Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 36

Sponsored Links

036
___________________
A Guje ta gangara zata fice daga gidan shikuma Ambassador ya shigo yana tsaye a gaban motarsa hannunsa riƙe da bottled water ya ɗan harɗe ƙafarsa yana waya cike da nishaɗi yana rausayar dakai yana shaƙar iskar wajen a hankali…Nikuwa oum Aphnan ɗinku nace hmm kaji masoya , ana ta baiwa Fulawa ruwa.
Yanda ta fito a hargitse tana wuri wuri tana Neman Hanyar barin gidan yasa ya bita da sauri
“Hey wassup”
Waigowa tayi ta kalleshi cikin dacin rai . A duniya ta tsani abokin miji mai damun mutane da yawan zuwa ,to shi wanann kuma mai ya dawo dashi ? Shikenan su basu da sukuni kenan?

Ɗan sakin dariyar yaƙe tayi “Ambassador kaine again?”
“Nine wlh …humm ya na ganki kamar a firgice ? Saƙone zaki amsa?”

Kafin ta bashi amsa ya jiyo Muryar ya Sheikh yana takowa da sauri yana kiran sunanta .

Wurrrr ta falla da gudu tayi hanyar back yard ɗin gidan ,tabar Ambassador a tsaye ,yau ta ƙudiri aniyar sai ta bar gidansa kuma in ta tafi bata dawowa har abadan.

Mamaki abin ya baiwa Ambassador ,lallai ba lafiya ! Shima kafin Ya Sheikh ya gansa ya wulƙa yayi hanyar da yaga tabi .
Yana shiga wajen ya ga ta jingina bayarta da bishiyar barankace,tana bulbular da hawaye kanta a sama.

“Salimart menene?” in a speed motion like a twinkle of an eye ta sa hannu ta goge hawayen fuskar ta ,ta kuma daura da washe baki .

Kallonta yayi ga hawaye ga dariya “Humm kina da matsala…”

“Ban dashi”
Da Karfi ya amsa ta irin na mazajen nan masu bada Authority

“No kina da matsala”

“Yes ina dashi and it’s your friend Kuma yau ko zaku kasheni sai gawata ta bar gidan miqdad ! Bazan sake zama dashi ko na sekwand guda ba”

“Is that what makes you to be running like a foolish rat? Calm down ok? I’ll help you solve the problem ,you knw here too might not be secured to you ,as you know is his house ,iyaye zai kira maki su Baki baki,and dole ki hakura bayan an muku sulhu…” Zaro ido tayi

“What is the solution ?” kafeta da ido yayi yasa haƙorinsa yana jan leɓensa na ƙasa yana tsotsewa.

Cikin ƙaraji da ƙosawa tace “Plz what is the way forward ,I need to move desperately ,oh like…..” kawai sai ta dafe kai hawaye na sharara mata

Ɗaura hannunsa yayi a kafaɗarta ya ɗan cakumi naman kafadarta yana murzawa a hankali

“Sorry ok? Zaki bar gidan Sheikh kina da dukkan makamanki , yanzu zan saka ki a motana inja tint in ya gama karakaina up and down sai in tuƙaki mu tafi”

Kallonsa tayi kamar bata yarda ba sai kuma ta murguɗa masa Baki cikeda tsiwa “To ɗan bar kama mun kafaɗa”

“An bari sarauniya,wa ya isa ya bata ma tsaleliyar mace kamar ki rai sai maras rabo”

“Ban gane ba?”

“Eh mana ,Nifa na daɗe ina gaya ma Miqdad ya sauya zamansa dake in Kuma Bai iyawa to wallahi muna gefe kamar kuraye yana sakaci kika fito ,caraf zamu cafe…”

Dariya tayi saboda yanda yayi magana

“You funny hahahaha”

“No I’m not,Gwara in fara shigar da ƙoƙon barata ,tun yanzu kafin manema su Kunno Kai a manta da ɗan bawan Allah ambassador ,tunda na lura dramar nan naki da ya Sheikh yana dab da karewa to na ajiye appointment Zan dawo inyi spilling ,Dama muna ciki tun a wancan karon ,ya Sheikh ne ya riga mu….”

“Are You serious? Kallon da kake ma matar abokinka dama haka ne? To ko kai ka hanamu zaman lafiya dama can ? I already knw abokan miji a yawan lokaci su suke hardasa rashin jin daɗin zaman ma’aurata,in kuwa har so kake in fito don ka aureni ,to na gunmaci in cigaba da zama da Ya Sheikh ko banza zai feeding Dina da ƙira’ar ƙur’aninshi,in bai bani abinci na ƙoshi ba …… unlike youuuuuu idonka akan mata .move jhorrr” ta hankaɗe masa kai ta fito

“Salima wait…wait…ki tsaya mana ,let me clear my self to you ”

Ko kallonsa batayi ba ,kawai ta juya cikin gidan ,wata zuciyar na gaya mata “Salima kafin ki tona sirrin zamanku da mijinki a duniya sit with him at first ,kiji meke damunsa ,me yasa yake da maƙo? Maƙonsa ya zarce na lafiya ya zama ciwo,me yasa baya sauke haƙƙinsa na aure a kanki….make some promises indai har yayi alƙawarin sauyawa a aikace gwara ki daidaita da mijinki da ki fito ƴaƴan mage suna farautarki (Ambassador and co. ) Saboda auren ki dai shine ƙololuwar mutuncinki”

Da wannan shawarin zuciyar nata ta koma cikin gidan ta ,saidai Ya Sheikh tuni ya fice ya banzama nemanta a gidajen en uwa da abokan arziki

Da gidan Dr Adnan ya soma ,ya fara dukan ƙofar na hauka

“Alhaji fito mun da ita”
Adnan da ya farka daga barci murtsuke ido yayi da ƙyar yana kallonsa muryarsa a doshe irin na masu barci yace “Ita wa?”

Tsawa ya doka masa “Kaiiiii ! ,Dont tell me rubbish . enough is enough fa,wlh in baka fito mun da matata ba hukuma ce zata rabani dakai ….banza baƙo kawai,kazo garinmu ka shiga cikin gidana kayi kane ²

Warass idonsa ya buɗe
“Dont tell me Salimart ta Kara ɓacewa for the second time?
Nunashi yayi da ɗan yatsa yana gargaɗinsa

“Wallahi summa tallahi,a wannan karon idan har Salimart ɓata tayi ,to kai zansa a kamaka kuma in tona asirinka akan halin ƙuntata mata da kakeyi,wallahi sai kayi gidan yari,adadin kwanakin da zata ɗauka ba’a ganta ba kai harma da surplus , shashasha kawai wanda bai san darajar matarsa ba ,ka tara gemu biya² ,dashi za’a jaka zuwa jahannama in bakayi wasa ba….banza illiterate”

Yanda Dr Adnan ya saki jiki yana ɗura ma Ya Sheikh magana ya tabbatar masa da Salima ma bata tare dashi ,don haka bai tsaya bi ta kansa ba ya kwasa da gudu ya bar gidan ya banzama gidan sister ta ,inda take sauka in tazo Nigeria.

Dafe ƙirjinsa Adnan yayi da sauri saboda yanda wani abu mai ƙarfi yazo ya sokar masa ƙirji kamar icce

“Shikenann zan rasa ta,Plz karki gujeni bazan iya jurewa ba Salima ,gwara inta ganinki a daga nesa matsayin matar Sheikh ,it will ease my pain ,akan ki haramta mun ganinki for life….oh goshh”

Ya zube a varendar dinsa cikin mawuyacin hali .

 

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button