TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 65

Sponsored Links

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/4, 7:48 AM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Na gaji sosai dana dawo don haka na kwanta da wuri a ranan
sai washegari dana tashi nayi dan gyara kafin in in fita na kwashi takardun
nasa don ranan nake son in turo wa Brother Bisi dasu kada yaji shiru.

  Na fito da shirina
zuwa cikin gida don in gaidasu kuma in sallamesu na samu Dije a waje tana cin
kayan bukin a wanan lokacin ya kirani a waya na dauko na daga ina fadin bari mu
gaisa da Dije da tana hangoni tace yau kina shiga makaranta ke nan nace eh
kwana biyu banje ba kada a wuceni da karatu sai na manta wayan a kunne take.

    Nayi mata inna
kwana kana na nufi wurin inna da itama tana zaune daga kofansu tana cin nata
kayan bukin nayi mata inna kwana cikin ladabi.

   Ta amsa min yadda
ta saba ba yabo ba fallasa na juya muna gaisawa dasu Aisha daga cab Asmau ta
leko ta daki tana fadin wai matar yaya wanan dayan mai cikin din da muka gani
itama yar uwankuce ?

   Nace eh itace akai
muna aure rana guda mu uku kai amma duk kin fisu kyau nisa ba kusa saidai su
gwada maki jin dadi yanzu kawai don suna da sallo sosai wallahi.

    Kai ji yar nan da
wani zancen banza su ba diyan masu kudi bane kuma yanzu suna aure me kudi in
akwai kudi ina ruwan mutum da muninka ?

    Wani kallon
takaici na watsowa inna din lokaci guda nace amma kada ki manta asalinmu daya
duk abinda suke takama dashi dashi nake takama nima ai kudin mazansu wasuke ba
?

    Don nawa mijin
baida kudi a cikon mu bashi ke nufin na koma baya ba Allah bai bashi ba yanzu
in Allah ya nufa zaiyi nan gaba sai muyi harma kila mufisu arzikin da suke
takaman dashi a yanzu.

    Wanan shine
maganan gaskiya Dije ta fada daga kofanta ni kuma ina fadin haka na juyo zan
bar wurin naji inna tace yanzu dawa kika wanga magana cikin mu ?

   Kemana Dije ta bata
amsa yara na maganan su mikaiki saka masu bakinki ciki don wanga maganan ma sam
bada wagga diya kikayin shiba danki kika hwadawa magana shida hannunshi bai kai
ba.

    Sam na mace wayan yana kunne har lokacin
saina dawo na fada a daidai lokacin da inna ke babatun fadin don na saka bakina
ba gaskiya na fada ba ai banki mijin nata yai arzikin ba nima.

  Dije duk ake magana
sai kiyi kokarin juyawa mutum maganan shi yanzu meya kawo zancen dan dije cikin
maganan nan ?

  Nidai na fita ina
jan tsoki ashe yanata magana a wayan banji shiba karshema dana fita na jefa
wayan a cikin jakata jin nafice daga gidan yasa ya kashe wayan tasa a lokacin.

   Na isa makaranta
daidai malamin zai shiga don haka kusan a tare muka shiga dashi lokacin bayan
mun fitone muke hiran da hannatu dataga yadda nake rai bace a ranan.

   Sam har ya kwana
biyu ya koma basu yarda sunyi zancen Ahmed dashi ba kamar yadda malamin ya fada
masu iya lokacin da zasu kai kafin su tunkareshi .

  Hakan yasa suke
kyale har ya tafi baisan komai ba gashi har Ahmed din ya kira Alh jauro kamar
yadda ya saba kiransu lokaci lokaci daya bayan daya yana gaisawa dasu a
matsayinsu na iyayyensa da suka tsaya mai a yanzu din cikin lamarinshi.

  Suma hakan sukan
kirashi suji lafiyab mu don hakanema nake dauka da mahaifinasa yake waya wani
lokaci sai daga baya na gane ba haka bane ashe.

   Koda ya koma komai
bai canza ba tsakanin shi da hjy Yabi har yanzu zaman nasu suna dai yinshi a takurene
da juna don sam yanzu baya shiga tsabgansu.

   Ita dai ke kokarin
taga sun gyara koshi don tacinwa manufartane akanshi yanzun din kuma yasan da
hakan don akwai ranan data fita ya kira mai aikinsu ya tsureta akan in bata
fada mai gaskiya ba zai koreta a gidan.

   Jin hakan yasa fa
kwashe komai data sani ta fada mai game da hjy saida hankalinshi ya tashi sosai
bayan ya gama jine ya sallameta da jan kunnenta kada ta yarda ta nuna mata
yasan da hakan don hakan zai jawo ta iya rasa aikinta idan ta shine tunda ta
taimaka ta fada mashi ba wani mahaluki da zaisan wanan zancen.

   Tayi maigodiya
shima yace ya gode amma duk lokacin da taga wani abin cutarwa a gareshi don
Allah ta taimaka ta fadamai tayi alkawarin hakan.

   Haka yasa ya kara
jan jikinshi da ita sosai dan dama dama diyanshi yana mu,amula dasu yadda ya
kamata ko wani mahaifi yayi da dansa.

  Ya dawo da kamar
sati uku tana dawowa unguwa ta hango yan aikina aikin gyaran dayan part din
dake rufe a gidan da mamaki ta fito daga dakin tana tana binsu da kallo har
zuwa wurin su.

  Basu dakatar da
aikin da sukeyi ba sukaci gaba dayansu take tambaya yace maigidanne ya kirasu
suyi aikin yana fadin haka yaci gaba da aikinshi ya barta nan tsaye tana ci
gaba da kallonsu.

    Ciki  mamaki da samun daurewan kai ta taka zuwa
part dinsu yarta ta sama a dakinta ta shiga a rude yarinyar na kwance tana waya
dakin duk ya turare da hayakin shi-sha a lokacin.

    Shigowar uwar ta
dan dago tana fadin mummy lafiya kuwa na ganki a haka kamar a rude salima wanan
uban hayakin da kika turara a daki haka anya kuwa zai baki lafiya karshe ?.

   Mum wanan ba komai
bane fa kin sani yarta fada ta mere baki uwar tace daddyn ku ya fada maki za ai
gyaran wancan part dinne kafin ya fita ganin yakan dan zauna da yaran yayi fira
wani lokaci yasata tambaya haka.

   Haba mum bai fada
maki ba ni zan sani kawai dai kila yaga kayan cikin sun dadene yasa a gyara
diyar ta fada cikin ko in kula sanin suna yawan gyaran gida akai akai.

   Salima ki dawo
cikin hankalinki ki natsu ki fahinceni maganan abinda ke shirin faruwa a gidan
nan nake maki kina karanto min hauka ke kuma.

  To ki sani idan ba
aure zai kara a yanzu ba akwai wani plain da yake shirin yi dolene akwai abinda
yake shiryawa bada sanina ba a yanzu ya zama dole in sani meye manufanshi da hakan
idan ya shigo.

    Amma mummy daddy
baya gari ya fada min da safe nan  kafin
ya fita zai tafi South Africa shida Alh badaru zasu wani business a can nima
naji hakan ne lokacin da Alh Badarun ya bugo mai waya suna magana.

    Mamakinta kara ya
fito a fuskanta har tana watsawa diyar wani irin kallo kamar itace tayi laifin
a lokacin yarinyar ta gand meke zuciyar uwan da sauri tace.

  No mum nimafa da
suka gama wayanne ya fada min cewa Alh badarune zasu tafi South Africa tare da
shine a yau din.

 Amma salima ya kamata
tun lokacin ki sanar dani ba yanzu ba don fadin baida rana tace sorry mum na
dauka aikin sanine ?

  Bata iya yin magana
ba lokacin sai dagawa da tayi ta dan kure yar nata da idanu na dan lokaci kafin
ta juya ta bar dakin zuwa nata dakin.

  Gado ta fada hankali
tashe a hankali ta mayar da idanunta rufe ta rasa ta ina zata fara tunane ma
don yadda take daukan zancen yafida nan a gidan nan yanzu.

  Tana nan kwance
tunanen ta ya tsaya akan danta yasir lokaci guda don shine kadai zai iya takawa
mahaifin nasu burki a yanzu kafin ya idda nufinshi dake cikin zuciyarshi
akansu.

   Don ita salima da
ita da babu a yanzu duk dayane kamar ba mace ba bata ko gwada kishin abinda
mahaifin nasu ke mata a yanzu.

   Bayan tunanenta ya
tsaya a yasir din ta samu zuciyanta ya dan rage zafi lokacin ne ta jawo waya
don labartawa yarta abinda ake ciki game da mijinta.

  Yadda take a rude
hakan ta labartawa yar uwan nata komai hankali tashe itama yar uwan ta rude ta
kwaso ashar ta dura masa tana fadin me yake nufi da gyarab daki a yanzu.

   Shin aure yake
nufin zai kara ko kuma dai shine zai koma ciki a yanzu ya barku nan haba dai
yayata yaya za ayi shidake tsakiya ya koma gefe ko kin manta yadda tsarin gidab
namu yakene wai ?

    Tsarin dama na
mutum biyune nasa a tsakiyan mu ba sai wani yaga dan uwa a cikin mu ba inyaso
hakan da sauri yar ta dakatar da ita da fadin kedawa ?

  A, a musali nake
maki ai gara dai ki gyara don bani fatan ace za a kawo maki wata a cikin gidan
nan yanzu da sunan kishiya kila kuma wanan kucakar ta nan zai dauka ya kai can
yarta fada.

    Ita kuma ta amsa
da sauri tana fadin tazo ina aiko da komai ya lalace min a yanzu da gaske in
har Naito tazo garin nan da sunan zama ko kin manta da cewa ya auretane da
yardana wai ?

  Maganan da ke nan ba
yanzu ba don yanzu komai da mukayi a baya da alaman abubuwan sun badamu a yanzu
gaskiya nima hakan dai nake gani amma ai idan yasan wata ai baisan wata ba.

    Tundai zancen
shigowan yaron nan da kika fada karkiji yanzu yadda nake jin zafin wanan zancen
don irin masu shigowan nan tsakiya sai suzo su zama wani abu a gida naka na
zaune.

   Don Allah bar
zancen nan aiko zan tafi hutuwace sam ba zan taba yarda da wanan shegen yaron
ya shigo cikin mu yanzu dai gobe in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nasarawa an
fada muna wani boka a can wani kauye zamuyi tafiyan tare da hjy liyyatu zuwa
can.

    Duk wanan wayan a
kunnen mai aikintane dake duke tana jera mata abincin don taba da umurnin a
kawo mata abincin a dakinta lokacin tagama jerawa ta fita tana sheda mata
angama komai.

    Muna zaune aka
gama tura koma zuwa ga e-mail din Bisi din duk wani takardan daya dace saida
muka tura mai a lokacin bandai fadawa kowa komeye ba balle zancen ya yadu kafin
hakan ya tabbata.

   Wayanane ya dauki
kara lokaci guda na lalubo daga cikin jakkata shine a Latin na dauka ina mashi
sallama ya amsa na dora da ina wuni ya amsa da lafiya lau kun fito break ke nan
?

  Nace eh amma yanzu
gida zan tafi don ba zamu zauna karatun yamma ba yau yace test zamuyi OK idan
kika koma don Allah kada ki kula duk wani abinda inna zatayi maki don Allah
nasan har yanzu tana jin zafin zancen daya faru da safe tsakanin Ku.

  Kai Waya fadama
hakan sai naji yayi murmushi kafin yace au had kin manta na kiraki a ways
lokacin kika bar wayan kunne da sunan zaki gaisa da Dije a lokacin don haka ban
kashe wayan ba ai lokacin.

   Naji koma naji duk
abinda ya faru had amsa da kika bata dan haka banson wani zance kuma ya kara
tasowa son run dazun nake son kiranki nasan kina class lokacin.

   Ni ya wuce ai a
wuri dama kawai don ta gane na bata amsa ai kuma shike nan ai yace na sani don
Allah ki bar tankawa daga yau don tana sane take komai ai.

   Kayi hakkuri idan
hakan ya bata min yayi murmushi yace is OK mashin zaku hau yanzu ke nan ko nace
eh don yau Nabila bata shigo ba nake gani motarta baya nan.

    OK ki kulamin da
kanki nace nagode harga Allah banji dadin da yaji wanan zance ba don ba komai
nake son ya dinga jiba tsakanin mu muna gama waya dashi na mayar ke nan a jakka
sai naji wani kiran ya shigo again

   Na dauka shine kuma
a lokacin ya sake kira said naji ummahce ashe dana dauko na dauka da sallama ta
amsa ina kokarin gaida ita naji tana fadin.

   Kina school din be
had yanzu nace eh ummah amma yanzu make son in koma gida min tashi ke nan race
to ki kira Aisha da mamaku kiyi masu gaisuwa .

    Don yarinyar nan
jaririyar ta koma dazun aka kaita da sauri na furta innalillahi was inna
alaihim raji,in yanzu yar nan ta rasu ummah ashe ?

   Have eh wallahi
kamar dama jira take ayi suna taiwan uwarta bara yadda aka fada son jiyama basu
kwana a gida ba saida suka koma asibiti da ita a can ta cika.

  Nayi mata adduan
dacewa da Rahaman Allah ga musulmi nacewa ummah yanzu zan kira Aishan insha
Allahu mukayi sallama ta kashe wayan nata.

  Jikina yayi sanyi
sosai ina dago kai hannatu na fadin yar Aisha ce ta koma ko nace wallahi a
cikin wani irin yanayi murya a raunane .

    Dama ai yana da
wuya ta rayu irin hakan sai in yaro rabone zai zauna bayan ansha wahala karshe
kuma ya taso a wahalce da ciwarwuta iri iri a jikinshi.

    A hankali muke
takowa data cikin school din muna maganan sai ga motar motana na gani ta gitta
muna nabi motan da kallon mamaki.

    Hannatuce ta
rigani magana da fadin ikon Allah wancan kamar motarki zahra nace itace wallahi
waye ke janta ciki nace naga kamar sanusi ne dan yayan mama dama dan dakintane
shi sosai zakace shidin ma Dan gidan mune shi.

   Kai wanan mama din
gaskiya ba mutumiyar arziki bace yanzun mortar naki zata dauka ta ba dan uwanta
bayan kowa yasan nakice dama taje su hau hannatu meye duniya baki dayanshi ma
balls mota da zai lalace.

    Wallahi ummah ta
riga da tace koda andawo da motan ma bazan haushi ba ko hakan zai zama sanadin
aurenta da Abba kuwa to kinga me zai dameni no yanzu da ita duk mai hawa ya
hauta ba abinda ya dameni a yanzu.

    Shiru tayi kafin
can kuma tace dani amma wuri ta samu ina ji a gari ana fadin ko wanan amaryan
Abba din yanzu hjy mama ta shiga gabanta amma fa yadda mutane ke fadine fa.

   Murmushi nayi bance
komai to waike zahra irin matan nan basu tuna cewa zasu mutu su koma ga Allahne
wai mutum ya rungumi duniya yasa a gaba irin wanan halin me zataje ta fadawa
Allah akan hakan ne wai ?

    Kofa bata mutu ba
zata iya tsufa ko ta nakasa kinga duk abinda tayi din nan ya tashi a banza
yanzu ai gara mu biya ta gida muyi masu gaisuwa ko ta fada jin tana ta magana
ban bata amsa ba lokacin.

   Bari to na kira
master in fada mashi na fada ina kokarin zaro wayana daga cikin jakata lokacin
wanan Sanusin ya kara fitowa daga cikin makaranta ya kwaso wasu yan mata yan UG
two a motan suna tafe suna shan kida sukazo suka wuce mu kamar farko.

   Ina jin hannatu
tace wallahi Allah ya isa dan iska dakai da uwar dakin naka sai kunyi kunya tun
a nan duniya in Allah ya yarda wani irin dariya ta bani lokaci guda har ya
dauki wayan ban sani ba ina karawa naji yana fadin a ina kike kike wanan
dariyan kamar an maki bushara ?

   Wallahi hannatuce
take zagan min mama da sauri naji yace subbahanallahi wace maman naki ciki nace
wallahi mama da mama ta gidan mu wai kawai don taga wanan sanusi din dan yayanta
a cikin motana yana ja ya kwaso yan mata keja masu Allah ya isa.

  Sai naji yayi
murmushi yace kai hannatu bata rabuwa da shirme wallahi ta bari idan nayi kudi
in saya maku motar daba me karbe muna saidai Allah.

  Balle har wani gardi
ya hauta wanan tamu dukane yanzu tunda na Abbane kowa yana da right din da zai
hauta yanzu namu nan zuwa da yarda ubangiji.

   Murmushi nayi tare
da fadin Allah ya nufa saidai kada ai kudin sayen motan aje a dauko min wace
zata hanani zaman lafiya dakai kuma.

   What ya fada da
karfi nayi murmushi tare da fadin nawa akayi muna gani dama tunanen ki ke nan
zahra a kaina bari anji mu karasa mun samu dan mashin yanzu zamu shiga na bashi
amsa na kashe wayan ina murmushi.

 

Leave a Reply

Back to top button