Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 39

Sponsored Links

039
___________________
Anty tana shiga ta zarce sama inda bedroom din Salima yake ,Ya Sheikh na ganin hakan ya ci burki a falo ya zauna a kan kujera ,zamansa keda wuya Saiga Adnan ya shigo ,wani mugun harara ya sakin masa ,cikin hargagi yace
“To meye meye kuma,Saliman ai tana ciki sai ka ɗan farin ta ko?”

Turus Adnan yayi cikin borin kunya “Allah yabaka hakuri daga jaje”

“Ba wani jaje iyayen sa ido ,munafukan banza munafukan wofi in Allah ya yarda bazamu sake samun matsala da Matana ba sai dai baƙin ciki ya kashe ku ,gobe goben nan ma zan siya mata mota zaka gani…”

Dukda maganar ya soki Adnan Amma haka nan yayi dariyar yaƙe “Mun gode Allah ,ya Sheikh bazaka san mu masoyanka bane sai kun zauna lafiya da matarka ,Abunda ka faɗa Allah ya cika maka burinka ,waikkkk wayaga Salima da mota kai mashaAllah”
Daidai nan Ambassador ya shigo “Mene ..mene? A sako farko kunsanni da son jin tsegumi”

“Wlh Sheikh ne yayi ma Salima kyautar mota ,gobe ma za’a kawo ta”

Dafe ƙofa yayi da sauri saboda yanda maganar ya firgitashi

“Mota? Wai da gaske miqdad?”

Miqdad da tuni ya fara nadama ,banza yayi masa ,wannan shi ake cema baki shi ke yanka wuya daga barazana anyi implementing

“Abokina Ashe Allah zai gwada mun wannan ranar da za ka zama changed person?”

Sunkuyar da kai miqdad yayi zuciyarsa na zafi ,yanajin ɗumin ruwan hawaye a idonsa ,mota fa jabu itace ta fara daga miliyon ɗaya ,anya bazaice ƙarya yake ba?
Ina ko dun yaron nan da yake neman ganin iyaka na sai na daure.

Zuwa sukayi suka zauna a gefe da gefensa suka dafa masa kafaɗa a tare
“Lafiya dai? Ko wani ya mutu ne?”

A harzuƙe ya ɗago yana kallonsu
“Wannan wani irin tambayar raunin wayo ne? ”

“Oh🤭 Allah bada haƙuri”
“Kayane haƙurin naɗa gammo ka ɗauka ambassador”

Ambassador da ya gane yana cikin pain ƙunshe dariyarsa yayi zai sake jansa ,wayarsa ta fara ringing . Ganin side chick ɗin sa ce da sukayi zasu haɗu a hotel, yasa yayi saurin miƙewa

“Ina zuwa”

Yana fita ya Sheikh ya juya da Kallonsa kan Adnan ,ya wani rashe masa akan kujera yana kallon TV hankalinsa kwance

“Shifa daga dukkan Alamu wannan ɗabi’un yahudu da nasara gidan duk da ya fito suke dashi….”

“Alaji
Alaji!!”

Yanda yayi masa kiran en tasha yasa Adnan da ya fara fahimtar Hausa ya sharesa

Littafi yasa a gefen hannun kujeran da Adnan yake zaune ya fara bubbugawa

“Malam magana nike ,ka wani hamshaqe akan kujera kamar wani naka ɗin nan”

Juyowa yayi yana wani basarwa “Yayane”

Sosai yaso ya tunzura ya Sheikh amma da ya Sheikh yayi tunanin Adnan a yanzu shine barazana a rayuwar auren Sa ,sai ya kwantar da murya ya ɗan gyara zama yana fuskantar Dr.

“Ahmm Adnan!”
Lumshe Ido Adnan yayi ya watsa su akan ya Sheikh

“Adnan sunanka ko?☺️”

“Eh, Dr Adnan”

“Yawwa Dr ,” ya wani muskuta yana gyara zama gamida ƙasa da murya

“Me yasa bakazo da matarka nan ba,ta Barka kaita yawon maƙota ,ana maka kallon banza”

Abun yaso ya bawa Adnan dariya shikam wa ya taɓa masa kallon banza inba Sheikh ba,infact gidan wa ya taɓa shiga banda gidan Sheikh

“Ayyah banda mata ai,
I’m single and searching ,muna jiran ta gari da yardar Allah”

“kai😳Gabjejen wulli dakai ba mata? A ƙasar Hausa ai ka kusa shiga stage din tuzurai…..Dole mu nemo maka mata shaf shaf shaf shafff” yana magana yina miƙi² da ido kamar uba da ɗan nan zai masa dole.

“Kai🥹 akan me? Ai ban matsu ba”

“Ni na matsun maka kai aure…yaro baka sani bane aure Akwai daɗi musamman lokacin daminan nan ….kuma ban mantawa da abunda malaman sunnah suke cewa kai harma da masu iya magana…”

Ƙureshi da ido yayi bako ƙiftawa
“Gwauro sheɗani ne…ba’a baiwa gwauro ajiyar mace”

Abun ya sosa zuciyar Adnan Amma ya shanye ,Ko a fuska bai bari an gane ba
“Nasan da hakan amma Ni ban ƙosa ba”

“Aah gaskiya duk gwauro a matse yake da sha’awa ,shikuma mai jin sha’awa baida zaɓi,duk inda ta faɗi shane…kayi lissafi da hankali Adnan🧏‍♂️”

“To naji”

“Yawwa 😃Don haka zamu samo maka budurwa kwana kwanan nan”

“Ha’ah ina ruwanka dani? Auren dole zakayi mun ko kai ubana ne…ko kana bani cine”

“Uhm uhm haƙƙin maƙotaka ne, amma fa budurwan nan sai an samo ta🤓”

Bai sake magana ba ya miƙe a sanyaye zai fita ,da sauri ya Sheikh ya janyo shi ya riƙe masa kafaɗa ya maidashi kan kujera ya zaunar

“Ba inda zaka ,ai ka jira kugaisa da bestyn taka ko? Ko ɗan lemu ma kasha… Hmmm besty” ya kare magana yana karkaɗa ƙafa yana taune leɓe.

Kallon tsoro Adnan ya fara yinma ya Sheikh “Anya Sheikh ba mugu bane ba? Karfa ina zaune ya haɗa mun wani tuggun ya kashe Ni murus har lahira” zabura yayi zai fita

“Zauna mana😡🤨” ya wani ɗaga masa murya yana haɗe rai kamar boss.

Muryar Adnan rawa ya kamayi ,idonsa cike da ƙwalla ya soma bashi haƙuri da kalar hausan shi “Nine don Allah kayi hakuri gida zani😢”

“Alƙuran sai ka tsaya kun gaisa da ita ,to da wajen wa kazo da zaka tafi baku gaisa ba,Ni tsaranka ne? Ko Ni abokinka ne.? Ina wasa da kai ne eyeeeh?” Duk amsoshinsa Adnan da girgiza kai yake amsawa

“To koma ka zauna…Salima…Salima a kawo plate 3 na abinci Ni,Adnan Da Ambassador”

“Allah srki Ashe hanyar mutuwa ta ta food poisoning ne dama?

Dama ance hausawa suna da juju kodai sheikh Yana da Rauhaniya ce da zata rikiɗa ta fito a suffar Salima ta bashi abinci da shayin ɓera yaci ya mutu…?”

 

Oum Aphnan
#Bad boys

*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

Leave a Reply

Back to top button