Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 19

Sponsored Links

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 19*

 

 

 

“Saida yayi nisa a bacci sannan ta mike tabar dakin, hannu ta goya a bayanta tana safa da marwa cikin ɗakin, wannan yarinyar kamar wacce ta yiwa ɗanta asiri? tana ganin laifinta kuru-kuru yana cewa batada laifi? dolene tasan hanyan da zatabi tasa yaron ya fita a harkan yarinyar ya daina tunaninta, to ta yaya?.

 

da wannan tunanin ta kwanta bacci, a gefen Elham wacce ta rungume pillow tana shekan bacci abinta, shafa kanta tayi tace “Allah ya rayamin ku”

 

 

*Washe gari*

 

da sassafe suka nufi gidan yari, su duka uku, saida suka zauna sosai sannan aka saki Umar, godiya sukayi bayan sun rungume juna suka juya zasu tafi, Amrish wacce ta fito kanta yana ciwo zasuyi mata allura a bata magani, sauro sun cijeta ba wasa a cikin cell ɗin, hakan ya haifar mata da ciwon kai me tsanani kaman zata mutu, ta gabansu aka wuce da ita batama san suna wurin ba dan hannunta ta dafe kanta dashi, likita akace yayi mata alluran maleria, sannan aka bata magani ta haɗiye, tashi tayi tana takawa da kyar, Ammi ɗauke kai tayi daga kallonta tana jiran su wuce itama su fita dasu Umar, baya baya tayi zata faɗi kasa da sauri faruk ya tareta ta faɗo kan hannunshi, haɗata yayi da kirjinshi yana ganin yadda ta rufe ido tana nishi da kyar, alama tana jin jiki sosai, murtuƙe fuska Umar yayi sannan yace “ka tashi mu tafi”

 

Ammi ma cikin ɓacin rai tace “kazo mu tafi”

Amrish jin haka ta fara janye jikinta a hankali tana son tashi saide babu hali jikinta yayi nauyi, rikeshi tayi sosai jikinta yana ɓari, wasu zafafan hawayene suka fara bin kuncin faruk tausayin yarinyar ya ɗarsu a zuciyarshi, ɗagata ƴan sandan sukayi sannan suka fara tafiya da ita suna janta, da haka har suka kaita ɗakin da take kwana a ciki, bin bayansu yayi da kallo yana cigaba da kuka, ɗagoshi Ammi tayi suka fita daga wurin, buɗe mishi mota sukayi ya shiga ya zauna, Umar ma ya shiga suka ɗau hanya Elham tayi shiru tana kallon Faruk jikinta yayi sanyi ganin yayanta yana kuka.

 

jan motan Ammi tayi suka fara tafiya babu me magana cikinsu, kowa da tunanin da yake yi acikin kwakwalwar shi, saida suka isa gida  Ammi ta buɗewa faruk ya fito yana murza ido, shiga ciki yayi ba tareda ya yiwa kowa magana ba, Umar ya juya zai bishi Ammi ta riko hannunshi “kyaleshi ka ɗan bashi time”

 

tsayawa yayi ta rufe motan suka jera tareda Elham suka shiga ciki, abinci na alfarma Ammi ta haɗa mishi abincin da yafi so wato coconut rice da kunun aya, zama yayi akan dining zai fara ci tace “wait je kayi wanka first”

turo baki yayi ya haura sama, ɗakinsu da Faruk ya shiga yayi missing sosai, yana kallon faruk ya rufe fuskanshi da pillow ya wuce toilet yayi wanka, fitowa yayi har yanzu yana kwance a inda yake kanshi a kasan pillow, Riga mara nauyi yasa sannan ya fita jikinshi a mace baison ganin faruk cikin damuwa saide wannan karon ya ɗibo da zafi criminal yakeson taimaka baisan aikata hakan babban sin bane.

 

Zama yayi ya fara cin abincin saida ya koshi dam yana yiwa Ammi santi kafin yace “thanks Ammi ba dan keba da har yanzu Ina cell, na gode uwa ta gari”

 

sunyi kwana uku Faruk baya yiwa kowa magana a gidan abin ya dami umar shiru kawai yakeyi, da safe kowa shiri yakeyi ya tafi wajen aikinshi, babu ko kala tsakaninsu, yau umar ya kudiri aniyan saiya kawo karshen wannan zaman, bayan ya dawo ya zauna akan kujera yana kallon Tv, faruk ya shigo cikin shirin kayan soja yana latsa waya ya wuceshi, Ammi tana ɗakinta tana bacci dan kanta yan ɗan ciwo tasha magani kuma ya sata bacci.

 

“kana fishi damu akan yarinyar da za’a rataye gobe?”

baiyi magana ba yaci gaba da tafiya yana latsa wayan, saida yaje bakin stair yace “da za’abi gaskiya tare dakai zasu rataye”

 

cikin mamakin da umar bai taɓa zaton wannan maganan zai fito daga bakin twins nashi ba yace “saide a rataye da kai kaida kaje kuka zauna wayasan me kuke aikatawa?”

 

murmushi faruk yayi “kafi kowa sanin mazinaci a cikinmu”

ran umar idan yayi dubu to ya ɓaci, kalman da faruk bai taɓa gaya mishi ba kenan, bama faruk ba babu wanda ya taɓa jefanshi da wannan mummunan kalman, cikin zafin rai yace “gara mazinaci akan makashi”

 

ran faruk ya ɓaci sosai “waye makashi?”

 

“ranka ya ɓaci ne? kai kake ɗaura yarinyar akan hanyan kisa hakan yasa ka rufe duk wani shaida da za’a gane tayi kisa”

cikin zafin nama ya sauko kasa ya kamo wuyan umar shima cikin zafin nama ya kai mishi naushi a baki, ganin bakinshi ya fashe ya fara kai mishi duka tako ina, dambe suka fara suna faffasa kayan ɗakin.

 

Elham ta fito da cup na ruwa zata kaiwa Ammi ta gansu akan centre table ɗin daya tarwatse suna dukan juna, sakin cup ɗin tayi a kasa ji kake tasss, da karfi ta tsala ihu tana kiran Ammiiiiii.

 

Ammi dake kwance tana jin ciwon kan yan ɗan saketa ta jiyo ihun elham da sauri ta janye bargon ta fita tana kiran “elham”

turus ta tsaya ganin yadda faruk ya danne Umar a kasa kan glass yana naushin shi.

 

uku-uku take taka stairs kamar zata faɗi har ta isa garesu ta fara janye faruk, batasan wayene akasa ba, ko umar ne ko faruk? bata sani ba, kallon kanshi tayi tace “faruk ka sakeshi kasheshi zakayi?”

 

shima umar ganin an janye faruk yaja kafarshi kasa, faɗuwa faruk yayi da karfi ya taka ruwan cikinshi, da iya karfinshi ya kama ƙafan umar ya jashi kasa, kokawa suka fara daga kwancen, Ammi tazo zata rabasu basu sani ba suka bugeta gefe, faɗuwa tayi tana rike kanta, dama yana ciwo gashi ya kara buguwa tace “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un, elham fita ki kira masu gadi zasu kashe kansu”

 

Elham da gudu ta fita tana ihu, masu aiki da gadi suka shigo ɗakin bayan ta sanar musu abinda yake faruwa, kan Ammi har ya fara jini dan ba karamin buguwa tayi ba, faruk ya janyo glass ɗin daya fashe yana shirin yankawa a jikin Umar haka zuciyarshi yake idan ranshi ya ɓaci baida hakuri ko kaɗan, Ammi ganin haka ta waro ido tazo da gudu tana rike kai ta fara janyeshi, tureta yayi da karfi ta kuma faɗuwa kasan tiles ya bugu da kafarta, a take ta faɗi a wurin tana rike kafa.

 

shigowa sukayi sun kai su huɗu suka fara rabasu, yaki sakinshi saida Ammi ta fara ihu tana cewa “dan Allah ka sakeshi zan mutu idan ɗaya daga cikinku ya mutu”

 

sakinshi yayi Umar yana ganin an sakeshi ya shaƙe wuyan Faruk ya haɗashi da jikin bango, wani sabon faɗan ne ya tashi, sai rabasu suke suna janye faruk abu yaci tura, kowannensu yanada karfi sosai.

 

Elham tazo tana jan umar tana kuka, wurgi yayi da ita ta faɗi gaban Ammi tana kuka, da kyar mutane biyu suka riƙe faruk biyu suka rike umar, turasu akayi a ɗaki daban-daban sannan suka rufe da makulli kafin abin ya lafa, umar dake bakin kofan yanata bugawa da karfi su buɗe mishi ranshi baiyi sanyi ba har yanzu, hannunshi yana zubar da jini, shi kuma Faruk kafarshi ne yaji ciwo ya taka kusa, zama yayi a ɗakin yana huci ranshi ya ɓaci ba kaɗan ba.

 

 

saida ya buga kofan kamar zai karya sannan suka buɗe mishi, fita yayi ya fara bugun kofan da aka shigar da Faruk yana bugawa jikinshi yana rawa yana cewa “ka fito saina kasheka”

 

jin haka bugu ɗaya Faruk ya yiwa kofan ya ɓalle, fitowa yayi ya tsaya yana kallon yadda suke rikeshi yace “ku sakeshi”

 

Ammi ganin faruk yayi tsalle ya tsinka fankan dake ɗakin ya rike a hannu ta faɗi kasa a sume, Elham tayi ihu tace “Ammi ta mutu”

ajiye fankan yayi yaje da gudu shima umar da gudu yaje suka fara kiran sunanta a tare suna tashinta, ganin bata motsi suka riketa a tare suka kaita ɗaki, Umar ne ya ciro kayan dubiya ya fara auna numfashinta ba komai bane sai tsinkewar zuciya, drip ya ɗaura mata sannan yayi mata allurai elham tana gefe ta haɗa kanta da jikin drowe sai kuka takeyi kaman ranta zai fita.

 

jikin faruk ne yayi sanyi yaje gabanta ya riko hannunta suka fita, har yanzu kuka take kaman zata shiɗe, akan sofa ya zaunar da ita yaje frij ya ciro ruwa a gora ya kawo mata, buɗewa yayi ya miƙa mata taji amsa sai kuka take, cikin tsawa yace “ki karɓa kona wankeki da mari”

 

jiki na rawa ta karɓa ta ɗaura a bakinta saida ta shanye tass ta ajiye goran tana kallonshi cikin tsoro har jikinta yana ɓari, zama yayi a gefenta jijiyoyin kanshi sun mimmike ya riko hannunta yace “ki daina kuka Ammi suma tayi zata farfaɗo”

kwantar da kanta tayi a kafaɗarshi yana ji tana sauke ajiyan zuciya har bacci ya ɗauketa, kwantar da ita yayi akan sofan ya wuce ɗakinsu ya kwanta akan gado.

 

 

 

 

 

_jiddah Ce✍🏻_

Leave a Reply

Back to top button