Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 28

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

28

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group ɗin*

 

“Idan har kana son rayuwar ɗanka to.

Kabi sharaɗin mu kabi tsarinmu, sannan kabi dukkan dokokin, muddin kana so Jameel ya rayu idan kuma ka kuskura kayi mana taurin kai kayi mana gardama kan sharuɗan da muka ginda ya maka to zakaga abinda zai biyo bayan gardama”.

Cikin tsanananin kaÉ—uwa Abba ke girgiza kai yayin da bakinsa ke rawa ya gaza furta komai.

Cikin wannan bauÉ—aÉ—É—iyar murya mutumin ya cigaba da cewa.

“Dama kai tsaye mu aikin kashe sa aka bamu. Toj amma saboda nagartansa da mutuncinsa yasa mukaji bama buĆ™atar kashe Malam Jameelu munfi É“uĆ™atar abada kuÉ—i musakeshi domin shi Jameelu na kowane, kauda irinsu a doron kasa asarace data shafi, dukkan al’umma, dan haka kabi sharuÉ—anmu mu sakeshi salamun-salaman ya dawo hannunku hankali kwance, idan kuma ka kuskura kayi mana gardama duk da na gartan Jameel zamuyi abinda muma ranmu bai soba!”.

Cikin tsanananin tsoro da tashin hankali Abba ya dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya kana yace.

“Innalillahi.

Dan Allah  ku faɗa min koma me kukeso zan baku bazan muku gardama ba da Izinin Ubangiji”.

Cikin wata kakkausar murya mutumin yace.

“Bayan kai wanda mu kejin sa agefenka kada ya mana gardama domin shine Amininsa Moddibo”.

 

Girgiza kai Abba yayi still jikinsa na rawa kana muryarsa cike da rauni yace.

“Ba zaiyi gardama ba”.

Gyaran murya Mutumin yayi kana yace.

“Kasa amsa kuwwa shima Moddibo yaji abinda ake magana akai”.

Kai Abba ya gyaÉ—a still muryarsa na rawa yace.

“Nasa, nasa, nasa”.

Cikin bada umarni mutumin yace.

“Ku nutsu ku zauna ku jini”.

Kai Abba ya gyaÉ—a kana yace.

“Toh”.

Gyara murya mutumin yayi cike da isa yace.

“Baku zauna ba nasan atsaye kuke”.

Atare Abba, Moddibo da Hajiya Karima suka zauna Araunane Abba yace.

“Toh mun zauna wallahi”.

Kai Mutumin ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Yayi kyau sharaɗin mu na farko da zamu ƙidanya muku idan ka bishi Jameel ya rayu idan kuwa baka bishi ba Jameel ya mutu wannan shine sharaɗi na farko kuma shine mafi tsauri”.

Ajiyar zuciya kawai Moddibo ke sauƙewa zuciyarsa na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.

Mutumin ya cigaba da cewa.

“Sannan yanzu rayuwar Jameel yana hannunka da kai da Amininsa da kuma mahaifiyarsa da ma sauran Makusantan ku, idan kuka mana gardama kamar kuna wasa da rayuwar Jameel ne”.

 

Atare Moddibo da Abba suka haÉ—a baki wajen cewa.

“Meye kuke buƙata menene sharaɗin naku?”.

Kai Mutumin ya gyaÉ—a kana yace.

“Sharaɗin namu shine wannan maganar kada ku yarda kada ku kuskura koda agigin bacci koda amafarki kusa hukuma acikinta!”.

Moddibo kuwa ƙirjinsa ne ya buga cikin sauri ya dafe kansa da hannunsa biyu tare da kifa fuskarsa ajikin kushin kana ya furta.

“Innalillahi wa’inna Ilahi rajiu’n”.

Cikin ƙasa da murya Abba ya runtse Idanunsa tare da cewa.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin”.

Cikin tsawa mutumin yace.

“Zaku faɗa kenan!?”.

Da sauri Moddibo ya girgiza masa kai dake kife akan kushin kamar yana gabansa kana yace.

“Ba zamu faɗa ba wa kowa ba, mudai fatan mu J ya kasance cikin ƙoshin lafiya, kada ku cutar dashi”.

Taɓe baki Mutumin yayi kana yace.

“Kada ku yarda kada ku kuskura ku sanya hukuma aciki”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.

“Ba zamu faɗa ba da izinin Ubangiji zamu bi sharaɗin ku.

Amma sai dai kafin ma ku kiramu mun kaiwa hukuma maganar amatsayin Jameel ya ɓata tunda mun kwana babu shi sannan mun wuni babu shi toh munje wajen hukuma amma bawai munje amatsayin mun kai ƙorafi akan ku bane”.

 

Jinjina kai Mutumin yayi tare da taɓe baki kana yace.

“Toh wannan sharaɗine Idan hukuma sun dawo dan suna nan kamar Mayu, daga sunji babu mutum idan sun sake kawo kansu kada kuce mun nemi kuɗi awajenku”.

Yarfe hannu Hajiya Karima tayi tare da girgiza kai ta ƙurawa Abba Ido tamkar shike maganar.

Cikin bauÉ—aÉ—É—iyar murya Mutumin ya cigaba da cewa.

“Muddin kana son ran Jameel to.

Kayi shiru da bakin ka idan mun kafa maka sharaɗi na biyu ko kuma mun faɗi abinda mukeso kun bayar to Jameel zai dawo amatsayin ɓata yayi sannan ba sace sa akayi ya dawo ba”.

Abba kuwa buÉ—e idanunsa dake lumshe yayi kana yace.

“Insha Allah zamu bi sharaɗin ku amma yanzu mai kuke so ku faɗa min”.

Cikin sauri ya janyo wayar tare da kallon screen É—in jin É—it-É—it-É—it alamar an kashe.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da rintse idanunsa da karfi kana yace.

“Innalilahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin”.

Moddibo kuwa da still hannunsa ke dafe akansa yana taune lip É—in sa na Ć™asa babu abinda ke fita abakinsa face kalmar Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n.

Hajiya Karima kuwa Girgiza kai kawai take tare da yarfe hannu kana tana mai maimaita kalmar Hasbunallahu wani’imal wakin ta juya tare da kallon Abba da idanunsa suka kaÉ—a suka yi jawur sannan tace.

“Innalillahi wa’inna Ilahi rajiu’n wannan wani irin zamani Allah ya kawo mu kenan Ć´an Kidnapping ne suka É—auke Jameelu”.

 

Lokaci ɗaya Moddibo ya sake dafe kansa da karfin yana cigaba da taune lip ɗin sa na ƙasa.

Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana ta cigaba da cewa.

“Amma Alhj wannan sharaɗin nasu zancene na banza ina muke da yaƙinin zasu iya kare Jameelu ba zasu cutar da shiba ba gwara mu faɗawa hukuma ta shiga cikin maganar nan ba”.

Cikin sauri Moddibo ya ɗago kansa daga jikin kushin wanda sai alokacin ya samu damar hakan hannunsa biyu ya haɗe waje ɗaya alamun roƙo kana ya runtse Idanunsa da ƙarfi ya shiga.

Girgiza kansa muryarsa na rawa yace.

“A’a,a’a,a’a Aunty Karima kiyi wa Allah da Manzonsa kada ki sako hukuma acikin maganar nan Wallahi kina sa hukuma zasu iya yiwa J komai kiyiwa Allah kada kisa hukuma aciki kiji abinda suka faÉ—a mana”.

 

Abba kuwa jujjuya kai ya shiga yi kana idanunsa akan Hajiya Karima yace.

“Karima ban yarda ba ban yafe ba wannan maganar ya fita muddin kinaso Jameelu na ya dawo kada ki faɗawa hukuma wannan maganar”.

Kai ta gyaÉ—a cike da damuwa.

Kallon wayarsa Abba yayi tare da cewa.

“Yanzu bari na sake kiransu naji me suke buƙata”.

Ya faɗa tare da dearling number amma swich off”.

 

ĆŠagowa Abba yayi tare da kallon Moddibo kana yace.

“Aliyu Wayar akashe”.

Cikin sauri Hajiya Karima tace.

“Ai dama zaiyi wuya yashiga ya za ayi ya shiga ai ba zai taɓa shiga ba”.

Daga Abba har Moddibo babu wanda yace komai  Allah ne kaɗai yasan abinda suke ji aransu.

 

Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo bakinta É—auke da Sallama kusa da Hajiya Karima ta zauna Idanunta sun kaÉ—a sunyi jawur har sun kumbura alamar tayi kuka ta gaji Idanunta akan Abba tace.

“Alhj har yanzu babu labarin Jameelu”.

Kafin Abba yace wani abu Hajiya Karima tayi saurin cewa.

“Yan zun nan ƴan Kidnapping sun Kira su suka ɗauke sa!”.

Cikin sauri Hajiya Turai ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

“Hasbunallahu wa niimal wakil Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n,Ćłan Kidnapping kuma Alhj!?”.

Girgiza kai Abba yayi sai kuma ya riƙe tafin hannunta kana yace.

“Ki zauna”.

Ba musu ta tazauna jikinta na rawa saboda tashin hankali da take ciki.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima tare da cewa.

“Wannan maganar daga mu sai mu iya mu nan kada ku kuskura maganar nan ta fita iya mu nan ban amince ba kuma ban yafe ba daga ke har Karima ban amince ku kai maganar nan kunnen hukuma ba, duk wacce takai abakin igiyoyin auren ta duka saboda sun sa sharaɗin idan na yarda hukuma  ta  shiga  zasu kashe min Jameelu”.

Ya ida maganar cikin raunin murya.

 

Kai Hajiya Turai ta girgiza cikin Muryan kuka tace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n in sha Allah ba zamu faÉ—a ba Alhj yama za ayi mu faÉ—a ai wannan ba abin faÉ—a bane!”.

Hajiya Karima ma cikin sauri ta girgiza kai kana tace.

“Insha Allah ba zamu faɗa ba, zamu kiyaye”.

Moddibo kuwa har zuwa yanzu yana dafe da kansa da hannu biyu still Idanunsa aruntse.

Ahankali Abba ya kira sunan sa tare da cewa.

“Aliyu”.

Araunane Moddibo ya ɗago idanunsa da sukayi Jawur kana sun kumbura ga lip ɗin sa na ƙasa sunyi ja kana ya ɗan kumbura.

Cikin rauni ya kalli Abba tare da cewa.

“Na’am Abba”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Aliyu ya zamuyi?”.

Zazzafafar ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da cewa.

“Abba sai dai mu jira kiran su na biyu muji mai suke buƙata magana ce dai na kuɗi atanadi abinda suke bukata a ajiye tun wuri”.

Kai Abba ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh Aliyu amma yanzu ya zamuyi da mahaifiyarsa inaga kada ka faɗa mata halin da ake ciki”.

Moddibo kuwa kallon Abba yayi kana ya girgiza kansa tare da cewa.

“Abba kar afaɗa mata kuma? Ai gwara tasan cewa J yana raye, domin zuciyar Ummi zata iya bugawa da idan ba afaɗa mata ba gwara in Faɗa mata tasan cewa J yana raye tasan cewa munyi magana da shi naji muryansa,   kaima kaji muryan J fa yanda muka yi magana dashi ƙilan sun dake shi!”.

Ya faÉ—a cikin raunin murya.

 

Runtse Idanu Abba yayi da ƙarfi hawaye masu zafin gaske suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar.

Moddibo kuwa still Idanunsa na runtse ya gagara buÉ—ewa har zuwa yanzu yana jin muryan M Jameel na cewa A.J bansan inda nake ba ban san ina nake ba.

Cikin rauni ya É—ago kansa muryarsa na rawa yace.

“Abba kaji fa J cewa yake baisan inda yake ba Abba ina suka kaisa ina suka cusa sa”.

Dafa kansa Abba yayi kana yace.

“Aliyu duk yanda za ayi idan ka faɗawa Fatima kada ta faɗawa kowa, sannan ka kiyaye yanda zaka faɗa mata kada hankalinta ya tashi!”.

Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

“Abba ba zata faɗawa kowa ba idan na faɗa mata halin da ake ciki”.

Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.

“Toh shikenan Aliyu ka kula”.

Kai Moddibo ya gyaÉ—a dai-dai lokacin kiran Ummi ya shigo wayar Moddibo kallon Abba yayi kana yace.

“Abba ka gani ko kirana ma take yi yanzu kafin na wuce gida ma saina biya wajenta”.

Cike da rauni Abba yace.

“Toh shikenan tashi kaje Aliyu gashi kaima har ƙarfe goma na dare yayi tsoro nakeji, jiya a irin ya wannan lokacin suka ɗauki Jameelu”.

Runtse Idanu Moddibo yayi tare da miƙewa kana ya yiwa su Hajiya Turai sallama ya fita har kofar gida Abba ya rakasa sai da yaga tashin motarsa kafin ya koma cikin gida zuciyarsa na zafi.

 

Cikin sanyin jiki yayi parking kana ya fita Ć™aramin Ć™ofar ya tura ya shiga A baranda ya hango Ummi, Asma’u da Bashir Idanun Ummi da Asma’u sun kaÉ—a sunyi Jawur dasu kana sun kumbura.

Bashir kuwa cikin dauriya kasancewar sa namiji yasa ya riĆ™e hannun Asma’u dake kuka tare da cewa.

“Ummi ki kwantar da hankalin ki da izinin Ubangiji ba abinda zai samu Yah Jameel Allah zai tsaresa aduk inda yake Asmey ki daina kuka dan Allah”.

Girgiza kai Asma’u tayi cikin Muryan kuka tace.

“Bashir taya zamu iya tsaida hawayen mu bayan bamu san halin da Yah Jameel ke ciki ba!?”.

Cikin rauni Ummi ta ɗago kanta Idanunta ya sauƙa akan Moddibo dake shigowa Iska na kaɗa sa duk yayi sauya  cikin sauri Ummi ta miƙe jikinta na rawa ta nufesa tare da cewa.

“Babana”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya zuba mata Ido cike da tausayawa ganin kamar bata cikin nutsuwarta ƙarasawa kusa da ita yayi tare riƙe hannunta kana suka zauna agefen barandar cikin sanyin yace.

“Ummi”.

Kallonsa tayi tare da cewa.

“Na’am Babana ya labarin Jameelu na”.

Sunkuyar da kansa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa wanda zuwa lokacin sunyi masifar ja kana sun kumbura yayin da Idanunsa ke tsats-tsafo da ruwan hawaye sai dai sun gagara zubo wa.

Ahankali ya ɗago kansa tare da damƙe hannun Ummi na dama acikin nasa kana yace.

“Ummi munyi waya da J”.

Cikin sauri Ummi ta zaro Idanunta duka waje kana tace.

“Kayi waya da Jameelu”.

Kai ya gyaÉ—a mata hawaye masu zafi suka zubo akuncinsa.

Kallonsa Ummi tayi tare da faÉ—in.

“Kayi waya da Jameelu Babana kuma kana kuka!?”.

Moddibo kuwa kallonta yayi cikin ƙoƙarin tsaida hawayen sa yace.

“Ummi anyi Garkuwa Da shine”.

 

Cikin matsanancin tashin hankali Asma’u ta É—aura hannunta akai tare da cewa.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Ta dire addu’ar tare da komawa ta zaun.

Ita kuwa Ummu wani irin zazzafan numfashi ta fesar tare runtse idanu kana ta buÉ—e su akan Moddibo cikin dan sassaucin tashin hankali da take ciki tace.

“Toh ai ba komai Babana kawai Abbansa yayi ƙoƙarin haɗa kuɗi da suke buƙata a basu, su sako mana shi.

Alhamdulillah tunda yana raye, domin ai wannan abune da ya zama ruwan dare, tunda su dai in an basu abinda suke so basa kisa.”

Sai kuma ta lumshe idanunta wasu sirran hawaye suka gangaro mata cikin raunatacciyar murya tace.

“Waya sace min Jameelu na!? Waya sacemin farin ciki na!?

Waya É—auke min jin daÉ—ina!?

Waya É—auke min Garkuwana da gatana!?

Wayake son yimin shamaƙi da bangona majinginata!?”.

Moddibo kuwa hannunta ya riƙe acikin nasa kana yace.

“Ummi dan Allah ki daina kuka addu’a zakiyi masa kamar yadda kikace abinda suke so kawai za’ayi musu, sun kuma gargaÉ—emu kada asa hukuma a cikin mgnar, sai muyi Ć™oĆ™arin kiyayewa”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a tare da share hawayen ta amma still wasu na zubowa.

 

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da zayyane mata duk yanda sukayi.

Atare Asma’u, Ummi,da Bashir suka sauĆ™e nannauyan numfashi.

Kallon Moddibo Ummi tayi kana tace.

“Babana basu faɗi nawa suke so bane?”.

Kai ya girgiza tare da cewa.

“Ummi basu faɗa ba tukunna sharaɗin su na farko suka bamu kada ayarda a faɗawa hukuma”.

Ajiyar zuciya mai haɗe da jan zuciya Ummi ta sauƙe still tana hawaye tace.

“Ba zan faɗa ba Insha Allah bazan faɗa ba Babana.

Ba zan faɗa ba”.

Kai Moddibo ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Ummi ki cigaba da addu’a Insha Allah babu abinda ya gagari Ubangiji kuma Insha Allah tunda suka fara kira zasu sake kira su faÉ—i abinda suke so sai ayi Ć™oĆ™ari amusu abinda suke so”.

Jinjina kai tayi kana tace.

“Insha Allah gobe zanje gidan su muyi magana da Abbansa idan Malam ya bari”.

Dai-dai lokacin Malam Ahmad ya shigo cike da tausayawa yake Kallonsu kana yace.

“Nama bari Fatima na bari Allah ya tsaresa ya kuma bayyana sa aduk inda yake”.

Atare suka amsa da Ameen.

Miƙewa Moddibo yayi kana yace.

“Ummi zan tafi gida”.

Kai ta gyaÉ—a kana tace.

“Toh Babana Allah ya kiyaye”.

Ameen ya amsa sannan ya juya ya fice cikin mutuwar jiki.

 

Yana isa gida yayi Parking tare da fitowa ya rufe Ć™ofar kana ya shiga falon baki É—aya abubuwan sun ca kuÉ—e masa ga rashin bacci rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya ga tashin hankali da damuwa baki É—aya zulumi sun mishi rubdugu ya fita hayyacinsa sai alokacin ya tuna baki É—aya wayewar garin yau baiyi wanka ba cikin kasala ya nufi toilet din sai dai baya tunanin zai iya yin wanka, al’wala ya É—aura kana ya fito tare da shimfiÉ—a darduma ya fuskanci alĆ™ibla cike da nutsuwa ya shiga gabatar da nafillah aduk lokacin da ya kai goshinsa kasa (Sujjada)Sai ambaci J dinsa, raka’a huÉ—u yayi bayan ya idar ya É—auki Alkur’ani mai girma kana ya fara karantawa Acikin Suratul An-Nisa’i har Misalin Ć™arfe 2:00am yana karatun idan ya karanta wani aya sai M Jameel ya faÉ—o Masa arai kana ya tuna da wasu lokutan idan yana karatu yazo wajen Ayar azaba saiya rufe Kur’anin ya Rungume kana yaita kuka idan kuma yazo wajen Ayar Rahma sai yaita sakin murmushi kana yana cigaba da karatun.

Ahankali Moddibo ya runtse Idanunsa tare da Rungume Kur’anin aĆ™irjinsa idanunsa sun kaÉ—a sunyi jawur dasu kana sun kumbura saboda tashin hankali da yake ciki har aka kira Assalatu Moddibo bai rintsa ba.

 

Haka zalika É“angaren Abba ma ya kwana ba tare daya rintsa ba acikin kwana É—aya da yini duk ya canza yayi zuru-zuru dashi.

 

Washe gari da safe:Misalin ƙarfe 8:00am Abba ne zaune afalonsa ya ƙurawa wayoyinsa Idanu koda motsin kirki ya gagara baki daya hankalin sa nakan wayarsa.

Cike da ladabi mai gadi yayi Sallama É—agowa Abba yayi ya kallesa kana ya amsa masa Sallamar.

Cike da tausayawa mai gadin yace.

“Alhj ga baƙi awaje”.

Numfashi Abba ya fesar kana yace.

“Su waye ne?”.

Tsayuwa mai gadin ya gyara kana yace.

“Hukumar ƴan sanda ne wai daga Taraba suka zo”.

Kai Abba ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh ka shigo dasu”.

Kai mai gadin ya gyaÉ—a kana ya fice yace su shiga.

Dai-dai lokacin Moddibo yazo Parking motarsa Yayi kusan atare suka shiga Ć´an sandan mutum biyar na gaba shi Kuma yana bayansu.

Bakinsu É—auke da Sallama suka shiga wajen zama Abba ya nuna musu bayan ya amsa Sallamar su.

Moddibo kuwa gefensa ya nufa ya zauna cikin mutuwar jiki da damuwa.

 

Gyaran murya ɗaya daga cikin ƴan sanda yayi kana Idanunsa akan  Abba yace.

“Sunana Asp Mahmud Adam Shani daga rundunar ƴan sandan jahan Taraba masu bincike akan abinda ya shafi ɓatan mutane da kuma kisan kai kana da fashi da makami ina fatan zaku bamu haɗin kai.

Mun samu kirane daga nan Ć™aramin Headquarter din mu”,’.

Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da kallon Moddibo da yayi ƙasa da kansa kana yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.

Kana ya cigaba da cewa.

“Mun samu masaniya Kan cewa Jameel É—an Alhj Bashiru Maidala ya É“ata shiyasa nazo da kaina inji ba’asin maganar sannan muga ta inda ya kamata mu fara da taimakon Allah da kuma baya nan da zaku bamu zamuyi nasara wajen gano inda yake”.

Jinjina kai Abba yayi tare da rintse idanunsa kana ya fesar da numfashi tare da sunkuyar da kansa ƙasa hawaye masu zafi suka zubo masa.

Cike da tausayawa Asp Mahmud Adam Shani yace.

“Alhj ka kwantar da hankalin ka kayi min duk kan bayanin da zan gane saboda yanda zamu kula da aikin da kuma abinda ya kamata ayi akai”.

Jinjina kai Abba yayi tare da ƙoƙarin hana hawayensa zuba kana ya daure yace.

“Jameelu nine mutum na ƙarshe da yayi sallama dani ya fita ina tsaye ajikin window har ya fita bayan fitarsa na kai kimanin awa ɗaya da rabi ina tsaye ajikin window, Bayan nan kuma duk cikin mu babu wanda yayi magana da Jameelu domin ya fita akan zaije wajen Abokinsa amma bai isa ba”.

A hankali ya fesar da zazzafan iska tare da taune lip ɗin sa na ƙasa tare da kallon Asp Mahmud Adam Shani kana yace.

“Adaren Abokinsa yazo domin rashin samun layinsa da bai yiba”.

Jinjina kai Asp Yayi kana yace.

“Eh anyi min wannan bayanin daga Headquarter din mu na Nan Inspector Ayuba Garba kumo ya sanar dani komai to amma daga ɓatansa zuwa yanzu babu wanda ya kira ka!?”.

Cikin sauri Abba ya Girgiza masa kai kana yace.

“A’a babu”.

Ido Asp ya zuba masa kana yace.

“A’a Alhj Bashir dan Allah kada kuce zaku bi sharuddan ire-iren mutane masu garkuwa da mutane, idan har akwai wanda ya kira ka ya maka barazana ko kuma ya nemi wani abu ka faÉ—a mana ko kuma ka bami number da suka kira Insha Allahu Jameelu zai kuÉ“uta sannan zai rayu da izinin Ubangiji zamu tsera tar dashi”.

Moddibo kuwa cikin sauri ya kalli Asp zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi ya Girgiza kai tare da cewa.

“Babu wanda ya kira ai da akwai wanda ya kira zamu sanar daku sannan mu ma da hankalin mu zaifi kwanciya ma, mun san cewa yana raye”.

Ido Asp ya tsira musu kana yace.

“Anya kuwa anya babu wanda ya kira ku!?”.

Cikin sauri Moddibo ya gyaɗa kai kana cikin ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa yace.

“Babu wanda ya kira  tashin hankalin mu kenan”.

Abba ya karɓi maganar da cewa.

“Da har ankira Asp Mahmud da ace ankira kamar yanda kake zaton ƴan Kidnapping ne kuma sun buƙaci kuɗin ai da tuntuni nayi muku bayani sannan idan yakama da in basu kuɗi zasu dawo min da Jameelu na da tuni na bayar an dawo min da Jameelu na!”.

 

Anutse Asp ya gyara zamansa kana cikin sauri yace.

“Alhj na roƙe ka dan Allah koda ankira ance kuɗi ake buƙata kada ka basu, kawai ka bamu Number sannan kayi mana bayani shine abinda muke bukata amma ana temakamu sune sannan ana ƙara basu ƙarfin gwiwa dayi musu abinda suke so shiyasa suke ƙara yin abinda suke su ɗin”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.

“Insha Allahu zanyi ƙoƙari duk abinda ake ciki zan sanar muku Nagode sosai musamman tattakin da kayi daga Taraba zuwa nan”.

Dai-dai lokacin Hajiya Karima tazo Idanunta akan Asp Mahmud Adam Shani da sauran Folisawan Kallonta ta mayar kan Abba kana tace.

“A baƙi mukayi ne sannun ku da zuwa”.

Asp dake rubutu awata ƙaramar takarda yace.

“Yawwa”.

Kana ya cigaba da rubuce-rubucen sa.

 

Kallon Abba Hajiya Karima tayi tare da kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe haƙoransa uku na sama na kan laɓɓansa na ƙasa numfashi ta fesar kana ta ƙara sa kusa da Abba da har zuwa lokacin bayansa ke jingine ajikin kujera tace.

“Alh ga Hajiya Fatima mahaifiyar Jameel ta iso”.

Ahankali Abba ya É—ago kansa kana cikin sanyin murya yace.

“Kice ta iso”.

Kai ta gyaɗa tare da juyawa ta fita ba jimawa ta shigo Ummi na biye da ita Ahankali Ummi ta ƙara sa kusa da Moddibo ta zauna Hajiya Karima ta juya ta fice cike da tausayawa Moddibo da Abba ke kallonta ganin yanda Idanunta suka kumbura sukayi jawur sun ƙanƙance.

 

Anutse Asp ya É—ago kansa tare da kallon Ummi kana yace.

“Wannan ce mahaifiyarsa?”.

Kai Abba ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Eh  itace”.

Atausashe Asp ya gyara zamansa tare da cewa.

“Sannu Mmn Jameel Ubangiji Allah ya bayyana sa ya kuma tsaresa aduk inda yake, ki kwantar da hankalinki in sha Allah zamuyi iyakar iyawarmu zamu samoshi a duk inda yake”.

Kai ta gyaÉ—a cikin muryanta daya dishe da kuka tace.

“Ameen ya Allah”.

Miƙewa Asp Yayi kana yace.

“Alhj to bari mu tafi amma dan Allah duk abinda ake ciki a faɗa mana”.

Kai Abba ya jinjina tare da cewa.

“Toh Insha Allah”.

Bayan tafiyarsu Ummi ta juya tare da kallon Abba cikin raunin murya tace.

“Alhj har yanzu basu sake kira ba!?”.

Kai Abba ya gyaÉ—a kana yace.

“Fatima har yanzu basu kira ba”.

A raunace ta sanya gefen hijabinta tare da share hawayen da suka zubo mata kana tace.

“To idan sun sake kira duk abinda suke so dan girman Allah kataima keni kaceci rayuwar Jameel kayi musu”.

 

Girgiza kai Abba yayi idanunsa na tara ƙwalla yace.

“Fatima ba sai kin roƙeni kin haɗa Ni da Allah ba, idan har banyi musu abinda suke so andawo min da Jameel ba menene amfanin dukiyata?”.

Sai kuma ya runtse Idanunsa kana ya cigaba da cewa.

“Jameel yafi min komai aduniyar nan zan iya sadaukar da duk dukiyata domin ceton rayuwar Jameel insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ya dawo”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Toh shikenan Nagode Ubangiji Allah ya kuɓutar dashi Allah yasa su faɗi abu mai sauƙi kada su faɗi abinda yafi ƙarfin mu Allah ya tsaresa Allah yasa yana cikin ƙoshin lafiya”.

Atare Moddibo da Abba ke Amsawa da Ameen cike da tausayawa.

Kallon Abba tayi kana tace.

“Bari na tafi gida”.

Kai Abba ya gyaÉ—a kana yace.

“Toh shikenan”.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Ummi muje in kaiki gida”.

Kai ta gyaɗa kana ta miƙe.

Suka fita da kallo Abba ya bisu cike da tausayawa.

 

Moddibo kuwa yana ajiye Ummi agida kai tsaye makarantar Malam ArÉ—o ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita ya nufi harabar makarantar iska na kaÉ—a shi kai tsaye Office din malam ArÉ—o ya MurÉ—a handle din ya shiga bakinsa É—auke da Sallama.

 

Anutse Malam Arɗo dake duba wani littafi ya ɗago kansa tare da sauƙe Idanunsa akan Moddibo ganinsa cikin wani irin yanayi yasa yayi saurin miƙewa tare da riƙe hannun sa kana yace.

“Moddibo ya dai?”.

Kai Moddibo ya Girgiza cikin sanyin murya yace.

“Bakomai”.

Kujera Malam ArÉ—o yaja masa ya zauna kana shima ya koma mazauninsa.

 

Cike da kulawa Malam ArÉ—o yace.

“To ina ƴan biyun naka?”.

ƙasa yayi da kansa tare da runtse Idanunsa kasancewar sa ba mai saurin kuka ba ya tabbata da ace yana da saurin kuka da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zaiyi kuka ko hakan zaisa ya samu sassaucin abinda yake ji Aransa ya sake damƙe lip ɗin sa da ƙarfi wanda zuwa lokacin ya sake kumbura kana yayi ja sai sheƙi yake.

 

Ido Malam ArÉ—o ya tsira masa kana yace.

“Ya dai Aliyu mai yake faruwa da Jameelu tun jiya da yamma naji ana raɗe-raɗin wai ba agansa ba nayi ta kiran wayarka baka ɗauka sannan shi kuma idan na kirasa akashe ina Jameelu da gaske ne babu shi!??”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago kansa still yana taune da lip ɗinsa kana cikin raunin murya yace.

“Babu J”.

Kai Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a kana yace.

“Na sani Aliyu ka nutsu ka dawo hayyacinka Aliyu na sani babu Jameelu sannan na gaskata  tunda har naga kai kaÉ—ai kazo nan na tabbata do min idan anganka tamkar anga wata ne dole za’aga zara”.

Ya faɗa tare da miƙewa ya dafa kafaɗar sa.

Runtse Idanu Moddibo yayi

 

“Yanzu ya ake ciki?”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da shafa ƙirjinsa dake bugawa da ƙarfi kana yace.

“Nima kaina ya kulle a duniya bansan me zanyi ba bansan ya zanyi na ganni da J ba?”.

Dafa kafaÉ—ar sa Malam ArÉ—o yayi cike da tausayawa yace.

“Toh yanzu wani mataki aka ɗauka akan lamarin!?”.

 

Cikin raunin murya yace.

“Babban matakin da aka É—auka shine addu’a da faÉ—awa Ubangiji abinda yake faruwa”.

Jinjina kai Malam ArÉ—o yayi tare da faÉ—in.

“An É—auki mataki mai kyau, da girma wanda ya dace  da dukkan Musulmi yanzu mu shiga cikin makaranta mu faÉ—awa yara su tayamu da addu’a Ubangiji Allah ya tsare malam Jameelu ya kuma bayyana sa aduk inda yake”.

Kai Moddibo ya gyaɗa tare da miƙewa kana yace.

“Toh Nagode Allah ya saka da alkhairi”.

 

Hannunsa Malam Arɗo ya riƙe bayan ya mike suka fita kai tsaye bangaren ƴan primary suka fara shiga Ajinsu Ramadan da Raudat yaran na ganinsa suka miƙe cike da farin ciki suna cewa Moddibo Moddibo Kusan a tare Raudat Ramadan da wasu ɗalibai uku suka ce Moddibo ina Malam Jameel munyi kewar ku bakwa zuwa.

Lumshe Idanunsa da yaji suna masa zafi da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zuciyarsa zata buga da masifar ƙarfi tsayuwar sa ya gyara agaban ajin tare da cewa.

“Ina ɗaliban Malam Jameel?”.

Baki É—aya yaran suka É—aga hannu suna tsalle tare da cewa gamu nan Moddibo ina yake munyi kewarsa bakwa zuwa yanzu, dan Allah kace yazo muna san ganinsa.

Kasa furta komai Moddibo yayi hakan yasa ya jingina bayansa da jikin bango yayi Ć™asa da kansa yasan yanda J É—in sa ke son Yara da kuma wasa da su wanda a ra’ayinsa baison koyar da yara amma saboda yanda J É—in sa ke son Yara Yasa yake shiga koyar musu ganin haka yasa Malam ArÉ—o yayi gyaran murya Atake duk yaran suka nutsu tare da tsirawa Malam ArÉ—o ido.

A hankali Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.

“Kuna jina?”.

Kai suka gyaÉ—a masa.

Ya sauƙe numfashi tare da cewa.

“To zaku yiwa Malam Jameel din ku addu’a Allah ya bayyana shi?”.

AruÉ—e yaran suka ce Malam Jameel ya É“ata ne?.”

Kai Modibbo ya gyaÉ—a musu cike da damuwa.

Cikin zare ido Raudat tace.

“Malam Jameel din mu ya ɓata kuma to ina yaje?”.

Ramadan kuwa miƙewa yayi tare da zuwa gaban blackboard ɗin cikin yanayin damuwa sosai ya riƙe hannun Moddibo da har zuwa lokacin Idanunsa ke lumshe yace.

“Moddibo ina Malam Jameel ɗin mu yaje dan Allah ka kira wayansa kace ya dawo Muna so sa”.

Kasa cewa komai Moddibo yayi sabida zulumi.

Gyaran murya Malam ArÉ—o yayi tare da cewa.

“Kuyi masa addu’a Allah ya bayyana shi idan kunyi sallah kuyi addu’a Allah ya bayyana Malam Jameel sannan ku faÉ—awa iyayenku suma suyi masa addu’a Allah ya karesa ya kuma dawo dashi cikin aminci da salama”.

Hawaye Ramadan ya fara zubdawa tare da cewa.

“Toh Malam zamuyi masa addu’a zan faÉ—awa Mommy da Addah Khausina suma zasuyi masa addu’a Allah zai dawo dashi”.

Ahankali Moddibo ya shafa kansa tare da cewa.

“Yawwa Ramadan kuyi masa addu’a ayanzu babu abinda Malam Jameel yake buĆ™ata awajen mu face addu’a”

Cikin rauni sosai yaran suka ce zamu yi masa.

Cikin sanyin jiki Malam ArÉ—o da Moddibo suka fita zuwa bangaren Secondary bayan sun fita anan suka shiga É“angaren na naziri saida suka gama zagaye ko wani aji suna sanarwa Ayiwa Malam Jameel addu’a Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin tashin hankali É—alibai suka shiga masa addu’a.

 

Bayan sun fito Moddibo ya nufi hanyar gate

Cikin kula malam ArÉ—o yace.

“Moddibo baza ka shiga office din ku ba?”.

Kai ya girgiza tare da cewa.

“Um-um bazan shiga ba zan tafi bazan iya zama babu J ba”.

Ya faÉ—a tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Abban M Jameel ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga falon bakinsa É—auke da Sallama A inda ya fita yabar Abba anan ya dawo ya sameshi zaune still wayarsa na gabansa ya zubanusu Ido da alama tun bayan fitarsa ko motsawa baiyi ba.

 

Ahankali Abba ya ɗago kai tare da zuba masa ido cike da tausayinsa baki ɗaya ya rame ya canza idanunsa sun sake girma da ja kana idanunsa sun faɗa, Ahankali Moddibo ya ƙaraso ya zauna agefensa aƙasan Capet Cike da tausayawa Abba yace.

“Aliyu ba kayi wanka ka sauya kaya ba”.

Siririn tsaki Moddibo yaja tare da yin ƙasa da kansa kana yace.

“Abba har yanzu basu sake kira ba!?”.

Kai Abba ya Girgiza tare da cewa.

“Har yanzu basu sake kira ba gani nan ina zaune tamkar gadin waya nake sai tsumayin kiransu nake amma basu kira ba, amma yanzu ka samu kaje kayi wanka ka samu kaci abinci”.

 

“Abba banajin yuwa”.

 

“Ya zamuyi Aliyu idan kaima baka ci abinci ba ai faduwa zakayi. Insha Allah addu’ar mu bazai bar Jameelu ya ta gayyara ba”.

Sai ya kuma maida kallonsa kan Hajiya Karima data shigo wacce ita ma baki É—aya tayi sanyi ahankali yace.

“Ki zubawa Aliyu sbinci”.

Kai ta gyaÉ—a tare da nufar dining ta É—auki Plate ta zuba masa jollof fice da yaji bushesh-shen kifi da namar kaza ta kawo masa.

Moddibo kuwa hannu ya daga mata alamar kada ta ajiye masa ganin ta ajiye yasa ya maida kansa jikin kushin É—in ya jingina tare da lumshe idanunsa yace.

“Ina ma ace tare suka ɗauke Ni da J da yafi min farin ciki ina rayu dashi aduk inda yake duk halin da yake ciki ace muna tare wallahi da yafi min farin ciki akan rabani da Jameel da sukayi”.

Kallonsa Abba yayi cike da tausayawa wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji Moddibo ya kira Complete sunan M Jameel cikin raunin murya yace.

“Toh ya zamuyi Aliyu ka daure kaci abinci”.

 

“Abba ba zan iya cin abinci ba”.

Cikin rarrashi Abba yace.

“Haba Aliyu ka naso kasake sa kamu cikin damuwa ne rashin cin abinka dai dai yake da yiwa kan ka illah, wanda bazan so hakan ba dan Allah ka daure kasa wani abu acikin ka”.

Kai Moddibo ya gyaÉ—a kana yace.

“Toh Abba abani tea”.

Miƙewa Hajiya Karima tayi ta nufi dining kana ta haɗa masa tea cup ɗaya ta kawo masa ahankali ya karba tare da kaiwa bakinsa da ƙyar ya iya shan rabi ya ajiye Cup ɗin.

Abba bai tilasta shiba dan shima akaran kansa yasan ba zai iya saka komai acikin sa ba baya ga tea É—in da yake sha dan raya kai, cikin sanyin murya yace.

“Aliyu kaje ɗakin Jameelu kayi wanka ka sauya kaya”.

Girgiza kai yayi cikin rawan murya yace.

“Abba bari in je gida saboda nabar Innayi ita kaɗai tun safe sannan na barta cikin damuwa”.

Kai Abba ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh Aliyu ka gaisheta”.

 

Yana isa gida yayi Parking tare da wucewa Bedroom É—in sa, kai tsaye toilet ya shiga tare da sakarwa kansa ruwan sanyi sai alokacin ya lura da Dick É—in sa daya kwanta luĆ™ui tamkar bai taÉ“a tashi ba tsanananin fargaba da tashin hankali da yake ciki yasa ya kasa tantance shin shi É—in wani irin halitta ko kuma wanne irin jinsi ne shin shi É—in namiji ne ko mace baisan matsayin da yake ba bare kuma ace sha’awa baki daya Dick É—in sa ya kwanta tamkar babu wani abu mai suna sha’awa daya taÉ“a ji cikin sanyi Jiki ya gama wankan tare da fitowa ya shirya cikin Jallabiya kana ya fesa turare kai tsaye sashen Innayi ya nufa.

 

Misalin ƙarfe 5:00pm da wasu Mintuna bayan antaso Amakaranta motarsu Ramadan na shiga harabar gidan tayi Parking Ramadan ya ɓude tare da ficewa da gudu.

Acan falo kuwa Mommy da Khausar ce zaune suna kallon TV cikin tashar Nat geo well Suna kallon namomin daji Ramadan ya shigo tare da zama gefen Khausar kana ya langwaɓar da kansa tare da cewa.

“Addah Khausi”.

Hankalinta na kan wasu irin halittun ruwa tace.

“Na’am Ramadan”.

Cikin muryan rauni yace.

“Addah Khausi wai Malam Jameel ya ɓata”.

Cikin sauri ta kallesa tare da riƙe hannunsa kana cike da mamaki tace.

“Malam Jameel ya ɓata kuma!?”.

Kai ya gyaÉ—a mata kana yace.

“Eh Addah Khausi Moddibo da Malam Arɗo su suka shiga ajinmu suka faɗa mana Malam Jameel ya ɓata ba asan inda yake ba”.

Cike da mamaki da kuma  al’ajabi Khausar tace.

“Ha’a wace iriyar magana ce wannan Malam Jameel ya É“ata ba’a san inda yake ba!?”.

 

Mommy kuwa cike da mamaki take kallon Ramadan kana tace.

“Ramadan ka tabbatar kuwa?”.

Kafin yace wani abu Raudat ta shigo da kuka fuskarta jage-jage da hawaye kana ta zauna kusa da Mommy tare da cewa.

“Wallahi Mommy wai ya ɓata!”.

Da sauri Mommy ta É—auki wayarta dake hannun kujera kana tace.

“Gashi kiramin Umminsa”.

Amsar wayar Khausar tayi still da mamaki atare da ita tace.

“Eyyy aikuwa Jiya naga miss call É—in Asma’u bana wajen daga baya kuma da nazo ina ta kiranta bata É—aga ba”.

Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta shigo sanye da hijabi har ƙasa kana ta zauna kusa da Khausar dake laluɓo number Ummi ya zama na sun sa Ramadan Atsakiya kasancewar kujeran 2sitter ne.

 

Bayan Mommy ta amsa Sallamar ta tace.

“Hajiya wai kinji abinda yaran nan suke faɗa wai Malam Jameel ya ɓata!”.

Kai Hajiya Bunayya ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Eh dama baki ji bane aini tun jiya da yamma Aminu ke faÉ—a min wai yaji Amasallaci ana cewa ayi addu’a Allah ya bayyana ya kuma tsaresa ashe dama ba kiji ba?”.

Kai Mommy ta.

Girgiza fuska cike da damuwa  tace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Wallahi ban jiba Subhanallah ya Salam Ubangiji Allah ya tsaresa”.

 

Hajiya Bunayya kuwa ahankali ta saci kallon Mommy sai taga idanunta nakan Khausar data maĆ™ala waya akunnenta cike da dabara ta sake murza turaren dake hannunta kana ta fito dashi ta É—aura akan Ramadan tana shafa masa aranta kuwa fari fess tana cewa Alhamdulillah wannan turaren dai na samu na shafa masa saura kuma gobe in faÉ—awa Boka Kar’uzu na shafa masa turaren.

 

Khausar kuwa jin Asma’u tayi Picking call É—in yasa cikin sauri tace.

“Asma’u”.

Cikin wata dashash-shiyar murya mai cike da rauni Asma’u tace.

“Na’am Khausar”.

Cikin alamun damuwa Khausar tace.

“Asma’u wai me nake ji?”.

Cikin muryan kuka Asma’u tace.

“Khausar an sace Yah Jameel yau kwana biyu kenan kusan na uku ba Yaya Jameel ba labarinsa”.

Atsorace Khausar ta dafe hannunta aƙirji kana tace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n ansace Yah Jameel Kuma?”.

Kai Asma’u ta gyaÉ—a hawaye na bin kuncinta tace.

“Eh”,

Cikin sanyin murya tace.

“Ubangiji Allah ya bayyana shi aduk inda yake Allah ya fito mana dashi”.

Ameen Asma’u ta amsa tare da katse kiran.

 

Kallon Mommy Khausar cikin tashin hankali tace.

“Mommy wallahi da gaske an sace sa”.

Girgiza kai Mommy tayi tare da cewa.

“Ya Salam wallahi bamu sani ba barin idan Abbanku ya shigo zan tambaye sa muje muyi wa Umminsa jaje Ubangiji Allah ya bayyana shi Allah ya tsaresa aduk inda yake”.

Khausar kuwa kasa tsaida hawayen ta tayi cikin Muryan kuka tace.

“Ameen Mommy Ameen ya hayyu ya ƙayyum Allah ya bayyana Malam Jameel har kwana biyu kuma!?”.

 

Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tare da marairaice fuska kana tace.

“Hakane kam wannan duniyar ta zama abin tsoro idan kana fama da talauci ka banu idan kayi wadata ɓarayi da ƴan Kidnapping su hanaka kwanciyar hankali da nutsuwa Allah dai ya kyauta”.

Ta faɗa tare da miƙewa ta fice ranta fess.

Baki É—aya Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yita cikin jimami da fargaba musamman Khausar ta gagara tsaida hawayen ta.

 

Moddibo kuwa yana fita daga sashen Innayi mota ya shiga tare da nufar gidan Abba yana isa ana kiran maghariba tare da Abba suka shiga Masallaci suka gabatar da sallah.

Acan É“angaren Mommy kuwa bayan an idar da sallar Isha’i ta sanarwa da LamiÉ—o suna san zuwa yiwa Ummi jaje nan yace ba damuwa ta kira Khausar da Hajiya Bunayya su fito bayan sun fito da kansa yayi Driving É—insu zuwa gidan Ummi.

Bayan sun isa.

Mommy ce agaba sai Khausar sai kuma Hajiya Bunayya bakinsa ɗauke da Sallama suka shiga dai-dai lokacin kuma maƙotansu suka fito.

 

Zaune suka samu Ummi kan 2sitter tana riĆ™e da Kur’ani Idanunta sun kumbura sun Ć™anĆ™ance yayin da Asma’u ke zaune gefenta hannunta riĆ™e da Carbi.

 

Cikin sauri Khausar ta Ć™arasa kusa da Asma’u tare da riĆ™e hannun ta kana tace.

“Asma’u da gaske wai dagaske ansace Yah Jameel!?”.

Cikin zubda hawaye Asma’u ta gyaÉ—a mata kai kana tace.

“Khausar da gaske ansace Yah Jameel tun randa kikazo ya maida kin nan, har yanzu babu labarin sa yanzu kusan dare na uku kenan za ashiga”.

Khausar ma cikin zubda hawaye ta damĆ™e hannun Asma’u tare da cewa.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Kallon Ummi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

“Ayyah Ummin Jameel Ashe abinda ya faru kenan toh Ubangiji Allah ya tsare Allah ya bayyana shi”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Ameen ya Allah Nagode”.

Mommy kuwa kafaÉ—ar ta ta dafa kana tace.

“Ba komai Ummin Jameel kiyi haĆ™uri ki daina kukan nan ki riĆ™a yi masa addu’a Insha Allah Ubangijin zai bayyana shi”.

Cikin sauri Ummi ta share hawayenta kana tace.

“Nagode Mommyn Khausar Nagode³”.

Cike da tausayawa Mommy ke sake ƙarfafa mata guiwa.

Ahankali Khausar ta juya tare da kallon Ummi cikin Muryan kuka tace.

“Ummi Allah ya bayyanar da Yah Jameel insha Allah ba zasu samu nasarar cutar da shiba zamu tayi masa addu’a Allah ya karesa”.

Miƙewa Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Bari mutafi Alhj na jiran mu awaje yace a gaidaki”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Nogeda Allah ya saka”.

Sannan suka fita a coumpund suka haÉ—u da wasu matan sun shigo yiwa Ummi jaje bayan sun koma gida.

 

Baki É—aya Khausar ta kasa nutsuwa kafin ta kwanta taje tayi alwala kana ta É—auki Kur’ani tana ta karatu tare da tawassali dashi da niyyan Ubangiji ya bayyana M Jameel aduk inda yake.

 

Misalin ƙarfe goma na dare kamar lokacin da aka dauke M Jameel Moddibo dake gefen Abba ya miƙe da niyyar tafiya Akuma dai-dai lokacin wayar Abba dake gabansa ta hau ruri.

Atare Abba da Moddibo suka kalli wayar cikin sauri Abba yayi Picking call É—in tare da kaiwa Kunnensa.

Daga ɗaya ɓangaren akace Alhj Bashiru mahaifin Jameel ko!?”.

Cikin sauri Abba ya gyaÉ—a kai tare da cewa.

“Eh nine nayi ta kiran layinku baya shiga”.

Cikin fusatacciyar murya Mutumin yace.

“Dama ce maka mukayi idan ka kira zai shiga?”.

Girgiza kai Abba yayi tare da faÉ—in.

“A’a to menene sharaÉ—in ku na biyu kaga ban faÉ—awa kowa ba!”.

Cikin bauÉ—aÉ—É—iyar murya Mutumin yace.

“Kuɗin fansa zaka biya shine sharaɗin mu na biyu”.

Kai Abba ya gyaÉ—a tare da cewa.

“To nawa kuke buƙata?”.

Kai tsaye mutumin yace.

“Milion ɗari biyu”.

Atsorace Abba ya dafe hannunsa aƙirji kana ya zare ido cikin tsanananin firgici yace.

“Milion ɗari biyu!?”.

Atare Hajiya Bunayya da Moddibo da maganar ya dakesu suka haÉ—a baki atare wajen cewa.

“Milion ɗari biyu?”.

Cike da gadara Mutumin yace.

“Toh idan ba zaka bada ba sai ka shirya karɓan gawar ɗan ka!”.

Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.

“Kuyi hakuri dan Allah dan darajar Annabi kada ku kashe wayar”.

Cikin Yanayin É“acin rai Mutumin yace.

“To ai mun riga mun faɗa muku abinda ake buƙata idan ka shirya gobe zamu sake kiran ka muji ko ka shirya”.

Yana gama fadar haka ya katse kiran…!

 

 

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button