Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 41

Sponsored Links

041
*Bonus*
___________________
“Wannan kujerar da kake gani ba gama garin kujera bane da kowa zai iya hawanta,wannan masarautar ba gama garin masarauta bane da kowa zai iya mata hawan ƙawara,sunada Rauhanai da ke kewaye dasu ,kujeran nan kuwa tana da sarauniya dake gadinta…Babu wanda ya isa yahau kan wannan kujerar shima sai ya kauce hanya.

Yarima nasha faɗa maka ,ka rage tsaurin ra’ayi ,indai kai jinin sarauta ne (Littafina na baya) to dole sai yarda da Al’adun gidan sarauta ,dole akwai mabiyan da kake buƙata da zasu kareka ,don kaima din bazaka zama gama garin mutum da zai mulki mutanen da suke ba a kwance ba….and above all dole ka koya girmama mutane ko yaya ne…..Eh ba na faɗa maka wainnan maganganun bane don in tsorataka ba ,aah don in zaburar dakai kasan ko kai wanene,da yanda zaka fuskanci ƙalubalenka…this is the enemy cripple.

Yarima dole muyi duk yanda zamuyi don ganin mulkin nan ya tabbata a gidanmu .

Yarima ka bani hadin kai don ganin mun ƙwato sarautar gidanmu da ake ƙoƙarin ƙwacewa,I tell you now and here.”

Bata saurari mai zaice ba bayan ɗimbin maganganun da ta jera masa,ta mike ta fice a ɗakin ta barshi kwance a gadon jinyar da har yanzu bai gama warƙewa ba .

***
2am
Yarima Lokacin sallarsa nayi ya mike kamar an tashesa ,saidai a yau maimakon yaje ya yi wanka ya dauro Alwala kamar yanda ya saba ,saka takalmi yayi ya nufi ,cikin fada .da hankula yasa hannu ya murɗa handle din ƙofar ya buɗe tangamemen falon sarautar. A nutse yake takawa har gaban karagar mulkin ba ko ɗar a zuciyarsa na tsoro . Yaje gaban kujerar ya kafeshi da ido yana tuna yanda yake ganin Ubanshi a kwance a kai yau gashi babu shi kuma kujerar ta gagari jininsa…..
Miƙa hannu yayi cike da karsashi zai taɓi kujerar ,a ransa yana jin kamar jikin babansa zai taɓa saboda kewa.

Wani yauuuuuuuun!!!! Yaji ƙarar kukan zuma ya cika ɗakin gabaɗaya ,kunnuwar yarima ta liƙe ya daina sauraron komai ,rumtse idonsa yayi ,Yana karanta ayatul kursy ,but stand still .

“Yarimaaa!” Yaji Muryar babansa na kiran sunansa ,buɗe idonsa yayi walai,ya sauke akan kujerar saidai baiga komai ba ,sai kujerar dake girgiza kamar ana karkaɗata .

Full of arrogancy yaja dogon tsaki ya fice daga fadan.

Yana komawa ɗaki a tsakiyar center carpet din falonsa ya zube yasa goshinsa a ƙasa ya ɓarke da kuka

“Allah na komai ya juya mun baya Allah na ka bani sarautar nan shine karshen prestige Dina …ya rab na Kira ka da ya Wahhab ,sunan da Annabi sulaiman ya roƙeka dashi ka bashi mulkin da bazaa ƙarayin wani mai mulki a bayan kasa bayan shi ba …..ya Wahhab ka bani sarautar mahaifina cikin sauƙi,ka karya maƙiyana akan kai na….😢”

A take ya fara shasheka ya kwanta anan cikin hawaye da tarin nadama.

***
The next day

Can garden yarima yaje ya zauna duniya tayi masa zafi ,shi ba aboki ba bare yaje yayi shawara dashi ko yaji sanyi .to girman kai bai barshi ya saurari kowa ba ,gani yake ɗagawarsa ,sarautarsa da arzikinsa zai bashi komai ,and Almighty yarima yafi karfin Sharing ɗinsa da kowa.

Jabir cikin damuwa ya shigo wajen ,he’s relunctant either way.

“Gaisuwa ga shugaba”

“Hummm” yarima yayi masa gyaran murya alamar ya amsa

“uhm uhm ,Yarima na ,ina cikin damuwa kamar yanda dukkan wani mai sonku yake cikin damuwa da halin da kuke ciki,to Ni zan iya cewa nafi kowa,naci moriyarka sama da kowa yarima na,ka fifitani sama da duk wani wanda yake ƙarƙashin ka yarima na ka….”

“Me kake son Fada mun…go streght to the point abeg” ya katseshi cikin ɗagawa.

“Yarima na kwanaki biyu suka rage mana ,in har komai bai daidai ta ba zata ci sarautar mu,jiya ban iya barci ba yarima na duba Alkhairan ka da dama a rayuwata yarima ,I’ll not allow those to go in vain…but I smell danger!!,Na Soma sarewa Yarima,duk abinda nikeyi a ɓoye don ganin ka samu kujerar nan yana neman yayi over powering Dina ,as you don’t know babana gawurattaccen boka ne ,ya gaji tsafi a wajen kakana kuma shine malamin sarki wanda ya shuɗe ,tsufa ne ya sashi komawa kogon dutse ya rabu da mutane ya koma bauta shi ɗaya a dutsen ,kowa ya wayi gari ya ɓace ,amma mu munsan yana nan ,babana shi ke kai masa abinci yana samun wasu laƙanonin asirin…Nabi trait din da na san zan taimake ka amma sai komai ya kawo gejin bayyana sai wani abu da bamu san ko menene ba ya tunkuɗe aikinmu,Wannan ya tabbatar muna da akwai mai bibiyar sarautar ka ta ƙasa ,akwai matsafiya a gabanka yarima,ita kuma take saka kake komai unwillingly !”

Das ! Gaban yarima ya fadi ,tsikar jikinsa ya tashi,idanuwarsa suka burkita suka zama Ja.

A mamakance ya ɗago ya kalli babban yaronsa
“Jabir ,ban ban fahimta ba”

“yarima na ,I want us to advert in fading danger ,Amma inaso ka gane su waziri ba maƙiyanka bane ,ka fara zama lafiya dasu ,dukda kwana biyu yayi kadan yasa ka gyara kurakuranka,amma da shiryawa da mutane lafiya ne kadai zai sa mu iya stepping forward,as a wise said fail to plan ,plan to fail..Zamu tashi tsaye mu gano matsalar mu daga yau daga yanzu ,indai zaka bani haɗin kai kabi wanda zata iya ka ɓata masu a rayuwa ka roƙesu gafara ,nikuma zan kaika wajen kakana,malamin kakanka ma ba babanka ba zai taya ka da Addu’an nasara ,as u know one magical power is far beyond comprehension ,kakana kaifi daya ne in kaje masa da arrogancy wlh bazai saurareka ba ,and you’ll be looser for ever.!

“me kake so inyi 🥹 you want to chook my brain joorh”

“Ka fara zuwa ka nemi yafiyar wanda ka ɓata mawa,Ni kuma zan kaika wajen kakana,ka sauke girman nan yarimana kar kace mun in tafi sai kayi tunani ,because delay is dangerous for now Yarimana!”

 

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

Leave a Reply

Back to top button