Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 43

Sponsored Links

043
___________________
Washekari

Wani sabon horn ɗin mota irin mai fasa kunnin nan Salima ta jiyo daga harabar gidan ta.
Ɓiiiiiiiiiiiiiii

Hankaɗe labulen window tayi daga can saman bene don ta hango baƙon da tayi mai lalataccen mota haka.,saidai bataga kowa ba. A ciki ciki taja tsaki “Wasu mutanen basu san haƙƙin Al’ummah ba ,ynz kasan injin motarka ya lalace sai ka sauya ba ka shigo unguwar mutane kanajinsa tsit ka fara masu fare Kamar motan kwana kwana ba…”Duk tunaninta daga maƙofta take jiyo ƙarar motar nan.saidai tana cikin ƙorafi taji Muryar ya Sheikh yana kwarara mata kira tun daga harabar gidan

“Salima
Salimaa”

Da sauri ta ke gangarowa ,ynz ta daina firgita in Yana kwarara mata kiran nan ,bata wahalar da bakinta sai ta amsa sai taje inda in ta amsa zaiji take amsa kiransa.
A bakin ƙofa sukayi kaciɓis
Kafin tayi wani yunƙuri ya fizgo hannunta

“Taho…Taho kiga Hadiyyatul ajibah(Kyautan ban mamaki)…Taho kiga suprise” tana kokawan sa takalmi yana janta ,haka ta bishi dakyar ta gama sa takalmi.

Wani dagargazajjen peogeot 207 ta gani a gaban front door ɗin ɗakunan ta ya ratso dashi wajen parking lot ya kawo mata har gaban daki kamar wani takalmi.

Shiru tayi tana ƙarema motar kallo ,an daddaki hancin motar kamar anyi Accidents dashi
Zuwa yayi gaban motar yana dakan saman motar da hannunsa kamar ya shigo da wata shimfiɗeɗiyar mota mai kyau da tsada

“Salimata kin ganshi ko? Ya sauka ,na siya maki mota…I’ve bought you a car” turus ta tsaya tana kallonsa ita bata motsa ba ita bata ƙarasa wajen ba ,saima leƙe leƙe da take ,tana addu’ar Allah yasa kar wani maƙoci yaga sanda aka shigo dashi.

“Dama na fada maki zan baki mamaki ,jibeshi gredi ne nigerian use”

Jinjina masa kai tayi alamar gamsuwa
“Kwarai kuwa nigerian use kafi ɗan cotonou daga Nigeria sai bola”

“Ban gane ba”

Shiru tayi masa ta lanƙwashe hannayenta a ƙirji tana kallonsa ta ma kasa magana

Waigawa yayi yana kallon motar nan yayi arba da gaban hancin motar da ya mole.

“Auhooo 😃Wai wannan da ya naushe🤛🏼karki damu dashi ana kaima masu gyara suka ɗagoshi akayi ma motar fenti wuwuwuw Salima kin faso gari ,inajin ma sai kin ringa bani aro saboda motar nan duniya ne wajen gudu…kinsan dashi turawa ke tseren gudu?”

Adnan Dake hangosu ta wajen gate Yana Murmushi shi Salima ta hango aikuwa ta falla cikin gida da gudu tana kururuwar ihu .

“Au au Baki so? Yarinya zakiyi wa kanki asara”

***
“Ynz Salima duk tattalina in cire sunanan kudade in siya maki motar nan giredi amma ki kasa mun godiya! Sai ma ki shigo gida ki barni kamar sakarai ,kinsan kuwa Taimakon da Allah yayi maki cikin mata miliyan nawa ne suke fatan samun mota basu samu ba? Haba Salima duk yanda Nike son in Sauya in kula da gidana sai kin hassala Ni?”

“Sheikh Ni zaka siya ma motar da direbobi ma en Kaduna habuja sun daina amfani dashi? Sunsan in suka faka a tasha ba passenger da zai hau?.kai irinshi kake hawa? Meye amfanin dukiyar da rabbana ya baka?…Su babu amsa? Hmmm Nagode amma ka sani wancan akwalar motar da ka siyo bazan hau ba”

“Me yasa? Saboda miqdad ne ya siya maki motar Ba Adnan ba? Ai da Adnan ne da cikin ɗagawa zaki hau”

“Eh zai iya zama hakan ne,ynz kalleni tunda Adnan ya shigo rayuwata na canja daga rayuwar sa nikeyi ina saka sutura tsumma²,saidai kaje ka siyo mun mama ta mutu saboda kallon tsohuwa wacce aka gama yayinta da kake mun today and always . Hmmm Amma fa a yau ka gama kaini nan (Ta nuna maƙoshinta),zaka iya maltreating Dina da maƙo in jure ,amma bazan juri rainin saa ba,and above all ,In aka ga ka na wulakantani kana horani da yunwa abun farko dake zuwa zuciyar mata shine,ai wane yana da big bullet🍌 shi yasa ya gama da Salima bazata iya barin gidansa ba ,bayan kuwa ba haka bane ,banga amfanin wannan Abar taka da na jariri ba,Sheikh ka zube mun daga sanda ka daina iya bani haƙƙina a gado na rainaka, daga sanda na gane mazantakarka bayi da tasiri ka sire mun,yau zan bar maka gidanka ,kuma bazan dawo ba zan fada ma su baba ,ba ci ba sha,ba jin dadi ba mu’amalan aure ,zamu gani in ka cika sharuddan aure…wlh Adnan da bai da mata yafika sanin hakkin mace amma kai tarin littafai ba aiki dashi…”

“Oho Ni kike dangantawa da yaron nan Adnan,wannan kazamin”

“Kai kaja dalilin da za’a dangantaka dashi, incompetence Dinka yasa har maza suke iya shiga cikin gidanka ,su dauki responsibility din iyalinka and you don’t bloody care….jibi rayuwa ta ? Tunda na aureka na fatare ,ba kudi ba aikin yi ,ba gayu ,ba farinciki ba zaman lafiya ba haihuwa ba ƴaƴa…babu babu….ina bukatar in auri sahihin miji da zai jiyar dani dadin auren da ake kwadaitar da mace,kai kam ba namiji bane mata maza ne”

Ta finciki hijabinta akan drawer ta wuce fuuu

“Salima…Salima”
“Dallah Ni bar dafa mun kafada ,bakasan haramun bane taɓa matan wani? Ni yanzu ba matarka bane ba”

Dariya ya fashe dashi “Wohoho mata shiyasa akace komun ilimin mace indai ta baro maka wani haukan sai kayi zaton alif bata sani ba a ɓangaren addini…Jeki Sai kin dawo ,wannan karon baki wahalar dani ina jele a titi kamar sakarai ,da kanki zaki dawo don I’m like Oxygen da kike shaƙa,bazaki iya rayuwa in bani ba..”

Har takai ƙofa ta jiyo shi aikuwa ta dawo

“Hhhh kana ganin idan babu kai bazan iya rayuwa ba ,a hakan? To bari kaji ba Ni ba,ko wata macen ka aura indai har zaka cigaba da uzzura mata da maƙo baci ba ciyarwa ba sutura ba kula da lafiya ba kwanciyar aure ,ya Sheikh bazaka samu wacce zatayi haƙurin zama da kai ba ,ko ka aura sai kun rabu”

“Baki zakiyi mun saboda ke ga muguwa?”

“Ohon maka dai”
Taja ƙaramin akwatinta ta fice.

Ɗage kafaɗa yayi “Ahaf ina nan zaki dawo”

_Illan mace mai yaji kenan sai ta fice a zuciyar mijinta ,tun in tace zata tafi yana firgita har ya dawo ya rainata,yasan ko ta tafi zata dawo…Allah ya bamu zaman lafiya a gidajenmu_
***
A bakin gate ta tsaya da akwatinta a gefe tana jiran keke,tasan abune mai wuya a samu giftawar keke ko taxi a unguwar su ,amma kuma batada strength din da zata fita wajen hanya

“Kiyi hakuri zaman aure ba samartaka ba ne ba,is not a courtship that u can quit so easily ”

Cikin ƙwalla ta jiyo jin muryarshi a bayanta ,yayi kyau cikin ƙananun kaya baƙaƙe ya manne baƙar shade a idonsa ya gyara ƙasumbarsa cif cif sai sheƙi ,yake .
Yayi mata kyawun da bai taɓa mata ba.

“Na gajine Adnan wlh I’m exhausted ”

“Na sani ,Plz karki rabu da ya Sheikh yana sonki ,kawai ke zaki dauki matakin gyara shi,amma ynz in kika rabu dashi kin zama ƙaramar bazawara mutane zaginki zasuyi tayi kin kashe aurenki”

“Saboda zagin mutane sai in kashe kaina,zawarci naƙasa ne? Allah shi ya halasta aure kuma ya halatta saki in da cutuwa ,shigowar ka rayuwata kai ka sauya mun komai na”

“Yes na lura da haka na lura da ke macece mai ma miji biyayya shigowa na rayuwarki yasa kika hutse ,shiyasa yau ma daga yanzu airport zan wuce zan koma ƙasar mu ko na barki ki cigaba da zaman hakurinki kamar yanda kikeyi a baya….samun numberki”

Kafeshi da ido tayi wasu hawaye na ɓulɓulo mata a ido

“Da gaske tafiya zakayi ka barni”

“Eh mana da kin Sanni ne😃 we met for a few days and now time to leave”

Mika mata wayar ya sake yi “ni samun numberki”

Tana kallonsa sarara ta karɓi wayar ta saka masa Number

Murmushi yayi tashi muje in Mai dake dakinki

Noƙe kafaɗa tayi “Ni bazani ba”

Ɗaure fuska yayi yana kallonta itama kuma shi take kallo ta yarda duk fushin da zaiyi ma yayi amma bazata koma ba.

Sun kwashe tsawon minti ɗaya suna ma juna musayar kallo.
A daidai nan ya Sheikh ya leƙo aikuwa ya hango Salima da Adnan a tsaye

Da gudu ya fito ƙafarsa ba ko takalmi “This boy again? ” basu ankara ba sukaji an kai mashi naushi.

Ƙishim ƙishim! Ta rufeshi da duka.

Kafin kace me maƙota sun taru ,da ƙyar aka rirrikeshi yana zabura yana nuna Adnan “Wallahi sai na kasheka…sai na kasheka takan matata ”

 

 

0um Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button