Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 37

Sponsored Links

37- Elbashir da jikinshi yayi sanyi, ba zaka tab’a cewa shine ba. Domin baki daya baya ji baya gani. Lokacin da abin ya faru, yana kallon yadda Malik yake girgiza mishi kai, kada ya motsa ya tsaya, har zuwa lokacin da yan sanda suka iso wurin. Domin ba karamin shirin yaki aka yi ba. Yan sanda har ta sama suka sauka. Inda suka kashe maharar suka kama mutane biyu a cikinsu. Kafin lokacin Malik ya zubda jini sosai wanda ba a tsammanin zai rayu. Dafa kafadarshi Barista Hayatu yayi yana faɗin. “An kama su, sannan IG na kasa yana kan al’amarin shi yake binciken kuma muna, saka ran za a samu adalci babban burinmu da damuwarmu Malik ya rayu. Malik nagartaccen mutum ne, ga wanda ya san shi yasan adali ne, in sha Allah zai tashi.”
_A yau al’ummar garin Keivroto suka tashi da mummunar al’amarin, da ya firgita su. Sakamakon harin yan bindiga Dadi da suka kawai Mayor Malik Menk Jordan, a hotel din three stars, har yanzu babu labarin makomar Mayor din amma muna saka ran nan da wani lokaci, zamu samu labari daga hukumar gwamnati. A baya Malik yayi fama da tasku daga abokan gabanshi, wanda suka yi sanadiyar rabuwarshi da me dakinshi Zeenobia Nasr Hadejia, yayinda wasu suka ce. Mai dakinshi ta rabu da shine sakamakon kashe mata iyaye da yayi, babu wata majiya da zata saka a fahimci me yake faruwa da rayuwar Malik din, domin kome yake yi rayuwarshi a rurrife yake yinta,Allah ya kyauta_
Wannan shi ne abin da yan jarida suke yayyatawa, kowa so yake ya fadi akasain abin da yake faruwa, a bakin Asibitin kuwa gidajen jaridu ne, suka yi dafiffin son jin labarin halin da Malik yake ciki, yana raye ne ko yana mace. Kuma wani abu da basu gane ba,.ba za’a tab’a barin a sake labarin mutuwar Malik cikin sauki ba, balle kuma babu wani labari daga likitocin da suke kanshi. Sannan su kansu nurse da suke kanshi, anki bari su fito domin gudun abin da zai je ya dawo.

Daga fadar shugaban kasa, ya bawa IG umarnin a amshe duk wayar kowa, ajiye sai bayan kome ya lafa. A cikin asibitin har da Zulfah wacce ta amshe wayar kowa da Kwamishinan yan sanda, an yi cirko-cirko.
Har zuwa karfe biyar na asuba, kafin Likitocin suka fara fitowa, daya bayan daya. A mugun gajiye Doctor wardah tana fitowa, Abin da ta fara faɗa shi ne. “Alhamdulillahi!” Jin haka yasa Zulfah kiran IG ya gaya mishi. Shi kuma ya isar ga shugaban kasa. Sai dai a gefe guda Elbashir ya bukaci da kada a fitar da labarin, kuma daga IG har shugaban kasa sun yi na’am da wannan shawarar. Domin tsira da lafiyarshi, sannan itama Zulfah ta gayawa Ammyn. Kada ta gayawa Zeeno Malik yana raye. Ta wannan hanyar ce kawai zasu ci ubanta. Koda ta bata labarin an samu nasarar cire yara uku, amma yaran suna can wurin kula da su. Yasa ta jin kamar tayi kuka. Ta nufi Elbashir ta gaya masa. “anyi nasarar cire yara uku, biyu maza daya mace, daga su har uwarsu suna cikin koshin lafiya. ”
Hawaye ne ya zubo mishi, da sassarfa ya isa dakin ya samu Malik yana ta barci. Rike hannunshi yayi yana faɗin. “congratulations Aboki, Zainab ta haifa mata yara uku. Ka farka kaji labarinsu.”
Zama yayi ya fashe da kuka yana jin tausayin Malik kamar yayi yayya, baki daya sai yadda Ubangiji yayi da shi. Yana ji kamar ya cire ciwon daga jikin Malik ya mai da kanshi, domin Malik yayi mishi kome a rayuwa, babu abin da zai ce sai fatan Allah ya bashi lafiya, Allah ya bawa Malik lafiya, wanna shine fatan shi da burinshi.
Sai da gari ya waye, sannan aka samu labarin haihuwar Matar Malik, bayan an dauki hoton Yaran da video dinsu, an saka a gidajen jaridu da talabijin. Abin gwanin ban sha’awa, wannan aikin Akram wazir ne ya turowa Zulfah. Yara mazan biyu sanye da kaya skyblue, macen kuwa sanye da kaya pink. Sunyi kyau duk da basu cikin bad condition amma uwarsu, ana kanta domin har ta wuce lokacin da ya dace ta farka. Hankali ya kuma dugunzuma ya tashi a can Malik anan kuma Zainab.

Baki daya sun rasa hope ɗinsu, haka akayi ta samun tashin hankali a tsakanin mutane, a cikin gari an tashi hankula al’umma, domin gani ake kamar akwai wata makarkashiya, akan matsalar Malik, haka yasa aka karo doctors daga Gista suka tawo duba Malik din. A wannan karon da a iya cewa everything is fine. Domin har ya koma barci. Wani irin farincikin Elbashir ya tsinci kanshi a ciki..


Sai da aka taru akanta, kafin aka samu kanta, inda cikin ikon Allah. Ta farka baki daya. “Ina Babyna?” Ta faɗa tana kokarin shafa cikinta. Riko hannunta aka yi suna faɗa mata halin da yaran suke ciki.
Lumshe idanu tayi kafin ta ce musu. “ina Malik?” Yadda tayi tambayar yasa suka zuba mata idanu, kafin aka mata allura barci yayi gaba da ita, sai Washi gari ta farka, shima da sunan Malik ta farka.
“Ina mijina?”
Shiru suka mata aka rasa wanda zai bata amsa, Hajja Yayye ta fara da nasiha. “Zainaba, rayuwa da mutuwa na Allah ne, ki yarda Allah zai kara baki.”
“Yaron ne ya mutu!?” “Ko daya!” Shiru tayi tana kallonsu cikin wani mawuyacin hali ta ce. “Daadi ne ya rasu?” Juya baya Ammyn tayi tana jin kuka na taso mata, bata san hikimar Zulfah da Elbashir da suka ce a boye mata yana raye ba, amma kuma akwai cutarwa idan aka cigaba da ajiye maganar a sirrace.
“Hajja Yayye! Shine ya rasu?” Jinjina kai tayi tana matse kwalla. Domin ko ita ba a gaya Mata ba, gudun kada ta ce musu babu kyau, amma nufin Elbashir ya san ya Zeeno zata amshi labarin mutuwar Malik?
*Kiyi hakuri! Wata rana zaki ji abin da ya faru, promise me, idan kika tafi ba zaki yi kukan bana tare dake, ki min alkawarin ba zaki yi kuka idan wani abu ya faru da ni ba, ki min alkawarin zaki bawa dan mu kulawa har girmanshi! Zainab ina sonki, ina kaunarki. Zan zauna jiranki da jiran kiranki. Kira daya kika min zan zo gare ki! Da kira daya kawai!* Wani irin ƙara kanta yake mata a cikin, ta lumshe idanunta tana jin yana juya mata, “Na kashe shi ko? Eh nice na kashe shi,” sai kuma ta fashe da kuka, kafin ta fara haki, kiran nurse suka yi. Aka fara kokarin hanata shiga attack. Amma ina tayi nisan kiwo. Sai da suka shafe awa biyu akanta, kafin ta farfaɗo. Amma barci yayi gaba da ita.

Haka alamarin ya kasance, a can bangarenshi. Ya farfaɗo kuma Elbashir ya gaya mishi gaskiyar abin da suka yanke. Ai kuwa sun sha faɗa, kamar ya dake su amma kuma daga baya sai ya ga kamar sun mishi kome, ta haka zai saka tasan amfaninshi. Sai dai kuma wani abun mamaki shi ne. Tun daga ranar Malik yake fuskantar hatsari mafi muni. Domin kuwa hari ake kawo mishi ta ko ina, har zai aka yi isolate din shi a barikin sojan kasar, daga nan yake samun duk wani kulawa.

Gidanshi kuwa sojoji ne ba na wasa ba, a hankali gwamantin kasar ta fahimci yadda ake tunkarar Malik da fitina, tow su abin zata shafa, domin ko daukar ma’aikata da yayi ai ba na wasa ba ne. A kamfanonin shi, wanda taɓa shi ya janyo zanga-zanga a kasar baki daya, suna sa state goma sha huɗu, sannan a cikin states din nan, yana da kamfanonin shi na kansa, bayan nan kuma gwamnatin kasar baki daya, tana samun kudin shigarta ne ta hanyar ma’aikatan shi da suke bin manyan Bus da taxi zuwa wurin aiki.

Taya ma zasu so a kawo karshen Malik, dama a duk lokacin da aka samu wanda ua ragewa gwamanti aiki, ba karamin nasara ake samu ba. Don haka aka kara ninka tsaro sama da baya a barikin da yake, sannan aka shiga bashi duk wani kulawar da ya dace, a wani majiya mai tushe, ta tabbatar da cewa. Ai kusan duk wani shugaba ko primeminista, tow Malik shi yake tsayawa a samo adali.

Haka yasa bayan party ɗinshi na siyasa, babu abin da ya dame shi, shi yana gefe guda yana nad’a wanda ya so ne, ya kuma sauke wanda yaso, ko primeministan da aka kashe, ai Malik ya saka aka daura shi, tare da alqawarin zai rike ƙasar da Al’ummarta, sai daga baya abubuwa marasa dad’i sukayi ta fitowa, sannan ko Khuldu Jahid Khan, yasan baya cikin jarin makiyanshi. Haushin shi sa Khuldu yake ji don ua kashe mishi ba bane, da bai kashe mishi uba ba, tow Banu abin da ya dame shi.
Sannan wani abun da yake damun Malik a wannan harin waye ne? Waye yake niman rayuwarshi? Yasan Ba Shatima bane tow waye ne?
Waye ne yake bibiyar rayuwarshi haka? Yasan Amjad yana hannunsu, sai Shu’iba yana sane da shi na zai iya ba, duk wanda yake bibiyar rayuwar Malik yasan shi, ya kuma san waye shi, ya shiga jikin Malik. Wannan yanayin yana mishi kama da wanda ya san waye shi, zaune yake a dakin da ke cikin gida na musamman. Ya zubawa Elbashir idanu da yake ta aiki da computer. “Bashir ko kai kake bibiyar rayuwata?”. D’ago kai Elbashir yayi yana kallon Malik. “Idan da ina son kashe ka, tuntuni zan yi haka. Sannan ba zan tsaya a gefe ina sararka ina boyewa ba. Malik idan ka kuma.kiran suna na Alqur’an sai na shigar da kai karar cin zarafi da sharri.”
“Allah ya baka hakuri kaji”
“Ban yi hakuri ba! Nace ban yi hakurin ba!”
“A’a al’amarin ya kai har haka? Tow kayi hakuri!”
“Malik sai nake ganin, kamar wanda ya san mu yake kawo mana irin wannan harin. Domin haka kawai ba za a samu me zuciyar kawo maka hari ba!”
“A wannan ranar da abin ya faru, akwai wani abu da na gani a tare da wanda ya harbe ni. Kasan me?” Girgiza kai Bashir yayi yana gyara zama. “Na ga wani abin hannu, wanda Lauyar Baba yake sakawa!”
“Ikon Allah, kace fansa ce kawai ake biyar ka da shi!”
“Yes Fansa ce! Na gamsu babu abin da tafi fansa kawazuci! A nimo iyalan shi, domin ta haka ne zan san ta iya nayi kuskuren.”
“Ta hanyar kashe mishi mahaifi! Ka kashe mishi mahaifi shima yazo daukar fansa kana tsammanin zai kyale ka ne? Don haka dole musan waye shi sai mu shiga bibiyarshi!”
“Ya Allah! Me yasa ban san cewa wani xai biyo bayana daukar fansa ba? Me yasa ban gane cewa daukar fansa yana iya zama alakakai, gashi nayi nawa . Wani yazo yana nashi. Ga na Zainab a ajiye a gefe wallahi na rasa yadda zan yi da rayuwa, Zainab ta rufe Ni” “kada ka damu zamu yi iya kokarin mu, mu nimo bayanin Lauyan babanka, domin ta haka zamu gano bakin zaren”

Dafe goshinsa yayi, kanshi kamar zata yi bindiga. Ya zubawa Elbashir idanu kafin ya ce mishi. “Ma rasa mene min dadi baki daya na cilla rayuwata cikin matsala!”
“Banu wata matsala kome zai zama da sauki in sha Allah ”
“Anya kuwa?”
“Da gaske!”
“Jeka wurin matarka mana”
“Tow xan tafi Malik, amma ka daina zargina domin raina yana ɓaci “….
*WAYE NE WANNAN ME ZUCIYAR KAIWA MALIK DIN MU HARI?*
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

 

Leave a Reply

Back to top button