Furar 2Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 6

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

 

……..Lulu bata sake fitowa falon ba tana a ɗaki, sai in lokacin sallah yayi ta tashi tayi, dan tunda ta dawo asibitin nan kuma sai hankalinta ya dawo jikinta sosai. Da lokacin sallah yayi kamar wadda ake zabura sai Smart yazo mata a rai, miƙewa take cikin jan ƙaramin tsaki da son kauda al’amarin sa tai sallarta. Alhamdullah game da shan kayan shaye-shayen ta ma tunda suka dawo asibitin tamkar wadda aka tsawatar mawa bata sake sha’awar shan wani abu ba dan sun gagareta. Hasalima data tuna sai zuciyarta tahau tashi kamar wadda ta tuno wani abinci. Wannan dalilin ne ya zare mata duk wani tunanin ɗaukar wani abu tasha ya bugar da ita. Sosai wannan zuwa na su Tajuddeen da jin zaiyi zaman aiki anan yasata shiga dogon tunani, bata sha’awar tunkarar Nigeria sam, dan harga ALLAH wani sashe na zuciyarta na tsoron haɗuwa da Uncle Yousuf, sannan kuma bazata iya cigaba da zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya da Tajuddeen ba. Dolene tasan mafita na barin ƙasar zuwa wata ƙasa daban ta karasa dogon hutun data ɗauro ɗammarar yi har sai sanda taso ta waiwayi gida Nigeria sannan. Kasancewar anan ba wani an damu da dare ko rana bane dan akoda yaushe ba fasa sabgoginsu suke ba sai in sanyin gari ya hana hakan yasa Lulu tunanin ɗan fita yau tasha iska. Miƙewa tai duk da yanayi rashin ƙarfin jikin da take ji ta sake sabon shiri cikin wando da riga da jibgegiyar rigar sanyi mai hula. Turare taɗan ƙarama jikinta ta ɗauki ƙaramin ledan chocolate ɗinta ta saka a aljihun rigar bayan ta ɗaure igiyar takalmanta ta fito. Tajuddeen kawai ta samu zaune a falo yana daƙilar waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shiko da sai da taɗan gittashi ƙamshinta ya dakar masa hanci ya sashi farga da ita da sauri ya ɗago. Ganinta da shirin fita ya sashi miƙewa da sauri yana faɗin, “Ƴammatan ina zuwa haka ba neman abokin rakkiya?”.
“Ba buƙata”.
Ta faɗa a daƙile tana ficewarta, kafin ya iso ƙofar ta maida ta rufe da sanya security ta baya tana hararar ƙofar da jan tsaki tai wucewarta. Sororo Tajuddeen ya tsaya bayan ya gama mummurɗa handle ɗin ƙofar ya tabbatar da ta kulle ta baya. Lips ɗinsa ya ciza da yanayin rashin jin daɗi ya koma ya zauna a inda ya taso. Itako Lulu cikin tura hannayenta dake sanye da Safa suma a aljihun rigarta ta fara tafiya bisa lafiyayyen titin street ɗin nasu a hankali dusar ƙanƙara na ɗan sauka mata a jiki ɗis-ɗis kaɗan-kaɗan. Duk da akwai sanyi sosai yanayin ya mata daɗi, dan rabonta da irin wannan fitar haka tun bayan gama jiyyar jikinta da Smart ya murza, tana kuma ɗan fara samun walwalar ta kwana biyu sabon yanayin ciwon nan ya sake kwantar da ita shima. Tayi nisa sosai da gidan ta samu wani shagon shan coffee ta shiga, coffee ɗin tasa aka kawo mata, sai dai tana kaisa bakinta taji zuciyarta ya fara tashi, a take ƴan cikinta suka shiga hautsinawa. Babu shiri ta baro gurin cikin tashin hankali bayan ta biyasu, duk yanda taso riƙe aman ya gagara dole ta koma cikin restroom nasu ta dinga sheƙasa har ɗan kunun gyaɗar da tasha a gida sai da ta zazzagar. Cikin galabaita ta samu ta wanke fuskarta ta fito dajan ƙafa. Can gefe ta samu ta sake zama tana maida numfashi ɗaɗɗaya zuciyarta a cunkushe da tunanin wai mike damunta haka ne?. Ita dai tunda take bata taɓa fuskantar kalar ciwo haka ba da amai. (Ni dai nace Hummm). Ta jima a shagon coffee ɗin kafin ta miƙe cikin ƙarfin hali ta sake nufo hanyar dawowa gida dan wani irin sanyi mai shiga jiki da ƙashi take jin na ratsata duk da yanda ta rufe duk jikinta da kariya harda su Safar hannu da facemask amma bata tsira ba. Da ƙyar ta iya kawo kanta gida, ta cire security ɗin data sakama ƙofar saboda Tajuddeen ta shigo cikin tangaɗi. Babu kowa a falon da alama Tajuddeen ya shige, gudun karma wani yazo ya sake damunta ya sata nufar bedroom ɗinta dan yau tayima Dada yaji akan bazata sake kwana a ɗakinta ba. Dan dama da nata zuwan Dadar ya sata komawa inda ta sauka kasancewar bata da lafiya. Gaba ɗaya hankalin Dada da Alh. Sulaiman da suka haɗe kansu a bedroom ɗin Lulun da tunanin bazata shigo nan ba koda ta dawo yanzu baya kan ƙofar, tattaunawa suke game da zancen cikin da suka saka aka zubar mata batare da tasan ma da cikin ba. Wani irin bugawa ƙirjin Lulu yay da ƙarfin gaske. Ta tsaya cak tamkar wadda aka dasa matsayin gunkin tarihi ba mutum mai numfashi ba tana cigaba da saurarensu. Kanta ne ya fara juyawa sannu-sannu ta fara ganin hajijiya babu zato sai jin faɗuwar abu sukai ƙasa yifff. A tare suka zaburo tare da kallon ƙofar cikin waro idanu…..

Bayan kamar awanni biyu ta dawo a hayyacinta, zuwa lokacin hatta da Tajuddeen na a ɗakin zaune a gefenta cikin damuwa dan har fuskarsa ta gagara ɓoyewa. Ɗaya bayan ɗaya ta gama binsu da kallo tamkar mai son tantancesu kafin ta maida idanun nata ta lumshe kawai batare data nuna alamar ta tashin ba. Hirar kakar tata da kawun nata ne suka shiga dawo mata dalla-dalla, ita Mawaddat ce keda ciki, ciki na haihuwar ɗan mutum, amma suka saka aka zubar da shi. To minene dalilinsu nayin hakan. Duk da a karan kanta bazatace son cikin take ko akasinsa ba, amma tanaji a ranta kamar ya kamata ace kafin su aikata zubar da shi a bari ta sani da kuma jin ta bakinta ai. Hannunta dake ajiye a saman cikin nata ta motsa a hankali, tare da sake matsar da shi ƙasa sosai ta shafa cikin. Wannan ne ya fargar da su Dada cewar ta farka. Gaba ɗayansu sukai kanta da sannu musamman Tajuddeen da Dada. Dan Alh. Sulaiman dai idanu kawai ya zuba mata batare da yace komai ba. Cikin damuwa Tajuddeen ke jera mata tambayar mike damunta? Ko zata tashi suje asibiti ne? Yanzu ina ke mata ciwo?. Idanun nata ta ɗan sake buɗewa ta kallesa, sai kuma ta maida abinta ta lumshe. Sake jera mata sannu da roƙon ta bari ya kaita asibitin yayi. Amma sai ta girgiza masa kanta kawai. Zai sake magana Alh. Sulaiman ya katseshi da faɗin, “Tajuddeen relax mana”. Shiru yay badan yaso ba, hakan yasa ɗakin komawa shiru. Lulu da gaba ɗaya take jin wani irin yanayi mai kama da jin zafi da ɗaci a zuciya ta sake buɗe idanunta da sukai ja akan Dada. Muryarta irin ta mara lafiya a dake ta ce, “Dada nice na samu ciki aka zubar?”. Ba Dada ba hatta Alh. Sulaiman sai da furucin nata ya razanashi. Kusan a tare suka kalli Tajuddeen da ya furta “Ciki kuma Mawaddat?!”. Maimakon amsa Tajuddeen ɗin Dada take kallo alamar jiran amsa daga gareta. Dada data ɗan daburce cikin inda-inda ta ce, “E… E… Eh hakanne Sweet heart. Mun…m…munji tausayinki ne da ganin halin da kike a ciki na wahalar ciwo. Sannan minene amfanin haihuwa da wancan sankaran shashashan yaron da ko kansa bai iya riƙewa ba sai baƙin talauci, ke akaran kanki ma baki isa haihuwar ba ai shekarunki nawa ma duka. Na biyu inaji a jikina bada yardarki aka samu cikin nan ba, sai dai in asiri yay miki tare da fyaɗe. Dan ke da bakinki kin tabbatar min baki taɓa bashi kan ki ba. Ki faɗa mana gaskiya, fyaɗe yayi miki ko?”.
Kai Lulu ta kauda tana mai lumshe idanunta batare data bama Dada amsa ba, dan wani irin zafinsu takeji kamar ta shaƙo ɗaya a cikinsu ta maƙure kawai, a mamakinsu sai ganin hawaye sukai na zirara ta gefen idonta yana sauka saman filon da take kai har a cikin kunnenta. Gaba ɗayansu babu wanda bai kasance a yanayin zama turus ba, musamman Tajuddeen da ke jin jikinsa na tsuma. So yake kawai yaji Lulu tace fyaɗe Smart yay mata, shiko ya ɗauki alwashin koda uwarsa yake yawo sai ya yagalgala masa rayuwa. Amma abin mamaki sai gashi iya lallaɓa Dada taima Lulu dan tace wani abu game da samuwar ciki taƙi tace komai. Da tagama zasu dameta sai taja bargo har saman kanta ta rufe kawai da faɗin “Not your business! Please live me alone”.
Wannan abin da tai ya ƙara sakasu a wasi-wasi, amma sai Alh. Sulaiman yace su manta da batunta tunda dai an ɗauki mataki, yanzu kawai abinda zasu maida hankali shine binciko inda Smart yake ya saketa a ɗaura aurenta da Tajuddeen. Sun gamsu da hakan, sai dai daga ƙarshe Dada ta bada shawaran in har fa anƙi ganin Smart dole ne su nufi Nigeria su makashi a kotu ta bama Lulu takardar saki kawai ko su nemoshi su dole ga amsa kiran kotu yazo ya bada ai. Nan ɗin ma sun gamsu, dan haka suka tsaya a bisa shawaran nan guda biyu…

Tun daga wannan magana Lulu ta koma musu shiru-shiru a gidan, dama ga yanayin rashin jin daɗin jiki da take fama da shi, wanda zuwa yanzu take kallon hakan a matsayin zubar mata da cikin da akayi ne. Su kuma su Dada ke fassarawa da asiri Smart yay mata kawai. Duk yanda Tajuddeen ke son shigema Lulu taƙi bashi fuskar hakan. Dole ya koma baya-baya da ita amma hakan na damunsa. Bama shi ba hatta su Dadan ta tattara ta watsar kamar bata san da su a gidan ba. Ummita kawai take kulawa dan yarinyar nada hankali da nutsuwa. (Ummita ta taɓa aure harda yara biyu, sannan zata iya girman Lulu kaɗan, wahalar da tasha wajen mijinta yasa bayan ya saketa iyayenta sukace bazata zauna musu a gidaba ta tafi wajen ƙanwar mamanta a Abuja. Karatu ta koma, bayan ta kammala rashin samun madogarar aiki ya sata amsar wannan aikin zuwa Canada ta hanyar Hajiyan Shuwa maƙwafciyar ƙanwar mamanta).
Duk da abinda Lulu ke musu duk abinda tace tana so sai Tajuddeen ya fita neman mata shi a cikin garin koda yana tunanin bazai samu ba. Duk da dai ma babu abinda tafi nacemawa a yanzu kamar kunun gyaɗa da fruits. Ita kanta har mamakin kanta take akan shan kunun gyaɗar nan na ƙaddara daya sarfaceta. Dan ita a baya ba gwanar shansa bace ba, zama ta iya rantsewa a ɗan zaman datai gidan Aliyu ne ta koya shansa. Sunan Smart da yazo mata a zuciya ya sata jan ƙaramin tsaki. Ɓal-ɓal taji cikinta ya bada har sai da takai hannu samansa ta dafa. Sai kuma akai shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta watsar da batun Smart gefe da kan faɗo mata a rai musamman idan tayi wani abu haka daya tuno mata da zaman nasu. Sannu a hankali jikinta kuma sai ya fara sauƙi, zuwa lokacin Alh. Sulaiman da Tajuddeen sun wuce wai duba Baba Garko, sai dai a baɗini shi Alh. Sulaiman nashi zuwan akwai manufa. Ganin Lulu ta samu sauƙi ta murmure sosai sai ma wata ƴar ƙiba da murjewar jiki da ta fara. Dan tayi wani irin ƙyau na farat ɗaya da haske tare da ƴar ƙiba. Zuwa yanzu babu abinda ke damunta sai ɗan zazzaɓin dare. Da zaran ance sha biyu tayi zazzaɓi zai rufeta, zuwa gabannin asubahi kuma sai ya sauka ta wayi gari garas tamkar komai bai faru ba. Shan kunun gyaɗa kam sai abinda yay gaba. Tana nan tana abunta. Tun Dada na maganar wannn shan kunun gyaɗa data laƙama suna na fitina har ma ta kawo ido ta zubama Lulun kawai………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button