Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 42

Sponsored Links

42-“ZAINAB!” Ya kuma kiranta in hucky voice, wani irin kuka take. “Talk to me! Baby Girl!” Kara sake mishi wani sakaltacen kuka tayi. “Oum Hassan!” Ya kuma kiranta. Jin wani abu tayi a tsakiyar kanta yana wani azabar yawo. “Abu Hussain!” “Wa Maidah!” Ya karasa mata, bata san lokacin da ta kuma sake mishi wani munafikin kuka me, cuccure da shashekar kuka ba, “Ya isa haka, gaya min me ya saki kuka? Kina niman wani abu ne?”
“Abu Hussain aure zasu min!” “Tow Queen Zeeh Allah ya bada zaman lafiya!” Bata san lokacin da ta wartsake daga kukan ba ta ce mishi. “Ka sake ni ne?” “Hmmmm! Me zance ai kin ce baki sona, so na baki damar kiyi kome.” “Amma auren da zasu min akan aure!”
“Tow ni yanzu zan tafi masallaci.”
“Ban gane ba?”
“Ki musu biyayya kawai.” A wani mugun rud’e ta ce mishi. “Mali….Abu Hussain!”
“Sai kiyi hakuri.” Ya kashe wayar, ta kira shi ya fi sau goma bai sauka ba, daga karshe ta mishi text. Amma mutumin nan bai dauka ba, asalima share ta yayi, kamar tayi hauka. A ranar tasan babu kome a cikin taurin kai da kafiya. Baki ɗaya kamar ta mutu ta huta, bata san me zata yiwa Malik ba, amma ta roke shi da Allah amma yaki sauraronta.

Ta kira Elbashir a ranar yakai sau goma, shima amsa daya ya bata, tayiwa iyayenta biyayya. Bata kuma sanin ta kashe kanta ba, sai da ta kira Sayyada Quddisiya ya roketa akan tayiwa Malik magana, ta ce ai yanzu shima maganar aurenshi ake don haka tayi hakuri ta zauna da wanda iyayenta zasu bata, a cikin kwana ɗaya, sai da tayi wani irin ramewa. Yaran ma baki daya kasa gane kanta suka yi, karewa wurin Zulfah suke, wacce ake ta hidimar baki, amma idan kaga yadda ta rungume Yaran ita da Ummi yar Gwaggonsu. Domin uwarsu bata da lokacinsu.

Kiran Alhaji Mustapha tayi, ta gaya mishi abin da yake faruwa. Shiru yayi kafin ya ce mata. “Yanzu zai abin da zaa yi shi ne, ki kwantar da hankalinki zan kira Malik din naji matsayinki.”
“Don Allah ka taimaka min Kawu!” “In sha Allah!” Daga haka ya kashe wayar,. Sannan ya kira Malik, yadda Malik ya mishi bayani shima ya gamsu, don haka bayan sun gama waya, ya kirata ya gaya mata.
“Kin ga koyi hakuri, tun farko ya dace ki san cewa ba kome kake samu ba, sannan ba kowa yake iya hakuri ya saukar da kai a zauna lafiya ba, lokacin da kuke samun matsala ya baƙi hakuri ki fahimce shi, amma kika ki. Shima wannan shi ne damar shi, domin ya samu wacce take girmama shi, kuma zata rike shi a duk yadda yake mata. Zainab iyayen mutanen kirki ne, amma ke kin samu Malik kika yi ta janshi a kasa kina mishi abin da ranki yake so, Zainab Malik ya so ki tsaki da Allah, amma ke sai da kika cusa mishi kiyayyarki.

Ba kowacce mace bace take samun namiji irin Malik ta sake shi ba, amma kin same shi, kin watsar da shi ai ko bai haife ki ba, ya ci darajar igiyar aurenshi da yake kanki. Ya turo min da sakon rabuwaku,tun tuni ya jima da rubutawa ya ajiye miki jiran wannan ranar, Yaran kuma yace yana jiran su cika shekara biyu zai zo ta dauke su. Amma ni nace mishi ya kyauta, kuma mun gode. Mutumin da bayan rasuwar Iyayenku shi ya kawo Zulfah har nan, sannan ya nimo dangin Mahaifinku ya hada ta dasu.

Mutumin da har kwanan gobe, bai yi barci ba, Yana can yana niman Fahad wanda shi ne ya kashe iyayenku, Maahifin Amjad Fahad, amma dake ke jahilace, kin zauna kina wulakanta shi, Yan waye gari ya waya? Waye ya rasa damar shi? Ke ce don haka kiyi hakuri ki rungume ƙaddarar ki, Allah ya baku zaman lafiya ”
Zuwa yanzu ta kasa kuka, sai ajiyar zuciya take bata san cewa tana masifar kaunarshi ba, sai yanzu da take ganin kamar ta rasa shi, a hankali ta fashe da wani irin kuka, sannan ta kira Malik din.
“Don Allah ka mai da ni dakina! Kayi hakuri zan girmama ka, zan maka duk abin da kake, wallahi ba zan tsallake duk abin da kace ba.”
“Zainab ba sona kike ba, kina bukatar na kasance dake ne, idan na biya miki bukatarki zaki mai dani abin tozartawa. Don Allah ki kyalr Ni”
“Me yasa ka ce zaka jira kirana daya tak? Me yasa ka sanya min yakinin cewa idan na kiraka kaddarata zata sauya? Me yasa ka saka min yarda cewa kai kawai zaka kawo min dauki a duk lokacin da bukaci agajinka.”
“Saboda ko lokacin da kike tsammanin kece kika kashe Ayuba da Wasim ba ke bace. Tabbas kin dake su amma ni ma saka aka karasu, duk wanda kika tsammanin kin kashe shi, nake bace. Ni na aikata haka. Saboda sun lalata min suna kuma sun tab’a min matata da idanuna suke kanta, Ki tambaye Ammynku ba haka kawai, Alhaji mahaifin Abbas yayi adopt dinki a gidanshi ba, ni na bashi Amanarki.

Zainab ni ne inuwarki, ina bibiyar rayuwarki da duk motsinki da kike a cikin tsohon garin Keivroto, domin na san wata rana zaki zo gareni. Amjada basu suka nime ki ba, ni na saka kuka nime. Saboda ta haka kawai zan mallake ki, ko da na bukaci muyi cantract marriage, idan nazo miki da kafa, ba zaki aure ni ba. Amma idan nazo miki as mara lafiya tausayin mutane a jininki yaƙe.

Zainab kece mace na farko da koda baki sona. Baki yi kokarin cutar da ni ko lafiyata ba, ke dai kaiwa na addabi rayuwarki ne, shi yasa kika yi ta min rashin hankali, da cin fuska haka bai tab’a damuna ba, amma nasan wata rana zaki bukaci nazo kina son na mai da ki, dakinki. Zainab ban san yadda zan gaya miki ba. Amma kin bani abin da ban isa na wulakantaki va, sai dai maganar komme kiyi hakuri. Kiyi hakuri Allah ya baƙi hakuri.”
Wani irin kara tasata tare da yankar jiki ta fadi, sumammiya.
—– Bayan awa hudu, farkawa tayi ya ganta a dakinta, Zulfah tana bawa Maidah abinci, dake yaran suna da hakuri da kuma kuzari basu jiran na shanu uwarsu, shima wani lokaci mita take tana cewa ita kan Nononta zai zube, don Allah su bar mata na kwalliya.
A hankali ta zuba musu idanu, kafin ta dafe goshinta. “Kin tashi?” “Malik ya kira ya tambaye ni ya jikin naki. Nace mishi da sauki! Shi ne ya ce na baki hakur.” Bata bari Zulfah ta karasa ba, tacce mata. “Ya isa haka.” Sannan ta mike tare da nufar ban daki, wanka da Alola tayi, sannan ta fito dakin tayi sallah, tana zaune Aunty Yaganah ta kawo mata wani katon kwanon sha, ta ce mata. “Maza ki shanye sannan ki hada da farfesun nan plat din!”
Dake ta saka damuwa a ranta, ko gyaran taki sake jiki a mata, tana idar da sallah, ta ci abincinta tasha ruwan da farfsun tana kuka, wanda ta jima bata yi ba, ganin wayarta a bakin gadon ta dauka, sannan ta kira shi. Bai daukar ba ya kashe ya kirata.
“Sannu ya jikin naki!” “Mutuwa zan yi idan baka zo ba, kazi nace ko na rataye kaina.”
“Kin ga matsalarki ko? Ba zan zo kin jima baki rataye kanki ba”
“Nadrah zaka aura ka manta da UWAR Yaranka.”
“Bani da lokacinki, aure ne nace bana yi.” Kuka da masifa, basu gyara kome ba, karshe ya kashe wayar. Ta daina samun shi. Tunda ta zauna a daki tana jin ana ta hira da hidima amma bata leka waje ba.

Haka zaman dakin ya aureta, washi gari ta tashi da mugun ciwon kai, a haka tayi wanka. Ta shirya sannan ta fito tayi mugun rama, kamar ba ita ba. Tana fitowa bakin Demark suka iso. Wahida da Wahiba, Sayyada Quddisiya da Jalilah, Adnan da iyalin shi. Shatima da Hafcy, haka akayi ya ta shige da ficce, bayan saukowa daga sallah juma’a aka daura auren Zulfah da Yasir Aswad Al Yemini, dake ba iya auren Zulfah ba akwai wani daurin auren aka yi har uku. Lokacin da labari ya zo cikin gidan, ba karamin farinciki aka yi ba, bayan daurin auren. Aka shiga shirin kai Amaren gidansu, ita Zulfah za a wuce da ita Yemen ne, yayinda Zeeno aka wuce da ita Borno. Yaranta sna wurin yan uwansu, shi da ta fahimta Yaran sun yaye kansu, domin baki daya sun ki nono, ga zazzabin kumburin da nonon suka yi, haka ta shiga mota aka wuce da ita Maiduguri, su sayadda suna biye da ita

Sai la’asar lis suka isa, sannan aka shiga wani gagarumin walima da ba a tab’a yi ba, sosai.aka yiwa walimar tanadi ba musamman, ba a gama walimar ba sai dare, sannan aka tafi aka yi sallah. Tana daki Wahiba ta shigo cikin girmamawa ta ce .. “Mommy kizo Aunty Jalilah tana son ganinki;”
“Tow!” Ta faɗa kamar zata yi kuka, a hankali ta mike, tana shiga dakin ta kalle ta, sannan ta ce mata. “Kwabe ki shiga wanka mijinki yana jiranki yau zaku wuce!”
“Ummi Yarana fa?”
“Sun yaye kansu, basu da matsalar suna da sabo da mutane. Cire maza ki shiga wanka.”
Haka ta wuce ban dakin tayi wanka, sannan ta fito ta tsuguna a gaba wani runshi da towel, shafe mata jiki Jalilah tayi da wasu kayan gyaran jiki, sannan ta jibga mata bargo, sai da ta bushe ta d’aga. Ta murje mata jikinta, kafin ta kawo wani oil ta goge jikin dashi, sannan ta kuma hada mata ruwan wankan. Tana fitowa, ta kuma saka mata wasu mayukan turare, ta shiga tayi wanka. Sai gashi tana fitowa ta ce mata. “Yanzu an gama, mijinki yana son kamshi, wannan shi ne damar da zaki yi amfani da shi. Domin kama zuciyarshi. Sai biyayya shi ba Malik bane, da zai na biye miki. Kike sake ya gano kina da taurin kai zai sake ki, sai a fara kirga miki aure.”
Gyada kai tayi, tana mata nasiha har da mata misali da kanta, har ta shiryata tsaf, sannan ta fito da ita, ta nufi cikin gida wurin Hajja Yayye ta mata addu’a, ta kaita wurin Alhaji Kazeem ya mata nasiha, Alhaji Mustapha ma haka, duk sai taji meye ribar taurin kai? Yau da ace Malik ne da babu abin da zai faru, haka hawaye yayi ta zuba mata, har ta iso wurin motar, ta shiga tana kuka. Haka suka tafi da ita bata san wani unguwa ba ce, amma tabbas. Sun yi tafi me dan nisa.

Haka aka kaita wani gida, ita ɗaya ta shiga cikin gidan babu kowa, dakin da ta gani a bude ta tabbatar nata ta shiga, sannan ta rufe kofar ta kwanta, har dare ya raba babu labarin miji, sai da bayan tayi barci. Aka shiga dakin aka kashe wutar dakin. Sannan aka ja mata kofar aka fita.

Washi gari bayan sallah asuba, aka bga mata kofar, ta shirya karfe tara zasu tafi Kano. Kafin karfe tara ta gama shirinta tsaf, sannan aka zo aka ɗauki kayan aka fita da shi. Koda ya shiga cikin motar tayi notice Imperial majesty da yake tashi, amma baki daya kwakwalwarta bai bata lissafi ba. Don haka ta cigaba da kunshe kanta tana kuka, har suka isa airport. Aka gama kome, ta shiga jirgin . Suka wuce kano,. Tunda suka iso jikinta yayi sanyi.
…….Tana saukowa wasu matasa biyu, da mace babba suka suka amshi jakarta, suka nuna mata mota, babu musu ta bisu. A hankali suke tafiya matar tana jan ta da hira. Har suka isa unguwar, rimin kebe. Babban gida me tarihin malamta da kasuwanci. Nan aka kaita, amma an zamantar da gidan. Nan ta samu anata harkan biki da jama’a, wani irin gud’a ake ana watsa mata kudi, ko ba a gaya mata ba Familyn mijinta suna da rufin asirinsu, yadda kake rawan jiki akanta ya kara mata sanyin jiki. “Ina Yaranmu, kai ba dai ita ɗaya kuma dauko Babu Yaran ba?”
“Suna tare da Hajja ai, zasu zo wata sati. Shi Abdul ai zai wuce da ita yau ne.”
*Waye Abdul? Lallai ma Abdul fa, wannan wacce irin ƙaddara ce* abin da zuciyarta yake raya mata kenan.
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button