Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 18

Sponsored Links

018
___________________
8days Later
Ummulsulaim ta soma sabawa da rayuwar gidan Yareema ,a iya zaman da tayi dashi ita ke masa komai na rayuwarsa ya maida ita baiwa sosai ,ta rame ta bushe ga abinci da bata iya ci sutura yaki bata sutura kullum tana daurin kirji da towel guda daya in tayi wanka ta sauya da mayafin Jakadiya

Kallo bata isanshi iyaka ne ta masa aiki ta ɓace masa da gani,A tsawan zamanta da yarima ta lura rayuwarsa yake shi kadai baida aboki bare abokin shawara babu mai ratsowa cikin rayuwarsa ,abunda ya shimfiɗo masa a rai shi zaiyi wannan yasa ya zama mutum mai gautsin hali ,daidai da gidansa babu mai zuwa sai in shi ya gayyace ka ,Yareema mutum ne mai mugun tsafta wannan yasa kusan kullum tana aikin ƙalƙale masa gida hatta fulawoyi gidan har aski kullum sai tayi masu ,sam bata dauki aikin nan wani nau’i na bautarwa ba saboda a gida tana aikin da yafi haka saidai kawai ƙunci da rashin sanin halin da iyayenta suke ciki shi yafi damunta ,tun tana ɗari ɗari dashi kar ya lalata ta ,sai daga baya ta gane Yareema comrade ne mata basa gabansa a yawan lokaci takan sata kallonsa ko zai bi jikinta da kallo in tana tafiya sai ta ga kwata kwata hankalinsa baya kanta…..indai yana gida to yana kan abu uku ne! Sallah…zikiri…karatun ƙurani ,ko kuma yana falo yana kallo ko karatun jarida ,da ya fita waje zai fara tamfatsa ma Al’umman Annabi mugayen aiki…..

Yareema ! Yareema mai salo na dabam …Allah ya gyara

Duba da hakan yasa Sulaim sakin jiki a gabansa zatayi komai ta kama kanta tasan ba wani hadinshi da ita ,ta dauki zamanta dashi matsayin wucin gadi daga zaran ya bushi iska zai sallameta gidan iyayenta.

***
Yau da misalin ƙarfe 11 na safe ,Sulaim na sunkuya tana gyara ma yarima farata sukaji knocking daga ƙofar daki ,da sauri ta kwashe kayanta ta wuce ɗaki ta ɓoye kamar yanda ta saba.

Gyaran murya Yareema yayi ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya maida hankalinsa kacokan akan jaridar daily trust da yake karantawa na satin nan

“Shigo!”
Cikin mutuwar jiki gimbiya Lubna ta shigo jikinta da rigar barci mai ruɓi biyu

“Yaya Inason magana dakai ne dama”
Ɗagowa yayi ya kalleta kana ya lumshe ido ya maida kan jarida ,ya nuna mata kujeran da yake can nesa dashi da jaridar hannunsa
“Zauna”

A sanyaye taje ta zauna cikin sanyinta na dindindin tace
“Yaya Barka da hutawa”
Da Muryar gadara yace “Yawwa”

“Dama yaya gameda halayyanka ne”

Dammm! Gabansa ya fadi ,ba’a taba masa magana kai tsaye ba sai yau

Kafeta da ido yayi ba tare da yace komai ba,cikin ɗari ɗari ta soma wasa da yatsun hannunta ta cigaba da cewa
“Yaaya…Yanda ka ɗauki kanka hanya ne da ba wanda zai alfahari da kai yaya….ka ɗauki rayuwar ka da tsaurarawa ta hanyar da kowa yake mugun shayinka…Yaya ba haka baba yake ba ,babanmu Mai sauki ne ,amma jibi yanda rayuwa tayi dashi ,yana kwance a gado rai ba amfani ,mune da jimami amma ciwo nashi ne,kafatanin likitoci ,malaman tubbu sun taru akansa amma sun kasa gano abunda yake damunsa…. yanzu sun yanke shawarar daura sabon Sarki shine zaisa baba ya warke ,Wanda dukkan hasashe ya ɗauru akan kaine Sarkin…..” Sanyaya murya tayi kamar zatayi kuka kana ta cigaba da magana

“Yaya to yanzu ka faɗa mun ,a hakan ne zaka ringa jagorantar Al’ummar ka? Ko kuwa sauya hali zakayi irin na baba? ko kuwa haka naka salon Mulkin zai kasance kowa na shayinka ,ana tsoron tunkararka”

Tunda ta soma magana Wani Murmushi yake yi mai sanyi yana mata wani irin kallo tamkar ba magana take masa mai ratsa zuciya ba ,ba alamun nadama ko ɗar a zuciyarsa

A tsorace ta hangame baki cikin tsantsan mamaki tana masa kallon ƙasa ƙasa “Yaya kana jina kuwa?…naga kana ta murmushine tun ɗazu ,kodai bana making sense ne”

Wani kallo ya jefeta dashi na nishadi,yana jin kansa tun yanzu kamar ma shine sarkin ,kana ya yafitota da hannu

“Zo ki zauna kusa dani ƙanwata” ya nuna mata gefen doguwar kujeran da yake zaune .

Tasowa tayi ta nufo inda yake cikin ɗari ɗari ,kodai yaya yasha wani abu ne?,ta lura har da ɗan alamun wasa da tsokana a fuskarsa ,yaushe yaya ya zama hakan ?

A ɗarare ta zauna kana yaja numfashi
“Hummm ,daga sanda kika fara magana sai naji dariya ya kamani ,wanann yasa kika ga ina ta murmushi” ƙurrr ta masa da ido ba tareda tace komai ba

“Kina da wani abu da zakice ne?” girgiza masa kai tayi alamun babu

“Ok let me clear your thought …..Daga lokacin da kikace mutane in sun ganni suna tsorona ,kawai sai naji wani sanyi a raina ,wannan ya tabbatar mun da cewa lallai na cika in zama cikakken Sarki mai Iko………..A matsayinka na cikakken shugaba dole ka sakawa mutane tsoronka a cikin zukatansu….dole ya zamana idan kazo waje Mutane su shiga halin furgici sanadiyyar ganinka… Kai a ambaci sunanka a matsayin shugaba ,sunanka ya sa jikin mutanen ka ɓari da kakkarwa don biyayya ma sunanka……. Alhmdullahi duk wainnan suffofin da na lissafa kuma ina dasu ,what else remain? In zama sarki ina mulki mutane na ,in kawo sabon sauyi ,gani gomna kuma gani sarki abun akwai daɗi fa”

Cikin tashin hankali take dubansa har yakai aya sannan ta daura da cewa
“Wannan se ya sanya ka zama ɗan Tijara! Ka zama ɗan gadara ,ka zama Dodo?!!!…..ka zama mutumi mai son kanshi, kwata kwata baka ɗaukan shawara…haba yaya akwai murginenen dutse bisa hanya nima ƙanwarka ina tausaya ma mutane in ka zama sarkin su ina ga mutane da rauhanannan da suke kewaye da fadar nan…. Tabbas Matsawar bazaka sauya halinka ba ,yaya zaka iya kasa mallakar gadon mulkinka ,a jikina nikejin matsala a tafiyar nan ,inaso ka mun kyakyawar fahimta ,yaya halinka zata ci sarautar ka….

“Ke wawiya ce Lubnah bakisan mulki ba”

“Na san mulki kuwa tunda naje England na karanci mulki da siyasa ,kaine nake fada maka ,coz I smell danger ,Yaya zaka rasa sarautar ka nanda kwana shida,kuma ka sani kasa samun kujerar ka daidai yake da a koremu daga masarauta ,zamu zama lay men Kamar kowa ,za’a naɗa sabon yarima mai cikakken iko irinka ,zai iya taka ka shima kamar yanda ka taka wasu a lokacin mulkinka….”

“LUBNAHHHHH!!!” ya daka mata wani wawan tsawa gami da miƙewa tsaye,ya nuna ta da yatsarsa

“Ni kike ma barazana da faɗuwa🫵🏻? Albishirinki ,Ni tun asalina mai nasara ne ,ban taba tunkarar abu na faɗi ba…..Nan da en kwanaki zan zama sarki ,zan dare karagar gadon mulkin babana.
Daga nan ne ma ,mutane zasu gano asalin kalana😕😠 wallahi mutane sai sun ringa jan gwuiwoyinsu cikin jini don tsira da rayuwarsu ❗babu mahalukin da zai zauna mun a masarauta na sai na manna ma gidanshi Hatimi….idan har ba da yardana ka zauna a masarauta na ba ,yankaka zanyi ❗ Zan yi gunduwa gunduwa da duk wani tsagera mai taurin kai,Zan yanka naman jikin mutum gutsi gutsi❗Zan aiwatar da Abinda gomnati tayi Ni da kaina” yana magana cikin ficewar hankali jikinsa na wani irin rawa kar kar kar Amma still Yana nuna ta da ɗan yatsa
Bakinsa tuni ya fara sarƙewa saboda bai saba magana mai tsayi haka ba

Jinin jikinsa a take ya soma ɓarka

“Ke kinsan waye sarki kuwa ? Har kike cemun in bar ɗagawa! Izzah! Shine Sarauta !!! Allah wadaran mulkin da ba Izzah….Mulkin damfareren masarauta kamar wannan na jarumine ,mara tsoro mai babban kwanya ,mai ɗayo aiki mai shirin taran fitina yayi kacakaca da duk wani munafiki,ba mai wannan tattauran zuciyar a kaf masarautar nan sai Ni,zan iya kashe kowa da komai don in rayu Ni Ni ɗaya………hummmm hummmmm
take your time ,kije ki sake nazari ke yarinyace ilimin ma yanzu kika soma degree daya tal gareki,nawa uku ne,da tarin kwasa-kwasai karki tunzura ni”

Dukda madaran fushin dake kan fuskarsa ,da yanda muryarsa ya daga saboda fitina gashin jikinsa ke mimmikewa ,lokaci daya ya koma luuu kan kujera ya natsu ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ,ya damƙi jaridarsa ya saita ƙwarar idonsa a kai ,kawai kuma sai ya saki Murmushi mai sauti “Zaki iya tafiya ƙanwata”

Fashewa da wani irin gigitaccen ihu tayi ,ta miƙe a karce ta fice daga dakin tana ganin yayanta kamar naman daji,anya wani aljani bai shiga kansa ba? Yana magana ne amma jikinta rawa yake gani take ita zai soma kashewa a yau ɗin nan kafin a kai ga sauran mutane”

Tana fita yayi wurgi da jaridar ya miƙe jiri na ɗibarsa
“Allah kasan barazana nike ,ko sauro bazan iya kashewa ba ,Allah ka bani mulkin nan don mutuncin gidan Annabi ,Allah ka barmun gadona da na taso a cikinsa ko don tsira da kimata….” wani mugun zazzaɓi ne ya rufesa.
ya mike cikin tangal tangal zuwa bed room.

Oum Aphnan
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button