Hamshakiya Complete Hausa Novel

Hamshakiya 8

Sponsored Links

 

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 

 

Na

_Jiddah S Mapi_

 

 

*Chapter 8*

 

 

 

“Kuɗaɗen data kwashe ɓoyesu tayi a cikin rami bata bari kowa yasan abinda ta aikata ba, bincike ake sosai akan mutuwan saide hakan bai tsorata ta ba ko kaɗan itadai tasan tsakaninta da masu kuɗi babu wanda ya isa ya hanata abinda tayi niya, gidan marayu ya hargitse sai kuka suke shugaba ta mutu, wanda suke da mukami kuma sai rarraba idanu suke dan sun tsorata ba kaɗan ba, sunfi kowa sanin abinda suke aikatawa.

 

Faruk yana rike da file na mutuwansu bincike yake yi sosai yana son gano wani abin saide abin mamaki bai samu komai ba, kwance yake akan gado kanshi duk yayi zafi, ya maida hankali sai dubawa yake yana kallon hotunan gawan, Umar yana gefe yana chatting bini-bini yana ɗagowa ya kalleshi, da sauri ya tashi daga kan gadon ya ɗau waya yace “cctv footage aje gidan Alhaji hamza ina zuwa yanzu”

 

ganin ya fara kiciniyar sa kaya Umar yace “ina zuwa by this time?”

 

“bakaji me nace a waya bane?”

ya faɗa yana sa wando, taɓe baki yayi “naga ai daka bari zuwa safe yanzu dare yayi nisa”

 

“no wannan babban case ne kasan Alhaji Hamza yanada mukami a kasan nan dolene asa kai akan binciken mutuwanshi okay?”

 

“to Allah yasa ku gano me laifin”

“Ameen” ya amsa yana tafiya, makullin mota ya fita dashi bai tsaya ko ina ba sai unguwan Alhaji Hamza, kai tsaye ya shiga gidan bayan ya nuna ID card nashi, ya damu sojoji biyu a gidan gaida matanshi da sauran mutanen wurin yayi kafin ya wuce ɗakin da aka nuna mishi na cctv, bincike suka fara na duk wani motsin daya faru jiya, yaranshi suna wurin domin ance su shigo, abin mamaki ganinshi sukayi zigidir yana shirin yin lalata da wata, kallon yaran Faruk yayi yace “su fita zuwa waje”

fita sukayi jikinsu a mace, kunnawa akayi akaci gaba da kalla, wata yarinya yake aikata masha’a da’ita, cikin ɓacin rai matarshi tace a kashe batasan ganin wannan abin, Faruk ya kalleta yace “bincike muke dole aga komai”

har zuwa na dare sukaga an shigo da kaya fuska a rufe, dama yasan macece tayi kisan, abin haushi lokacin data buɗe fuskanta bata kallon camera ta bawa camera baya, hakan yasa ba suga fuska ba, yarfa hannu yayi yace “shit”

 

kashewa sukayi kafin suka bawa matanshi hakuri suka tafi, yaso yaga fuskan saide ya gagara, abin haushi, haka dai ya koma gida ranshi ba daɗi, Umar na zaune yasa kayan bacci ya ganshi ya shigo rai ba daɗi, yasan basuyi nasara bane “ba nasara ko?”

jijjiga kai kawai yayi yana cire rigan jikinshi

“Me kisan nan koyon kisa takeyi saide bata bar shaida ko ɗaya ba, ban taɓa haɗuwa da case ɗin daya bani wahala irin wannan ba, na kasa gano komai, kayan bacci shima yasa yana ɗan tsaki.

 

“Kanada tabbacin macece tayi kisan?”

 

“Kwarai macece, domin a tsorace tayi kisan da alama bata saba ba”

yayi magana yana zama a bakin bed, Umar yayi shiru domin shima abin yana bashi mamaki, kwanciya yayi akan Bed ɗin yana kallon Umar wanda yayi shiru.

 

“Ka bani shawara ta yaya zanyi na gano wani abin?”

 

“Gaskiya nima kaina ya ɗaure ban san yadda Zakayi ba, kasan nifa ba aikin bincike da soja na karanta ba, kaine ka karanta bincike ta fannin aikin soja, ni kuma doctor ne lafiyan ɗan adam na karanta”

 

janyo Pillow yayi ya rungume bayan ya kwanta rub da ciki ya ɗago kai yana kallon Umar, yace “ya kamata ka koyi wani abu daga cikin aikinmu saboda wata rana, ni kaga na koyi aikin doctor a wurinka duk da ban wani iya ba amma na koyi wasu abubuwan, kaga nuna kama sosai ba lallai mutane su ganemu ba, kafi kowa sanin risk ɗin da yake cikin aikin soja”

 

“ba zan iya koyan komai a aikin soja ba, kasan banson wahala”

murmushi kawai Faruk yayi ganin ya janyo blanket ya rufa har kanshi, janye blanket ɗin yayi yace “yau ba bacci hira zamuyi kai baka gajiya da bacci ne wai”

 

“kaga bani blanket nawa”

 

“bazan bayar ba” yayi maganan yana ɓoyewa, tashi Umar yayi ya fara kwata, nan suka fara guje-guje a cikin ɗakin, saida Faruk ya gaji kafin ya wurga mishi blanket ɗin ya shige toilet, freshen up yayi kafin ya dawo shima ya kwanta a gefe, ganin Umar har yayi bacci ya shafa kanshi tareda yimishi peck a goshi, kwanciya yayi ya kashe wutan ɗakin, hannu ya ɗaura a kanshi bayan ya kwanta yana kallon sama, tunani sosai ya fara ta yadda zai gano me kisan, da haka har bacci ya saceshi.

 

 

*Amrish*

 

duk masu kukan mutuwan shugaba kallonsu kawai takeyi, daga me cewa gatanshi ya kare sai me cewa sunyi babban rashi, da ido kawai take binsu, hankalinta yana kan sauran mutanen da sukayi zuru-zuru sun san abinda suke aikatawa tare dasu Alhaji Hamza da shugaba, atake kowa ya kara masu tsaro a gidanshi, cikin ranta tace “ko duniya zasu tara su zama masu tsaronsu saita kashe su.

 

da dare taje ɗakin data ɓoye kayan tasa ta fita bayan tasa wukan agefen cikinta, fita tayi daga gidan domin ta bari saida kowa yayi bacci, a unguwarsu masu tsaro ne sosai ba hanyan shiga, a gefe ta tsaya tanajin sanyi sosai  domin yanayin garin akwai sanyi sosai, daurewa tayi tana cije ɗan karamin leɓenta, tunanin abinyi ta fara saide kanta ya toshe, katon dutse ta ɗauka ta wurga gefe, basuje su duka ba sun bar mutum ɗaya a bakin get gashi kato baki, cikin sanɗa taje ta bayanshi ta ciro wani babban kyalle ta ɗaure wuyanshi dashi, shaƙuwa ya fara da karfi ta bugi kafarshi ta baya, faɗuwa yayi ta fara janshi da kyallen wuyanshi saida ta kaishi lungu kafin ta ɗaure bakinshi, yana bugunta da kafarshi tana jin ciwo amma bata bar abinda takeyi ba, saida ta gama ɗaureshi a galabaice ta shiga gidan har tana layi dan ta daku ba kaɗan ba a wurinshi, ta rufe fuskarta babu me ganinta, kai tsaye ta shige cikin gidan, fara ratsa ɗakuna tayi, babu iyalanshi a gidan hakan ya mata daɗi, bedroom ta shige ta leka baya nan, saide taji karan ruwa a toilet da alama wanka yake, shiga tayi ta zauna a bakin gado ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana wasa da wuƙa a hannunta, fitowa yayi yana waka kasa-kasa, towel ya ɗaura a waist nashi ganin mutum a bakin gado da baƙin kaya ya juya ciki zai koma da gudu, jefa mishi wukan tayi a daidai wuyanshi, nan take ya caki wuyan ya fara jini, faɗuwa yayi a wurin yana cewa “waye kai?”

 

murmushi tayi saida tazo dab fuskanshi kafin ta cire facemask na hulan tace “marainiya ce ni”

da hannu ya nunata “kece?”

“eh nice Amrish ba? wacce kuka yiwa yara ƙanana fyaɗe a gaban idonta, nice nan kawar zainab wacce kukayi luwaɗi da ita hakan yayi sanadiyyar mutuwan ta, sannan nice ƴar uwar yaran da kuke zuwa kuna ɗiba kuna kawalcinsu har kasashen waje.

 

cire wukan tayi daga wuyanshi yayi kara dan yaji zafi sosai, kafa yasa ya tureta kasa, ganin ta faɗi yazo kanta zai kama gashinta da karfi tasa kafa ta bugeshi ta baya, nan suka fara dambe tasa iya karfinta suna dambe dashi, cikin ikon Allah ta janyo wukan dayake gefe, bayan ya gama buga bakinta ya fashe yana jini tasa wukan a bayanshi ta yanka, faɗuwa yayi, ta caka mishi a ciki nan take bakinshi ya fara fitar da jini, saida ya daina motsi ta zauna dirshan a kasa tana kuka, cikin shesheƙa tace “bada sona nake kisa ba ku kuka sani, kune kuka tunzurani nake aikata abinda ba dai-dai ba”

 

kyallen ta ɗauka tana goge jikinta daya zuba a wurin domin bakinta ya fashe, tasan idan ƴan sanda sukazo zasu ɗibi jini da komai suyi gwaji, jaka baƙi ta gani a jikin gadon saida tasa facemask kafin taje ta ɗauka, buɗewa tayi taga wasu kuɗaɗe masu yawa a cikin jakan, lumshe ido tayi kafin ta rataya jakan ta fita, haurawa tayi ta katanga kafin ta fita daga gidan, bata tsaya ko ina ba sai ɗayan gidan saida ta ajiye jakan a kofa kafin ta shiga, yadda ta kashe wancan haka ta yiwa wannan, fita tayi daga gidan, a ranan saida ta kashe mutane uku da dare kafin ta koma taje ta binne kuɗin a inda ta ajiye wancan na Alhaji Hamza, kayan ta ɓoye a ɗaki ta dawo cikin ɗakinsu ta kwanta.

 

 

_washe gari_

 

Labari kota ina sai yaɗuwa yake an kuka kisa wannan karon mutane uku aka kashe, kuma har yanzu masu bincike basu gano komai ba, mutane da ƴan jarida sun taru a kofan gidajen wanda akayi kisan, kowa so yake ya samu rohoto.

 

Dafe kai yayi yana kallon gawan da aka jera guda uku a gabanshi, wannan dai ya kasa gane komai game da kisan, wayanshi ne yayi kara kirane daga general, yana ɗagawa yace “wannan karon ma ba gagara samun shaida”

ajiye wayan yayi yana cigaba da bincike, kalma ɗaya ya kuma furtawa shine “macece take kisan”.

 

har aka birne gawa babu wani Information, komawa barack yayi sukayi zaman meeting akan wannan maganan, manyan sojoji ne suka taru a wurin meeting ɗin ciki harda captain Faruk wanda case na binciken kisan yake hannunshi.

 

sun tattauna abubuwa masu amfani, bayan ya fita ya tara ƴan jarida saida yaga sun cika kofan office nashi kafin yace “wannan kisan da akeyi nayi alkawarin nemo wacce takeyi, da hannuna zan kamata kuma na kaita gaban hukuman ƴan sanda, tanada wayo shiyasa bata barin shaida amma ni Faruk nayi alkawarin nemo ta da yaddan Allah.

 

labari ya fara watsuwa a cikin cikin gari captain Faruk yayi alƙawarin nemo wacce take kisan kuma mutane sun shaida aikinshi idan yasa kai dole ya samota.

 

 

tana zaune a cikin banɗaki tana kallon hotonshi, wannan shine next target nata, dashi da wannan likitan daya ɓatawa zainab rayuwa, zubawa hoton ido tayi, “gashi kyakkyawa amma babu kyaun hali”

 

ɓoye hoton tayi a kirjinta kafin ta fito daga toilet ɗin, ɗaki ta shiga taga Najma tana tsala ihu, da sauri taje ta ɗauketa ganin mamanta bata nan tace “yi shiru zan kaiki wurin umma”

 

bata sani ba hoton ya faɗi lokacin data durkusa, Ahmad dake gefe yana karatu yace “laaa unty Amrish wannan shine sojan da yazo lokacin da shugaba ta mutu, jiya ma na kalleshi a Tv yana cewa zasu kama wanda yake kashe mutane”.

 

karɓan hoton tayi tana kallon Ahmad  gabanta ne ya faɗi da sauri tace “ka ganshi ne?”

 

“eh na ganshi ɗazu ma yazo ya shiga gidan wai sunzo su kara yiwa ƴar shugaba tambayoyi, a tv na ganshi tivin gidan shugaba”

 

zama tayi da Najma a hannunta ta kirashi yazo shima ya zauna a gefe tace “Ahmad ka tabbata wannan ne?”

 

“shine har nace mishi nima inaso in zama soja, kuma ya taɓa zuwa gidannan ya kawo kayan abinci a office na shugaba harda kuɗi ya bata yace a rabama marayu sai tasa a jakanta”

 

“Okay tashi kaje kada ka gayawa kowa”

fita yaron yayi ta sauke najma wacce tayi shiru.

 

“Kenan shi ɗin soja ne? yana zuwa gidannan ya kawo abinci domin ya samu daman ɓata yara, kuma shine yake bincike akan mutuwan waɗannan azzaluman? taji labarin wanda yake binciken yanada matukar basira kenan shine? Lalle dolene ta buga wasa da wannan mutumin, dolene ta juya mishi ƙwaƙwalwa ta yadda saiya ajiye aikinshi da hannunshi.

 

juyawa tayi gefe ta window ta hango inda take birne maƙudan kuɗaɗen da take kwasowa daga gidajensu waya ƴar karama ta ɗaga kira ɗaya aka ɗaga tace “a nemamin mansion ginanne me kyau wanda zai ɗauki marayu kaman guda ishirin sannan nima na samu wurin zama a ciki, gidan daya amsa sunanshi gida shi nakeso”

 

tana gama  maganan ta kashe wayan, lalle wannan sojan sai tayi wasa da hankalinshi kafin shima ta ɗau fansan abinda ya yiwa ƴar uwarta Teema.

 

 

 

*Hamshaƙiya littafin kuɗine ki biyani hakkina idan ba na sata kike so ki karanta ba, ₦400 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta wannan layin 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, masu vtu kuma kuyi ta layin dana ajiye*

Leave a Reply

Back to top button