirari daga inda kake, har sai yakai inda zai kai ya zauna sannan kowa zai kama gabansa .

Ƙiftawa da bissmillah kowani mai numfashi na gidan ka ganshi hululu a ƙasa ana jiran fitowar Yarima… Sarkin Busa yana ganin yarima ya sawo ƙafa ya tsaya akan jar carpet din digrigir ,ya ruga da gudu yaje ya sunkuya yana zuba masa kirari .

“Allah yaja da ran yariman dudduniya ,ɗan sarki kake jikan sarki takawan ka lafiya gwamnan gobe da ikon mai duka”

Shaƙan wani iska mai kauri yayi tamkar Oxygen ɗinsa ne ya siya a karti ,kana ya ɗage kai yana kallon kowani bil’adama Dake rusune a lungu da saƙo na gidan ,yanajin kansa na sake gingiringin ,babu wanda yake a tsaye akan ƙafafunsa daga mamansa ,sai ATHEELAH ,Budurwarsa.

Sarkin Magana na ƙare zuba kirarinsa ,sauran ɗaukacin bayin gidan suka fara rigerigen gaishesa murya a tare da alamu ma sun hardace kirarin da aka saba yin masa tamkar National Anthem

Yanda suke Zabga masa kirari yasa mamansa ,budurwarsa dashi kansa ɗan murmusawa kana ya fara Takowa cike da ƙasaita .

A guje ATHEELAH ta taho inda yake tana buɗe hannu alamun zata rungume shine.

Da sauri ya ɗaga mata er matsakaicin kambin girmansa mai kwalliyar gold. Wannan ya sata ja ta tsaya
“Keeee!🙄”

Ya doka mata wani wawan tsawa da ya sa hanjin cikinta hautsinawa ,taja burki ta tsaya
Cikin Muryar ɗagawa da fizgar rai ya soma mata magana
“Me ya hanaki rissinawa ki gaisheni kamar saura?…..

Das gabanta ya fadi ,bai duba halin da take ciki ba ya cigaba da cewa

“Anya kina da tarbiyya….? Anya ke cikakkiyar ɗiyar Ahalinku ce kuwa?”

Rassss ,ƙirjinta ya cigaba da bugawa ,a furgice ta ɗago ido tana kallonsa

“Anya ba Alamar fitsara a ƙwarar idonki?..” da gudu ta rausayar da ƙwarar idon ta ƙasa

Daka mata tsawa tayi wanda yafi na farko tada hankali

“Bani Amsa!!!!”
Jikinta rawa ya fara yi ,kar kar kar .
Da sauri mai babbar Ɗaki ta kwatse shi amma cikin laushin murya.

“Haba Yarima Take it easy ,matarka ce fa da zaka aura”

“Wife to be You said mama,she’s yet tobe ” (Matar da zan aura kikace mama amma ba Matana bace a yanzu)

Dawo da kallonsa yayi kan ATHEELAH
“Ke kuma ,zoki rissina a gabana ki sumbaci yatsotsin ƙafana”

Ba ATHEELAH ba ,harta bayin gidan saida suka firgita ,amma kawai sai mai babbar ɗaki ta hankaɗe kafada irin ko a jikina ɗin nan

Tana ji tana gani ta matsa gabansa ta sunkuya ta ɗaura kyawawan tafukan hannunta a ƙasa ,ta kai laɓɓanta saman rufaffen takalminsa sau ciki ,ta yi kissing takalmin nasa .

Sautin kiss dinta na dokan kunnen sa ya saki wani ajiyar rai yaja numfashi sama gami da miƙar da kansa ya kalli sararin samaniya kana ya kalli ƙasan inda take turmushe ta kasa ɗagowa saboda yanda tana kissing takalmin wani kuka mai ciwo ya turniƙe mata maƙoshi .

Tsawa ya daka mata irin na rainaswa da wawantarwa

“Tashi ki bamu waje ….sha….sha…..sha!!”

Haka kikaji sautin muryarsa a yayin zaginta da shashasha yana amsa kuwwa a ilahirin gidan…..lallai ran en maza ya ɓaci.

Da gudu ta mike ta falla da gudu wajen motarta ta buɗe motar ta shige ta zauna ta daura kanta akan kambin motar ta goce da kuka.

Tana barin gabansa ya wani washe baki kamar bai taɓa fushi ba a duniya,ya buɗe hannunsa ya taka ya rungume mamansa

“Oyoyo my love Na sameku lpy”

“Lafiya lau Yarima na,Mu shiga daga ciki” suka rankaya ɗaki.
Saida suka bace sannan kowa ya mike ,masu mota suka shiga suka mata key ,itama sai sannan ta kunna motarta ta fice a karce ,tana jin ranta kamar zai tsalle ya fice waje.

 

*_BAD BOYS_*

Leave a Reply

Back to top button