Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 32

Sponsored Links

32- dakyar ya lallabata tayi wanka, suka kwanta. Wani irin gajiya ce ya taru mata, barci me nauyi yayi gaba da ita, bata san wani duniya take ciki ba, sakamakon shi da ya kasa rintsawa. Idan har zata cigaba da bashi kulawa haka, yasa rayuwarshi zata fi haka sauyawa, amma yarinya ta haɗa mishi jagwal, rungumeta yayi ya baya, suka cigaba da barcinsu. Da asuba ma dakyar ta tashi bayan ya shirya suka bar gidan, domin wanka yayi ya shirya cikin shigar kamala.

Abin burgewa haka ma Elbashir, a tare suka shirya, shi shaddar shi fari sol. Suka nufi gidansu Hafsy. A nan suka yi Sallah asuba, ana idarwa aka daura auren Elbashir da Hafsy. Duk da ba a samu labarin akan lokaci ba, amma kuma an taru a masallacin, mutane dayawa sun yi murna domin ana daura auren suka shiga rabon kuɗi. Kafin suka shiga wurin Mahaifiyarta, suka gaishe ta sannan suka fito. Gidan suka dawo suka saka Hafsy da Zeeno a gaba. Aka kai su gidan su Hafsy, Mahaifin Hafsah kuwa don jin dadi kamar ya rungume Zeeno, don murna.kamar ya kwantar da kai ta hau kanshi. Dake basu san me ke faruwa ba, don haka aka saka su a duhu.
“Mama lafiya kuwa?”
“Aunty Hafsy kin zama amarya yau!” Kallon juna suka yi, suna masu maida hankalinsu kan Adi, “kamar ya?” Dariya yayi yana fitar da sabin kudi, ya cigaba da cewa. “kun ga wannan mijin Aunty Zeenobia ya raba mana, bayan an daura auren Aunty Hafsy da Uncle Elbashir!” Ya kwasa da gudu ya bar dakin. Safe kirjinta tayi, “Ni!” Sai kuma ta rufe dakin tana tana me fadawa gado. “Omo nice matar Elbashir?” Sai kuma ta fashe da dariya, tana me sake kallon Zeeno da tayi sororo.
“Me ya faru jiya da Mayor ya miki faɗa?”
Dariya tayi sosai, kafin ta ce mata.
“Jiya ne muka kusan cinye juna” ta faɗa tana kare fuskarta. “Meye?” Kunnen Zeenobia ta nufa ta ce mata. “Ya nima kuma na bashi ya tab’a shi ne zai wuce iyaka, Mijinki dake dan Aljanna ne ya zo ya nima mana me gaba-daya. ”
“Ke yanzu Hafsy sai ki bar shi ya!”
“Ai ni kaina ba a tukunya yake ba, yanzu yarinya zaki ga yadda ake bura uba, domin sai kun bar mana gidan nan, domin amarci zamu ci!” Buga kofar dakin yasa ta yin shiru, suka bude kofar. Wani katon kula Mamar Chu-chu ta bata, tana faɗin. “Tun daren jiya aka gaya mana, shi ne yau na kawo miki dahuwar kaza!”
“Taci a hankali dai, domin wallahi ba kome a cikin auren sai aiki daya.” Zeeno ta fada tana hararan Hafsy.
“Na shiga uku ba zan ci ba” ta ajiye kular.
“Ke ki rabu da Zeeno, da babu abin arziki shi wanann kunshin gaban rigarta ita ta kunsawa kanta?” “Ni ba haka nake ba!” “Ai dama na san ba haka kike ba, yasa na gaya miki oya maza wuce ki ci ki rabu da Zeeno kada ta yi spoiled din tunaninki.”
Tana fita Hafsy ta zauna ta cinye tas, ta ciro kayanta ta fara fito da wasu kayan matan, Indonesia ta fara sha tana duba expire date dinsu.
“Hafsy baki tsoro ne?”
“Ina tsoro mana, amma duk abin da zan ji dadin daren farkona wallahi zan sha. Babu wanda ya san me gobe zata haifar.”
“Amma Hafsy!”
“Kin ga ina sonshi, koda Malik bai hada mu ba, ban tab’a mafarkin samun wanda ya kai shi ba, bai tab’a mik maganar banza ba, jiya ma abin da ya faru kuskure ne, so don haka zan gyara jikina ni ba sakarya ba ce da zan bar mijina a banzace!”

“Hafsah magana kike gaya min?” Zeeno ta tambaye ta jikinta a mace, “A’a kawai na gaya miki abin da ba zan iya ba ne, duk abin da zai saka shi farin ciki ina maraba da shi”
“Yayi!” Ta faɗa tana me kwanciyarta, sannan ta ce mata. “Nima ba kin Malik nake ba, ba kuma sonshi ne bana yi ba kawai akwai abin nake dubawa ne, idan wani abu ya same shi, nice zan yi maraici har karshen rayuwata, idan wani abu ya samu cikin jikina, zan ta danasani har mutuwata. Idan nace bana sonshi ai nayi karya, sannan cikin jikina ma ya isa ya tabbatar da irin son da nake mishi!”
“Ai ba cewa nayi baki sonshi ba, wulakanta shi kike a gaban kowa!” “Karya kike Hafsy, baki kai, ki gaya min magana ba, baki isa ba. Har yaushe kika kai wacce zaki gaya min magana!”
“Ai matsalarki kenan, rashin fahimta. Wannan rashin fahimtar da nutsuwa a magana zai kai ki inda zaki yi kuka da kanki mtseew! Banza mahaukaciyar wofi! Wacce bata san darajar kanta ba, ana gaya miki abu kina wani kauce hanya!”
“Ni kike gayawa Magana?” Ran Zeeno yayi bala’in b’aci. “Anga miki, me zaki yi wacce bata san darajar aurenta ba! In sha Allah sai Allah ya kawo wacce zata rabaki da Malik, kin zata zan kyale ki ne don kawai mazajen mu abokan cinikayya ne? Idan kin so ki duba wannan sakon, na boye ne babzan gaya miki ba, gashi ki je ki ta tsanar mijin naki mahaukaciyan banza”
Yadda ta ajiye matar wayar ya saka jin kamar ta rufeta da duka.

*Ina son ki bawa Zeenobia wannan sakon, ta karanta domin na fahimci mahaukaciya ce ta gaske, mutumin da ya shiga rayuwarta da take dauke da cikin shi. Shi ne wanda ya kashe iyayenta. Don haka ya rage gare ta ta zauna da shi ko ta dauki mataki! Idan kina ganin karya ne ta tambaye shi.*
Wani irin rawa jikinta ya dauka, tare da jijjiga me bala’in tashin hankali. Bata iya fahimtar me kome, ta zube a wurin daidai lokacin da aka ɓalle dakin.
“Hafsah me ta miki da zafi kika mata sakayya haka? Me Zainaba ta miki da zaki bita da sharri haka.
—- kafin nan, bayan zuwan su gidan Malik yana hanyar zuwa office din yan sanda. Aka kira shi a waya. Daukar wayar yayi ya duba yana kallon Elbashir.
“Lalla Salmah ce!”
“Dauka mu ji me zata ce!”
“Dauka yayi ya saka a kunne!”
“Na turawa Matar Elbashir sakon da zai kara muku, kaunar juna kai da Zeeno dinka. Kayi fatan ta haifi cikin jikinta lafiya!”
Wani irin taka birki Elbashir yayi ya juyar da kan motar, saboda a handfree wayar take. Lokacin da suka isa ai sun same Safina Maman Chu-chu a tsaye ita da iyayen Hafsy. Dukar kofar Elbashir yayi, yaki budewa, cikin fushi Malik ya daki kofar dakin yayi da kafa, budewa yayi ya hangota kwance. Ita kanta Hafsy din a razane take. Bata san me ya shiga kanta ba, shiga dakin Elbashir yayi ya dauki wayarta ya shiga duba inbox dinta. Kudin da ya gani ya bashi tsoro.
“Kuɗi suka baki kika fada mata haka?” “Ina sonki da aure da kome, amma soyayyar da nakewa Malik!”
“A’a Bashir!”
“Wallahi ba zan zauna da ita ba, domin zata iya kashe mu. ”
Ya juya ya kalli Mahaifinta. “Bani da kowa sama da Malik! Dangina suna can wata duniya Malik shi ne dangina. Malam kayi hakuri ba zan iya zama da yarka Hafsah ba, ta zauna kafin na yanke hukunci.”

“Wayyo Allah na, don Allah ka rufa min asiri.” “Allah ya wadaran halinki, hankalinki ya kwanta sai ki cigaba da zama wallahi ba zaki tab’a jin dadinmu ba” asibiti suka tafi da Zeeno. Ba karamin wahala ta sha ba, domin cikin jikinta so yayi ya fito akai ta mata allurai dole ya tsaya. Domin wa’adinshi bai kai ya fito ba. Ya kira Ummi ya gaya mata, sannan ya kira Jalilah Zulfah da kanshi ya daukar mata excuse a wurin aiki.
Kwana uku tana barci domin jininta yayi mugun hawa, dukkansu suka iso. Suka saka ta a gaba, kamar zasu cinyeta. Sai ranar na hudu ta farka, Malik na gefenta. Kallonshi take da dukka zuciyarta, sonshi take kamar zata yi hauka, hawaye ke bin idanunta cikin tsananin kauna. Amma jinin iyayenta ba zai tafi haka kawai ba. A hankali ta janye hannunta daga na shi, ta juya mishi kai.
“Sannu Zainab” kallon Jalilah tayi, sannan ta juya ga Ammyn da Zulfah, haki ta fara tana miƙawa Zulfah hannu. Da sauri ta isa wurinta. Tana haki da kyar ta ce.
“Ki ɗauke ni daga wurinshi!” “Ki nutsu ayi fama da lafiyarki!” “Ya tafi bana son ganinshi!”
Ta faɗa da mugun ƙarfi, tana haki da tari. Fita yayi suka tawo da likita, allura aka kuma mata. “ku bar ta huta don Allah! Kunsan ba ita ɗaya ba ce sannan tana ganinku hankalinta zai tashi.”
Fita sukayi, sai dare ta kuma farkawa. Jalilah da Ammyn ne a wurin, da taimakon Allah da su, suka mata wanka, ko tsayuwa bata yi. “Ammyn!”
“Na’am!” “Ku mai dani wurin dangin Abban mu”
“Amma kya bari ki samu lafiya ko?”
“Ammyn idan na tafi can zan samu lafiya!”
Suna fama da ita, ya shigo tana had’a idanu da shi. Ta fara haki tana nuna shi da yatsa. Tana son magana haka ta kasa a hankali suka fahimci, bakinta yana shirin komawa gefe, “ka fita Malik!” Jalilah ta tura shi waje, tana kara cewa. “Ka kira mana likita!” Ko kafin su iso, yanayin da ba ason ta shiga dole ta fara shiga. “Me kuka mata?”
“Ni ta gani shine ta shiga wannan halin!”
“Don Allah ka daina zuwa! Zamu rike ta, idan cikin ya kai wata bakwai zamu cire shi. Saura wata guda ne, ka taimaka a cire cikin lafiya.”
“In sha Allah” ya fada yana me tafiya, idan hankalin Malik yayi dubu ya tashi, Elbashir hauka ne bai yi ba, amma har ga Allah yaso sake Hafsy. Malik ya hana shi ya ce ai itama ba laifinta bane, ba kowa bane yake da irin zuciyarshi, wani da kudi ƙalilan za a sayi tunaninshi. Malik yayi hakuri amma a wannan karon cewa Elbashir yayi dan barshi na kwana biyu, baya son hayaniya.
Tunda ya tattaro kome na shi ya dawo Waterfall ya zauna, kome da yake tafiya yana ji a bakin Jalilah. Ya tabbas sun yi nasarar wurga shi cikin kadaici. Bashi ga tsuntsu ba shiga tarko.
Yana zaune idanunshi akan wayarshi, hotonta ne da ya dauka, kafin ta zo Keivroto. Shatima ne ya kira shi. Ya dauka sannan ya ce mishi. “Ka tattara ka bar garin nan kawai, idan ba haka ba, shima cikin jikinta bai tsira ba. Sai nayi draging dinka to the hell.”
Dariya Malik yayi ya ce masa.
“Shi yasa ka nace sai ka ci dukiyar da baka san lokacin da aka tara ba ko? Ka saka a handfree domin Lalla Salmah ta ji, kin kyauta sosai. “Arwah da tana nan lafiya lau, kamar yadda kike boyewa duniya kunna tv kusha kallo lafiya, Shatima ai ka makaro, yanzu zaka ji bugun kofa. An kama yarka da hodar iblis.. ban san me yasa ka nace sai ka tab’a ni. Ita kan yarka bata cancanci samun uba irinka ba, yanzu zaka samu sallame manyan baki, zaka kamo inda ka fito a can zaka kare rayuwarka Idan na kyale ka kaci banza amma tabbas zaka rayu kana niman mafita kana jin labarina ina raye! Escape before su kama ka! Dama na kara baka domin rayuwa idan babu kai ba zan tab’a jin dadi ba. Ka sani zakai ta gudu ba dare ba rana, domin kare rayuwarka. Ni kuma na mamaye Keivroto daga cikinta har wajen ta. Shatima kenan ba fada da ni bane kwana mita, ba zan yi farautar rayuwarka ba, amma zan saka maka jin kamar ina bibiyarka. Zaka rayu kana kara jin ina bibiyarka.”
Ajiye wayar yayi yana murmushi, baya son hayaniya ko wani abu ya lalata tsakaninsu, amma dole ya hakura da Shatima.
Kuma yasan idan yadda ya tsara ne, ba su kama shi, zai ta jiranshi har ya kawo kanshi.
Lalla kan baya tunanin zata waiwaye shi.
****
Acan kuwa labaran da aka fara nunawa, yarta Arwa, da tayi fama da jinyarta laka aka nuna. Tare da cewa.
“Boyayyen sirrin Lalla Salmah”
Kafin aka fara magana kanta, bata iya sauraro ba, ta shiga hada kayanta. Zata bar gidan domin bata san yadda Shatima y kare da Malik ba, tana fitowa Yan sanda suka yi gaba da ita, tare da kin gaya mata inda zasu kaita. Domin rufe mata fuska suka yi, suka bar gidan da Ita.

Shatima kuwa gudu yayi ta yi, domin ceton rayuwarshi.
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button