Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 38

Sponsored Links

038
___________________
Yareema cikin matsanancin ciwon kai ya buɗe ido ,wanda suka kada sukayi jajawur ,ya ɗauka zai buɗe ido ya gansa a kabari sai ya ga fanka na yawo a saman tangamemen bedroom ɗin mai babbar ɗaki

Auta na gefe tana shafe masa fuska da ruwan tofin Addu’a.
Yana bude ido ya kamo hannun Auta
“Nagode …Nagode”

Fashewa da kuka tayi tana jin Muryar yayansa ”Yarima ka gani ko? Kaga abunda nike fada maka ko? Gayinan taurin kanka zaija mu rasa ka ɗingurgum ,mutanen nan tsafi garesu,duk wani masarauta da kaga ta ginu ,an kafata ne ta hanyar asiri da tsunburkai ,in ba don hakan ba da kowa ya kawo masu farmaki…kai da kowa ma yace zai ƙwace kujeran mulkin tun kafin kai kayi a yau….”

“And so fucking what?” Yayi magana cikin ɗagawa ,full of confidence. Cikin ɓacin ran baƙin taurin kansa tace “Sai gayi can dattijan fadan da ka wulaƙanta suna jin daɗi suna tereraka a duniya…suna jin daɗi”

“Su jira inyi lafiya in haye karagar sai na fitinesu ɗaya bayan ɗaya ,da kansu zasu tattare kan iyalansu su bar garin nan”

“Uhum ! Ni na gaji da gafara sa banga ƙaho ba ,kasan danbarwan da akayi ne kana kwance? To kaji nan,zai wuya ka zama sarki rather you will put your self into higher jeopardy as I heard this morning ,Wai ba mu kaɗai bane yaran baba yina da wani yaron a wani waje kuma dashi zaku fafata wajen amsan sarauta wanda yayi nasara shine sarki….”

“What??!” yayi zumbur ya miƙe zaune ,tsikar jikinsa na tashi saboda fitina

“Kenan baba yaci amanar mama kenan ya aje ɗan shege a waje?”

“Baba ne kadai zai tabbatar da hakan kuma yana kwance rai a hannun Allah”

“Subhanallah ,Me yasa baba zai mana haka? Me yasa zai gurɓata mana zuri’a ,mai yasa zai ja mana zagi da abinda za’a ringa nuna mu ? Mai yasa zai ɓata mun carrier matsayina na candidate ɗin da na fito takarar gwamna? A yanzu bani buƙatar sarautar gidan nan,mutuncina nike so ,da mutuncin ahalina, na yafe zama sarkin ,su bawa wanda suke so ,Ni zan dage in zama gomna daga nan sai in tunɓuke sarkin da suka ba ,in Sauya da wanda na ga dama,Ba yanda za ayi rigimar cikin gida da rashin cancanta na yasa a baiwa shege sarauta ,in akayi hakan anci mutuncin sarauta ,anci mutuncin Garina….

“Yaya ba wanda fa ya tabbatar da ko shi Shegen ne ,akan me zakayi saurin sarewa,akan me bazaka fito ku fafata ba,Wanda yafi cancanta sai a bashi karagar”

“Ina! Ɗan Asali ne kaɗai zan iya goga kafaɗa dashi wajen neman wani abu ,banda ƙasƙantacce ,na bar mashi yaje yayi sarautar sai me?”

“Idan ka bar mashi sarautar ke nan ya gwada kaji tsoro ne,Azabar da akayi maka da wuta yayi tasiri a zuciyarka ne,kuma wannan zai shafi har takarar ka ,ka sani ko?”

“Ina maman? Kira mun ita muyi magana ke yarinyace Nihla ”

 

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button