Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 7

Sponsored Links

Volume:7 Primero Eatery
The best restaurants ne a garin Keivroto, gidan cin abincin da kudin table daya ya isa wasu iyalan cin abincin kwanaki shekara guda zuwa biyu, kafin ma wannan lokacin, ita kanta gidan abincin tun karfe biyu na rana aka rufe shi, tare da ɗaukar abincin da ya rage aka yi sadaka dashi domin Malik yayi odar gidan cin abincin baki daya na tsawon awa daya zuwa biyu.
An gyara wurin tare da kawata shi, da decorations masu daukar hankali kamar biki za a yi a wurin. Duk wanda y zo wurin za a maida shi a ce an rufe babu abinci wanda a ka’ida sai karfe sha daya ake rufewa, ba karamin kudi Elbashir ya kashe na kawata wurin ba.

Don haka sai da aka saka masu yar kid’a, irin cool music din nan, yadda kana gani zaka san an shiryawa zuwa wurin ne, na musamman domin wannan daren
A bangaren Malik kuwa, me gyaran fuskarshi ne yazo ya shiga gyara mishi fuska babu abin da ya bari sai yar kakkaurar gashin baki me zagaye da yar kasumba, itama an rage shi ya fito kamar dan matashi me shekaru arba’in a duniya, doguwar fuskarshi da gashi ya kawata shi,

Ana gama mishi gyaran fuska da aski ya shiga bandaki, yayi wanka, sannan ya fito daure da towel. Yana amfani da kekenshi, a hankali ya iso gaban closet ɗinshi, ya shiga ciki yana kallon kayan da suka dace da shi. Idanunshi ne ya sauka a kan wani expensive suit, Stuart Hughes diamond edition, dark maroon sai wani irin sheki yake me matukar daukar idanu.

Idanunn shi ne ya sauka akan boxes Calvin Klein, ya dauka tare da sakawa sannan ya tura keken ya Ciro kayan dake leken automatic ne, tana iya karawa mutum tsawo, yana gama daukar kayan ya shiga sakawa, sannan ya dauki takalmin shi. Da safa da duk abinda zai bukata ya nufi waje a can ya cigaba da sakawa. Yana gamawa ya dawo dakin ya agogo da zobenshi masu daraja, sai sandarshi wanda yake makale a jikin kekenshi. A hankali ya nufi wurin mirror ɗinshi, ya shafa man gashi na maza, sai ga gashin yana wani irin sheki har da ɗaukar idanu.

Haka ya fito ya nufi waje, koda ya ido falon sassanyar kamshin turaren imperial Majesty ya cika falon, juyawa Elbashir yayi ya sake baki yo ko zamanin samartaka shi bai wannan wankar ba, sannan ya san wannan suit din jikinshi ba kasafai yake saka su ba, sai idan zai yi baƙi na musamman. Yake saka su amma yau dake ya shirya haduwa da Zeeno shine hr da cancad’a kwalliya.
“Malik anya kai ne kuwa?” Cikin basarwa ya ce mishi. “What happen?” Gyada kai yayi yana faɗin.”not amma kuma duk kwalliyar ganin Yar kunama?”
“Me kake na gaya maka Bashir?” “Tsakani da Allah aurenta zaka yi?” Sunkuyar da kanshi yayi sannan ya d’ago ya kura mishi idanu ya ce mishi. “Ina son haihuwa ne, koda ace na mutu zata kula da abin da muka haifa, sannan ita daya ce ba zata bukaci raba dukiyata ba, sai dai daga ranar da na aureta zan daidaita kome da ita.”

“Malik ba a yabon dan kuturu, sai ya shekara arba’in da yatsu, sannan da kake ganin kamar duniya da dukiya basu dame ta ba, zata zo ta bukaci haka. Ni dai abin da nake gani kawai ka hakura da ita domin ga Jalilah da Lalla Salmah zasu iso gobe, ya zaka yi da su?”
“”Tunda na zaɓe ta, ba daina jin fargaban yadda kome zai zo min, amma ka sani idan ba kai ba waye ya gaya musu zancen Zainab;” girgiza kai yayi cikin damuwa ya ce mishi. “Wallahi ban tab’a daukar zancen ka na bawa wani ba. Malik baka yarda da Amana na bane har yanzu?”
“Baku nake tsoro Baz dabbobin da suke kirazanku nake tsoro, domin zuciyar mutum tafi gangan jikinshi illa!”
“Bana cikin masu irin wannan zuciyar, Allah zai nuna min lokacin da xan biyaka!”
“Hmmm! Muje ko”

Kamar ba zata shirya ba, sai da ta ci kukanta, ta koshi sannan Ammy ta shigo dauke da wasu jakuna ta mika mata tana faɗin. “Yanzu Abbas ya kawo min, wai inji Malik a kawo miki, zaku fita.” Sharrrrr hawaye ya zubo mata.
“Tow me na kuka kuma?”
“Ammyn tsoho ne fa?”
Murmushi tayi sannan ta ce mata.
“Amma ai kin kai aure ko za a barki ne kina kallon kowa ba dadi? Aure shine cikar mutuncin kowacce Y’a mace, na kira Hafsy ta gyara miki fuskar ki.”

Share kwallan tayi, tana faɗin. “Ammy kin yarda na je kenan!”
“Kayya ai yarda da nayi dake, ko cikin maza dubu kika kwana ba zan tab’a zarginki ba. Maza watsa ruwa ki fito!”
Hawaye ne sharrrrr suka zubo mata, haka ta shiga ban daki ta watsa ruwa, kafin ta fito Hafsy ta iso. Tana fitowa ta shiga fitar da kayan tana faɗin. “Durun uwa salatin maguzawa. ”
D’aga rigar tayi tare da fadar sunanshi. “Odette Square neck, midi dress!” Zaro wayarta tayi daga aljuhun rigarta ta ce bari na ga kudin rigar. Zeenobia Kinsan nawa kudin kayan?” “Kin san Allah, zan fasa zuwa!” Ajiye kayan tayi ta shiga tayata shiryawa har ta gama ta mata makeup, sannan ta shiga dauko dan kunnen Baroque pearl , stone wave, sai agogon Ferragamo women’se.
Haka ta saka, ta Ciro mata jakarta a cikin perpa bag din, a ledar shi.
“Allah ya saka ni a damshi. Jimmy Choo, Callie black suede bag and shoe.

Shirya tayi cikin nutsuwa ta kuma gyara mata fuskar ta sosai, sannan ta ce mata.
“Bani mayafinki tunda kayan red ne, zai dace da bakin mayafi sai na daure miki shi kamar turban ”

Haka ta dauko dan kwalin abayar ta mika mata, ta daura mata, shi yayi mata kyau, sannan ta dauko kwalin turaren Shumukh ta fesa mata. Kwankwasa kofar aka yi, “Yes!” “Elbashir ne Malik yana jiranki!”
Tashi tayi ya kalli Hafsy da ta ce mishi. “Okay yayi hakuri gata nan zuwa.”
A hankali ta karasa saka takalmin ta bar dakin makale da jakarta, ta nufi dakin Ammyn. “Ammyna na fit….” Sake baki tayi tana kallon Elbashir a falon Ammyn suna hira da Inna da Abbas. “Kai yar nan kinci sunarki sarauniyar girka me daraja, sai kin dawo.
Haka suka fito, daga dakin tana baya yana gaba, har wurin motar da Malik yake, phantom menace Ii, a hankali ya bude mata ta shiga, hango Malik tayi a hakimce yana wani baza hanci, kamar ta rufe shi da duka, wannan shi ne yake niman aurenta, wacce irin lalacewa tayi da zata kare da auren tsoho, dube shi don Allah? Wata zuciya ta hasilata.
“Tsaki tayi tare da dauke kai. Yaji zafin tsarkin don haka ya ce mata.
“Ko ba ni ba, kada ki kuma yiwa wani tsaki!”
A tsiwa ce ta ce mishi. “Idan nayi me zaka yi? Kashe ni zaka yi? Iyakaci ka saka a kashe ni!”
Domin ya bata haushi ya ce mata.
“Wai ai nafi karfin na kashe kyakyawar irinki, kawai abinda na sani zan cinye wannan kyakyawar bakin naki yadda gobe ma ba zaki kara min tsaki ba”
Rufe bakinta tayi, tana faɗin.
“Na shiga uku, ni ba yar iska ba ce, wallahi ban kai nan ba, rashin kunyata bata kai har nan ba”
“Idan har bata kai har nan ba tow wallahi a dai na min tsaki ko kuma sai na cinye bakin!”
Kauda kai tayi tana jin kwallan bakin ciki yana cika mata idanu. “Yau kinci abinci kuwa?”
“Ban sani ba! Idan kaji haushi ka daura min nace idan kaji haushi ka dura min!”
“Kayya saurin me kike? Nan wani lokaci zan dura miki abinci har da masu cin abinci anan dinki!” Ya nuna mata cikinta.
A firgice ta ce mishi. “Amma ai babu maganar ciki a sharadina?”
“Eh tow idan kika cigaba da gaya min maganar da ta miki, sai nayi koda karfin tsiya ce!”
“Innalillahi! Ubangiji ya min tsari da fyade yanzu kai baka ji kunyar cewa zaka min fyade ba?”
“Kina mata ta, meye a cikin don na miki fyad’e? Sunnar ma’aiki na gyara sai ma samun ladar da zan yi!” Toshe kunnanta tayi, tana jin kamar ta bude kofar ta fice da gudu, baki daya Malik ya goge mata yar karatun sallah.
“Dama haka kake?”
Tab’e baki yayi yana faɗin, “na wuce haka, me kike tunanin tsohon kasungurmin tuzuru zai aikata bayan haka?”
“Akwai mata irinka kaje ka same su mana why me?”
Shiru yayi kamar yana nazarin maganarta ya ce mata. “Gaskiya ba zan samu irinki ba, su duk sun tsufa ke kuma danya jagab ce!” Wani irin kara ta sake sai da drive ya taka.birki jin tayi shiru kuma Malik bai ce kome ba, yasa shi cigaba da tafiya.
Har suka isa wurin cin abincin, bata kuma yarda ta takale shi da magana ba, ta lura bakin shi bai da cikakken daraja, a bakin wurin cin abincin suka tsaya aka fitar mishi kekenshi, sannan ya fita a hankali. Ya zauna a keken kallonshi tayi wani malolon bakincikin ya kuma turniketa.

Ta wani haɗe rai, domin min har da Manager gidan Abincin suka tawo tarban su. Haka kawai sai take jin wani irin abu, wato daraja da girma yana tare da Malik ko yayya ka rabe shi, sai duniya ta mutuntaka, kamar su kwanta a kasa haka suke ta gaishe su, har suka isa inda zasu zasu ci abinciin.

….. Wurin babu haske sosai, da duhu suka isa wurin. Zama tayi tare da kallon shi. Shima tashi yayi a kekenshi ya zauna a kujeran a hankali yana murmushi.
“Kiyi hakuri, ki karbe ni a haka laluran shekaru goma sha uku da samun shi, ba haihuwa ta aka yi da shi ba.”
Duk da haushinsa da take ji, ta wannan bangaren sai taji baki ɗaya ya bata tausayi.
Ta bude baki zata yi magana, aka fara kida me taushi mara kara da sauti. Irin blue sounds me daukar hankali, ga sanyi me dadi a wakar, kallon yadda lokaci guda ta dan sake ranta, tsayawar da kidan. Wata dattijuwa ya fara kid’a piano, me ana amfani da gitta. Ga wani irin yanayi na fuskarta yanayin damina, iska me zafi zafi sanyi sanyi hade da kamshin kasa.

“Sannunku da hutawa!” Jerin yan mata, dauke da kayan abinciin aka shiga jera musu, Idanunta yana kan waje. Har suka gama shirya wurin. Sannan suka juya suka bar wurin. “Zainab!”
“Na’am;”
“Mu ci!”
A hankali ta dauki fork ta rike a hannunta, tana juyawa tana kallon shi. “Wannan yanayin yafi dacewa da Yaro Matashi ko?”
Hadiye yawu tayi tana kallon kasa, “ki ci zan duba al’amarin, idan da hali sai na rage yawan watanin zuwa wata biyar ba?”
Hadiye yawu tayi tana fad’in. “Wata biyar da gaske? Da gaske wata biyar kawai.”
“Baki yarda da abinda nace ba ne?”
“Na yarda mana”
“Tow ci abinci!”
A nutse ta fara cin abincin, tana sake murmushi tana kallonshi. “Kayi kyau!”
“Ai kin fini kyau”
“Hmmm ji wani wayo.”
“Bai kulata ba, sai ma cin abincin da yake tayi, itama tana ci a hankali. A hankali ta ajiye Fork ɗin. “Ki kara mana!”.
“Na koshi, bana cin abinci me nauyi da dare!”
“Ai gara ki fara ci, domin ina son kafin mu rabu, ki tara kumatai!”
“Hmm nafi son na rayu babu kiba sosai, domin ba zai min kyau ba……
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button