Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 8

Sponsored Links

Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

008
___________________
_Bite & links republic_

Ya Sheikh kallon Ambassador Rashid yayi da suke zaune a gaban ƙatoton teburin cin abincin da aka shafe masu shi taf da su chicken wings da mahaukatan drinks masu shegun tsada ,an decorating table din sa fulawoyi masu daukan hankali sai sheƙi yake da walwali.

“Rashid kai abokina ne tun na yaranta ,har kawo yau muna tare ,amma haƙƙi na ne in maka nasiha , Almubazzarancin nan yayi yawa…Ta yaya zakayi mana ordern abun nan da bazamu iya cinye su ba mu biyu ? Sannan da nauyayen kudade kamar wannan? Kudi kwata miliyon ,akan me? Jarin wani ne fa”

“Ban gane ba Miqdad? Nifa ba a ƙasar nan nike rayuwa ba ,na saba rayuwa tsakanin tsibirin hong Kong da su Germany ,we spent alot wa ‘yan mata ma ba cikinmu ba ,a America Gidan yin tausa ,in mun dawo daga aiki muna biyan kudi Naira dubu dari biyar to meye wannan? Aini arha yayi mun ,Alhaji meye amfanin samunka in baza kaci ba ,in fa ka mutu Salima kake tara mawa don har yanzu ka kasa bamu baby…”

Ya sheikh harzuka yayi ,ya fara keta kayan abincin uku yana jan kashi daya gabanshi sauran ya bar masa a wajen

“Ni zan biya kudin wannan sauran ka biya ,tunda asara dai ka ja mun…Ku kun saba da asararar da kudinku ma en mata to Ni Ko matata na koya mata tattali ,komai sai an ƙididdige ”

Zaro ido Ambassador Rashid yayi “Ahhhh (,kawai kuma sai ya fashe da dariya) bros kanaji ka barshi zan biya duka ,amma Plz naji point of error a maganar ka , fada mun gaskiya baka ƙuntata ma Saleemart?
Naji kana cewa ka koya mata tattali ,anya baka lalata fine cutie pie ba kuwa? Kasan dai yanda mu abokanka muka dinga santin Saleemart ,bro bari in Fada maka gaskiya da ace na kyalla ido akan salimart Kafin auren ku ,wlh sai na ƙwace maka ita”

Wani malolon kishi ne ya taso ma Sheikh abinda bai taɓa ji akan Salima ba tun bayan auren su sai yau ,nan take idonsa suka kada zuwa jaaaa.

“To Rashid ko zan saketa ne ko aureta kawai?”

“Hehehhee ,Meye yayi zafi miqdad,? Gsky nike fada maka,ynz ga tambaya yaushe rabon da ka fita da salimart outing irin yanda zakaga maza na fita da kyawawan matansu a gaban mota matsayin ƙawar su?”

“To ko shekaranjiya mun fita”

“Zuwa ina?”

“Munje kasuwa mana ,mun siyo kayan cefanen gida”

“Hmm just imagine,bafa cewa chilling kuka fita ba,irin kace babes Shirya muje musha ice cream din na ,come on ,kana fa da wayewan nan kudi kuma akwaisu ,kaji dalilin da yasa nace in baka so ka sallama abarmu mu shigo filin mu ririta Rose🌹”

Sheikh yanda kasan ƙaramin yaro haka ya zama ,abunka da bai taɓa samun wanda ya nuna masa zalama ido biyu ba ,kuma yasan halin Rashid ba karamin ɗan duniya bane ba ,ya kwallafa rai akan mace ko ba aure sai ya nemeta .
Jikinsa na bari ya daga waya ya fara kiran Salimart .

Dammm! Ƙirjin Salima ya buga ganin kiran ya Sheikh daidai ta rufo ƙofar falon ta dawo ,gode ma Allah ta shigayi a ranta da ta sallami Dr kafin nan.

“Assalamu Alaika ya zaujiy”(Mijina)

“Waalaikis Salam ya ustaziya ,kina jina”

“Eh ya sheikh”

“Yau Inason kici ado nan da sa’o’i biyu ina dawowa zamu fita shaƙatawa”

Ras gaban Sayyada ya ɓaci ,out of joy ta daka tsalle tace da gaske kake Habibiy?”

“Kwarai kuwa ustaziya zamuje musha Ice cream muci ɗan pizza ko ya kikace,ɗan flexing din nan dai kema ki fita gari ayi dake”

“Umuuuuh😘 Ina sonka mijina ” ta manna ma wayar kiss ta kashe da sauri ta yi cilli da wayar akan kujera ta haura sama da gudu zuwa sashen ta.

Ya Sheikh waigawa yayi ya kalli Rashid cikin Murmushi
“Mata wato sudai mata’ul hayat ne(Ƙyale_ƙyalen rayuwa) sudai a kashe kudi a ji daɗi,yanzu zo kaga farinciki da murna”

Rashid lumshe ido yayi yana kora drinks din hannunsa yana sanyaya maƙoshi
“I can perceive bros”

***
“Salima
Salimaaaaa
Wai kina Ina ne?”

Ya shigo gidan hannunsa rike da Car key .

A ruɗe tace “Na’am ya Sheikh Ahlan wa sahlan”(welcome)

Sannan ta fito daga ɗakin tana biyo stairs din da takalminta mai tsini yana ƙara cakas! Cakas! Cakas!

Ya Sheikh Binta da kallo yayi ,kawai sai yayi zumbur ya mike

Ta saka wani dandatsatsen less an mata ɗinkin bubu ya fita sosai ya zauna ɗas a jikinta ta murza daurin turban gingiringin ta sagalo mayafi a kafada hannunta daure da wrist watch da zobentana gwal daya hannun na azurfa sai ƙamshi take zubawa.

“Salima meye hakan kenan?” cak taja ta tsaya ba tare da ta gangaro ba ,sai bin jikinta da ya nuna da yatsa take da kallo,tana neman abinda yayi aibu a jikinta

“Salima wannan ba shine leshin da Anty uwani ta kawo maki tsaraba daga cotonou ba?”

“Eh shine mana ya sheikh” tafa hannu ya shigayi yana salati

“Hazbinallahu waniimal wakil ,yanzu Ke Salima ɗingurugum leshin nan kika bada aka tsiyata da wannan ɗinkin? Ji leɓatu kotaina suna reto a iska ,meye amfanin dinkin nan kenan? Kinsan tsadan leshin nan kuwa? Da aka tsiyata leshin da gown kwara ɗaya jal!!!”

Marairaice murya tayi a shagwaɓe tace
“Ni Ina son style din ne”

Dafe goshi yayi

“Ohwuuuuu,Salima meyasa bazaki zama irina ba, Leshin da za ayi kaya uku dashi anyi daya…..ya salam
Ya kamatane kisa tela ya maki dinkin yadi hudu doguwar riga,sai kuma ki siya wani yadin ko satin ne dai ayi maki combination dinki a maki ko riga da siket ,ba sun zama dinki biyu ba kenan?”

Langaɓe kai tayi ta ɗaura hannu a ƙarfen benen ta masa shiru

“Yanzu dai nawa aka maki ɗinkin nan?”

“kyauta kawata tayi mun”

“Ehennn kinji maganar nan,ta cuce ki! Ni dama nasan ɗan jikinki bazakici 6yards ba ,ta maki wayo kamar anci ƙyalle a ɗinkin ta kwashe sauran yadin….kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya nuna gefen kansa kamar wani super professor

Caɓe fuska tayi duk ya sattar mata da gwuiwa

“Shikenan bari inje in sauya kayan ”

“Ke😳Tare nike da Ambassador ,sai kuma ki sake ɓata wani lokacin,kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya sake nuna mata gefen kansa 😄

“To shknn muje ,za’a kiyaye gaba”

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button