Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 25

Sponsored Links

25 pregnancy
Karfin fisgota ya janyo mata kullewar mara, tare da jin bugun zuciyarta sauri-sauri, rike shi tayi tana jin wani irin zazzaɓi tare da bugun zuciyar lokacin guda, bata san lokacin da ta rungume shi ba. “Are you okay?” Ya tambaye ta, juya kanta tayi tana kara rike shi gam, zufa yana karyo mata. “Ci…ki…na” ta faɗa dakyar tana rike shi, kasa magana furta kome yayi ya ɗauke ta cak, ya wuce ciki da ita, kwantar da ita a kujera yana me zama kasa. “Meke damunki!” “Kasar cibiyana, ya daure?” Ta faɗa tana cizon fatar bakinta. Riko hannunta yayi ya ce . “Ko muje asibiti ne?” Juya kai tayi ta rasa meke mata dad’i, komawa yayi ya kuma shiga dakinta, kafin ya kuma fitowa, ya dauke ta cak suka fita daga gidan. Wani irin tausayi take bashi, domin baki daya ta kasa magana, sai zufa take. Ganin yadda zaman ya gagareta yasa shi kwantar da sit din. Yana mugun gudu, har suka isa asibitin. Daukarta yayi yana kiran “Doctor!!!” Yana rungume ta ita. Da sauri suka nufe shi.
“Ina likita?” Ya kuma kara kwala musu kira, da gudu suka turo gadon, aka kwantar da ita. “Me ya same ta?” “Oh she’s bleeding.” Suka faɗa da sauri aka nufi emergency room da ita, “what’s going on?” Ya tambaye su a fusace, “Calm down! ” Suka dakatar da shi, da sauri wasu nutsu biyu suka fita, can suka kuma dawowa da blood bank, suka shiga cikin dakin da aka.kwnatar da ita, Kiran Elbashir yayi a waya, “Bashir!” “Na’am Malik lafiya?”
“Zainab ba lafiya!” “Gaskiya ta cika ciwo” “Jini take zubarwa!” “Subhanalillah, gamu nan zuwa!” Ya kashe wayar yana kallon yadda suke kaiwa da komowa. Yana zaune ta daura daya a kan daya, ya dunkule hannunshi ya saka a.kasar habbarshi.

Har su Elbashir suka iso, yana zaune he shock, suna zaune likitan ta fito, tana yarfe hannu. Mikewa Malik yayi yana kallonta, ya kasa magana baki daya. “Sir mun bata bedrest, damuwa da gajiya idan da hali, a dan rage yawan sexual affairs da ake, a dan bawa cikin lokaci yayi kwari. Idan kana son ganin yadda zuciyar Baby yake bugawa sai mu shiga ka gani amma daga uwar har Yaron,suna cikin koshin lafiya.” Ƙasa motsi yayi, bakin shi yana rawa ya ce. “She’s pregnant?” Ya fada kamar me tsoron a ce karya ne babu cikin. “Yes!” Ƙasa yarda yayi ya kalli Elbashir ya ce. “Kaji Zainaba tana da cikina wai cikina ne? I gonna be a Father!” Wani irin abu yake ji, dama haka uba yake when aka yi gaya mishi ana dauke da babynshi, ko kuma shi ne yake jin haka, kasancewar ya tsufa bai haihu ba.
“Alhamdulillahi!” Ya furta jikinshi yana rawa, jikinshi yana kerma kamar zai tashi sama. Ganin yadda ya gigice da farin ciki nurse din ta kuma sake kara mishi wani ta hanyar kaishi dakin ya ganta. Sannan ta kuma mata wani scanning ɗin tana faɗin. “The baby is weak, saboda abubuwan da uwar take fuskanta na damuwa. A kyale uwar ta huta Babyn zai samu kulawa na musamman!” Gyada kai yake yana kara kallon Zeeno.
“Thank You doctor!” Murmushi yayi yana kallonta. Baki ya kasa rufuwa, kalmomin da zai amfani da su na godiya sun yi ƙaranci a bakin, zama yayi ya gaban Zeeno tare da kai hannunta a gefen fuskarshi. “Zainab i love you!” Ya furta a hankali yana kara jin wani irin kaunarta, ga ta dauke da babynshi. Barci take sosai. Shigowa dakin Ammyn tayi tare da Sayyada Quddisiya, dai Zulfah da Jalilah. “Wai ciki ne da ita?” Zulfah ta tambaye su.
“Ba wai bane cikin ne da ita, tana da da cikin Malik!” Kallon Zeenobia tayi tana ta barci kafin ta ce musu. “Ina mamaki baby sister da ciki!” Ta faɗa tana dariya, irin abin y zo mata bazata. “Ba a mamaki da ikon Allah, kome zai yi domin tabbatar da ikonshi.”.
Dake dare ne, dole wasu suka tafi, Malik kan sai da suka yi da gaske, ya saka kai ya tafi. Karfe biyu na dare ta farka. Tana jin yunwa. Kallon Ammyn tayi tana kan abin sallah. “Ammyn!” Ta kira sunanta a hankali, juyawa tayi ta kalle ta, kafin tayi magana Malik ya danno dakin,ashe bawan Allah nan bai tafi ba, cire ruwan yayi ya ɗauke ta cak. Kallonshi tayi sannan ta maida kanta kirjinshi. Shafa fuskarta yayi lokacin da suka shiga ban daki. “Likita ta ce ban da aikin wahala!” A hankali ta cire pant dinta, ta zauna tana fitsari. “Ni kan ka fita zan yi pupu!” “Tab’a na fita garin nishi ki fitar min da D’a?” Bata fahimci me yake nufi ba, don ta fahimci ba zai fita ba.
“Malik fita don Allah!”
“Wallahi bani fita! Ki ja min masifa.” Haka kuwa ta gama fitsarin, ta mike zata gyara zaman pant dinta, yayi maza ya gyara mata. “Bana son janyowa kai masifa, don Allah babu ruwanki da yin kome ni zan miki na gaya miki.”
Gyada kai tayi, domin bata da karfi, suna fitowa ya ajiyeta a gadon. “Me zaki ci?” Komawa tayi da baya ta kwanta tana lumshe idanunta. “Ina son kunun alkama, da kosai!” Kallonta suka yi daga shi har Ammyn. ” A ina zamu samo miki wannan kayan?” Murmushi yayi ya ce mata. “za a samu bari na fita.” Haka ya fita cikin daren ya shiga yawo, yana niman any African restaurant. Kamar yayi hauka, dakyar ya hadu da wasu yan Ghana, ya sayo kunun. Kafin ya iso yayi sanyi. Koda ya zo ya samu tayi barci, rike abincin yayi yana kallon yadda take barci.
“Ammyn bari na jira a waje!” Ya fito ya zauna yana kallon mutanen da suke shige da ficce. Har wurin karfe biyar na asuba . Kafin ya nufi wani karamin masallaci yayi Sallah ya dawo ya samu bata farka ba. “Malik ko zaka tafi gida ka huta ne?” Girgiza kai yayi..”tow ni ya zamu yi, kwana kayi baka yi barci ba, kuma ka ce ba zaka ka kwanta ba.” “Shi kenan zan tafi zan dawo karfe sha daya in sha Allah!” “Allah ya kai mu” daga haka ya fita, itama Ammyn ta kwanta ta huta, sai wurin goma na safe suka farka, shigowar Wahida.
Matakin farko da Zeeno ta fara fuskanta shi ne, yawu yaki tsayuwa a bakinta, da farko ta zata rashin brush ne, sai da ta wanke bakin ta fito ta gane ba daga bakinta ba ne, a’a wani yanayi ne na daban da ta tsinci kanta a ciki. Kunun da ya kawo mata, Ammyn ta nuna mata, taba gani nmta fara yunkurin amai.
“Sannu kin ji!” Gyada kai tayi tana kallon kular da Wahida ta zo da shi. Budewa yayi ta ga arish, soyayye sai farfesun kifi. Dakin ya dauki kamshi. Sai dai me madadin taji kamshin sai ta fara jin kamshin ta cika mata hanci ta fara yunkurin amai. “Ikon Allah. Haka zamu yi da kai bawan Allah? Ba zaka bar yarinya ta ci abinci ba?” Hawaye ya zubo mata, tana son cin abinci amma ba hali, a irin wannan halin Malik yazo, yana zuwa ta fashe da kuka. “Mayor!”
Kamar ya kanta ya haye kanshi, ya riko hannunta. “Babynbaby me kike so?” “Yunwa nake ji.” Ta faɗa muryanta yana rawa. “Me za a kawo miki?” “Baby duk abinda aka kawo min zan ci”
Gyada kai yayi ya fita can dai gashi da fruit. Ya wanke mata, sannan ta fara cikin apple, tana kallonshi. Sai da ta cinye tass sannan yayi gyatsa. “A kara min!” Mika mata avocado yayi, ta shiga ci tana lumshe idanunta. Har ta cinye, tunda ya gano abinda take so. Shi kenan ya samu sauki idan ya fita zai kawo mata apple da avocado da ayaba. Sam bata gajiya da cinsu. Kwana uku a jere tana cin apple da avocado da ayaba, ai kuwa a ranar na hutu yana shigowa ta ce mishi. “kai mai da shi bana son shi, grapes nake so, ba pink din ba, green din nake so”
“An gama ranki shi dade” ya fita da shi, can sai gashi ya kuma dawowa dauke da grapes.

….. Zama yayi yana ciro plat ya fara kokarin zuba abincin yana kallonta. “Ko a sallame mu,mu koma gida ne?” Girgiza mishi kai tai tana faɗin.”Wurin Ammyn zan wuce;”
“Hmmmm! Ba zan iya ba!”
“Don Allah” ta faɗa a marairaice, girgiza mata kai yayi. A haka suke ta hira har ta gama, “Mayor! Ka zuba min nima ya ji miyar sosai.”ta jima bata ci abi cikin ba, na yau kuwa taji ance Mama Jalilah ce tayi, har da soyayyen planter. Haka ya zuba mata, tana tana tsoron kada tayi amai.

Har ta gama bata ji amai ba, sai ma jin dadin girki. “Mayor abincin yayi dadi ko zaka kara min!”
“Kada ki min amai”
“Ba wani amai da zan yi, please kara min.
Haka ya kara mata, taci ta koshi. Sai dai kuma tana gama cin abincin, ta fara yunkurin amai. Haka ya dauko mata kwanon aman tayi sosai. Har sai da jikinta yayi laushi, kwanciya yayi tan nishi.
Wasa wasa sai da Zeeno t kwashe wata biyu d sati Uku, kafin aka sallame su.

Gidan Sayyada Quddisiya aka kaita, a ranar taga soyayyar da bata taba gani ba, wani irin nutsuwa take ji, amma ta gefe guda bata yi na’amar da cikin jikinta ba. Ranar da take da kwan biyu da dawowa ya zo ai mata. Kiri-kiri ta ce mishi. “Ni da zaka taimaka min a zubda cikin nan gaskiya ban yi na’am da shi ba.” Kura mata idanu yayi ya ce mata. “Idan kika ce baki son gani na yarda. Amma idan kika yi wani tunani mara tushe akan cikin, sai na baki mamaki! Ina son abuna, halataccen jini na ne a kasar maranki!”
“Bana son shi, cire shi zan yi bana son shi ba zan.tab’a haihuwa da kai ba.”
Ta faɗa da karfi tana ihun da ya ja hankalin kowa na gidan, “na gaya maka , ka raba ni da shi ko na sha magani mu mutu baki daya da cikin! Ban shiryawa zama da kai ba!”
Sake baki yayi yana kallonta idan wani ya ce mishi zata yi mishi haka, ba zai yarda ba amma yadda take mishi a akan cikin yasa shi zuba mata idanu. “Ok kiyi duk yadda ya miki!”
“Zaka sha mamaki kuwa wallahi ba zan bar shi ba” takaici ya sa shi barin dakin bai shirya ba, domin ranshi ya masifar barci, ya tsani kayan haushi…..
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM]

 

Leave a Reply

Back to top button