Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 33

Sponsored Links

033
___________________
Da gudu aka sunkuci Salima sai asibiti ba wanda ya bi ta kan Adnan Dake kwance a sume. Anty da bata samu waje a mota ba ,da gudu ta koma ɗakin Salima zata ɗauko car key dinta tabi bayansu ,anan tayi tuntuɓe da ɗan bawan Allah . Ƙwalla ihu tayi ta je kitchen da gudu ta dauko bottled water ,ta ɓincine hancin goran ta diddila masa a kai . firgigit yayi ya miƙe zaune ya soma sambatu “Salima ta waye ya maki haka ,bazan yafe ma ɗan ta’addan da yayi maki wannan ta’addancinba….” Shau Shau Shau ya fara hawaye .
Zuciyar mace mai rauni a take zuciyar antyn Salima ya karye ta tsuguna a gabansa tana bashi hakuri ,jin maganarta a saman kansa ya sashi maida hankalinsa ,ya miƙe cikin borin kunya ya saka takalmarsa ya fice a gidan.

Rafka tagumi anty tayi cikin damuwa ,wai meke faruwa ne da rayuwar ƙanwata? Waye wanann din? Kawai maƙocine ,zai nuna tsananin damuwa da ita haka fiye da mijinta? Da walakin.

Ɗaukar wayarta tayi tana ta kiransu a waya don tasan inda suke ta bisu amma basa dauka ,nan taja tsaki ta ajiye wayar a gefe .

Minti 30 baya ,sai ga kiran wayar Ya Sheikh nan yake shaida mata Salima ta ji sauki dama firgicine an bata alluran barci an daurata akan drip in ta farfaɗo zasu dawo gida ,so basai ta taho ba ta zauna a gida saboda masu kaico kaico.

Hankalinta sosai ya kwanta ta koma ciki ta dauko juice Mai sanyi a firinjin ya Sheikh ta kwalkwala kusan rabi ,ta dauki bottle din ruwa guda ɗaya ta yafa dankwalin abayanta ta fito wajen gate ɗin gidan tana ƙarewa street din kallo tana ɗan miƙe ƙafa tana kurɓan ruwan time to time.

Kamar ance ɗage kanki ta hango Adnan a ƙofar gidansa ya zauna akan kujeran roba kamar mai gadi yayi ma hanya tsuru da ido ,daga gani yana sone yaga dawowarsu Salima safely.

A hankali ta tako inda yake har ta tsaya bai sani ba saida ta katse shirunsa da cewa “Meye ita a zuciyarka?”

Firgigit ya ɗago yana kallonta “Me…me..kikace?”

“Meye matsayin Salimart ƙanwata a zuciyarka?”

“Anty ban fahimce ki ba…Salima makofciyata ce bayan nan ba saura sai mutunci”

Kafeshi da ido tayi tana son gano gaskiyar maganarsa ,amma sam babu ƙamshin gaskiya a yanayin yanda yake wuri wuri da ido na marasa gasky da son ɓoye wani abu.

“Ka tabbata?”
Muryarsa rauni yayi idonsa ya ciko da ƙwalla
“Eh mana anty ,Salima fa matar Sheikh ne tana da aure koda ace ina sonta ai ta haramta a gareni ,saidai kawai ina yaba ɗabi’unta ne,Salima mutum ce da duk miji zaiso ta zama matarshi ,Bakomai ina mata fatan Alkhairi ai”

Tsura masa ido tayi har yakai aya ya zarce da sharce ƙwalla ya rasa wata irin yaudararriyar zuciya gareshi ,da take cutar dashi wajen bayyana ma duniya son da yake mata ,abun na bashi haushi amma baya iya daurewa…..”

“Mun gode Adnan ,Ina maka fatan samun mace ta gari kwatankwacin Salima ta ”

Ta juya da sauri ta dauki hanyar gidan Salima ba tareda ta sake waigawa ta kalli Adnan ba ,tabbas ta tausaya masa ,rashin masoyi ba daɗi ,soyayya da matar aure ai masifa ne
A sarari take cewa “Bari Saliman ta warke zan ja mata layi akan wannan makocin nasu ,tunda dai bayi da matar da zasuyi zumunci to ta kiyaye masa , musulunci bai yarda da zumunta tsakanin mace da namiji ba ba”.

 

Oum Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button