Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 27

Sponsored Links

n Mata: 27
*Mtsew!* Ta tura mata tsaki, murmushi ta turo mata, sannan ta ce mata. _Allah ya shirya ki_ ta faɗa tana dariya. *Allah ba abin wasa bane, Yarona na rasa fa? A matsayina Na uwa kin ji yadda nake ji kuwa? Sai yanzu na fahimci irin kaunar da nakewa cikin!* _Koma mene ne ya wuce Allah ya baƙi na mora_ haka suka yi ta hira tana jin kuka yana taso mata, domin son da takewa cikin ƙara samun matsuguni a ranshi. A hankali ta sauka daga gadon ta nufi waje, bayan ta saka hula da sweatcoat. Tana jin kamshin tutaren Malik. A bakin can wurin zaman masu son ganin likita ta zauna, tana shafe kwalla. Tana wurin wasu couples suka fito da Babyn rungume a kirjin Uwarshi, uban yana tallafe da uwar, sai wani rawan jiki yake akansu. Ko abokansa ne da yan uwansu, suna haba haba da Babyn.
Haka kawai take jin kadaici, a hankali kuka ya kwace mata, me yasa bai kuma zuwa ya ganta ba, ko yayi fushi da ita ne? Cikin shashekar kuka ta d’ago kai, yana tsaye rike da sweatcoat dinshi, ya zuba mata idanu, da sauri ta mike, da wani irin sassafar ta isa gare shi, bude mata hannun yayi ya shiga, tana sake fashewa da kuka. Rungume ta yayi yana faɗin. “Sorry!” Rungume shi tayi tana shashekar kuka. “Zan tafi Keivroto ne, nayi missing flight shi ne dawo!” Kara rungume shi tayi tana kukan!” A hankali ya dauke ta cak ta zuba hannu a kafadarshi, tana sauke ajiyar zuciya. Bayan ta kura mishi idanu. “Kayi hakuri ba da gayya na zubda cikin ba.” “I knew that!” Ya faɗa a hankali, yaba zuwa ya kwantar da ita a saman gadonta. “Me yasa kika fita a wannan sanyin?” “Kana jin haushina ne?” Yake yayi yana gyara mata zaman lullubi, “baka ce min kome ba!” Kallonta yayi, na wani lokaci kafin ya ce mata. “Me zance?” Ya tambaye, kasa tayi da kanta tana jin kuka na zuwa mata. “Malik!” “Shiii ya isa haka, kwanta ki huta!” “Ina son babyna!” Kura mata idanu yayi dominya lura rigima take ji. “Wani baby bayan wanda ya zuba?” “Ina son wani ne!” Murmushi yayi ya ce mata. “Allah ya kawo masu albarka!” “No Ni yanzu nake so” wayar shi ce tayi kara, murmushi yayi a hankali ya nime wuri ya zauna. Ya fara waya, daga yadda yake wayar ta fahimci da mace yake, fashewa da kuka tai, ta zo ta fisge wayar ta buga shi da bango. Durkuswa tayi ta shige jikinshi. “Me kike so?” ” Ka dai na waya da wata a gabana” kara rungumeta yayi yana shafa bayanta. “Kince baki son cikin, me zaki yi da shi?” “Haka kake so na zauna cikin kadaici? Nima ina son abokin hira, nima ina son wanda idan baka nan zai zame min abokin hira!” Jan hancinta yayi yana faɗin.”idan muka rabu, sai ki haifi wani. Kin ga yanzu kin lalata min waya.” Wani irin kuka ne ya kwace mata tana kallon shi.
“Ni babyna nake so, idan yaso ka tafi ma kada na kuma ganinka!”
“Me yasa baki sona?”
“Bana sonka babyna nake so!” “Ok zan tafi idan ban dawo ba,me zaki yi?” “Zan fara sabon rayuwa zan manta da kai!”
“Shi kenan babyna ya tafi sai kiyi hakuri!” Rigima sosai ta saka ita dai ya nima mata baby, ya rasa yadda zai yi da ita baki daya bata gane yadda yake danne kanshi, amma taki fahimta. A hankali ya janyota jikinshi yana shafa bayanta, har ta fara hamma. Daukarta yayi ya daura a saman gadon. “Ina zaka gudu kaje, bayan baka gaya min yadda zan samo babyna ba”
“Zan yi tunanin inda ake sayar da Babyn sai a sayo miki!” Ya faɗa yana Sosa mata kai, a hankali barci yayi gaba da ita.
Kwantar da ita yayi, yana shafa fuskarshi. Ya koma ya zauna tare da daura daya akan ɗaya, yana kallon yadda take barci a dan takure. Tashi yayi ya kara dumin dakin sannan ya koma ya zauna yana me cigaba da kallonta. Yana zaune a wurin aka buga kofar, “Yes!” “Malik na kawo maka abin rufuwa ne!” “No muje gidan kawai!” Ya tashi yana me zuwa gabanta, sumbatar goshinta yayi yana shafa kanta. “Kina tare da babynki, hala kafin ki san da zaman shi hankali ya kuma shiganki” daga haka ya bar dakin, a daren jirginsu ya wuce Addis Ababa, domin jinkirin da aka samu, yasa shi dawowa asibitin.

Washi gari da wuri Ammyn ta zo asibitin, ta shiga dakin tana kallonta yadda take barci. Bata tashe ta ba har zuwa wani lokaci kafin ta farka, tana kallon Ammyn. “Ammyn ina yake?”
“Wa kenan?”
“Mayor mana” ta faɗa tana sauka a gadon, tana nufar ban daki, wanka tayi da brush, sannan ta fito dakin, ta zauna ta fara cin abincin.”Ammyn zan iya sallah? Na ga jinin ya tsaya.!” “Eh zaki iya sallah!” Ta faɗa mata, tana cin abinci. Idanunta yana kan kofar dakin. Tana nazarin yadda zata kuma samun wani cikin ne, daga nan sai ta rabu da Malik. Wani bahagon tunani da ya shige ta, shi yasa ta kudiri a ranta yau yana zuwa za a sallame ta, ta kuma kunna data ta shiga tambayar Hafsy!
*Hafsy wai an ce daga lokacin da aka yi bari, ana kuma samun wani cikin ne?*
Sakon ya tafi ya bada al’amari ya shiga ba a duba ba, sake tura mata wani tayi tana faɗin.
*Bana son iskanci ki bude sakona*
Nan na shiru, ganin sai jera mata ashar take bata duba ba, kawai ta shiga kiranta.
“Ke bana son bura uba, uwar me kike da ba zaki duba sakona ba?”
“Aiki nake ba wasa ba, please be having yourself, an gayyace ni wani aiki ne!”
“Ki bar aikin zan biya ki sama da abin da zasu baki. Duba sakona!”
“Gaskiya ba zai yiwu na duba wayar ba, domin kwalliya nakewa yar command sojojin Keivroto, ki taya ni godiya Malik ya min hanya ta hannun wannan Baturen abokin shi?”
“Kuna dating juna ne!”
“Hmmm bayan gaya miki ba, kawai dai na gaya miki abin da na sani ne.”
“Banza kawai ki duba sakona don Allah!”
“Ok bani minti ashirin zan duba!” Ta kashe wayar, ita kuwa Zeeno kamar ta shiga ta wayar tayi ta zubawa wacce akewa kwalliyar mari, tayi tsaki ya fi sau dari. Agogon wayarta da agogon dakin akan idanunta suke bugawa, kamar zata fasa ihu.
After like 20mins sai ga ta a Whatsp,
_Babban magana! Wai ma me ya faru har aka rasa cikin?_
Nan ta shiga bata labarin abinda ya faru, sannan ta tura mata, emojin kuka tayi tana faɗin.”ina son babyna ne!”
Murmushi Hafsy tayi tana faɗin.
_Yarinya you too late!_
*Bana son iskanci, ki gaya min ya zanyi?*
_Gaskiya na gaya muku_
*Babu wata hanyar da za abi ne?*
_kinga Zeeno wallahi ban sani ba, Malik ya fi ni sanin hanyar da zai kuma dirka miki wani cikin_
*Tun jiya da ya zo o ya sani barci, ban kuma ganin shi ba*
_Ba dole ba. Cewa kika yi baki son ganin cikinshi ya burge ni me shegen taurin kan tsiya_
*Kai Hafsy!*
_Mtsew_ ta rufe datar bayan ta tura mata sakon. Wasa wasa lokaci yayi tafiyar ba zata da zata kai ka inda baka zata ba, domin kuwa kwanaki sunyi ta haurawa har aka samu sama da sati sannan aka sallame ta, a lokacin ta kara yarda Malik ya tafi abinshi. Ranar tayi kuka for God sake, ta ji babu dad’i. Abu goma da ashirin ga Wahiba rashin mutunci take mata. Da bakaken magana, wannan abin ya dami Zeeno. Da ta gaji da mata rashin kunyar, ta mata duka biyu sai da ta suma, Sayyada Quddisiya bata yi magana ba, domin itama tayiwa Wahiba faɗa, amma taki ji, dake yar gata ce, ta kira Malik tana gaya mishi abinda ya faru. Shiru yayi kafin ya ce mata. “na san halinku daga ke har ita, Zainaba vata saurin hannu sai ka kure ta, sannan bata cin zalinka don tafi ƙarfinka, Anne ta fada min yadda kike mata rashin kunya, she’s my wife bana son rashin wayo da reni, idan na kuma ji zan sab’a miki!”

Kuka ta saka ta kashe wayar, kiran Wahida yayi ya ce ta kaiwa Zeeno, tana wance tayi sallama tare da mika mata wayar. “Second Mother, Abba yana magana!” Amsa tayi ya saka a kunnenta. “Maman Yara, naji anyi hukuncin!” Kuka ta saka masa tana karawa, taki magana. “Meke damunki?”
“Shi ne ka tafi ka bar ni?”
“Tow ya zanyi? Na bar abubuwa dayawa, kuma don ke na bari ba don kaina ba, farin cikin da na fara samu kin hana ni, likita ya ce a barki,ki huta shi yasa kike rigima damuwa ta miki yawa?”
“Ni yaushe zan kuma samun Babyn? Kullum sai nayi mafarkin ina bawa babu abincin shi, ga marana ciwo yake min.”
“Ciwon mara kuma?”
“Eh mana!”
“Ok Adnan zai kawo likita ta duba ki?”
“Ni bana son magani Alkur’ani kawai zata min.”
“An gama gimbiya!”
Haka suka sha hira sosai, kafin suka ajiye wayar, can yamma sai ga Adnan da likitan, ita tazo ta dubata, dake Malik ya gaya mata kome, bata gaya mata kome ba, magani ya bata, sannan tayi musu sallama, kiran Malik ya shiga wayarta.
“Dr ya kika ganta?”
“Tana lafiya, cikin ya fara kwarine, shi yasa maranta yake ciwo, da zarar ya kai wata biyar zuwa shida ciwon zai ragu, idan bai ragu ba, dole mu cire mata shi a 29 to 30weeks.domin ina jin bugun zuciyar Babyn yana yawa.”
“Allah ya sa mu dace, amma ita uwar tana lafiya?”
“Eh tana lafiya.”
Nan suka tattauna, kafin suka yi sallama ya kira Zeeno, ta fara mishi rigima ita ice cream zata sha yasan yadda zai yi da ita wallahi. Kiran ya katse ya kira Adnan, ya gaya mishi. Ya kirata ya gaya mata, kaya ta dauka zata saka, tayi ta kokuwa da kayan, karshe wandonta a iya cinya ya tsaya, bata san lokacin da ta kira shi tana kuka.
“Kuma me kike so?”
“Kayan sunki shiga ne?”
“Shi ne na kuka?”
Shashekar kuka ta ja, tana faɗin. “Kawai ba gaya maka ne, kayan sun ki shigana”
“Ki saka abaya mana!”.”Ni bana so ne!”
Ta faɗa tana kashe wayar ko sauraron shi bata yi ba, ta kira Hafsy tana kuka take gaya mata, kamar sun hada baki da Malik suka ce ta saka Abaya, kuka sosai take har da shashekarta.
Kafin ta ciro abayar tana hararanshi. Bra ta dauka zata saka, domin ta kwana biyu bata saka ba, ai kuwa suna de basu san da wannan zancen ba. Hawaye na zuba mata, ta dauka tana cusawa da zafi ya ishe ta wurgi tayi da shi, ta dauki abayar da hafvest ta saka sannan ta fito tana kallonsu. Kamar ba zata shiga motar, babu wanda ya bita, domin ta koyi bakin hali. Bata gayyaci kowa ba, tayi tafiyarta.
Haka suka jido kayan kwalama da makulashe,ta wuce daki da wasu wasu ta bawa atika ta saka a frij, sannan ta wuce dakinta, apple ta zauna tayi ta ci tana lumshe idanu, kamar ta cinye da yatsunta.

Kiran Malik tayi tana gaya mishi. “Kunna data ki nuna min na ganki!”
Kunna wayar tayi tana nuna mishi kome, sannan ta juyar da Wayar tana kallon fuskarta. Wani munafikin kalli yake mata kasa kasa, tayi kyau fatarta ta murje idan ya fahimta har da shi a masu takura mata, kirjinta yayi bala’in d’aga mishi hankali, fatarta tayi kyau wai wani glowing take. Kamar daren goma sha huɗu….
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button