Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 35

Sponsored Links

35- Elbashir ji yake kamar ya fashe da kuka, yana kallon yadda Malik ya shanye kome kamar bai faru ba, “Malik!” “Muje gida ai sun tafi!” Daga haka ya juya suka nufi wurin motar, bude mishi kofar yayi ya shiga ya zauna yana me kwantar da kanshi. Har suka bar airport ɗin. Koda suka shiga cikin gari kai tsaye gidan su Hafsy ya mishi magana su tafi, babu musu suka nufi gidan, suna zuwa da kanshi ya fita ba tare da ya bawa Elbashir damar fita ba, ya nufi cikin gidansu Hafsah. A mutunce suka gaida juna ya kalle su yana murmushi ya ce, “Nazo ne na tafi da Hafsah tunda daga ku har shi, zaku mai da ita wata iri!”
“A’a yallabai Malik ka saka shi don Allah ya sawwake mata!” “Ba zai yiwu ba, tazo mu tafi ai kowani mutum yana kuskure. Sannan dama can Allah ya ƙaddara haka zai faru, shi yasa ban wani ji ciwon abin ba, idan muka ce abin da muke so zamu yi ai ba zamu tab’a ganin daidai ba. Amma idan muka barwa Allah lamarin sai ya iya mana, bana tunanin haka zai saka na butulcewa Ubangiji, abu ne da dama na gaza tsayuwa na fahimtar da Zainab kuma da bata saurin fahimtar abu sai daga karshe.. wallahi babu kome ta fito mijinta yana jiranta!”

Kasa magana iyayen Hafsah sukayi, wani irin zuciya ce da Malik, a maka laifi kabi da alkhairi. Murmushi yayi ya ce musu. “Ku barta ta tafi da mijinta, nima tafiya xan yi.”
“Shi kenan, tunda kayi magana me yafi haka?” Murmushi yayi ya ce. “Babu!” Haka suka ya fita ya barsu, suka shiryata. Suka fita da ita, suna musu fatan zaman lafiya. Gaba ya bude mata suka saka ta. A hankali ya ce musu. “Mun gode!”
“Mune da godiya!” Daga haka suka bar kofar gidan, “Hafsah bani numberki idan wannan dan iskan ya miki, shiritita ki kira ni ki gaya min domin ba zai yiwu ya tab’a mana sahiba ba.”
Kuka take a hankali ta kasa magana, “Malik a bayan idanunka ba zan tsalleke maganarka ba, balle a kan idanunka. Malik duk abin da kace haka zan yi!”
“Tow ajiye a hotel din three stars!”
“Malik!”
“Haka na ce, ka sauke ni a three stars!” Ba mu ya nufi hotel din, ya sauke shi ya raka shi har cikin hotel ɗin, zuwa gobe ka kawo min kayana, suna shirye.”
“Me yasa Malik?”
“Ba xan iya jin kuna amarci, matata tana wata duniya ba.” Ya faɗa yana kallon Elbashir. “Don’t rejected your wife, she meant to you, and she need from you. Babu wanda baya kuskure.” Yana fadar haka ya juya ya nufi cikin luxury room din da ya kama, kusan penthouse ne a cikin hotel din, iya part din anyi shi ne domin mutane irinsa. Zuba gwiwanshi yayi ya fashe da kuka, yana cewa. “Malik ka bani daga abin da Allah ya baka, ka tsaya min domin Allah ya tsaya maka. Malik an maka laifi ta sanadina, Malik me yasa ka nisanta kanka damu? Ko kana ganin ta sanadina haka ya faru?” Juyawa yayi yana kallon Elbashir.
“Ka ji kunya, kato da kai kana kuka. Dariya ka bani. Ko daya kaje Allah ya baƙu zaman lafiya.!” Yaso Malik ya fahimce shi, amma yaki fir yana ganin kamar duk laifinshi ne da bai nime Hafsah ba a daren da haka bai faru ba, shi mutum ne da yasan waye Malik, kuma zai bugu kirji ya ce yasan waye Malik. Amma bai tab’a fahimtar Malik yana da karfin zuciyar ba zaka gane ba, ai irin wannan yanayin ba a faru. “Tashi ka je Allah ya baƙu zaman lafiya!”
“Malik me yasa?”
“Saboda haka zai saka ka samu nutsuwa, zaka sake da matarka kayi yadda kake so, sannan baka tunanin ina gidan, don Allah kada ka tab’a ran yar mutane.”
“Shi kenan!” Ya juya ya fita yana jin kamar ya dawo ya zauna da Malik. A haka ya bar hotel din, yana jin kamar yayi ta rugawa Hafsah zagi.

Bayan tafiyarshi, Malik yayi wanka. Babu kaya a dakin dole ya saka wanda ya zo da shi ya nufi Bouquet dake ƙasar hotel din ya dauki kayan, ya basu kati. Sannan ya dawo dakinshi ya zauna ya cire na jikinshi ya sauya, sannan ya zauna yana kallon tv. Lokaci zuwa lokaci hankalinshi yana kan wayarshi. Har dare yayi sosai, yana kallon wayar yana jiran kiranta.
***
Sai da safe suka isa Dutse, kafin nan ta farka sau biyu tana komawa, koda suka sauka a airport. Babban Asibitin dutse aka wuce da ita, kafin ta ji sauki a maida ita hadijia. Suma Nurse da Doctor sai da suka bada kome nata, suka huta sannan suka wuce airport. Dama abun da ya kawo su kenan, sun gama zasu koma inda suka fito. Yan uwa da abokan arziki, da suke hadeja da nan dutse suka yi ta zuwa ganinta, wasu su koma gefe su ce babu aure ta kwaso cikin shege. Wasu su ce da aure kafin wani lokaci kan mutane ya rabu da rumors na bala’in tashin hankali.
Duk yadda Zulfah taso kauda kanta, sai da ta kasa, domin abin da take yar iskar yarinyar nan amma taki. Haka suka yi ta fama da mutane babu wanda ya fahimce su. Kwananta uku dake ana zuba kudi dai gashi ranar na hudu ta farka, a gajiye. Bayan an gama dubata suka tabbatar lafiyarta lau. Sannan suka dan rike ta saboda case dinta.

A wasa a wasa, sai da ta kwashe sati biyu bata ganin kowa sai Zulfah da Ammyn. Sai Kanen Babansu mutum biyu. Baffa Barde, da Gwaggo Karime. Duk da bata cika son hayaniya ba, sai dai ta lura da mata yar tijara ce ta gaske. Ko waye ya vata labarin yadda ta tawo ba tare da son ran Malik ba, ai kuwa ranar har da gasa mata bakar magana. “Ce miki akayi zamu miki gatar da Yake miki ne? Ai bamu da wannan arzikin, Allah ya baƙi miji na rufin asirinki. Amma kika saka kafa kika mauje wannan gatar, sai kici uwar da zaki ci domin nan kan babu me karawa kanshi damuwa da matsalarki. Ai wallahi ko namar jikinki yake yaga yana ci kya hakura baki san yadda rayuwar take ba, shi yasa mara kunya da idanun a tsakar ka!”
Hawaye ne ya cika mata idanu, bayan ita ma sai da wata coursin din Babansu ya zo yayi ta mata rashin mutuncin daga yadda suke bala’i zaka fahimci akwai matsala a cikin zancensu.

Kwananta Biyu dangin Mamansu har da Jalilah suka zo, Wayyo Allah a nan tayi ta zuba shagwaba. Ana kara kambamata da riritatta. Ai kuwa yace ita a wuce da ita Maiduguri. Dake Familyn Mamanta suna da arziki sosai, shi yasa basu wani damu ba, aka dauke ta domin Aunty Yaganah sai wani mita take, akan an takurawa Zeenobia da maganar Malik, ai ya mata tsufa tunda babu aure a tana haihuwa kawai ta mika masa dansa ta yi fama da kanta. “A’a Aunty ba zan bashi Yarona ba, kawai ya san na haifa amma ba zan bashi Y’ata ba.”
“Allah sarki! Kada ki damu babu me rabaki da danki!”
Wasa wasa dai Washi gari aka wuce da Zeeno Maiduguri. A can aka shiga zancen haihuwarta tunda ance aiki ne, amma dake akwai yan uwan Mamanta da suke step Mother, suma suna aure manyan mutane nan bornon. Domin Alhaji shuwa ya rabu da uwargidansa, sai ya auri kakarsu Zeeno Hajja Abuh.
Dake matar kafin wannan abin ya faru, ta musu rikon tsakani da Allah sai gashi abin mamaki, suma suka lullube Zeeno da alkhairi. Kuma Mamansu Zeeno Batulah a wurinsu ta girma basu nuna mata yan ubanci ba. A gidan Babban wansu Mamanta aka sauke ta, a part dinta tare da saka.mata me aiki.
Akwai Mahaifiyarshi Kawunsu Zeeno, dake hutu da kulawa uasayba ka ganta kace tsohuwa ba, ita ke saka idanu akan Zeeno. Idan tayi wani abu zata fada, yace ba a haka ake ba. Suna kiranta Hajja Yayye. Tana da kirki da mutunci ga ilimin addini da ya samu mazauni a ranta, dake bayan rabuwa da kakansu Zeeno ta auri wani Kanuri ne suka tafi Madina a can ta kwashe shekaru sama da talatin da biyar. Koda ta dawo mijinta ya rasu. Suna da Yaran uku. A gidan kakansu Zeeno ta haifi maza uku mace daya, Alhaji Kazeem wanda suke gidanshi, sai Hajiya Kaltumah tana nan mai Borno, sai Alhaji Mustapha, yana Abuja yana aiki, sai Alhaji Awwal yana Rivas yana aikin banki,

. Fahdeelah tana auren W IIazirin Borno, Yaranta biyu Akram wazir (kun tuna shi🤗😂) sai Haris yana can owerria can matattan man fetur na kasa. Sai Umaimah Yaranta hudu ne, Babba namiji sai yan mata uku, biyu sun yi aure saura daya. Zata kai age mate Zeeno.
Sai Sumayyah wacce take aure a Kaduna, da Yaranta takwas, biyar maza. Uku mata matan ne manya ta aurar da daya saura biyu manyan.

Tun da suka ji labarin Zeeno dama suna shiri da Zulfah sosai. Sai ga Zeeno ai baki daya suka koma jikin Zeeno ana riritatta. Satinta daya da zuwa aka yi bikin murnan zuwanta. Sai dai a bari guda bata farincikin da haka, domin tunda sukayi idanu da Akram. Ya sakata a gaba da fitina. Tsoronta daya kada ya mata akuyancin da ya mata a Keivroto sai ta sha mamaki ko da wasa bai mata wannan kallon ba.
Haka ta cigaba da renon cikinta, har ya shiga wata bakwai, domin Malik ya roki Ammyn da ta zauna sai ta haihu, kuma ta amince. Sai da ta shanye wata na bakwai tass, sannan aka fara shirin mata aiki. Domin batun gaskiya bata iya barci cikin ya hanata sakat, bata da ikon cin abincin ta koshi sai ta kaza zama ta kasa tsaye.

Abin tausayi baki daya ya fita hayacinta, dake ana bata ruwan Addu’a sai take samun saukin abin, a satin da za a mata aiki. Ta je ganin likita kallon Ammyn tayi sannan ta ce mata. “Hajiya idan da hali kuyi hakuri da aikin nan, domin yarki bata da wani dogon matsalar .da za amata aiki. Sannan idan aka yi aikin Babyn sai ta dauki lokaci tana zaman kula da shi, shima aiki ne a wannan yanayin. Sam bana son ganin anyiwa mace aiki idan ba dole ba. Babyn bai gama kwari ba domin naga rahonta akwai zubda jini,idan aka duba da matsalar kin ga kwanakin ya koma baya, idan da hali a bar cikin ta cika wata tara mu gani zuwa sati 42 sai a cire domin zai fi kyau da koshin lafiya..amma idan ita tana so kuka zata iya jigilar jinya ba laifi sai a cire mata.”

Kallonta sukayi, baki daya idanunsu yana kanta. “à kin ji? Me kika ce?” “Ammyn a bar min shi kawai!” Ta faɗa tana cijewa. Idanunta yana cika da kwalla. Daren ranar da Washi gari abin ya faru, sai da ya gaya mata cewa. “No matter how much you want the baby out, a will sure that I’m there, for sake of you and my child!” Dakyar ta mike ta fito waje, tana son tayi kuka amma bata son tayi kukan for sake of Malik, bata son tayi kukan ta ji a ranta don shi ne. But she miss him badly. Bata taɓa sanin shi din wani gefe na rayuwarta ba ne dai da ta fahimci tana matukar bukatarshi, asalima ba shi yake hanata barci ba, bukatar Malik. Share hawayen tayi, tayi tana shashekar kuka. A hankali take tafiya a duk inda take ji take kamar ita ɗaya ce me matsala babu wani me shi, toh ya zata yi? Ya kashe mata iyaye ne fa, kamata yayi ya dauki wuka ta soke shi har lahira, amma ta zabi tafiya ta bar shi tafi mata kome sauki shi ne zuciyarta take cutar fa ita da kewarshi. Amma ai bata yi laifi ba, asalima gaskiya ce kawai ta tsaya akan ra’ayinta.
Gabanta ne ya fadi lokacin da ta tuna da takardar da ya bata har biyu. Bata yi aune ba, sai jin tayi ta tafi da baya zata zame…….OMG ME ZAI FARU🙄🤗🧐CIKIN ZAI RAYU KO ZAI SHEKA TARE DA UWAR…
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button