Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 3

Sponsored Links

Volume 3 My Sinner.

Kafin ta rufe baki motar ta shiga tangal-tangal, dira tayi dama basu saka mata handcuff fa, tana sauka kafin mutanen Malik su iso, Black ya iso da mashin ta haye bayanshi. Da masifafen gudu ya bar wurin. Baki dayansu suke baki suka yi, kafin su dismissed suka bi bayansu.

Sai dai kamar dama jiransu suka su bi bayansu, kawai shaidanun Yaran nan, suka shiga bawa yan sanda da mutanen Malik.
Duk da tana bayan mashin din sai da ta ce.
*Kai gayyan awaki, idan kun isa ku kama ni,idan baku iya kama ni ba ku gayawa Malik ya taso da kanshi ya kama ni, don dai naci dubu sai ceto;” ta musu gwalo, suka kara gaba a guje. Ai ya kamata a ce sun tafi amma Zeenobia don masifa sai da ta bubuga bayan Black, suka tsaya kusa da motar Zulfa, ta wani d’aga mata gira.
“Ohohoho, yar sanda ki cire rigarki ki fara sayar da fiyo wata, idan kin isa ki kama ni ”
. Suka manna a guje, tana dariyar shakiyanci da mugunta, domin dai ta gara kansu. Sanan ta wuce abin ta. Koda suka bi bayansu, su b’ace babu al’amarinsu. Abin ya bawa zulfah haushi, daga ita har mutanen Malik, wato duk yadda ka kai da takaici dai an kunsa maka, mutanen Malik ganin laifin Zulfah suka yi yayinda Zulfah take ganin laifin mutanen Malik. Don kafin kace me fada yana shirin shiga tsakaninsu.
★★★
Demark.
*07:49 pm*
Dai dai lokacin da jirgin Malik ya isa garin kenan, dake akwai Yaran Elbashir a garin musamman masu kula da Ayyukan Malik na kasar, sune suka zo tarbanshi.
A hankali aka buge jirgin domin har bakin kofar aka kawo motarshi, daga yadda aka zuba jami’an tsaro zaka fahimci Malik yana da karfin da ba kowa yake da shi ba, sannan akwai kyakyawar alaka a tsakaninshi da mutanen. Ai ko babu kome garin mahaifiyar shi ce, sannan yana da lasisin zama a kasan domin shima haifaffen kasar ne. Sannan kuma an bashi damar shiga kasar duk lokacin da yaso domin dai yana kawowa kasa cigaban da ake bukata.

Kuma halo yana da damar yadda yake so, don haka tun kafin ya isa gidan da yake zama aka fara mishi tarba na musamman. Duk da saukan dare ne, haka suka wuce da shi fadar shugaban kasar, ya fara kai gaisuwa sannan suka gaisa kafin suka tattauna. Da zai bar fadar shugaban kasa ya ce mishi.
“Nasan ka gaji! Akwai masu kula da kai, zasu maka tausa yadda kake su, an tura su gidan ka. Ka ji dadinka!”
“Godiya nake.”
Haka yayi sallama da shugaban kasa, ya nufi wurin motarshi, aka wuce da shi gida. Juyawa Security Adnan yayi ya ce mishi. “Sir ana kiranka a waya?” Ya mika mishi wayar. “Anne! Kiyi hakuri sai na huta, ki cewa su Angels sai zuwa gobe in sha Allah!”
“A’a babu ruwana, gaya musu da bakinka;” ta fada tana miki musu wayar..”babys kuyi hakuri ba iso karfe takwas saura, ko sallah isha ban yi, na gana da shugaban kasa, yanzu a gaji!” Kamar zata yi kuka ta ce mishi. “Ok Dadi!” Daga ta mikawa Wahiba wayar. “Dadi, kasan mun d’aga bikin karin shekarun mu sabo da kai, me yasa kai ba zaka cika mana alkawarin mu ba.”
“Sorry baby, zan zo gobe in sha Allah!”
Kashe wayar yayi, domin Wahiba tafi Wahida rigima, haka ya isa gidanshi da yake wajen birnin.
Koda ya isa ruwan wanka ya damu an tara mishi, sai da ya cire kayanshi ya sa bathtub, ya nufi ban dakin ya samu ruwan yana tururi, an zuba flower din rose. Yana fitar da wani irin kanshi. A hankali ya shiga cikin ruwan,. Bayan ya cire rigar shi.

Nutsewa yayi cikin ruwan, ya ɗan dauke numfashinsa, sai da yayi second talatin, ua fito yana sauke ajiyar zuciya. Shigowar Maidah, ta dauki shower gel, ta shifa mishi. A hankali musamman kafad’arshi zuwa kirjinshi. Bude idanu yayi ya rike hannunta. A hankali ya ce mata. “Jeki ya isa haka”
Sake hannunta yayi ya fumita daga dakin. Kafin ya fito ta shirya mishi abubuwan da yake bukata, sai da ya jima kafin ya fito ko ina take bai kalla ba, bai ma san dalilin da ya sata zaman jiran fitowar shi ba. Fuska ya daure ya ce mata. “You can go;” tashi tayi ta dauki kimono ta saka a gaban shi.
Tana fito yana dauke ajiyar zuciya, duba kayan sanshi yayi ya ciro robar magani. Watsawa yayi a bakinshi ya shiga taune su, yana hàdiyewa, yabi da ruwa yana dauke ajiyar zuciya.

Koda ya gabatar da sallah isha, tea kawai aka kawo mishi da cookie. Yana ci yana duba sakon da yake cin karo da shi martanin da Khuldu Jahid Khan, ya ce zai kai mishi nan da ba da jimawa ba.
A hankali ya shiga shafinshi na tweet ya ce.
*Ina son na tsaftace Keivroto, don haka ina rokon al’umma su tsayar da tunaninsu aikin mu! Bana cikin masu Kasuwancin sayar da al’ummarsu. Kamar yadda Khuldu Jahid Khan da mutanenshi;*
Mayor Malik Menk Jordan.
Lokacin da Malik yayi posting din gidajen jaridu, suna nan dama jiran takunshi suke kuma kai tsaye yake harba sakonshi, kafin wani lokaci an fara screen shot ana turawa gidan jaridu, kada ku manta Malik baya kasar, kiranshi da wasu manyan mutane suke yi, yasa shi bada umarnin a rufe KJK groups tv, da gidan rediyo dinsu.

Aikuwa hankalin kowa ya tashi, sannan kafin ya kwanta. Ya rubuta.
*Zan maka sassauci! Zan biya ka asarar da kayi, ka mikawa hukuma mai laifin da yake bayanka* daga haka ya kashe wayar baki daya.
Kwanciya yayi uana yana sauke ajiyar zuciya, sai dai me? Baki daya daren barci kaurace mishi yayi yana son lallai yayi barci, amma ya kasa.
Karshe tashi yayi zaune yana kallon yadda kome yake faruwa, jan kekenshi yayi ya hau, sannan.ya nufi ban daki.

Alwala yayo ya zo ya bude jakar shi, ya shimfida abin sallah, ya shiga gabatar da sallah. Haka ya raya daren nan da bautawa Allah. Har kusan karfe uku, sannan ya kwanta. Barci yayi gaba da shi.

***
Washi gari bayan ya idar da sallah asuba, ƙwanciyar shi yayi sai karfe sha daya na safe ya farka, ya nufi ban daki, ya wanka yayi ya fito, yana shigowa dakin ya shiga shiri yana nazarin Elbashir da bai kira shi ba.
Yasan yanzu dare ne a wurinsu, don haka ya kyale shi, ya shirya sosai sannan cikin nutsuwa. Vaseline ya sha domin shine man shafawar shi, yana gamawa ya saka farin rigar material, an yiwa rigar ɗinkin senator suit, fari ne sosai rigar kuma shara-shara sai bala’in tsada.
Don har kana iya hango singlet din cikin rigar, trouser dinshi baki ne. Material din kaftani. Me karfi sosai sai wata hular da ya saka, ya fito wani like Igbo Men.

Takalmin Saint Laurent shoe, shi kanshi kallon kanshi yayi a madubi, a hankali ya shafa kasumbar shi, wadanda rabinsu sunyi fari sosai, murmushi yayi maganar Zeeno ya fado mishi a rai. *Ka daina abu kamar yaro, idan kayi haka kyau kake min, ni kuma haushi kake bani* shafa kanshi shi yayi yana lashe kakkauran lips ɗinshi, man Vaseline ya shafa a bakinshi.

Dauko imperial Majesty, shi ne last abin da ya fesa, har ga Allah ganin Zeenobia yasaka mishi kwadayin aure,. Aure yake bukata musamman idan ya tuna yadda suka yi a rangama da abin da Zeenobia ta mishi. Tsigar jikinshi ya mike har tsakiyar kanshi yake jin wani irin motsi. Bude side bed din yayi ya ciro maganinshi ya shiga hàdiya. Sannan ya nufi wurin water dispenser ya dibi ruwa ya kora. Sannan ya fito daga dakin bayan ya ajiye kofin.

A hankali yake tura kekenshi shi, ya iso falon. “Good morning Sir!”
“Morning Adnan! Ya iyalinka da Mamanka?” “Suna lafiya!” Shiru yayi yana son mishi magana amma kuma yafi son a tambaye shi, kamar ba zai magana ba.. “how about Jalilah!” Da sauri ya ce mishi. “She’s fine and healthy!” Sannan ya sunkuyar da kai. “what she don now? Ko har yanzu tana karuwancin da kawalancin ne?” Girgiza kai yayi yana faɗin. “No sir wancan satin ta sallame kowa.” Cizon lips ɗinshi yayi ya ce.”kai ni estate!” Yanzu idan ya ce ya tuna daga SIN din shi Allah zai yafe mishi kuwa?

Yau da ya sauka a garin nan, bai kyautawa kanshi ba. Domin dai shi ya fara lalata Jalilah. Sannan ya koma gefe bayan abun da ya faru da Nuratu ya zargeta har da kiranta karuwa. Bayan yasan kome shi ne silar tarwarsewar rayuwarta. Taya ma zai iya zama da ita, bayan abin da ya faru har hoton Jalilah aka kawo mishi, da makiyinshi, abun da ya fusata shi kenan ta tafi ko ya kashe ta. Domin ya tsaneta.

“Sir muje ko?” “Yawwa Adnan. Kawunka ya kiraka?” “A’a bai kira ni ba.” “Idan ya kira ka, let me know!” “Ok Sir!” A hankali suka shiga tafuya har wurin motarsu. Tunda ya shiga motar, rayuwarshi ta baya take son dawo mishi, kokari yaƙe ya binne kome ya cigaba da rayuwarshi amma ina, tsoron shi daya ka da Allah ya kama shi da laifin abinda ya aikata. Suna isa estate tun kafin ya isa kofar gidan, ya hango Yaranshi. Wani yalwataccen murmushi ya sake. Kamar nuratu ce a tsaye a wurin.
Tsayarwa da motar tayi, yasa suka fara rige-rigen bude motar. Suna budewa, Adnan yana kawo kekenshi. Ma hankali ya motso tare da hawa kan keken, rungumar shi suka yi. “Oyoyo Dadi!” Rungumar su shima yayi yana faɗin. “Happy to see you my angels”
“Dadi I pass my test!” “Masha Allah!” Kallon Wahiba yayi tare da lumshe mata idanu.. “Me too Daadi!” “Anne Yarana sun girma saura aure fa!” Rufe fuskarsu kayi. Kallon Nadrah Khamis Shatima yayi da ta koma gefe tana kallonsu.

Shima kallonta yayi yana murmushi, , cikin gidan suka nufa tare da cewa. “Daadi, yau muna tare da kai har gobe.” “No da la’asar ina da meeting da shugabannin yan kasuwan kasar nan” “but Dadi mufa.”
“Ka da ku damu, zan d’aga lokacin sai dare shi kenan yayi muku.” “Eyeeeeee Daadi!” Inji Wahiba, dama ita kan Sayyadah Qudussiyah ta fada munafuncinta baya motsawa sai ta ga Ubanta.

“Dadi yau Ni zan maka tuwoo miyar kuuka!” Dariya yayi yana kallonta ya ce . “Ke ce ai tuwoo miyar kuuka! My Angel har yau tsinewa Hausa kika fa!” “Ok Dadi zan saka mishi blessing;” “ke tafi can bagwariya, muje ka ci abinci domin nasan baka karya ba!” Murmusawa yayi ya ce mata. “ai kuwa dai!” Nufar table tayi, Yaranshi suka zagaye shi suna bashi abinci.
Wannan ya mika mishi ta nan, wannan ta nan. Sai da suka ji yace ya koshi suka kyale shi, ya ce musu. “Ku shirya mu shiga gari!”
Haka kuwa aka yi, da gudu suka wuce dakinsu. Tare da bugawa Maidah kofa, bude kofar tayi tana. “Lafiya Wahida?” “Kizo zamu je yawo da Dadi!” “Bari na gani” ta rufe dakin ta kira Uwarta. Ta gaya mata.
“Maza shirya sexy dress!” Ok Maama!” Haka yayi shigar wanda rabin Kirjinta a waje, kusan ita ta cinye musu lokaci, kallon agogo yayi ya ce musu. “Angel pass two zan yi sallah sai na idar zan turo a dauke ku!” Kwalla ne ya cika idanun Wahiba . “Muje Daadi babu wacce ta isa a bata mana lokaci.” Ta fada kamar zata fashe da kuka. Can suka ji karar”kwas-kwas-kwas!” Juyawa suka yi suna kallonta, kafin sake baki ganin yadda suka mai da attention ɗinsu kanta, ta glass din Adnan ya ce mata. “Koma ki saka abaya kamar yan uwanki”

Jikinta ne yayi sanyi, fashewa da dariya Wahiba. Irin dariyar bosawa har da niman wuri ta jingina da piilar gidan. Can kuwa sai gata fuskarta a haɗe, tana wani dauke kai kamar ba ita, sannan suka shiga motar bayan Malik Wahiba da Wahida suna motar Malik.
“Daadi yaushe xaka yi aure? Na gaji da zaman nan kasar!” Inji Wahida. “Na kusa! Amma kuma ba naji Gran Mother tana faɗin cewa akwai maganar ku da Nadrah Shatima ba!” Juyar da kanshi yayi yana faɗin. “Zan yi in sha Allah!”
*A’a Malik! Za a fahimci abin da ya faru, don Allah kada ka min haka ina sonka amma bana son wannan abin don Allah!*
Idanunshi yayi bala’in tara kwalla,
Kasa sakewa yayi baki daya hankalinsa, yana kan Yaranshi yaki sake jiki ya kula su Nadrah. Mika mishi Americano coffee ta yi, d’ago kai yayi ya ce mata. “Thanks Maidah Sheikh!” Murmushi tayi mishi tare da mika mishi cup din, “bana shan sugar.” “I know.” Ta fada a kunyance..
*Ya Allah forgive my Sinner* abin da ya furta kenan a kasar zuciyarshi…..
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*

*Update safe zaku na samun 3 readmore in sha Allah, na dare in sha Allah zai na kai 5 readmore bi izinillah👏*

Black Arab🧕🏿

Leave a Reply

Back to top button