Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 16

Sponsored Links

016
___________________
Masarauta
Mai babbar ɗaki hankalinta in yayi dubu to ya tashi ,daga ɗakin mai martaba cikin garden ta wuce ,tana kaiwa da dawowa ranta in yayi dubu to ya ɓaci
Auta ma a furgice ta fito tana neman mai babbar ɗaki,can garden ta hangota ,tana kaiwa da dawowa ta goya hannu a bayanta cikin zuzzurfan tunani.
A nutse ta tako zuwa bayanta ,tana tafiya kamar ƙwai ya fashe mata a ciki .

“Mama !”

A zafafe ta waigo ,ganin Auta a gefenta yasa ta saki ajiyar zuciya saidai batayi magana ba sai zura mata ido da tayi.

“Mama tsoro nake ji🥹”
“Menstral stringling?”
Girgiza kai tayi da sauri kamar zata fasa ihu
“Aah Yareema!”
Haɗe gira tayi da sauri kamar ta fada mata wani abun mamaki ,itama ba akan damuwar hakan take ba
“Me ya faru da ɗana!”

“Maama ,bakiji abunda malamin fada yace bane? Nan da sati biyu za’a naɗa Yareema sabon Sarki,to amma kuma idan har mabiyan sarautar (Rauhanai _Spirit_)basu bada goyon baya ba ,To kinsan fita zamuyi ,a masarautar da ɗingurgum ko?! Za’a kore mune!”

“Ke Auta🙄Sa idonki cikin nawa, Bana son sakarci, abunda nike so ki Gane shine cancanta shine ya kai ga mahaifinku ɗarewa gadon mulkin nan ,kuma gadajjene kaka da kakanni,kuma a halin yanzu ba mahalukin da yake da ikon gadon wannan sarautar sai Yareema…maganar Malamin fada ,su Ciroma da kowa ma ai bazai tasiri ba,Na lura gidadanci shi yake ɗawainiya dasu ,saboda sun kasa gano dalilin ciwon mai martaba zasu fake da tsubbace_tsubbace don su ƙwace sarautar nan ,Babu Sarki a garin nan sai Yareema !”

Ɗaura hannu aka tayi ta yarfe da sauri “Mama🥹😞ba maganar da nikeyi ba kenan Yaya bai cancanci zama shugaba ba… ”

Diddilo ido mai babbar ɗaki tayi tana kallon ta

“Yes mama,naje masarautu kala kala naga yanda yarimansu suke unlike ours…he’s Self centered ,kanshi kaɗai ya sani…very Arrogant ga ɗagawa da gadara, he’s very very rude😔…Mama , Yaya Yana da tijara ,mutumin da idan an gansa mutane ke fallawa da gudu?!🤦🏻‍♂️To duk ba wannan ba ,Baya ɗaukan shawara misƙala zarratin….kai ! Mama na karanta politics a university fa ,Yaya shine yake da cikakken suffan mugayen shuwagabanni da ake koyar damu a…..”

“Keee! Ya isheni…..Babu wani mahaluƙi da ya isa ya ƙwace sarautar nan a hannun mu ba malaman fada ba bare ke da kananun maganar ki na dolaye🫵🏻” ta nuno ta da yatsa cikin fushi ,ƙirjinta na sama da ƙasa tamkar ta watsa mata wuta.

Jirgawa tayi da sauri saboda yanda jikin mai babbar ɗaki ke bari gani take rufeta da duka kawai zatayi

Da ƙarfi ta finciki rigar alkyabbarta tayi hanyar cikin gida da sauri ta bar Auta a tsaye.

Durƙushewa tayi a kasa ta saki kuka mara sauti

“Allah mama na da yaya na ,Allah ka ganar dasu gaskiya!”

Kuyanga Lantana da kuyanga Adama ne suka shigo cikin garden din

“Barka da hutawa uwar ɗakina ,Kayan marmari sun yi yabanya mai kyau a cikin garden din nan,musamman korayen tuffa da ƴaƴan Inabi ,zamanki a lambun zai ƙara armashi in kina ci daga cikinsu….”

Ɗaga mata hannu tayi cikin kwatse mutum

Da sauri kuyanga Lantana ta ɗago ta kalle ta ,nan taga idonta sunyi ja kamar garwashin wuta

“Bani buƙata ,ku fita Lantana!”

Sum sum sum ,suka fice ,aikuwa suna kaiwa ƙofa Adama ta kalli Lantana ta bushe da dariya

“Allah ya ƙara maganin mai shishigi kenan!…Na faɗa maki fadan nan ba zaman lafiya kin kasa ganewa”

“Ko dai menene ai shugabata ce tana da daman yi mun komai…banza munafuka!”

 

 

Oum Aphnan✍🏽
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button