Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 41

Sponsored Links

41- Hawayen da suke makale a cikin idanunta suka sauko, “Kiyi hakuri Zeeno!” Bata rai tai, ita don dole zata kula Hafcy, amma ba wai don ta cancanci haka ba, asalima haushin Hafcy din take ji, dangin Babansu, kwanansu uku, dake ba ayi suna ba, sai bayan zuwan su Elbashir aka yi taron sunan, sai a daren ranar ta tuna sa wayarta. Kwanansu Elbashir uku da zuwa kenan, da dare ta nimo wayar da ta faɗa can ƙasar gado, har mantawa take da shi. A hankali ta saka a charge, tana faɗin. “wai sako kenan!” Ta zauna tana buɗe Wayar, Allah yasa Yaran ana can ana musu wanka saboda jigilar da suka sha na taron suna.
Inbox ta shiga na text messages, ta fara karo da wani sako. _Wawuya jaka, dama haka mijinki yake sarrafa mace kika bar shi a hannuna?_ hadiye yawu tayi ta kuma ganin wani sako. Ta ce mata.. _Jakar ashe baki Whatsp! Ki duba Email ɗinki, mahaukaciya ashe haka yake binki da masifar kauna shi yasa mana ya kasa hakuri da kanshi yake bin yar abokin shi_
Da sauri ta duba Email dinta, bayan ta kunna data. Jikinta yana rawa kamar an jona mata electric, hotuna ne da video Malik ne Nadrah, na farko inda ya dauko ta, na biyu a dakinshi, yana kwance ita tana kanshi, sai aikin arziki suke. Na uku ya fito yana dariya daga shi sai towel a daure tana mishi video yana dariya, duk videon nan babu murya.

Wani irin kuka take tare da buga wayar da kasa,ta dauki kasko turaren wuta tayi ta bugawa a samar wayar, da bai mata ba ta dauko kwalbar turare tana bugawa har sai da ta fasa wayar, daidai shigowa Ammyn ta ganta a durkushe. “Ammyn! Don Allah ki ce Malik kada ya kuma takowa inda nake idan ba haka ba, zan kwashe Yaran mu gudu.”
Cikin gajiya da halin Zainab ɗin ta ce. “Ni ba yarki ba ce, baki san number Malik din ba ne? Mtsew mahaukaciya wacce bata san ciwon kanta ba, zan bi su Elbashir na tafi, idan kin gadama ki tuna rayuwarki da ta Yaranki idan baki so ba, ki lalata gobenki da dangatakar Yaranki da mahaifinsu. Na gaji da abun da kike, ki godewa Allah da ya baƙi miji nagari da har kike hauka ya miki laifi, sannu waliyiya mara laifi!” Tass Ammyn ta mata, dake iya su biyu suka san abun, bata kuma bin ta kan Zeenobia ba, saboda abin nata har da iskanci, ai zuwanta ta ga yadda wasu mazan suke kula da matansu, wasu ma kamar su ke da hakkin aure a kansu, amma ita ta samu dattijo mutumin kirki, duk da tasan yana da baya mara kyau, amma haka baya nufin ta wulakantashi ba, shima rayuwa yake bukata ne kyau, ta zauna tana shirme.

Har ana gobe zasu koma, sai da Ammyn ta mata tass, domin kuwa da safe ta yanki jiki ta suma, saboda damuwa. Aka kaita asibiti suka ce jininta ne yayi sama, don haka Ammyn take gaya mata. “Namiji halittar shi ce son mata, sannan kuma idan akan mace kike suma da faduwa me yasa baki zauna a wurinshi ba? Dole yayi yadda yake so, naji labarin aure zai kara. Sai ki shirya da kyau” duk da bata yi haka don ta cutar da ita ba, tayi haka ne domin ta zaburarr da ita, amma yarinyar nan me shegen taurin kan tsiya, da suka dawo samun Elbashir tayi ta ce mishi. “Ka gaya mishi, ya sake ni don Allah! Duk cikin sakonnin da ya bani babu saki na duba, yayi hakuri ya sake ni. Ina son kwanciyar hankali. Don Allah ya bar ni haka don Allah ” ta faɗa tana kuka me tsananin gaske.
“Malik yana sonki sosai, amma tunda baki ga wannan soyayyar ba, Zainab zai gaya miishi ya sake ki. Amma ki sani kafin ki samu namiji irin Malik wallahi sai kin sha wuya, domin shi daya ne a cikin dubu. Shi kenan ai”

Daga haka suka bar Nigeria, cike da takaicin Zeeno. Har ga Allah haushinta yake ji. A jirgin suka tattauna akan matsalar Zeeno da Malik, nan Ammyn ta ce kowa ya fita harkanta, ganin ana bibiyarta da zancen Malik ne yasa take yiwa kowa abin da taso shi yasa take wasa da rayuwar aurenta.

Koda suka isa abin da Elbashir da Zulfah suka gaya mishi haka ya dauka karshe, ma booking apartment yayi ya koma Saudiya da zama, tare da mai da hankalin shi akan Ibadarshi, Allah ya mishi arziki da zai iya zama na tsawon wani lokaci. Don haka kamar yadda ta mishi iyaka da Yaranshi. Haka yayiwa kanshi alqawarin ba zai taba zuwa inda take ba, sai ta nime shi. Karshe ma da ibada da tuba yasa kanshi mantawa yayi da ya tab’a rayuwa da wata mace. Yana jin shi a wannan lokacin kamar yana tare da Ubangiji ne, a can kuwa an ta niman shi babu labarin shi, Elbashir yana Demark, domin can ya koma aikin kamfaninsu na can, anan kuwa gwamnati take ruined din kamfanonin Malik din. Haka ya tsara kuma yake tafiya dai-dai.

★★★
Kwanaki suna rikidewa zuwa satittika. Satittika na juyewa watanin a haka har su Zeeno sun Shure wata bakwai, yayinda yaranta suka yi nisa a zama da rarrafe. Tunda suka shiga wata bakwai, suka koma Hadeja. Ashe Maiduguri tana cikin kwanciyar hankali da jin dadi. A hankali ta fahimci dangin Babansu, suna da mugun son kai, da son abin duniya kuma kowa nashi ya sani. Don ma Allah ya taimaka sun karshen wata, zata ga kudi ne in dollas ya shigo a account dinta, wanda tasan aikin Malik ne, sai gashi basu nime kome sun rasa ba, sannan a bangaren Alhaji Kazeem da Alhaji Mustapha, suma ba a barsu a baya ba, domin sosai suke mata aike shi yasa da farkon dawowanta Hadeja, ta fuskanci halinnsu. So daga baya sai ta koyi zama da su, and wani abun da ya kara d’aga mata hankali yadda kowa yake jiran ta mishi ko ya daka mata warwaso akan dan abin Yaranta.

Da farko idan tayi wankin kayan Yaran, ta shanye. Zata samu an dauke Kayan. Bata kuma gani sai dai idan wani harkan biki da suna ya haɗa sai ta ga a jikin Yaran matan Cousins dinta, da farko bata yi magana ba, sai da aka yi na biyu a na uku. A gaban jama’a ta cirewa Yarinyar kayan Maidah ta saka a jakarta ta kalli Uwar Yar.
“Kika kuma ɗaukar min kayan Yara ba ke ba, wata ma sai na karya hannunki!” Tayi maganar a asalinta wato yar kunama.

Sai gashi maganar har wurin, stepbrother din Babansu, shine kakan Yarinyar da ta cire mata kayan. Bayan sun dawo yazo ya ci mata mutunci, har da kiran Yaran shegu marasa asali. Tunda a bariki inda aka kashe ubansu anan ta dauko musu Yaran, shi ba kome bane yasa shi yin haka, sai masifar hassada da tsana da yakewa Mahaifinsu, saboda family babu me rufin asirinsu, da mahaifinsu zance na gaskiya ana ma zargin shi yayi sanadin barin Alhaji Nasr din gida.

Kallonshi tayi ido ciki ido ta ce mishi. “Yarana ba shegu bane, idan da naso nayi alfahari da samun uba irinsu, da da shi zaj zo yayita bina kamar bindi. Da ban gadama ba nazo abina, sannan da kake cewa bariki eh bariki ne, ka gayawa Matar danka idan na kuma ganin ta ɗaukar min kayan Yara sai na karya hannu!”
“Ke shegiya karuwa!” Inji dan Baffanta, a wani fusace, ta kai mishi wawan naushi, a fuskar sai da hancinshi da bakinshi ya fashe. Ta yarfe hannunta. “Kul ka kuma kirana da sunan banza nan, idan ba haka ba sai na gigita maka lafiyarka da dukar. Kai kuma Baffa ka fita idanuna. Maganar mata ne idan ka kuma shiga sai na karya kafarka na saya maka keken guragu!”
Daga haka ta samu sauki, kowa shakkar ta yake, kuma aka daina tab’a mata kayanta, sannan kiri-kiri aka ce ta bar part din da take, ta koma na babanta, wanda sun san wurin ba a gyare yake ba, don haka ta kira kanin babansu da yake Dutse aka turo mata wasu ma’aikata na gini na musamman.

Haka ta bar garin ta koma dutse, ta saka suka rushe part din aka shiga mata, wani irin part me bala’in Kyau. Domin ta ajiye a ranta, koda Malik ya zo ya ce zai zo anan zai sauka, haka idan Zulfah tayi aure ta zo da mijinta ba sai sun tafi hotel ba. Anyi mata ginin kamar a kasar Turai, to meye banbancin Keivroto da Turai din. Sati uku aka gama ginin, Baba Umaru yana ganin ginin kamar zai mutu, baya fatan yaga cigaba Yaran Nasiru. Kwafa yayi yana kara jin tsanar Zeeno.
Ana gama aikin ta dawo, ita da Muttallab dan kanin Babanta, shi ya je har kano ya saya mata katon Injin da kayan electronics, ya kawo mata bata jin ta rabu da mamaki amma zata maida kanta ga gyara gobenta.
Don haka ta cigaba da gyara gidan, har ta dauki hoton gidan ta turawa Zulfah. Taji dadi sosai, tunda suka gama gyara ta ja ruwa da wuta, albarkacin zumunci da bawa cikin gidan, amma dan ta mutanen gidan ne ba zata basu ba. Sannan wannan aikin da tayi ya saka dayawan yan gidan dawowa jikinta, domin sun ji a bakin mutane ita din mijinta mahaukacin arziki yake da shi, wanda bata san iyakar shi ba,.sannan ba rabuwa suka yi ba, idan Zainab ɗin ce ta bukaci ya rabu da ita. Amma yana sonta haka yasa baki daya suka goge zarginsu da karya da Baba Umaru ya shirga musu.

Watansu sha daya, Zulfah ta zo mata da wasu takardun da Malik ya bata kafin ya bar kasar, wurin shakatawarsu ce da Mutane biyu suka bude, jininsu ya zuba akanta. A ranar tayi kuka da take ganin kome like a dream. “Har yau babu labarin Malik?”
“Gaskiya babu!” Kallon yaranta tayi, tana faɗin. “Zulfah nice nace kada yazo, na samu kome, kowa tsorona yake kuma ana min kome domin ina da shi, Zulfah ban san me yasa nayi abandoned ɗinshi ba, Kin ga Khalifan da Afif, ban san yadda aka yi suka iya kiran Daadi ba, duk da nayi kokarin ganin ban koya musu ba.”

“Kina son ganin mijinki ne Yanzu?”
“No kawai ina jin babu dad’i ne, ki sau daya ya bukaci ya ga halin da Yaranshi suka ciki, domin dayawa basu yarda ta aure na same su ba”
“,Allah ya kyauta, idan kina son ganshi. Sai ki nime shi!”
“A’a ba zan nime shi ba,nasan zai zo.”
Shareta Zulfah tai, haka suka tattara suka tafi Umrah dake bara tana bayan sallah ta haifi yaran, bana ita dasu da Yar Gwaggonsu suka tafi Umrah. Domin yarinyar ta dawo gaban Zeeno, tana mata reno da hidimar yara. Ita kuma Zeeno ta biya mata school of nursing, idan suka yi hutu, yarinyar take zuwa mata.
Basu tsinke da kirkin Zeeno ba, sai da kafin su tafi Umrah ta sayi kome na azumi ta raba musu, sannan ta haɗa har da kayan sallah, ta bar ƙasar. Dake a can zasu yi sallah. Hatta abin da zasu bukata duk ta ajiye musu, ( malam arziki yayi ne, babu egen da zai rainaka idan kana da shi 🤔🙄)
Haka abin ya kasance, suka yi hidimar azumi da sallah, suka dawo lokacin Yasir ya turo magabatan shi, aka yi maganar aure. Dage ba yarinya ba ce kawai aka saka bikin wata bakwai masu zuwa, a lokacin ne aka fara takura mata da maganar idan babu aure a kanta, tow ta fara shirin aure don yaranta sun shekara guda.
Ganinta a haka yana damunsu, ita ba matar aure ba, ita ba sakakkiya ba. Haka suka uzura mata har bikin yazo, a lokacin Dr Tahir Sani Malami Jajja, shima ya sako kai, ga Akram wazir da ya sako kai. Ana cikin wannan Yanayin Dr Tahir ya bata hakuri an mishi mata a gida(Guess? Waye wannan! Ku ajiye a ranku! Akwai labarin Dr Tahir Sani Malami Jajja)
Akram kuwa bata sonshi, kuma taya ma zata gaya musu ita tana son mijinta domin bai sake ba, ana saura kwana biyu bikin ta kira Wahida ta tura mata number Daadi, tunda da ta tura mata, ta kasa zaune ta kaza tsaye. A hankali ta zubawa number idanu. Kafin tayi gundunbalar kiran shi. Ringing daya yayi ya kashe, ya biyo kiranta.
“Zainab……… *Shin kira daya zai sauya ƙaddara ko zai kuma haifar da wata ƙaddarar…. Kira daya!
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button