Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 50

Sponsored Links

0- “Idan baka yi nasara ba, zan kashe ku tare da binne tarihinku anan!” “Ina da tarihi akan chess don haka mu buga a ga waye gwanin.”
Basu kuma magana ba, sai da Malik ya fadi, Haris ya ce masa. “Da alamu tun zagayen farko zan tashi kanka da harsashina. ” Malik bai ce mishi cikanka ba, suka tafi zagaye na biyu. Nan ma Malik ya kuma faduwa. D’ago kai yayi ya kalli haris ya ce masa. “Kuskuren da ka aikata bai ishe ka ba, sai ka shiga rayuwata meye na maka da na cancanci kyautarka haka?”
“Ko wannan don bai da ra’ayine amma waye zai zauna da kai ka mai dashi bawanka? Shima don bai da zuciya ne, taya zan zauna da kai kullum ina ganin yadda kake cigaba. Kai bako ne, kazo kasar mu ka cigaba mu kuma muna binka kamar bingo!”

“Amma kasan dukiyar nan ba nawa bane, na dangina ne da aka rike me yasa kuka min haka!?” Ya faɗa bayan ya bude dogarin da yake tsaye ya saka farin sarki, a gaban bakin Sarki. Kallon juna suka yi. A fusace Haris ya ce. “Kowa a garin nan Malik yake ambaton ka tab’a tunanin yadda nake mutuwa da jin an kira sunanka?” A lokacin Malik Allah ya bashi nasara ya turo bakin Sarki ya kai sarauniyar farin doki sansanin Haris. “Ban sani ba, amma me yasa ka zabi cutar dani sama da kome bayan na maka adalci.” Ya fadi haka , bayan ya ture dakarun bakin Sarki ya kafa bakin Sarki da sarauniyar shi, alamar ta cinye wasar.
Saukar bindigar Haris yayi ta cire bullet din, ta kalle shi. Sannan ya ce masa. “Ga Camera can na kallon, ba zan iya share hujja ba. Amma zan ajiye hujja idan ka gama bayani bullet uku ne, na farko ni na biyu Elbashir, na uku ka ajiye shi domin gobe zaka ji sabon labari, ai na gaya maka ni me nad’a sarki ne! Sannn sai batu na gaba, ka goge abin da ake yayyatawa domin ta haka ne kawai zaka min adalci s tsawon rayuwar da na muku adalci.”
Daga haka ya ajiye shi, suka bar gidan. Zuwa yayi gaban camera footage ya tsaya.
Karfe bakwai na safe, sabon labari ta watsu a social media da gidajen jaridu, inda Haris yake tabbatar da cewa shi ne ya sake cin mutuncin Malik maganganu masu yawan gaske, sannan ana kallonshi ya kashe kanshi, ba tare da wani ya saka shi ba.
Bayan awa daya da mutuwarshi, Malik da damuwa ta hana shi barci, domin raba daki yayi musu, ita kanta Zainaba ganin halin da yake ciki yasa ta nutsuwa, bata je mishi ba. Yana barci aka kira shi a wayarshi. Dakyar ya ɗauka ya saka a kunnen. “Malik!” “Meye?” “Haris ya mutu! Kuma kasan dan jam’iyyar adawa ce.”
“Elbashir Jamal Arab, tare da Khuldu Jahid Khan, sune zasu zama shuwagabannin kasar.”
“Allah ya taimaki Malik, an taya su murna. Amma Khuldu Jahid Khan kuma?” “A rayuwa ana bukatar abokin ciniki koda kuwa makiyi ne, a ya zama Mataimakin Elbashir din!”
Haka kuwa aka yi, Khuldu Jahid Khan, yana kallon labarai aka ambaci sunanshi a matsayin mataimakin Shugaban kasa, sai da yaji kamar ya gudu ya bar kasar, domin abin yazo mishi a bazata, Elbashir kuwa kofar part din Malik ya nufa, ya durkusa yana faɗin. “Na haɗaka da Allah, ka raba ni da mukamin nan, na amince zan amshi Mayor shugabancin kasar nan na jarumi ne irinka, ba irina ba.”
Yana faɗa yana karawa, Banza Malik yayi da shi, bai ko yarda ya bude kofar shiga part din ba. Shiga dakinshi Zeenobia tayi tana kallon shi, yana tsaye a jikin Window zuwa tayi ta rungume Bayanshi tana dariya. “Me yasa ka bashi bayan kasan baya so.”
“Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya ce hana Abuzarin gaffari, matsayi a cikin Muslunci ne don yasan yana da rauni, tunda ya tambaya, shi kuma gudun matsayin yake yasa ba bashi wannan zai kamanta adalci.”
Kwantar da kanta tayi a bayanshi ta ce mishi. “Ina tare da duk hukuncin da zaka yanke domin nasan mai kyau ne.” Goyan bayan da yake samu daga Zainaba yafi mishi kome dad’i. Haka yanayin ya kasance ana ta kiranshi aka taya Elbashir murna.

Garin Keivroto kuwa, bai tashi yin kome a kai ba, sai da za a rantsar da shugaban kasa, sannan ya ayyana Jalilah shuwa a matsayin Mayor, ya haɗa mutanenshi a duk inda Idanunshi yake kai.

Abu daya ya lura da shi, shine idanun matarshi akansu Wahida, don haka tare suka tafi asibiti aka mishi gwajin jini dasu. Aka tabbatar babu alaƙar jini da ya hadasu. Anan ma sai da ta nuna damuwarta amma bata gaya miishi ba.
Tunda suka dawo, ta bude mishi damar cin uwar sabada, gefe guda tattara tsufar mijinta, tana ririta shi.
Haka aka yi bikin rantsar da su, Elbashir aka tashi lafiya lau, Hafsah kanta rawa yake sama da kullum domin yanzu ta zama First lady, duk da haka tana matukar ganin girman Zeeno.

***
Bayan shekara daya, sunan Matar Abbas ake inda ta haifi ya mace aka saka mata sunan Ammyn, an sha suna domin bajintar da suka yi ba na wasa ba ne. Bayan sunan Ummi ta tafi hutu Nigeria, dake har zuwa lokacin Elbashir bai hakura ba, bai boyewa Hafsah ba, itama dake yanzu tana mugun sonshi, bata son ya dauko mata wata mace a waje ta amince ya auri Ummin domin da kanta ta samu Malik ya kore ta. Da cewa Elbashir ne ya turo ta, sai da ta sako iyayenta a gaba suka roki Malik din ya saka baki aka tafi har Nigeria aka nimo mishi auren Ummi, wanda Malik ta ce musu. Shi ya dauki nauyin kome da kome mata kawai zasu basu.
A lokacin bikin ne Akram ya roka a bashi Auren Wahiba, yayinda Sultan kanin Rahmah ya ce yana son auren Wahida, ganin hakan yasa aka haɗa kome aka yi, Malik ya musu kome musamman Yaran da basu da kowa sai shi, shi kuma Malik din ta dauke su a matsayin mahaifinsu baki ɗaya.
Sai da aka yi gaggarumin bikin da ba a tab’a yi ba, domin a Kano aka daura auren, duk da ana bikin nan, Zeeno karfin hali take, domin Malik ya mata shuka, wanda yasa baki daya bata da wani kuzari sai yadda yayi da ita, abin dariya abin tausayi domin a gajiye take wannan karon cikin ya shiga jikinta, domin hutun da tayi ya ratsata.

Haka aka gama bikin, ana laulayi aka turowa Elbashir matarshi, aka tafi da ita. Ita da Malik suka zauna hutawa, domin ta masifar laushi, shi kansa wannan karon lallabata yake yaki zakewa akanta. Haka suka kwashe wata biyu, tana laulayi. Yana mata sauki suka wuce gida, a ranar da suka isa Zulfah ta haihu da dare, kusan wani hidimar ya karu mata, ita da Jalilah. Wacce take Matsayin Mayor.
Sati daya suka yi ta zirga-zirga, tsakanin gidanta da na Zulfah, har aka fita suna. Sannan ya dawo ta nutsu. Abin gwanin ban tausayi. Domin tana samun hutu. Jikinta ya dawo sabo sai da asibiti suka rike ta.
Tsawon sati Uku, kafin suka sallame ta. Alhamdulillahi cikin yana nan lafiya. Domin tana shiga wata hudu, ta samu lafiya babu wani laulayi ko rashin cin abinci. Ranka shi dade kuwa yace ya dawo kan duties.
***
Goge gashin kanta take, yana kwance yana kallonta, “Baby girl! Kin ga wannan karon cikinki ya fito sosai.” Bude towel din tayi tana murmushi. “Ajiyarka sai kara girma yake ba!”
“Da alamu wannan karon babban mutum zan kuma samu, babban mutum an ga gender ɗinshi kuwa?”
“Ai kuwa ban tambaya ba.” Ta faɗa tana daka riga. Ta sanshi da son sanin meyye zata haifa, taki yarda a gaya mata. Wannan karon tana jin nauyin cikin har cikin jikinta.
Hafsah da Ummi, zaman lafiya sosai suke da junansu, ga girmama juna haka yasakawa mijinsu mugun kaunarsu. A hankali zaman ya kara samun fahimtar juna musamman da ya kasance yana boye son da yakewa Ummi domin har ga Allah yana sonta, sama da Hafsy da kawai Malik ne ya zaba miishi ita.
Haka suka zauna cikin Amincin Allah.
★★★
Kwanaki dari biyu da yan kai yake daukar mace,renon cikinta da haihuwa, idan aka hada jimilar kwanankin zai bada sati arba’in da daya ko da biyu. Wanda shine kawai lissafin da azayi kafin a kai da wata tara, ranar haihuwar kuwa daga ita har Malik sai da suka san haihuwa tayi, domin an ci wahala, sannan aka haifi Yaranta mace da namiji. Ɗaukarsu yayi ya musu huduba, namijin shine karami ya saka mishi. Muhammad Elbashir, macen kuwa Sunan Mahaifiyar ya saka, tare da jin kaunar Yaran ita kanta tana son yaran,

Lokacin da Elbashir yana jin labarin, yana da Meeting da manyan mutane, haka ya ajiye ya tawo Keivroto. Sai da Malik ya kore shi. Ranar suna kuwa ba karamin walima aka yi, kyautar da Elbashir ya mata, da yaran, sai da Malik ya tsare shi da tambaya.
“Da fatan ba dukiyar Al’umma ka dauka ba? Ina cewa ba kuɗin mutane ba ne?” Girgiza mishi kai yayi yana faɗin. “Wato Malik baka yarda da nagarttta ba ne? Malik ba zan iya cin hakin kowa ba, ina da shi ina da abin da ko bana raye matana zasu kula da kansu, wallahi daga aljuhuna na cire wannan na basu.”
“Alhamdulillahi, ina tsoron kada Allah ya kama mu da hakkin al’umma ne, shi yasa na ji tsoron kada hakkin Al’umma ce ”
“Rayuwar da babu aboki irinka bata da ma’ana Nagode Malik”

Bayan suna suka cigaba da wankarsu, har zuwa bayan arba’in, inda suka zo Nigeria ta’azxiyar rasuwa Baffa Umaru, wanda yayi fama da dogon jinya, a bakin Gwaggonsu take jin labarin abin da ya faru, tun kafin bikin Ummi yayi hatsari. Shi kenan ya kwanta jinya, satinsu biyu ta wuce Maiduguri, kowa sai son Barka, Inda ta samu Wahiba, tana jan cikinta itama.
A dakin Hajja Yayye ta zauna suna hira ta ce mata. “Hajja Yayye, kin san lokacin bikin Abbanmu da Ummin mu a ina suka hadu?”
“Maganar gaskiya ina Saudiya lokacin, amma labarin da naji ance yazo karatu ne nan, makarantar nan Maiduguri, suka hadu a jami’a, kuma a lokacin har an mata miji amma tace sai shi, ba a ja da ikon Allah ba. Domin mahaifinta mutane da Allah ya mishi baiwar ilimi da yarda da ƙaddara shi yasa ya bata wanda take so.”

“Tow ya aka yi suka yi aka bar Ummi Jalilah Demark?” “Wannan kuma hatsari ne ko nace fashi da makami, ita Mamarku bata bisu ba, don tana makaranta, aka samu labarin abin da ya faru, Allah masani!”
Kawai abin da ta yarda da shi, ƙaddara da rabo. Haka ta gama kwananki ta koma,

Bayan wata biyar, suka zo sunan Wahiba, wacce dama.sai da tayi tunanin haka, domin ta riga Wahida samun ciki.
Bayan sun da sati Uku, Wahida ta haihu itama suka sha hidima sosai. Dukkansu abin mamaki sunan Malik suka saka mata.
Tana nan aka kira Ummi tana asibitin. Dole suka koma kafin su isa aka kira su aka gaya mata ta sauka lafiya, koda suka isa. Bata bai gista ba, sai da aka yi suna da sati biyu. Sannan ta bar garin, ta dawo gidan mijinta.
★★★
Bayan shekara hudu.
Tun safe da Paul yazo gidan, bata san me ya kawo shi, sai bayan tafiyarshi Malik yake bata labarin ashe son Auren Jalilah yake, dake shi yake kare lafiyarta. Shi ne ya gaji yazo rokon Malik ya aure mishi ita, domin zai iya kome domin mallakarta da karfi da yaji. Shi ya shirya musulunta.
Shi kuma Malik ya kira su Alhaji Mustapha ya gaya musu.

“Yanzu dai kinji abin da ake ciki” daukar Adnan tayi dan wurin Abbas tana dariya.
“Allah ya bada zaman lafiya!”
Jan hancinta yayi yana dariya, haka aka.daura auren Bayan Paul ya musulunta.
Walima aka yi, kawai. Jalilah kamar zata yi hauka. Amma wani abin dariya, tunda ya nuna mata shi ba lusari ba ne, tuni tayi watsi da cewa bata son Yaro domin ta bashi kusan shekaru goma sha huɗu.
Yana da talatin tana da arba’in da hudu, sannan abin ya matukar bada kyakkyawan Chemistry.
Duk wasu mutanen da suke jikin Zeeno, Suna cikin amincin Allah da cigaba, musamman wadanda suka yi daba tare, kai ko iyayen Hibba sun ci albarkacin auren Abbas da Hibba tayi, Al’umma Charity House, yana can da su Maman Chu-chu Malik ya dauke musu kome.

Lalla Salmah tazo sau biyu niman, yafiyar Malik da Zeeno ta ce ta yafe, Shatima kan yana can yana girban rayuwa, itama yarshi tana can sai godiyar Allah.
****
Tun da ya shigo ya samu tana tsakiyar Yaransu. Muhammad Nasr, Hussaini, Muhammad Menk Hassan, Maidah, Muhammad Elbashir, sai Sassabilah Mami suke kiranta. Zama yayi ya ce mata. ” Da ace ke wata ce sai ko karo.mana Ammyn da Alhaji Ahmed” mahaifin Abbas da Ammyn. Dariya tayi ta nufi kitchen, tana aiki. Biyota yayi ya rungume ta. “Da gaske ki kara mana biyu ko!”
“Wanda yake ajiye a kasar marana cikin wata hudu fa.” Juyata yayi da sauri ya shiga sumbatar bakinta. “Happy birthday Daadi!” Breaking kiss din yayi yana kallonsu da dukkan mamakin shi. “Gashi nan, Uncle Elbashir ya ce a maka surprised!”
Sumbatar goshin Hassan yayi ya bi sauran ma haka. Tana murmushi, sannan ya sumbaci cikinta da yake cikin riga.
*ALHAMDULILLAHI, NA KAMMALA A PAGS SABA’IN DA DAYA IDAN MUKA HADA DA BOOK 1&2 NA GODE SOSAI MUSAMMAN MUTANEN DA SUKA NUNA MIN KARA NA GODE SOSAI FA KADA KU MANTA NI TAKUCE HAR KULLUM*
*Arewabooks iya book 2*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*

Leave a Reply

Back to top button