Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 8

Sponsored Links

olume:8 behind the truel .
Ganin yadda take wasa da drinks din da aka saka musu ya ce mata.
“A matakin karatu me kika karanta?” Juyar da kai tayi tana b’ata rai kafin ta ce. “Diploma a business administration!” Kallonta yayi sosai sannan ya ce mata.
“Me yasa baki yi degree ba?” Watsa mishi harara tayi ta ce mishi. “Hala kaji a falo na girma, shima diplomar don kar a rena ni nayi, amma babu abin da zai saka ni abin da ban yi niyya ba.”
“Kinga kuwa ni degree na uku a fannoni daban daban, na farko akan course ɗinki nayi, na biyu akan tattalin arzikin kasa da na duniya, na uku akan siyasa da kabilanci. Yanzu ina dab da hada na hudu akan nazarin dan Adam!”

Tabe baki tayi tana faɗin, “hmmm! Tow me yasa baka yi karatu a cos daya ba, kabi ka bata lokacinka a kan kwasa-kwasai?”
“Ai ban gama baki labarin ba, ina da kwarewa akan!”
“Ka hana gaji da labarin digirin digirgir dinka, kai ko lahiranka baka tunawa sai aikin karatu da kashe mutane?!”
“Inji waye ya ce miki na kashe mutane? Eh na kashe su, sai dai Allah ya ce idan ba zaka iya hakuri ba ka rama daidai da abin da aka maka, ko ke da zaki bincika rayuwarki ta baya, Allah ne zai raba ki da mutanen da suka zalince ki.

Shi ɗaukar fansa ba kasafai ake bukatar shi ba, idan kayi hakuri zai wuce amma idan ba xaka iya hakuri ba ramawar yafi, duk da hakurin yafi ramawar alkhairi.”
“Tsakaninka da Allah baka danasanin kashe mutane?” Gyara zama yayi ya ce mata.
“Sam bana danasanin domin sun kashe min kowa nawa, sannan suka bani makami domin na daure kaina kina tsammani zan yafe musu?”

Kura mishi idanu tayi sannan ta ce mishi.
“Kana nufin kashe naka iyaye aka yi?” Gyara zaman shi yayi sannan ya ce mata.
“Ai shi ne cinikin rai, kuma Allah ya gani ban yafe musu ba, shi yasa na rama. Domin har gidan Yarin suka bini.”
“Kayi zaman gidan kaso?” Ta tambaye shi a tsorace. D’aga kafad’arshi yayi alamar Eh.
“Na shiga uku, kuma ka fito bayan shekara nawa?” Gyara zaman shi yayi yana faɗin. “Matsoraciya, na fito bayan shekaru ashirin da biyar!” “Kuma kana da shekara nawa ka shiga?” “Like 17 years!”
“Sha bakwai a tara da ashirin da biyar, shekaru arba’in da biyu!” D’age mata gira yayi yana faɗin. “Tow meye a cikinshi?” “Gaskiya i pity for you! A can ka haɗa duk digirorinka?”
“Eh a can nayi na farko da master! Na uku nayi shi a demark, yanzu ina yi nan Keivroto.” Gyara zama tayi tana faɗin. “Kuma kana zuwa class;” kallon yadda ta ɗan k’amk’ame jikinta yasa shi ɓalle botirin top din rigar shi ya janyo kekenshi ya zauna sannan ya matso har inda take. Ya ya daura mata rigar.
“Ko zamu tafi ne?” Ya tambaye ta,
Yatsina fuskarta tayi, sannan ta ce mishi.
“A’a ka bani labarin yadda kake atandin class!” Murmusawa yayi ya ce mata. “Zainab kenan.” Ya dan sosa goshinsa, sannan ya ce mata. “Ina karatu ne ta online, ba sai naje makaranta ba, bana buƙatar sai na shiga aji, amma idan lokacin Jarabawa yayi ina attending hall.”
“Yo ko da kudi zaka iya sayan jarabawar?”
“Ba dai ilmi ba, akwai masu saya amma yana da kyau, kayi karatun duk inda aka kai maka duka ka kare da kwarewa ba da baki ba.”
“Me yasa kake da kwarin gwiwa?” A hankali ya dauki kwalbar red wine ya zuba, sannan ya dauki cup din zai sha ta ce mishi.
“Wannan ba giya ba ne?” Dake ita normal juice aka kawo mata. Dariya yayi sannan ya ajiye cup ɗin ya ce mata. “Taya ina cikakken dan musulmi kuma bahaushe da ya fito kasar hausa na sha giya? Duk da mahaifiyata baturiya ce, amma bana fatar shan giya.”
Ya dauki kofinta ya zuba mata, kallonshi tayi sannan ta ce mishi. “Kada ka sani shan giya, bayan na hana harshena dandana na duniya, domin ina son naje na sha na lahira me masifar dad’i!”
“Allah ya baki hakuri, sha idan giya ne ki saka a kama ni!”
Kallonshi tayi, ya gyada mata kai dauka tayi ta sha, jin dandanon ba iri daya ba ne yasa ta ce mishi. “Hmm kuma yana da dadi!”
“Allah ko? Kika ce ana sayan ilimi?” Gyara zama tayi tare da saka hannunta dukkan biyu ta harde a Kirjinta. “Tabbas ana saya, ana saya da kudi ko da wani abu dai!”
“Gaya min, me ya faru?” Tura baki tayi tana faɗin idan na gaya maka, ba zaka ka min dariya ba.”
Murmushi yayi ya ce mata. “Duk abin da ya faru zan baki shawara, i by now we’re friends ko?” Gyara zama tayi, ta ce mishi.
“Dakyar na gama secondary school, domin a lokacin yara suka ganni kirana mahaukaciya suke, ko su kira me kashe mutane, na sha wahala a wurin mutane gashi ban san dangina ba, wancan gidan sune komi na, kuma nice kominsu. A lokacin na hadu da wata yarinya bayan na gama secondary school, lokacin da na shiga college. Ita take gaya min idan kana son pass sai ka bada cin hanci ko ka bari Malami ya kwanta da kai!”
“Kuma kin yarda kin kanta da Malamin?” Ya tambaye yana kasa da hannunshi, me dauke da cup ɗin, duk da na glass ne, karfin rikon da ya mishi ya janyo cup ɗin ya fashe a hannunshi. Girgiza kai tayi tana faɗin.
“Kullum nasihar Ammy na tsare mutuncina, sai dai na basu kuɗi. Ni bana cikin yan matan da suke bada jikinsu domin nasara, a lokacin na hadu da wani Malami shi kuma yace ba dan yi pass ba, sai ya kwanta da ni. Ni kuwa na tara yan daba suka mishi shegen duka.”
Ajiyar zuciya ya sauke, yana me sake fasashen cup ɗin, yana faɗin. ” Kin kyauta! A duk lokacin da mace ta bada kanta, domin faranta ran wani tow daga ranar na tsane ta.” Tura baki tayi tana faɗin.”ai ni ba yar iska ba ce.” Daga haka ta juyar da kanta.
“Bani hankychef a saman rigar nan!” Cirewa tayi ta mika mishi, ya ɗaure hannunshi, sannan ya ce mata.
“Naji VOGUE MAGAZINE sun cire hotonki a cover dinsu!”
“Hmmm! Dama ai ko basu cire ba, ni zan tafi har can na roke su, su cire hoton!”
“Saboda me yasa?”
“Saboda kazaman mutane da shaidanun bibiyar rayuwata suke, akwai wani mutum something Wazir yazo har da rungumata.”
“Kuma baki daki gaban dan iska ba?”
“Ai rikon bazata ya min, amma na mare shi. Ya ce zai dawo amma ni ma zan saka su Black su mishi mugun dukka!”
“Yawwa gara da kika kira min sunansu! A ina kuka hadu dasu?”
“A unguwar muka taso, Iyayen Black suna can wani kauye hari, sai Dundurosu a gaban kakarshi ya tashi iyayenshi sun rasu.”
“Sun yi karatu?” “Eh sunyi karatu suma diplomar ce, Black cos din mu daya. shi kuma Dundurosu ya karanci art ne!”
Murmusawa yayi ya ce mata. “Dundurosu yake meye sunan shi na asali!”
“Kabir haruna, sai Black Mas’ud, akwai Paul, ya tafi garin su wurin babanshi a can wani gari wai calaba;”
“Idan sun yarda sun amince, ki gaya min a waya shi Kabir zan tura shi Demark yayi aiki da kamfanin mu na can, shi kuma Black zan tura shi Fisto ina da babban gidan saukar baki ya rike a matsayin Manager, shi kuma Paul me ya karanta!”
“Shi aikin soja yake nima kuma har yau bai samu ba, shi ne aka ce ya kawo kudi, ya tafi garinsu kawo kudin.”
“Ki kira shi, ki ce mishi ya kawo takardunshi zan duba mishi.”
Kallonshi tayi dake ba zata iya shiru ba ta ce mishi. “duk me yasa kake ta basu aiki,domin na gode maka zan yi ba!”
“Nayi haka ne na raba ki da kowani d’a namiji da yake zagaye dake, ki rayu like princess! Ba kamar maza ba.”
“Ban fahimce ka ba?”
“Daga yau ni dake, mun fara soyayya kuma duniya zata shaida haka ne, shi yasa nake son duk wani namiji da yake rayuwarki na nisanta shi dake, domin kada ayi amfani da su wurin cutar da rayuwarki. Kawarki Hafsy ko? Hmmm! Na hadata da Elbashir shi me biyayya ne a gare ni ba zai ki ba, kasancewar ita ta fiki rawankai. Sone friends suna iya dawo da friend dinsu kasa ba tare da sun san da haka ba.”
“Taya zata dawo dani kasa?”
“Hmmm! Ta hanyar da baki zata ba, ba wai zarginta na ke ba, kudi shegen abu ne, babu abin da ba zai iya sakawa ba. Ban yarda ki fita ko ina ba, sai da umarnina.
Babu ke babu harka da yan sanda, babu ke babu fada a layi ko kasuwa, duk wanda ya tunkare ki, kalli can!” Ya nuna mata wani dogon gidan sama ya ce mata
” Dubi wuyarki!” A hankali idanunta ya kai kan jan danger din da aka yi points ɗinta.
“Rayuwarki daga yau, tana tare da ni ne. A duk lokacin da wani abu ya same ki, don take any action! My men there be with you, sannan wannan tracking devices ne, kada ki rabu dashi wanka ko ma meye kiyi da shi, da zarar any weapon ya tunkare ki, zai shaida min ko barci nake.”
“Duk me yasa haka?” A karon na babu adadi da yake jin wani irin tausayinta, ya janyota ta sake shiga hatsari sama da baya. “be a strong lady, as I know you. Kada tsoro ko kasawa ya sa ki fara feel guilty. Ba nace ina tare da ke ba?”
Gyada kai tayi, sannan ya cigaba da cewa.
“Amma ki sani ko ban kawo maganar aure ba, akwai mutanen da ba zasu barki ki rayu cikin salama ba, domin na san waye ni. Ina rayuwa ne cike da makiya, i hope kin fahimci Ni!” Gyada kai tayi sannan ta ce mishi.
“Hatta bindinka baka yarda da a shi ba?”
“Elbashir din ne bindina? Lallai yarinyar nan kin rena min Elbashir. Na yarda da shi dari bisa dari, kai dubu bisa dubu na yarda da shi. Idan kin ga Elbashir ya ci amanata tow wallahi wani abu aka mishi ni dashi ba. Har kwanan gobe Elbashir baya kwana a cikin gari sai a can Waterfall island. Na dawo nan ne kawai don ke!”
“Ni!”
“Yes domin an tab’a gaya min, matar da zan aura ita ce ajalina.” Ware idanu tai tana pointing kanta. “Yes kuma zaki zo ki canza min ƙaddarata! Tun daga lokacin da na ganki naji kece. Amma kuma ke ai cantract marriage zamu yi ko? Kuma babu zancen soyayya da tsoho!”
“Hmmm! Da nayi soyayya da tsoho gara nayi renon dan kwaikwaiyo.”
“Nima haka na gani!” Ya kalli agogon hannun shi ya ce mata.
“Muje mun ji dare!”
Kallon agogon hannunta tayi ta ce. “Sha daya saura!”
“Eh muje!” Haka suka fito garin ya fara sake iska me dad’i da sanyi. “Sai yaushe zaki kara bani damar mu sake haduwa?”
Tabe baki tayi tana faɗin.
“Wai! Ai ni ba zan kuma fita ba!”
“Ai shi kenan!”
“Mutumin tsibiri, na rike ka ko?” Murmusawa yayi, tare da bude mishi kofa ya shiga ciki.. itama kallonshi tayi tana faɗin. “Bindin malik kana murmushi mana, ka wani haɗe rai!”
Ta shiga tana kwantar da kanta, domin barci take ji, “ba zaki yi musu tsara ba?”
“Muje na gaji!”
“Jibi zan zo mu tafi shopping!” Juya kanta tayi tana faɗin. “Ka san me? Ni ba zan iya rayuwar nan ba, domin karya ce ire-iren waɗannan rayuwar!”
“Ni ne makaryaci?”
“No kai ban isa na kira ka haka ba, ni yar talakawa ce, wa ya sani ko Ubana dako yake kafin ya ciyar damu, kasan me? Irin wannan yanayin ga Yaran talakawa irina yana sawa ayi tunanin ko wani abu muka bada. Ƙarshe a ce kwadayi ya sani makalewa. Ina da gishiri ana bani manda!”

“Ko kina bada V ana baki I ba” kallonshi tayi.
“Kai amma baka da kunya;” ta rintsa idanunta, domin sai da tayi dogon nazari ta fahimci v da i……
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button